Thursday 4 May 2017

AKAN SO 6


*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

      
       06

Fu.ad arabi shine yaro na hudu cikin yaya bakwai da Alh.salman arabi da haj.aisha suka mallaka.

Alh. Salman da dan asalin garin kano ne kauyen bichi. Sai haj.aisha ita barumiya ce yar asalin garin katsina.

Anas shine dansu na farko yana aiki da NNPC da matarshi da yaranshi biyu.

Fatima da nurse ce itama da aurenta da yara guda biyu.

Haneef da yake shekararshi ta karshe a makaranta.

Fu.ad, pha.iza da tagama secondary school dinta. Hassana da hussain yan biyunsu da suke aji hudu kuma sune karshen haihuwa.

Alh. Salman basuda yawa gidansu duka su ukune shine babba sai yan biyunsu duk maza.

Babansu shahararren dan kasuwane kamun Allah yai masa Rasuwa.

Shi kadai ya gado babansu. Wato harkar kasuwanci. Kuma Allah yai masa albarka. Dan yana da gidaje da filayen da shi kanshi inba takardubaka dauko ba bazai ce ga yawansu ba.

Dai-dai gwargwado daga alh har haj sun iya bakin kokarinsu wajen ganin sun ba yaransu tarbiyya da ilimi na bokon da addini.

Fu.ad ya fita daban da sauran yan gidansu. Tun tasowarshi bashida aiki sai buga wasan kwallon kafa.

Yasha kin zuwa makaranta akan wasan ball. Tun suna duka da fada har suka gaji suka soma bashi goyon baya.

Tun yana aji hudu secondary ya soma jagorantar garin kano fita kwallo garuruwa.

Nasarorinshi sun soma daga shekaru kasa da sha takwasa.

Sanda ya shiga aji shidda secondary lokacin ya samu daukaka zuwa kasar Europe.

Dole su Alh.salman suka kyale fu.ad ya tafi. Dakyar ya dawo ya zana jarabawar waec kadai.

Can ya nemi gurbin karatu. Classes dinshi ma online yake yinsu saboda rashin lokaci.

Yakan dawo gida daya samu lokaci. Ya kasance da girman kai da tsanar talakawa wanda haj.aisha da alh.salman ke dangantawa da kudin da yake dasu a shekaru ashirin da biyu.

Don su duk arziqinsu mutanene masu saukin kai da girmama dan adam.

Labarin zai fara ranar da fu.ad ya cika shekaru Ashirin da biyu a duniya.

****

*22/12/2005*

"Kasan na kusa tafiya wallahi"

Cewar lukman da alamun kosawa a muryarshi.

Dariya fu.ad yai da ko gezau maganar lukman din bata shige shi ba. A nutse yake daura takalmin shi.

Wani tsaki lukman yaja.

"Wanne irin iskanci ne wannan? Ka tara mutane wajen minti talatin ka tsaya yanga. Banza kawai"

Bai daice komai ba. Banda lukman din babu wanda ya isa ya tsaya saman kanshi yana mishi wannan maganganun.

Lukman abokinshi ne tun suna yara dan makotane. Abokantakarsu ta kara karfafa zumunci tsakanin iyayensu.

Ko yanzun da fu.ad ba cika zama yai ba. Bashida wani abokin daya wuce lukman. Bama mai jure zaman kwana biyu da halayyarshi.

Dagowa yai ya sauke idanuwanshi da suke ruwan kasa masu wani irin haske kan lukman.

"If you will stop nagging for a minute zakaga nagama shiryawa"

Harara lukman ya watsa mishi. Ya bude kofar ya fita fu.ad yabi bayanshi.

Har sunkai kofa ya tuna yabar wayoyinshi. Da gudu ya juya dan ya dauko dai dai tahowar atika mai aikinsu da sam bata kula da fu.ad din ba.

Karo sukai har saida ta fadi. Jikinta na rawa ta mike tana bashi hakuri.

Wani irin mari ya dauke ta dashi.

"Daqiqiyar ina ce ke?"

Lukman ya karaso da sauri ya ture shi.

"Atika jeki please"

Idanuwan yarinyar cike da hawaye ta wuce da hanzari. Wanu kallo lukman yai masa.

"Tir da halinka wallahi. Kaifa ka tureta still ta baka ha....... "

Katse shi fu.ad yai da fadin.

"Karka sake batamun mood ranar birthday dina. Ka rike wa.azinka banaso. Muje kawai na fasa daukan wayan"

Girgiza kai kawai lukman yai suka fita. Ganin Benz din da suka tunkara yasa lukman yima fu.ad kallon baka da hankali.

Dafe kirji yai.

"Na shiga uku ni lukman. Dan ubanka da wannan motar zakai stunt?  Rashin sanin darajar kudi ko?"

Fu.ad ya kwashe da dariya.

"chill mana. Birthday ina ne fa. Da ita dai zamu fita. Hamza nacan da motar da zan amfani da ita. Banaso momma tai fadane"

Lukman ya bude baki yakai sau uku yana rufewa. Dan ya tabbatar motar dazai ragargaza tafi miliyan biyar.

Mota ya bude ya shiga da fatan shiriya wa fu.ad a ranshi.

*

Suna karasawa wajen fu.ad ya fito aka rudewa da sowa da ihu.

"Moh!  Moh!! Moh namu!!!"

Kaman yanda suke kiranshi. Wani murmushi ya kwace masa. Sabon girman kai na kara ratsa shi.

Ko minti goma basuyi ba. Lukman na gefe yana kallon yanda fu.ad din keta gaisawa da jama.a cikin yangarshi.

Wayarshi ta dau ihu. Ya fito da ita ya matsa nesa saboda hayaniya dan yaga pha.iza ce.

Dauka yai da sallamarshi.

"Yaya lukman in kuna tare da Yaya fu.ad kuzo yanzun Hajiya babba ce ta rasu yanzun Abba yayo waya"

Salati lukman yahau yi. Jikinshi yai sanyi sosai. Ya kasa ma amsa pha.iza harta kashe wayarta.

Hajiya babba kakarsu fu.ad ce sukanje bichi gaishe da ita da yan gidansu fu.ad.

Tsohuwar akwai kirki da karamci. Lokaci yayi. Yakai mintina biyar a wajen yana tuno haj.babba da kirkinta.

Jiki ba kwari ya karasa wajen da fu.ad yake da suke shirin fara wasan su da mota yace mishi yazo.

"Koma meye ya jira ni in gama abinda zanyi"

Fu.ad din ya amsa rabin hankalinshi kan lukman.

"Haj babba ce fa Allah yai mata rasuwa shine momma tace muje yanzun"

Fito da idanuwa waje fu.ad yai hadi da fadin.

"Holy crap. Dammit. Bad timing hajiya. Why yanzun?"

Lukman kaman ya kwada mishi mari. Halayyar fu.ad saikace kara lalacewa take ma duk rana.

Wato bama mutuwar bace ta shige shi. Yana kallo ya wuce yai magana da hamza sannan ya dawo.

Suna mota yana fadin.

"Tsohuwar nan tamun tsiya wallahi. Ran birthday dina"

Lukman da yake ta ma hajiya babba addu.a ya juya ya kalli fu.ad kamun ya maida hankalinshi kan tuqin da yake hadi da fadin.

"Shekaru nawa amman kana surprising dina wasu lokuttan wallahi. Kakarka ce fa. Ita ta haifi abba.

Haba fu.ad mutuwa tai ita. Kai tunanin banzan party dinka kake?  Addu.a ma baka san kayi ta ba?  Kaima zaka mutu"

Tabe baki yai alamar bai shige shi ba yai rolling idanuwanshi yace.

"Whatever. Allah ya jikanta. Bakada aiki sai wa.azi saikace dan gidan limamai"

Lukman bai kara kulashi ba har suka kai gida. Dan yasan zasu iya yin rikici inya biye masa.

****

Da lukman din suka tafi bichin. Waya kadai yaiwa mamanshi ya fada mata rasuwar.

Itama tace zasu biyo su a baya. Fu.ad ne ke tuqin wannan karin.

Lukman na gefe. Sai yayar fu.ad din anty fatima da wata cousin dinsu anti maryam.

Kukan da suke ya soma kular da fu.ad. Dan shi baiga abin kuka ba. Shekarar hajiya nawa a duniya.  Aita sha miya a ganinsa.

Basu tsagaita da yan koke kokensu ba saida suka dauki hanya sosai.

Banda lukman dayaima fu.ad
magana daya rage gudu su anti fatima ko kula ma basuyi ba. Bai kuma rage gudun ba.

Har suka shiga garin bichi duk lungun da suke bi fu.ad bai rage gudu ba.

Ba kuma ya horn inzai shiga kwana. Ido lukman ya saka masa. Suna karya wata kwana wani babban mutum magidanci da itace akanshi.

Rashin horn din da fu.ad baiyi ba yasa bai kula da shigowarsu ba sai a kurarrwn lokaci.

Da hanzari yai kokarin kaucewa. Itacen kanshi na watsewa kan motar su fu.ad din da ko ina.

Wani mugun birki fu.ad ya taka daya razana su anti fati. Motar ya bude a fusace ya takasa wajen mutumin daya fadin kasa.

Ya tashi yana kakkabe jikinshi. Dai dai fitowar su anti fati daga mota ji kake wani.

Tas!

Fu.ad ya dauke mutumin da a haife ya haifi irin fu.ad din uku da mari.

"Baka ganin motane?  Wanne irin jahilci ne wannan?"

Daga anti fatima har su lukman suka karaso wajen da salati.

Marin fu.ad anty fatima tai tana salati da girgiza kai da danyen aikin da fu.ad yayi.

Mutumin ta kalla da yake rike da kunci yana kallon fu.ad da mamaki a fuskarshi.

Hannu fu.ad ya daga lukman ya rike shi a tsawace yace.

"Haba mana fu.ad ya isa haka. Wanne irin masifa ne wannan"

"lukman daka kyale shi ya rama marin. Dan wallahi ba wata rashin kunya dazai nunamun kuma"

Kallonsu fu.ad yai a kyamace ya wuce ya koma mota yana huci.

Har kasa anty fatima ta tsugunna tana ba mutumin hakuri. Su duka suka hada baki har da lukman.

Mutumin ya jinjina kai.

"Bakomai yata. Kuje kawai Allah ya shirya"

Mota ta koma ta dauko kudi a jakarta ta dawo inda mutumin ke tattara itacen shi.

"Baba ga wannan"

Ya dago ya kalleta. Ya girgiza kai yace.

"Nagode 'ya ta amman bazan karba ba"

Wasu hawayen takaici suka zubo ma anty fatima. Ta goge su ta tsugunna murya na rawa tace.

"Badan abinda kanina yai maka ba baba. Kyautatawa ce dan girman Allah ka karba"

Ya jima yana kallonta kamun yasa hannu ya karba yace.

"Nagode"

Ta juya ta shiga mota.

No comments:

Post a Comment