Thursday 4 May 2017

AKAN SO 37

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

           37

*PLEASE inajin dukkan comments dinku nakuma gode. Abu daya zance sa readers na AKAN SO. Gaba dayanshi zai zama da happy ending. Sai dai ina tafiya da reality as much as i can. So please amin hakuri in gama cikin kwanciyar hankali. ILYA*

*Naga addu.o.inku daga kan masu mun text da masu kirana a waya. Allah ya saka da alkhairi. Alhamdulillah na samu sauqi sosai. Hopefully zaku dinga jina lokaci lokaci. #AnaTare*

Kallon fu.ad take sai kai kawo yake da Nana akan kafadar shi yana ta bubbuga bayanta a hankali. Tunda suka dawo daga ganin nawaf yake lallashinta har tai bacci.

"Ka kwantar da......."

"Shhhhhhh"

Fu.ad ya katse ta yana daquna fuska. Shirun tayi ta zuba masa idanuwa kawai. Da alama baya ji da ganin kowa banda Nana a yanzun.

A hankali take jin wani abu a zuciyarta yana dokawa a hankali. 'Ina sonki sofi' kalamanshi suka fado mata.

Kowa ya turo kofar ya taimaka mata ba kadan ba. Murmushi ta dora kan fuskarta ganin Ansar ne. Shima murmushin ya mayar mata.

Fu.ad dake tsaye yana kallon su yadan runtsa idanuwanshi yana jin kaman ya shaqare Ansar din nan. Ya ringimo katon kanshi yazo.

Karasawa yai ya mikama fu.ad hannu. Ya karba yana kauda kai gefe. Murmushi ansar yayi. Fu.ad din nan na bashi dariya ba kadan ba.

"Ya jikin nana?"

"Da sauqi. Mungode"

Ya amsa dakyar. Karasawa yai yaja kujera ya zauna suna gaisawa da safiyya. Wani irin abu yaji ya tsaya mishi a wuya.

"Zan wuce safiyya. Idan Nana ta tashi ki kirani a waya mu gaisa"

Kasa kasa fu.ad yace.

"Kaman kasan bama bukatarka"

Harara safiyya ta watsa mishi. Ya dan bude mata idanuwa dake fassara 'Gaskiya na fada'.  Murmushi Ansar yayi ya mike ya ajiye ledar dake hannunshi.

Mikewa safiyya tayi.

"Ina zaki je?"

Fu.ad ya bukata yana tsare ta da idanuwa. Wucewa tai tabi bayan ansar. Safiyya ta raina shi yanzun shine tunanin da yake yi.

Karasawa yai a hankali ya kwantar da Nana yana gyara mata kwanciya yaji an kwankwasa kofar.

"Yes....."

Ya furta batare daya juya ba. Sallama akai aka turo kofar. Duk dadewar dayai baiji muryarba bai hana shi ganeta ba.

Da sauri ya juya dan ya tabbatar da abinda kunnuwanshi suka ji. Aikam hamza ne. Shima tsaye yai rike da kofar yana kallon fu.ad din.

A hankali ya saki handle din kofar da yake rike dashi ya na shigowa cikin dakin sosai.

"Hamza....."

Fu.ad ya fadi cikin sigar gaisuwa. Da dan guntun murmushi hamza ya amsa da fadin.

"Moh...."

Sosai ya karaso cikin dakin. Sai lokacin yaga da mutum a bayan hamza.  Daga kasan kafafuwanta ua fara yawatawa da idanuwanshi.

A hankali har yakai kan fuskarta inda ya tsayar dasu cak. Tsaye take tana wasa da hannayenta. Idanuwanta na yawo ko ina na dakin banda kan fu.ad.

Wani abu yaji zuciyarshi tayi. Ga bakinshi ya wani bushe. Dakyar ya hadiyi miyau ya furta.

"Hussaina. Little sis"

Hannuwanshi yasa ya goge fuskarshi da yake jin kaman zufa a jiki. Mikewa yai daga kan gadon ya karasa inda take tsaye.

"Hussaina........"

Bata kalle shi ba. Asalima rabashi tai ta wuce inda hamza yake tsaye ta tsaya kusa dashi sosai. Hannuwanta ta saki.

Takai daya ta kama na hamza ta dumtse gam. Idanuwanta na kasa. Kallonta sosai fu.ad yayi. Inda take tsaye. Sannan ya maida hankalinshi kan hannunta.

Hannun hussaina cikin na hamza a dumtse. Lokaci daya ya fahimci me hakan yake nufi. Sai sannan ya lura da yanayin hussaina.

Cikine a jikinta harya turo. Hussaina tayi aure. Lumshe idanuwanshi yai. Yakai hannu yana murza goshin shi da yake jin wani abu na yawatawa.

Safiyya ce ta turo dakin da sallama ta shigo. Tagansu tsaye cirko cirko. Kallon hussaina take. Sai lokacin ta gane ta.

"Hussaina?"

Dagowa tai ta sauke idanuwanta kan safiyya.

"Anty na"

Da sauri fu.ad ya kalleta. Baisan yanda yai kewar muryarta ba sai yanzun. Baisan kewarta dayai tayi girma haka ba sai yanzun daya ganta.

Wani abu yake ji a dukkan jikinshi. Gaisawa safiyya tai da hamza sannan suka gaisa da hussaina. Taja musu kujeru suka zauna.

"Ya jikinta?"

Hussaina ta bukata. Safiyya ta amsa ta da.

"Da sauqi. Bacci take"

Kai hussaina tadan daga mata hadi da dorawa da.

"Daman munzo dubata ne. Zamu dawo gobe in shaa Allah"

"Allah ya kaimu goben. Mungode sosai"

Da sauri hussaina ta katse ta da fadin.

"Saboda ita nazo. Badan kowa ba"

Kallonta safiyya tayi ta rasa me zatace. Mikewa tai hamza ma haka. Gani yai sun nufi kofa. Da sauri ya karasa inda suke.

"Hussaina.....!"

Bude kofar tayi ta fice. Hamza ma haka. Da sauri fu.ad yabi bayansu. Gudu hussaina take tana nufar hanyar da zata fiddata daga asibitin.

Tsayawa hamza yai yana tare fu.ad. Hannunshi dake kan kafadarshi fu.ad yabi da kallo. Yana jin wani irin daci a zuciyarshi.

"Me hakan ke nufi hamza?"

Da wani yanayi a muryarshi hamza yace.

"Please ka kyaleta kawai. Ba lafiya gareta ba sosai....."

Ture hannun hamza fu.ad yai yana mishi wani irin kallo.

"Ka sake bani dalilin binta kenan"

Dafe kai hamza yai kamun yace.

"Look. Ba wai ina so in hanaka bane. Kanwarka ce. Amman inada hurumin dazan damu da lafiyarta"

Kaman daga sama fu.ad yace.

"Kana sonta?"

Kallon wannan wacce irin tambaya ce hamza yaima fu.ad.

"Kawai ka amsa ni. Kana sonta?"

Wani dan murmushi hamza yai.

"Baka ga shaida a jikinta ba"

Duka fu.ad yakai mishi ya kauce yana dariya.

"That is disgusting hamza. Kanwata ce"

Dafa shi hamza yadanyi.

"Karka damu. Ina son hussaina. Ina sonta sosai wallahi. Please zata sauko. Right now space take bukata kabata"

Sauke murya fu.ad yai sosai.

"Badamuwa. Just...... Just take care of her"

Kai ya daga mishi. Yana kallo ya juya yakoma. Hanya ya nufa yana ficewa daga asibitin. Cikin mota ya samu hussaina a zaune ta hada kanta da jikin motar tana wani irin kuka.

Saida ya shiga motar ya kullo sannan ya matsa ya rikota. Hannunshi ta rike cikin nata ta na dora fuskarta akai. Kuka take sosai da sosai.

"Shhhhh baby please. Kukan ya isa...."

Cikin shesshekar kuka tace.

"Duk....duk shekarun da nake son mishi magana.... Yanzun ban kula shi ba..... I.....i miss him sosai...."

Hannunshi ya zame daga nata. Ya tallabi fuskarta. Cikin idanuwa ya kalleta.

"Shima yai kewarki."

Girgiza kai hussaina tayi.

"Daya neme mu. Saboda me bai neme mu ba duk lokacin nan?"

Bashida amsar tambayarta. Don haka yasa hannunshi yana goge mata fuskarta.

"Saikin haifo mana baby rigimamme ko"

Murmushi tayi. Yadan kissing gefen fuskarta.

"Ko kefa. Komai zaiyi dai dai kinjini ko? Bana son kukan nan"

Gyara zamanta tayi tana kara goge fuskarta.

"I love you"

"I love you more"

Ya fadi yana kunna motar.....

****

Kwance take jikin mamansu nawaf. Tun jiya bayan ankai nawaf makwancin shi ta nemi hawaye ta rasa.

Sai dai zuciyarta da take ji kaman anbi takanta da mota. Ga wani irin zafi da take ji tana mata. Bawai bata yarda da cewar nawaf ya rasu ba.

Tadai kasa yarda data rasa shi har abada. Ta kasa yarda da cewar ya tafi bata gama fada mishi duk irin son da take mishi ba.

Bata gama fada mishi duk yanda take godiya da kalar taimakon dayai mata ba. Tunda yasanta burin shi yaga ya tsameta daga rayuwar da take ciki.

Amman ita ta kasa janye shi daga tashi. Kirjinta tafasa kawai yake kaman an zuba mishi garwashi.  Maganar mutane sama sama take jinta.

Gaba daya duniyar ta mata wani irin empty. Ji take ba tada kowa daya rage mata a cikinta. Duk da farhan da zuciyarta ke sane da zamanshi bai hanata jin bata da kowa ba.

Tana jin mazaunin nawaf daya bari a zuciyarta can wani gefe da take da yaqinin har tata mutuwar ta same ta babu abinda zai cike shi.

****

"Tun dazun inata maka magana baka ce komai ba?"

Ajiyar zuciya ya sauke.

"Banda abinda zan fada indai kan fu.ad ne saboda na jima da cire shi daga zuciyata ballantana ya dame ni"

Dafe kai momma tayi. Wani lokacin sai taga da gangan ake cewa fu.ad din na da taurin kai.

"Ni dai zanje in sake dubo yar yarinyar nan."

"A dawo lafiya. Allah ya bata lafiya"

A sanyaye ta amsa da.

"Amin thumma amin"

****

Baije ko ina ba sai hotel din daya sauka shima wanka yai ya sako kaya ya dawo. Safiyya taje ta dawo.

Yana zaune kusa da Nana da tunda ta farka bata ce mishi komai ba tayo shiru. Ya rasa me zai fara ce mata. Duk sai yake jin shi ya wani daburce.

"Ya rasu ko?"

Ta tambaya. Da sauri fu.ad ya riko hannunta yana girgiza mata kai.

"Kibar wannan maganar Nana. Mumynki taje ta dawo. Zata taho da abinda zamuci.

Ko kina son wani abin daban?"

Kai ta girgiza mishi tai shiru kawai. Tun jiya yaqi barin zuciyarshi tazo mishi da zancen nawaf saboda ba karamun tsorata shi hakan yake ba.

Da dare baiyi bacci ba sam. Ya rasa me ya hana shi bacci sai yanzun ya tuna result din test din da akai mishine zasu karba yau.

Zuciyarshi yaji wasu abubuwa na tsinkewa a ciki suna barin mazaunin su. Matsawa yai wajen fuskar Nana ya sumbaci goshinta.

Wani kasalallen murmushi ta sakar mishi.

"Mumy ta koya maka ko?"

Murmushin ya mayar mata. Yadan daga kafada alamar baima fahimci me take nufi ba.

"In mumy tana son jin ko jikina da fever bata son tambaya haka take yi fa. Bata san nagane ba"

Dariya fu.ad yayi.

"I love you......"

Da sauri ya ware idanuwanshi akanta. Yana jin yanda zuciyarshi ke ta tsalle tsalle cikin kirjinshi. Baisan wanne abin arziqi ya aikata ba a rayuwarshi daya cancan ci wannan kalaman da Nana ta fada mishi.

Wasu irin akwatina ya bude ya rufe su ciki dan bazai so ya batar dasu ba. Kallon shi nana tayi ta ci gaba da fadin.

"Ina kaunarka kaman yanda nake kaunar mumy tun kamun in sanka"

Sake sumbatar ta yai a goshi yana riko hannunta. Baisan kalaman da zai amfani dasu ba dan ya gaya mata kalar yanda yake jin kaunarta daga randa ya dora idanuwanshi a kanta.

Hannun ya kamo ya dora kan kirjinshi. Wasu emotions ne yake ji ta ko ina suna danne shi. Muryarshi nadan rawa yace.

"Kaunar da nake miki ta girmi abinda kenan ciki"

Dariyar nan dayake jin sautinta yafi na komai daya taba ji cikin kunnuwanshi tayi. Kasa tai da murya tace.

"Ta fi ta mumy?"

Ware idanuwanshi fu.ad yadan sake yi akanta. Itama nata a ware suke cikin nashi kamun su bushe da dariya a tare.

Haka safiyya ta turo kofar ta same su. Tun daga bakin kofar take jin sautin dariyarsu. Suna kallonta suka sake wata sabuwar dariyar.

Da mamaki take kallon su. Girgiza kai kawai tayi ta karasa gefe ta ajiye kayayyakin dake hannunta.

"Nana tashi muje in miki wanka"

Daquna fuska tayi. Tana turo baki.

"Na iya fa"

Kallonta safiyya take.

"Muje in tayaki to"

Daka kallo fuskarta kasan bata so. Kawai dai ta sakko ne daga kan gadon. Saida ta sumbaci fu.ad a kumatu sannan.

Kallon shi tayi sosai.

"Kaje gidansu please. Nima zan mishi addu.a"

Kai fu.ad ya daga mata hadi da fadin.

"I promise"

"Thank you"

Ta fadi. Tana wucewa toilet din.

*

Ita kanta safiyya tunda taga doc jana tazo ta dudduba Nana bata ce musu komai ba ta bita taji maganar result din tace mata sai karfe hudu haka ta dawo ta zauna gabanta na wata irin faduwa.

A haka fu.ad ya fita yai sallar azahar ya karbi key din motarta ya fita ya siyo musu take away da lemuka ya dawo.

Amman daga shi har safiyya sun dan taba ne kawai saboda Nana ta musu magana. Bawai dan suna jin dadin abincin ba.

"Mumy baki kiramun su ba fa har yanzun?"

Sauke numfashi safiyya tayi. Ta dauko wayarta da jakarta. Lalubo dan katin da yusra fari ta bata tayi. Ta duba number dinta a jiki.

Text tai mata sannan ta dago ta kalli nana.

"Na masu magana yanzun"

Daga nan kan gadon inda take tai kissing tafin hannunta ta hura ma safiyya hadi da fadin.

"You are the best mum ever"

Dariya tadanyi. Fu.ad dake gefe ya tabare fuska.

"Princess mumynki kawai kika sani ko?"

Dariya Nana tayi. Ya sa hannu ya dan taba kuncin shi. Babu musu ta matsa kan gadon ta sumbaci kuncin shi. Yace.

"Ko kefa"

Wayarshi dake gefe ta dauka. Bai hanata ba. Ta mika mishi saboda akwai key a jiki. Kallonta yai yadan kalli safiyya sannan ya ware mata idanuwa.

Hannu tasa ta rufe bakinta tana danne dariyar da take ji. Sannan ta saka 'Safiyya' a jikin wayar sai dai ga mamakinta wrong password.

Kallon fu.ad tayi ta daquna fuska alamar baiba. Yadan daga mata kafada yana murmushi dake nuna ta sake guessing dai.

Dan daga idanuwa tayi tana tunani. Can tace.

"Yes......"

A fili. Dariya yai. Safiyya ta kalle su. Su biyun nan bata gane yanda suke magana. Saidai ko taji sunyi dariya.

'Sofi' ta rubuta sannan tai masa 👌 sign da hannu alamar ya bude. Images takai. Hotunan ta ta fara gani duk tana bacci.

Ta dago ta kalle shi. Bai ce mata komai ba ta ci gaba da swiping gaba tana kallon hotunan dake ciki. Yawanci duk shida abokanshi ne da kayan ball.

Gaba daya hotunan babu wanda yai fara.a a cikinsu. Fita tai ta shiga wata folder din daban amman key ne a jiki. Sake kallon fu.ad tai da tambaya a cikin idanuwanta.

Ta juya mishi wayar yaga folder din. Wani numfashi yaja sannan yadan yi gefe da kanshi cewar ta sake saka sunan dazun.

Ware mishi idanuwa tai yasan so take ta fadi kalar son da yake ma sofi. Ya girgiza mata kai yana dakuna fuska.

Dariya ta kamayi ta bude folder din. Hotunan sune shida safiyya a ciki lodi guda. Tasa hannu ta shafi screen din tana kallon yanda suke dariya a tare.

Haka taci gaba da wucewa sa duk hoton da zata gani da qarin karfin alkawarin da take daukarwa kanta na saita zama silar komawarsu koda shine karshen abinda zatayi.

Saida ta kai karshe sannan ta koma ta bude video record ta soma daukar fu.ad dake zaune yana kallonta.

"Me kike?"

Ya tambaya. Dariya ta kamayi. Ta juya wayar saitin safiyya data ce mata.

"Nana ki bari fa"

Sauke wayar tayi tai saving video din. Mikewa fu.ad yayi yana miqa da jikinshi yace ma nana.

"Karfe nawa"

Duba wayar tayi.

"Karfe uku da minti arba.in"

Da sauri ya fita baima san lokaci yaja ba haka.

*

Yana dawowa daga masallaci yana hango motar lukman. Dan haka suna gaisawa suka shiga ciki tare.

Da fara.a Nana tace.

"Uncle lukman...."

Gefen gadon ya zauna ya shafa kanta. Sai da suka gaisa da safiyya sannan ya maida hankalinshi kan Nana da fadin.

"Ya jikinki"

Dan daga mishi kafa tayi dayaga ta masa yanayi sosai da fu.ad. Bata san ana ce mata ya jiki saboda bata son ganin yanda idanuwan mutane ke canzawa in zasu mata tambayar.

"Ina uncle haneef?"

Lukman ya amsa da.

"Nasan zai zo"

Yana rufe baki suna jin turo kofa da sallama. Mikewa lukman yai yana fadin.

"Momma sannu da zuwa"

Su dukansu gaishe da ita sukai. Fu.ad ya janyo mata kujera ta zauna suna hira da Nana.

Doc jana ta shigo suka gaggaisa ta sake duba Nana tace ma safiyya.

"Zaku iya tafiya gida ma. Inda wata matsala dai ku dawo"

"In shaa Allah. Mungode sosai"

Yar ledar data shigo da ita ta mika ma nana da ta karba tai hugging dinta hadi da fadin.

"Thank you anty jana"

Da murmushi ta amsa da.

"Don't mention sweetheart."

Hankalinta ta mayar kan safiyya tace.

"Zan ganku yanzun kamun ku tafi"

Wani irin dokawa fu.ad yaji zuciyarshi tayi kaman zata fito daga kirjinshi. Binta safiyya tayi. Fu.ad ya kalli lukman sannan ya fita shima.

Juyowa safiyya tai idanuwanta cike taf da hawaye ta hade hannayenta duka biyun cikin sigar roqo. Muryarta a sauke tace.

"Ina bukatar yin wannan nikadai. Please......"

Saida yaja numfashi ya fitar dashi sannan yace.

"Ki daina irin wannan maganar sofi. Bana so wallahi"

Kai ta daga mishi.

"Na daina. Ba zaka gane ba. Ina son fara ganin result din ni kadai....."

Juyawa tai tana goge hawayen da suka zubo mata. Binta zaiyi yaji an rike mishi hannu.

Juyawa yai lukman ya sake shi yana fadin.

"Ka kyaleta. A karo na farko a rayuwarka kaji rokon da akai maka mana"

Jingina fu.ad yai da bangon wajen baice komai ba. Yaga yarshi ce yana da right din dazaiga result din baisan me yasa safiyya zata dage ita kadai zata gani ba.

*

Sanda ta shiga office din doc jana na zaune da takardun a babban envelop. Waje ta samu ta zauna jikinta babu karfi ko kadan.

Ita kanta bata bude result din ba tunda ta karbo shi daga lab. Dan har ranta tana kaunar Nana. A shekarun nan biyu yarinyar ta wani shiga ranta.

Gabanta na faduwa ta bude envelop din ta zaro takardun da na Nana dana fu.ad din. Kallonta safiyya take idanuwanta cike da buri.

Runtsa idanuwa doc jana tayi. Lokaci daya wata irin zufa ta karyo mata. Kallon safiyya tayi.

Da kallo dayan datai mata komai ya tarwatse. Da wannan kallon taji dalilin rayuwarta ya kare. Da wannan kallon datai mata taji ta karasa rasa komai na duniya.

Cikin wata irin murya da bata gane tata bace tace.

"Wata nawa nake da?"

Bude baki doc jana tayi safiyya ta daga mata hannu hadi da sake maimaita tambayarta.

Sauke numfashi doc jana tayi tana jin idanuwanta na cika da hawaye.

"Da yanayin yanda komai ke spreading kasa da wata hudu"

Mikewa safiyya tayi. Tana jin yanda kafafuwanta ke takawa sai dai komai take ji kaman ba nata bane ba. A haka ta fice daga office din bata ko kula da cewar bata ja mata kofar ba.

*

Tsaye suke nesa da office din kadan shida lukman yana jin yanda yake fada mishi komai zaiyi dai dai in shaa Allah.

Baice uffan ba. Shi kadai yasan halin da zuciyarshi take ciki. Ganin safiyya ta fito ya sa daga shi har lukman suka karasa inda take.

"Sofi......."

Juyowa tai ta kalle shi kamun ta ci gaba da tafiya. Zuciyarshi yaji ta ci gaba da dokawa. Ita kanta bata san inda zata ba.

Wani waje take son zuwa inda ba kowa. Inda babu wanda ke ciki sai ita da halin da take ji. Da sauri fu.ad ya bita.

Tare hanyar yayi. Yana mata wani kallo cike da bincike. Idanuwanta ta dago ta sauke cikin nashi tana son yaga yanda zuciyarta ke ciwo.

Girgiza mata kai yake yi.

"No sofi. Dan Allah karki fadamun. Please na roqe ki banda sauran zuciyar da zata dauki wani rashin"

Kafafuwanta taji sun kasa daukarta. Durqushewa tai a wajen tasa fuskarta cikin hannunta tana sakin wani irin kuka marar sauti.

Matsawa yake da baya. Ya kasa gane meke shirin faruwa dashi. Babu abinda yake gani cikin idanuwanshi yana gilma mishi banda fuskar Nana.

Lukman ya dafashi a tsorace yace.

"Fu.ad ya akai?"

Ture hannunshi yai yana ci gaba da ja da baya a hankali kamun ya juya da gudu ya nufi hanyar office din doc jana bai damu da yanda lukman ke kwalla mishi kira ba.

Tura kofar taji bana wasa bane. Da sauri ta dago kai ta sauke idanuwanta kan fuskar fu.ad.

"Yes ko No?"

Ji take da da yanda zatayi da tayi. Sai dai babu. Ko da anyi transplant dinma ba wai warkewa zatai ba. Lokaci ne ake sa ran zata kara samu.

Muryarta can kasa tace mishi.

"No"

Lumshe idanuwanshi yai. Yana jin yanda zuciyarshi ke rugujewa kala daban dana lokacin barin shi nigeria.

Juyawa yai hannuwanshi cikin aljihun wandon shi. Yana jin yanda girman kalmar da jana ta fada ke samun waje cikin jikinshi.

A hankali komai ke tafiya kamun yakai inda zai zauna daram. Iskar asibitin ta mishi kadan. Lukman yaga yasha gabanshi.

"Fu.ad..... "

Kallon lukman yai. Kallon shi yake da roqo cike da idanuwanshi kaman hakan zai sa lukman ya taimaka ya karbi kadan daga cikin nauyin da zuciyarshi tai mishi.

"Fu.ad kaimun magana please. Safiyya ma taki cemun komai. Wai menene?"

Yana jin yanda iskar tai mishi kadan. Dan numfashin shi harya soma samun matsala. Yana fitar dashi da sauri sauri yace.

"Lukman my little girl. Yarinyata...... Yarinyata lukman....."

Yanda yake watsa hannaye yana jan numfashi yasa lukman kama shi yaja shi gefe yana jingina shi da bangon wajen.

"Calm down. Me yake faruwa?"

Numfashin shi yaqi kaiwa inda yakamata har yanzun. Yana jin yanda komai yake amsa wa cikin kanshi.

"Mutuwa zatayi lukman......."

Ware idanuwa lukman yayi yana jin yanda tashi zuciyar ke karyewa. Kallon fu.ad yake da ko ina na jikinshi kyarma yake.

Haneef ya hango yana tahowa. A hankali ya karaso inda suke. Kallo daya yai musu yasan ba lafiya ba.

"Lukman?"

Ya tambaya a dan tsorace. Cike da wani irin yanayi lukman yace.

"Nana....."

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un......"

Haneef ya fadi yana kallon fu.ad dan in shi yana jin zuciyarshi na mishi wannan zafin baisan yanda ta fu.ad take ba a yanzun.

Hannu yakai a hankali ya dafa kafadar fu.ad din sai lokacin ya dago. Hawaye ne suka biyo fuskarshi. Abinda rabon da haneef yagani tun suna kanana.

Zame jikin shi fu.ad yayi ya hada kanshi da gwiwa. Kuka yake kaman karamin yaro. Nana mutuwa zatayi. Shine abinda yake ta masa yawo.

Dafa shi lukman zaiyi haneef ya rike shi yana girgiza masa kai. Wannan ba abu bane da kowa zai iya taimaka mishi.

Dole subar shi. Shi da kanshi zai accepting abinda ke faruwa. Fu.ad kam bai taba jin duniya ta mishi kunci ba sai yau.

Yar shi da ko damar saninta bai samu ba. Kuma wannan ba laifin kowa bane saina safiyya. Sofi ta boye mishi ita gashi yanzun mutuwa zatai.

Mikewa yai yasa hannu ya goge fuskar shi yana shaqar iska mai nauyi kamin ya fitar da ita. Daga haneef har lukman kallo suka bishi dashi.

Hanya ya nufa da lukman kadai yasan safiyya ce a wajen. Dan haka yabi bayansh. Hakama haneef. Tana nan zaune inda suka barta tana wani irin kuka.

Karasawa fu.ad yai dab da ita. Ta dago da jajayen idanuwanta da fuskarta data kumbura ta kalle shi. Wani irin abune cikin idanuwanshi.

Muryarshi a dakushe yace.

"Saboda ke bazan san abubuwa da yawa ba akan Nana.

Saboda ke na rasa shekaru goma sha daya na rayuwa tare da ita.

Bake ya kamata kiyi kuka ba sofi. Saboda ko da ace yau babu Nana kina da shekaru goma sha daya a cikin kanki da zaki dinga dubawa kina samun sauqi.

Banida komai!!!

Banida abinda zan duba nata banda watanni!!!

Wallahi bansan yanda akai zuciyata tai kuskuren sonki ba!!!"

"Fu.ad...."

Haneef ya kira shi dan yasan yanayin da yake ji zai iya saka shi fadar abubuwan da zai zo yana nadama daga baya.

Mikewa safiyya tayi taba kallonshi cike da tsanar da take ji tashi da rashin adalcin da rayuwa take mata ta ko wanne fanni.

Batare data kalli haneef ba tace.

"Kabarshi!  Kabarshi ya fadi duk abinda yake so ya fada. Kabarshi ya fadin son ranshi dan baisan kowa ba sai kanshi.

Kana da bakin da zaka doramun laifi fu.ad?"

Ji yake kaman ya makareta. Taya zata iya tsayawa gabanshi tana masa wannan kallon kaman shine da laifi.

"Kai ka tafi. Ban kama ka na turaka waje ba!  Kai ka zabi kabarni. Saboda me zaka ga laifina?"

Sosai yake kallonta.

"Saboda me zaki kasa ganin a kowanne zabi danayi kece a cikinshi?
Kina son yara nikuma bazan iya baki ba. Sai nayi laifi dan na barki ki auri wanda zai iya baki abinda na kasa?"

Girgiza kai safiyya take tana jin wasu hawayen na zubo mata.

Kama shi haneef yai yana fadin.

"Wannan bazai baku mafita ba fu.ad......."

Kwacewa yai yana kallon shi da fadin.

"Ni nai mata laifi inma laifi ne haneef saboda me zata hukunta mu harda Nana? Saboda me zata hanamun rayuwa da yata?"

Ya karasa maganar da wani sanyin murya daya karyama daga haneef har lukman zuciya. Muryarta can kasa safiyya tace.

"Na nemeka. Na nemeka daga lokacin dana gane ina da cikin Nana. Na nemeka fu.ad gaba daya numbers dinka a kashe"

Kallonta yake yana tuna yanda ya kashe wayoyinshi gabaki daya na tsayin watanni. Kamun cikin daga murya da kukq safiyya tace.

"Ya kake so inyi?! Meye banyi *Akan so*nka ba? Saboda me zaka dauka kai kadai ne zaka rasa Nana? Ko ka dauka ka fini sonta?"

Kallon lukman yai.

"Kaji ta ko? Kaji ta ko lukman. Zan dauki yarinyata. Zan kaita ko wacce kasa ta duniya. Zan kashe komai dana mallaka dan ta samu lafiya"

Wata dariya safiyya tayi da bata san daga inda ta fito ba.

"Welcome to reality fu.ad muhammad arabi. Inda tarin dukiya bazai maka amfanin komai ba!

Zunubanmu ne muke girba ta wannan hanyar. Wallahi fushin iyayene muke gani"

Kuka take sosai. Kalamanta sun girgiza shi. In haka rasa da yake me su abbah suka ji da ya tafi? In haka soyayyar yara take wacce iri su momma ke masa dayake dauka a arha?

Tabbas safiyya ta fadi gaskia. Gaskia sofi ta fada. Barin iyayenshi ne ke bibiyarshi. Fushin abbane yake bibiyarshi.

Kallonta yai da wani irin nauyi.

"Zamu gyara komai. Babu wanda zai iya saving Nana. Allah daya dora mata ne kawai zai iya.

Sofi zamu gyara komai. Zamu ba kowa hakuri. Inna da baba. Su abbah. Zamu fara ganin dai dai in suka yafe mana"

Hawayen dake zubo mata tasa mayafinta tana gogewa. Da wani sabon kwarin gwiwa ta kalli fu.ad.

"Komai zai gyaru in suka yafe mana. Munyi kuskure na daukar zamu iya tsara rayuwarmu da kanmu"

Jinjina kai fu.ad yayi. A karo na farko yana ganin laifukanshi a shimfide. Haqiqa babu mai iko sai Allah. Babu wanda ke tsara komai sai Shi......!

*#TeamAs*

No comments:

Post a Comment