Thursday 4 May 2017

AKAN SO 7

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

      
          07

"Fu.ad yaushe ka kara lalacewa haka? Wancan mutumin bai isa ya haifeka ba har zaka iya daga hannu ka mareshi?"

Anty fatima ke fadi rai a bace.

Wani numfashi yaja da alamun relief. Yace

"Thank God bashi ya haifeni ba. And karki sake dagamun hannu ba yaro bane ni"

Wani abu ya tokare mata wuya. Anty maryam tace.

"Fu.ad rashin kunya ko?"

Juyowa yai daga inda yake zaune ya watsa mata wani kallo hadi da fadin.

"Mind your own fucking business"

Fu.ad ke rashin kunyar amman lukman dake zaune shi yake jin kunya.

Gabaki daya ji yake daman motar su pha.iza ya shiga da baiga wannan bacin ran ba.

"Ka wuce muje fu.ad. And do us a favour kayi shiru muji da abu daya"

Lukman ya fadi ya juya ya kalli anty fatima dake sharar hawaye. Anty maryam kuma tayi tsuru tsuru a gefe yace.

"Dan Allah anty kuyi hakuri. Abar maganar nan. Muji da abu daya"

Kai kawai anty fatima ta daga. Fu.ad ya wani fizgi motar duk yana gwara su da jikin motar.

"Maza kashe mu to"

Lukman yace rai bace. Ko kula shi baiyi ba. Kawai tafarfasa yake a ciki.

Kaman shi anty fatima zata daga hannu ta mara akan wani tsohon daqiqin talaka.

Ya tabbata da basu hada jini ba saiya rama marinshi. Kuma sai yasa an kulle masa ita.

Suna karasawa ya samu waje yai parking. Mutane ne cike unguwar kaman zata fashe.

Anata alwala kasancewar yamma tayi sosai. Dan a hanzarta akaita makwancinta.

"Ku nemi wani ride din home"

Fu.ad ya fadi bai jira amsarsu ba ya fice ya doka murfin motar da karfi har wasu dake gefe suka juyo suka kalle shi.

"What?!!!"

Ya bukata a tsawace. Suka sadda kansu kasa. Yace yan sa idon banza kawai a ranshi.

Fitowa su anty maryam sukai sunata kuka. Dan yanzun mutuwar ke kara shigarsu da wani sabon yanayi.

Basu bi takan fu.ad ba suka wuce abinsu. Lukman yazo ya raba zai wuce shima fu.ad yace.

"Ina kuma zakaje? Aika tsayani ko?"

Cikin idanuwa lukman ya kalle shi.

"After abinda kai wallahi kunya nakeji ace tare muke"

Yana gama magana ya wuce abinshi. Wani mutum yai ma sallama suka gaisa ya karbi butar hannunshi da fu.ad ke jin ai ko wajen zai hade bazai iya wanke ko takalmi da ruwan ciki ba.

Ballantana har azo ga jikinshi. Allah kadai yasan daga inda butar ta fito da kuma kalar germs din dake jiki.

Motarshi ya bude ya dauko robar faro daya sabuwa. Ya rufe motar. Wajen ya karema kallo dan baiga inda zai tsaya yai alwala ba.

Da alamar tsantsar takura a fuskarshi ya hango wani dutse. Ya karasa wajen ya zauna ya kwance takalmin kafarshi.

Alwala yai sannan ya mayar da komai ya daure takalmin. Haneef ya hango ya karasa wajen shi.

Wani kallo haneef yai masa daga samanshi zuwa kasa.

"Ka cire wannan glass din"

Haneef yace yana dauko mukullin motarshi daga aljihu. Ya mika masa.

"Car dina yana bayan can. Kaje ka dauko takalmi ka cire na kafarka"

Kabar mukullin motar yai daga hannun haneef muryashi can kasa yace.

"Bana so ana fadamun abinda zanyi. And menene matsalar takalmina?"

Wucewa haneef yai ya kyale shi. Gaba daya gidansu haneef ne baya jurar rashin kunyar fu.ad.

Bashi bane babba amman har su anty fatima suna ganin girmanshi.

Saboda yanada hankali. Magana ma sai dole yake yinta. Baya shiga harkar kowa. Kuma sunfi shakuwa da fu.ad.

Ko a yarinta in fu.ad ya janyo rigimar data fi karfinshi haneef din yake shigar masa dole.

Shi da kanshi yakan rasa ta ina haneef yake bullowa sanda yake bukatarshi.

Wucewa yai ya dauko takalman haneef din yan zire. Ya saka da alkawarin suna dawowa jana.iza zai sake su.

Dan sun bala.in bata mishi shiga. Badon haneef bane bama bazai sake ba.

*

Suna dawowa yaje ya sake takalmanshi. Bai nemi lukman ba. Shima yai zuciyar kowa yai harkar shi.

Haneef ya lalubo dakyar saboda taron mutane. Ya mika mishi mukulli yana fadin.

"Saikun taho"

Da mamaki haneef yace.

"Meaning?"

"Gida zan tafi. Yunwa nake ji like sosai fa"

Jinjina kai haneef yai.

"Wai yaushe zakai hankali? Will you go and remove that shoe ka dawo a zauna dakai. Kama ga abba?  Ka mishi gaisuwa?"

Kaman fu.ad zaisa ihu yake kallon haneef.

"Abba gaisuwan me zan mishi? Bana zo ba anyi jana.iza and dare yana yi fa"

Wani murmushin takaici haneef yai. Muryarshi da alamun gajiya yace

"Anan zamu kwana har sai anyi sadakar ukku"

Wani pale fuskar fu.ad tai. Ya kwana uku a ina?  Wannan garin da tun daya mallaki hankalinshi zai iya kirga zuwansa.

Ya bude baki ya tabbatar ma haneef da cewan ya samu matsala inhar yana tunanin zai kwana daya ma ba uku ba a wannan kauyen.

Kaman daga sama sukaji muryar abba yace.

"Yawwa fu.ad ka kira lukman kuzo zan aike ku"

Juyawa yai da fara.a a fuskarshi yace.

"Abbah..."

Fu.ad ya fadi da farin cikin ganin mahaifin nashi. Dan tunda yazo yau sati daya kenan bai saka shi a ido ba.

Da sassafe ya tafi wajen training kamun ya dawo kuma ya fita.

"Fu.ad lemuka zaku siyo da ruwa. Sai nama kadai samu mamanku ko ka kirata a waya saita lissafa maka"

ATM baba yake kokarin daukowa a aljihu fu.ad yace.

"No abba. Zan siyo kome ake bukata. Kabarshi kawai"

"Allah yai maka albarka. Ya kara daukaka kaji"

Ya amsa da amin. Abbah ya maida hankalinshi kan haneef.

"To kai muje ko da za.ai wani abun"

Lukman ya kira harta yanke bai dauka ba yai mishi text.

"Idiot. Abbah ne ya aikemu to mu hadu mota"

Momma ya kira ta fada mishi abubuwan da suke bukata.

*

Har suka gama siyayyarsu tas lukman bai kula shi ba. Suka koma gida dan su dauko kayan sakewa.

Gaba daya fu.ad ji yake an takura ma rayuwarshi. A ina zai kwanta ma?  Me zaici a ina zai wanka?

Cake ya kwasa leda biyu ciccike ya dibi cincin da yoghurt da yawa.

Zaka rantse sati biyu zaiyi. Yawan training din da yake yi yana burning mishi energy da wuri.

Yasan abinda ya diba ya masa kadan. Balle ba wani abincin kirki bane. Ko kaya kala takwas ya diba dan baya iya wuni da kaya daya a jikinshi.

A mota ya samu lukman zaune. Lokacin anata kiran sallar isha.i.

"Ko muyi sallah mu sauke nauyi?"

Fu.ad ya bukata. Kallon shi lukman yai ya fito daga mota sannan yace.

"Da ace yanda kake kyautata sallah haka halayyarka take da kaji dadi"

Dariya abin yaba fu.ad sosai.

"Halina is just fine dan rainin hankali. Ka gama fushin kenan"

Yamutsa fuska lukman yai.

"You disgust me. Ewww"

Da gudu fu.ad ya bishi ya ruga yana dariya.

*

Waje suke zaune har wajen tara da wani abu na dare. Haneef na kallon yanda fu.ad ke sosa hannuwa alaman sauro ya ishe shi.

Dariya yai kasa kasa. Tabararren banza ya fadi a ranshi. Gani yai abun yai yawa dan shi kanshi sauron ya dame shi.

Balle kuma fu.ad da kwata kwata bai saba shiga irin wannan wajajen ba.

Kallon shi yai shida lukman yace.

"Ku tashi muje in kaiku inda zamu kwana ko?"

Ba musu suka tashi. Gidan wani dan uwan baban sukaje bayan gidan hajiya babba.

Saboda cikin gidan hajiya babba mata ne kawai. Kasancewar daga ita sai yan aikinta da take da rai. Sai wasu yayan dangi da take rikewa.

Gidan ba wani babba bane can.

"Tafdi"

Fu.ad ya fada ganin gidan da suka tunkara. Wani saurayi da zai kai tsaran haneef da sai lokacin fu.ad ya kula dashi.

Ya karasa ya bude wani shago jikin gidan da kyauren langa langa.

Hannun haneef yaja gefe. Kaman zai kuka.

"Kasan bazan iya kwana anan ba ko?"

Ya karasa yana nuna shagon da hannu. Hannun haneef ya kama ya sauke kasa yace.

"Last i check baka da wani option. Inkuma zakaje kace ma abbah ba zaka kwana bane saika dawo"

Kasa ya kara yi da muryar da yakanyi amfani da ita ya samu abinda yake so wajen haneef din da suna yara.

"In tafi gida. Da sassafe in dawo"

Kallon baka da hankali haneef yai masa.

"Please..... "

Yanda haneef ya zaro ido zai tabbatar maka da fu.ad fadin please din nan da fu.ad yai abune mai bala.in wahala a wajen shi.

Numfashi ya sauke.

"Ka hakura fu.ad dare yayi wallahi. Gobe in Allah ya kaimu saika koma gida"

Yanda yai da fuska yaba haneef tausayi. Dan yasan bai saba ba sam.

Kama hannunshi yai kaman yaro. Yaja shi zuwa cikin shagon.

Ko ina share yake tsaf. Da leda a shimfide sai katifa an lailayeta da zanin gado.

Kusurwar dakin jakunkuna ne da wasu kaya a rataye jikin kusa. Sai takalmansu can gefen wni bango kan siminti wajen da alamu ledar dakin bata kai ba.

Haneef ya karasa ya cire takalminshi ya ajiye inda yaga masu shagon na ajiye nasu.

Ya koma kan katifar kusa da lukman ya zauna. Fu.ad suka kalla tsaye kofar dakin.

Idanuwan nan nashi kalar na turawa sun wani yi haske. Suka bushe da dariya.

Baice musu komai ba dan ya kusa kuka. Ya fara takawa da takalmin bai ko kula haneef dake mishi magana ba.

Wani farin hanky ya dauko daga aljihunshi kato ya shimfida kan zanin gadon dake jikin katifar sannan ya zauna kaman wanda zai hau k'aya.

"Kai da zakai birkida kan katifar. Meye na saka hanky kuma. Ko kan leda zaka kwana?"

Cewar lukman da ya sake bushewa da wata irin dariya.

"Fuck you and damn your mouth"

Fu.ad ya fadi yana kai mishi duka.

"Manners fu.ad. Kamata yai ace momma na wanke maka bakinka da sabulu"

Haneef da yake dariya shima ya fadi. Pillow din dake gefe fu.ad ya dauka ya jefa masa a fuska ya kauce pillow din ya samu lukman.

Dauka yai ya rama suka soma hauka cikin dakin haneef ya musu ihu.

"Dan kaniyarku mutuwa akai mana fa. Kuma ba a gida kuke ba. Ku nutsu please"

Dakyar haneef ya samu fu.ad ya cire takalminshi yabar socks.

Ga katifa daya su uku. Ga sauro. Tashi fu.ad yai ya hada kanshi da gwiwa kawai yana jira gari ya waye.

No comments:

Post a Comment