Thursday 4 May 2017

AKAN SO 29

  *💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

    29

*Kuyi hakuri. Saboda chapter din tayi tsaho bazan samu saka sakonninku ba. Kuci gaba da turomun ra.ayoyinku AKAN SO. Zamu hadu a chapter na gaba in shaa Allah. Nagode*

"Ni dai ba surutu ba. Yunwa nake ji kazo ka dauke ni please"

Dariya lukman yayi ta cikin wayar sannan ya amsa da.

"Ni nace kazo babu sanarwa. But seriously ban sa ranka yau ba. Duka satinka uku ko?"

Daquna fuska fu.ad yai hadi da fadin.

"Oww lukman. Surutun nan in kazo munyi. Ka taho nidai"

Dan jim lukman yayi kamun yace.

"Ba wani dan ladabi"

"Please.."

Fu.ad ya fadi yana kashe wayar da alkawarin shake lukman in ya karaso.

So yake yaga fuskar sofin shi saboda sam bata sa ranshi ba. Daya kirata jiya harda kukanta saboda yace bazai dade ba yana kuma gaya mata saiya kara kwana goma.

Murmushi yake tayi shi kadai. Yana hango soyayyar da zai nuna mata yau din nan. Ji yake kaman yai tsuntsuwa ya karasa gida.

Motar lukman ya hango. Ya mike bashida kayan komai sai jakar system dinshi.  Hannunshi cikin aljihun 3-quarter dinshi ya taka zuwa inda lukman yai parking.

Ya bude motar yana fadin.

"Allah yai maka yanda kamun lukman"

Dariya yai yaja motar.

"Ya hanya?"

Lukman ya bukata. Hararshi fu.ad yai ya sake yin dariya.

"Da na taimaka nazo? Bacci nake wallahi ka wani tashe ni"

Wannan karin fu.ad din ne yai dariya.

"Haneef na kira nace yazo ya daukeni. Zagina ma yai"

"Madallah. Nima kawai saboda safiyya. Da sai dai ka shiga taxi"

Hira suke jefi jefi da lukman har suka karasa. Bai shiga da motar ba iya kacin shi kofar gidan fu.ad din.

"Zan shigo anjima in shaa Allah.  Ka gaishemun da hajiya please"

Tabe baki lukman yai.

"In ka shigo kaje da kanka"

Ficewa fu.ad yai daga motar yana fadin.

"Zanzo dinne ai. Sai anjima"

"Ka gaida safiyya....."

Wucewa fu.ad din yai. Lukman ya juya da motar.

*

Zaune take kan kafet tana yanke farce. Kwankwasa kofa taji anyi. Bata kawo ma ranta komai ba tace.

"Shigo....."

Zatonta ma anty laurat ce. Tunda suna hutu yanzun. Wani lokacin indai ta fito takan biyo su gaisa da safiyyar.

Dago kai tayi dataji an turo kofar. Wani ihun murna ta saki ta tashi da gudu ta karasa ta rukunkume shi.

Dariya yake shima hugging dinta yai sosai. Sun jima a haka sannan ya sake ta yana sumbatarta.

"I miss you sosai sofi"

Ta kasa daina fara.ar da take yi. Hannu tasa tana jan kumatunshi.

"Shine kace mun sai nan da kwana goma ko"

Rike hannunta yai yana fadin.
"Wayyo sofi. Yi hakuri ina son surprising dinki ne fa"

Jakarshi tasa hannu ta cire daga bayan shi tana kama hannunshi. Kan kujera ta ajiye jakar a hankali dan tasan system dinshi ce a ciki.

Zama yai yana kwance igiyar takalminshi. Ya ajiye su gefe ya sauke mata idanuwanshi dake cike da gajiya.

"Yunwa sofi"

Hannunta rike sa kugu ta harare shi a zolayen ce. Hadi da fadin.

"Bansan da zuwanka ba ai. Banda abinci"

Ware idanuwanshi yai akanta. Ya yamutsa fuska.

"Da gaske?"

Kai ta daga mishi alamar eh. Kai ya dafe dan inyace har saiya fita ya siyo abinci yunwar nan ta gama wahalar dashi.

Coffee ne kawai a cikinshi. Shima dan baccin daya ji yana jine ya sha. Baici komai ba.

Ganin yanda yai da fuska yasata kwashe wa da dariya. Kitchen ta wuce ta samu plate ta zubo mishi taliyar datai jalof da dankalin turawa.

Duka ta juyo mishi dan tasan da wahala ma ta ishe shi. Tana gamawa ta zuba ma maigadi da mama indo nasu ta juye tata a warmer.

Bama taci ba ashe rabonshi ce. Da cokali ta taho mishi da cup. Ta soma ajiye abincin kan table taja shi zuwa inda yake.

Sannan ta wuce ta zubo mishi lemo a cup din ta hado da robar ruwa. Tana fadin.

"Bari ko dankali in kara soya maka...."

Da sauri yace.

"Dawo please. Wannan zaiyi rikeni na wani lokaci. Zauna kawai inganki"

Murmushi tayi. Ta samu waje ya zauna tana kallonshi yana cin abincin cike da yanayin nan da yake burgeta.

Hira suke danyi kadan kadan harya gama. Rakashi tai ya shiga wanka ta zauna ta jirashi ya fito.

Ita ta tayashi shiryawa ya gama tsaf sannan yai kissing dinta.

"Bara inje gida sofi. Inma dauko mana wata motar nagaji da wannan"

Murmushi tai mishi.

"A dawo lafiya. Ka gaishe dasu"

Tare suka fita falo ya dauki jakar system dinshi ya fice. Kitchen ta shiga ta dora indomie.

****

Su hussaina na islamiyya. Bai samu kowa gidan ba sai momma da haneef.

Take fada mishi babban yaya ma yai accident amman da sauki tunda babu karaya sai ciwuka.

Sama yahau ya samu haneef suka gaisa.

"Muje gidan babban yaya mana in duba shi"

Gyara kwanciya haneef yai.

"Sa.ankane ni da zamu jera muna zuwa unguwa tare"

Dariya fu.ad yayi.

"Dan Allah"

"Ka kyaleni fu.ad bacci zanyi"

Daga nan saman fu.ad ya wage baki yana kiran.

"Mommaaa!!!  Kice haneeef ya rakani!!!"

Mikewa haneef yai yana toshe Kunnuwa fu.ad ya kama dariya.

"Wallahi ranka zai mugun baci. Kaje ku tafi da kukman mana"

Juya idanuwanshi fu.ad yayi.

"Hajiya ta aiki lukman. Ka tashi muje tare"

Yasan halin fu.ad sarai bazai barshi ya huta ba inba tashi yai ba. Dole ya mike suka fito tare.

Motar fu.ad din suka shiga. Haneef ya dauke jakar system dinshi dake ajiye a inda zai zauna.

Saida ya zauna ya dora jakar kan cinyarshi. Fu.ad yaja motar suka tafi.

*

Basu wani dade gidan babban yaya ba. Dan yama fita sai matarshi kawai suka gaisa da.

Fu.ad din yace a gaishe masa dashi zasu dawo ko zuwa gobe ne in Allah ya kaimu.

Sun fito suna hanya ne fu.ad a dole saiya tsaya ya siyi shawarma. Biris yai da tsegumin da haneef yake mishi.

Yai parking din motar ya fice. Siyowa yai ya dawo suka wuce gida zai ajiye haneef din.

Fu.ad ya fara fitowa daga motar. Haneef ya bude motar shima yana fitowa jakar dake hannunshi yakai zai ajiye zip din ya bude.

Da sauri ya tare system din da takardun da suke kokarin zubowa yana fadin.

"Ya Rabb......."

Komai yake kokarin gyarawa yanda yake wasu takardun asibiti suka ja hankalinshi. Zaro su yai ya rufe motar yana dubawa.

Fu.ad ya zagayo bangaren haneef din. Das yaji gabanshi ya wani fadi ganin takardun da suke hannun haneef.

Har ranshi yai niyyar gaya mishi amman ba yanzun ba. Sam ba ta haka yaso haneef yagani ba.

A hankali yace.

"Haneef....."

Hannu kawai haneef ya daga mishi fuskarshi kafe kan takardun dake hannunshi. Lumshe idanuwa fu.ad yayi.

Baya son damuwa da wani ciwon kai. Fuska haneef ya dago ya kallo fu.ad da wani irin yanayi da yasa zuciyar fu.ad dokawa.

Kallon shi haneef yake yana so yaga ina kaninshi yake. Kaninshi daya san bazai taba wannan abin bai shawar ce shi ba.

Kaninshi da bazaiyi wannan rashin hankalin ba. Wannan ba fu.ad din saya sani bane. Wani fu.ad ne a tsaye a gabanshi da baisan daga inda ya fito ba.

A tsorace fu.ad yace.

"Haneef nine...."

Saboda ya karanci kallon da haneef din ke mishi. Takardun ya sake kallo ya dago ya kalli fu.ad. Girgiza kai fu.ad yake ganin katangar da ke ginuwa tsakanin shi da haneef din lokaci daya.

Tunda yake a rayuwarshi bai taba jin yayi kuskure har cikin ranshi ba kamar yanzun. Kuskuren daya shiga tsakanin shi da dan uwanshi.

Cikin gida haneef yai da takardun a hannu. Da gudu fu.ad ya bishi yana fadin.

"Haneef. Ka saurareni dan Allah....."

"Mommaaaaaa!"

Haneef ke kiranta. Hannunshi fu.ad ya riko ya fisge yana ture fu.ad din.

"Don't. Just don't....."

Fuskar haneef daya kalla yasa shi tsayawa kawai yana dafe kai.

"Damn.....!"

Momma ce ta fito daga daki da sauri kallo daya tai ma yanayinsu tace ma haneef.

"Lafiya? Me ya faru?"

Dai dai lokacin da abbah yai sallama. Momma ta amsa mishi. Ganin su cirko cirko yasa shi cewa.

"Me ke faruwa ne?"

Kallon haneef momma tai. Shikuma ya kalli fu.ad idanuwanshi da wani irin distant look a ciki. Har yanzun ya kasa yarda da abinda yake gani.

Takardun ya sake dubawa dan ya tabbatar da gaske ne abinda yake gani fu.ad ya aikata.

"Fu.ad wai lafiyarku kuwa? Kuna ji anata magana kunyi shiru"

Cewar momma a tsawace. Idanuwa fu.ad ya sauke a kanta. Shi baima niyyar gaya musu ba. Daga lukman sai haneef.

Sake kallon haneef yai da idanuwanshi yake rokonshi da abin ya tsaya tsakaninsu. Kai ya girgiza mishi ya maida hankalinshi kan momma.

Sannan ya dubi abbah. Pha.iza ce ta fito daga kitchen itama tai tsaye tana kokarin fahimtar abinda ke faruwa.

Cikin wata irin murya da wani yanayi a fuskarshi haneef yace.

"Momma fu.ad. Fu.ad bashi da hankali ko kadan.........."

Kanshi ya nuna da duk hannayenshi ya ci gaba da fadin.

"Ni banda wata daraja a idanuwan fu.ad ban isa ya fadamun ba kamun yai wannan haukan"

Ya karasa yana mikama momma takardun data karba bakina sake. Lumshe idanuwa fu.ad yai hadi da fadin.

"Haneef......"

Hannu ya daga mishi alamar baya son ji. Sannan ya juya ya sauke idanuwanshi kan fuskar fu.ad.

"Bana son ji. Bana son jin duk wani abu dazai fito daga bakinka........"

Takardun momma ke dubawa hannunta har rawa yake. Idanuwanta sun tsaya kan kalma daya *VASECTOMY*.

Cikin kanta take duddubawa inda ta adana bokonta take son fahimtar kalmar. Kai take girgizawa. Abbah dake tsaye ya karaso ya karbi takardun daga hannunta yana fadin.

"Wai menene?"

Dubawa ya shiga yi. Jingina da bango fu.ad yayi yana jin kaman ace yana da wani sihiri da zai iya bacewa bat.

Su neme shi su rasa da su tirke shi kan abinda yake tunanin bai shafe su ba. Rayuwarshi ce ba tasu ba.

Wani irin kallo momma take ma fu.ad muryarta na rawa tace.

"Kace mun kokarin yi kake baka aikata ba......"

Abbah ma idanuwa ya zuba mishi. Yana jiran yaji amsar dazai bayar dan ji yake zuciyarshi har wani daci daci take yi saboda takaici.

Duk wata kaddara mai muni da zata auka mishi daga fannin fu.ad take tasowa. Yau shi ya haifi yaron da baya son haihuwa.

Daya bayan daya fu.ad ke kallon fuskokinsu. Cikin sanyin murya yace.

"Na riga nayi momma. Shi ya mayar dani wannan karin. Inajin cikin ku abbah ne kawai baisan bana son yara ba.

Na sha fada ba sau daya ba. Kuma a gabanku. Ban dauka dan nayi wannan zai zama wani babban abu ba..."

Wannan karin momma ce ta karasa inda fu.ad yake ta dauke shi da mari. Rike kunci yai yana kallonta cike da mamaki.

Abinda bata taba mishi ba tun daga yarinta sai yau. A kufule tace.

"Fu.ad ka fita idona wallahi. Har yaushe kai hankalin da zaka yanke irin wannan hukuncin"

Pha.iza kuwa tana ta ware idanuwa jin fu.ad yace.

"Banga wani abu a vasectomy ba momma. Rayuwata ce wannan saboda me zaku kasa fahimta....."

Da mamaki da wani yanayi momma ke kallon fu.ad. Daga hannu tayi zata sake marin shi abbah yai sauri ya rike hannunta da fadin.

"Ki rabu dashi kawai. Ba zamu zauna shi kadai yana bata mana rai ba.

Alhamdulillah tunda bashi kadai muka haifa ba. Kai da ba a haihuwa za a haifoka ne.

Duka shekarunka nawa da har zaka yanke hukuncin baka son zuri.a?"

In ran fu.ad yai dubu ya baci. Ya rasa meye abin daga hankalin cikin wanna abin. Jikinshi ne. Rayuwarshi ce idan basu bashi goyon baya ba sai su zuba mishi ido.

Kanshi a kasa yace.

"Abbah bani da wajen su ne a rayuwata. Yanzun nake kokarin building career ta.

Dame zanji? Me......"

Hannu abbah ya daga mishi yana jin kaman ya shake shi ya huta kawai. Muryarshi a dake yace.

"Duk wani abu daka sani naka ne a gidan nan ka kwashe. Aje ai building din career lafiya.

Kar kafarka ta kara shigomun cikin gida?"

Gabaki dayansu ware idanuwa sukai akan abbah. Momma kanta kallonshi take yi tana ganin tsaurin hukuncin daya yanke.

Su hussaina ne suka shigo da sallama an rasa me bakin amsa musu. Abbah suka fara rikewa da murna kamun hussaina taga fu.ad.

Da gudunta ta karasa inda yake ta riko mishi hannu. Duk da abinda yake ji bai hana shi yi mata wani guntun murmushi ba kamun ya maida dubanshi zuwa abbah daya ce.

"Kaji abinda nace. Kabarmun gida fu.ad kabarmin gida karka sake shigomun ballanta na inganka raina ya baci"

Momma ta kalli abbah kamun tai magana yace.

"Zabi biyu kike dashi. Ko ni ko danki. Nagaji da halinshi. Ban haifi yaron da zai samun hawan jini ba.

Tunda ban saka ma nawa iyayen ba."

Yana rufe baki ya juya ya nufi sashin shi.  Wasu hawaye suka zuboma momma ta kalli fu.ad tace.

"Kaga abinda rashin hankalinka ya janyo ko"

Hussaina da bata fahimci meke faruwa ba ganin momma na kuka yasa ta kama ita. Pha.iza ma kukan take.

Wani numfashi fu.ad yaja yana jin gaba ki daya duniyar ta mishi zafi. Zuciyarshi yaji ta wani bushe. Saboda me abbah zai mishi haka.

Akan ya zabi ya tsara rayuwarshi ba tare da ra.ayin kowa ba. Hussaina dake rike da hannunshi ya kalla. Yasa hannu ya cire nata ya nufi sashinsu.

Kowa kallo yabi shi dashi harya bacema ganinsu. Dakin shi ya shiga. Jaka ya dauka ya bude wardrobe dinshi.

Kayane kawai a ciki. Gani yai babu abinda zai dauka ciki. Karema dakin kallo yake. Wani pink din hanky ya hango kan gadon shi.

Hussaina ta bashi shi. Bazai manta ba har yana ce mata na mata ne tace ta rubuta sunanshi a jiki da hannunta har cakewa tai da allura zaice baya so.

Hannu yasa ya dauki hanky din yana jin kaman ya ciro zuciyarshi ya ajiyeta gefe daya yadan huta. Dakin yake kare ma kallo.

Yana ma kanshi da zuciyarshi alkawarin kin sake tako gidan ma ballantana dakin. Bazai saka ma abbah hawan jini ba kaman yanda yace.

Lumshe idanuwanshi yai tamkar wanda yake son dibar duk wani memory daya taba spending cikin dakin ya adana su dan karsu bace mishi.

Jakar ya ajiye kan gadon saboda babu abinda zai zuba ciki. Wardrobe dinshi ya sake budewa ya dauki wata riga da momma ta taba siyo mishi.

Bai taba sakawa ba saboda ta mishi girma sosai. Ya ajiyene saboda yasan yanda ta siyo mishi rigar cike da kaunarta a wajenshi.

Kafarshi da wani irin nauyi ya ke takawa ya fito daga dakin. A hankali ya janyo kofar karar rufeta na rufewa da wani kyaure a zuciyarshi da baisan inda ya samo shi ba.

Dakyar kafafunshi suka kai falon. Suna tsaye inda yabarsu. Pha.iza ya fara samu. Tana tsaye tana kuka. Kallonta yake.

Muryarshi a dakushe da dacin abinda yake ji yace.

"Be safe. I will always love you"

Rike mishi hannu tayi tana wani irin kuka saboda ta kasa ma magana. A hankali ya zame hannunshi daga nata ta durkushe a wajen tana wani irin kuka.

Kome fu.ad ya aikata. Bataga dalilin dazai sa a kore shi daga gidan ba. Abbah ba kanshi kadai ya kamata ya duba ba har dasu.

Wajen momma ya karasa ya zuba mata idanuwa. So yake ya kalleta sosai dan zai musu nisan da bainsan randa zai sake ganin fuskarta ba.

Cikin kuka tace.

"Karkayi fu.ad karka sake wani kuskuren. Kaje gida zan shawo kanshi......"

Kaiya girgiza mata yana jin wani abu game da abbah daya kasa fahimtar ko menene. Zuciyarshi yaji ta kara bushewa.

"Momma ki yafemun. Zamana zai iya samar miki da matsala......"

Kasa karasawa yai saboda wani abu daya tsaya mishi a wuya. Wuce ta yai ya karasa inda haneef yake.

Baya kaunar abinda yake gani cikin idanuwan haneef sam. Baya son yanda yake kallonshi.

Karantar hugging dinshi da fu.ad ke shirin yi yasa haneef dan matsawa baya. Ware idanuwa fu.ad yayi da mamaki.

Cikin wata irin murya haneef yace.

"Inhar ka tafi karka dawo. Inka tafi ka tabbatar da ka barmu kenan. Ka tabbata shine kuskure na biyu mafi girma da za ka aikata........"

Wani abu daya tsaya mishi a wuya yake kokarin hadiyewa amman yaki wucewa sam. Shima haneef din ya tsane shi kenan.

Kallon shi yai sosai baice komai ba ya nufi hanyar waje. Da gudu hussaina ta bishi ta rike masa riga tana kuka.

"Ina zaka tafi wai?  Momma kuce ya tsaya"

Lumshe idanuwanshi yai. Ya juyo ya tallabi fuskarta dake jiqe da hawaye. Rankwafawa yai ya sumbaci goshin ta.

"Duk nisan dazan kina zuciyata hussaina....."

Hassan ya kalla. Ya girgiza mishi kai hadi da fadin.

"Karka tafi. Kome kayi muna bukatar ka. Wazai je yaga ko zan iya zama dan ball nima?

Wa zai rabani fada da hussaina?"

Miyau fu.ad ya kara hadiya. Dakyar ya iya cewa.

"Ga haneef nan. Ga pha.iza gasu babban yaya"

Girgiza mishi kai hussaina take.

"Babu wanda zai somu kaman ka. Dan Allah karka tafi"

Banbare hussaina yake kokarin yi daga jikinshi. Pha.iza ta karaso inda suke idanuwanta a bushe.

Hussaina ta kama ta janye tace.

"Tunda ya zabi yabarmu ki kyale shi mana. Sai mu fasa rayuwa dan baya nan?"

A hankali yace.

"Pha.iza...."

Ware idanuwanta tai akanshi. Irin kallon da haneef yake masa yake gani cikin idanuwanta. Wani numfashi yaja kamun tace.

"Ka tafi abinka. Kaunarka ba zata kashe mu ba"

Jan hussaina tayi da take wani irin kuka tana kokarin kwacewa. Momma ya kalla ta kauda kai gefe.

Itama ya karanci zabin dasu haneef suka bashi take bashi batare data furta ba. Wucewa yai da duk takun da yake zuwa fita daga gidan yana jin yanda yake barin wani bangare na zuciyarshi.

Dakyar yakai mota. Ya bude ya shiga
Wani dishi dishi yake gani.......!

*

Ta rasa me yasa gabanta yake ta faduwa tun dazun. Wayarta ta dauko ta kira fu.ad har sau uku bai dauka ba.

Mikewa tai taje wajen window ta tsaya saboda haka kawai taji hankalinta ya kasa kwanciya. Tana nan tsaye taga motarshi ta karaso.

Wata ajiyar zuciya ta sauke saboda yanda taji hankalinta ya kwanta. Tana ganin ya fito daga mota ta karasa ta bude kofar.

Dai dai shigowarshi. Bai ko sallama ba yajata jikinshi yai hugging dinta. Wani sauki sauki yake ji a zuciyarshi.

Hugging dinshi tai itama tana karantar akwai abinda ke faruwa. A hankali ta zame jikinta ta daga kai tana kallon fuskarshi.

Wani irin haske taga idanuwanshi sunyi. Gabaki daya ya canza kaman ba fu.ad din data saba gani ba. A tsorace takai hannu ta taba kuncin shi.

"Menene?"

Ta tambaya da wani yanayi a muryarta. Hannunta ya rike ya sauke numfashi kamun yace.

"Abbah ya koreni sofi. Baya son in sake shigar mishi gida"

Ware idanuwa tai ta rike baki hadi da fadin.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un. Me kayi mishi? Ko akan aurenmu ne? Baka ce ya hakura ba...."

Ganin yanda ta rikice yasa shi rikota jikinshi. Kuka take wanda baya so saboda tana kara rikita mishi lissafi.

Tana kirjinshi kwance luf tace.

"Me kayi?"

A hankali yace mata.

"Vasectomy....."

Da rashin fahimta tace.

"Menene shi din?"

Dan bata san ma.anar abin ba bakuma taga alakarshi da korarshi da abbah yai ba. Muryarshi can kasa taji yace.

"Kwayayen haihuwata na kashe gabaki daya."

Kamar wadda akaima allurar rashin kuzari take dagowa daga jikinshi. Yana jin yanda take zamewa daga jikinshi.

Wani irin ihu zuciyarshi keyi. Kallon safiyya yake harta bar jikinshi ta sauke idanuwanta cikin nashi da wani yanayi.

Kunnuwanta ke amsa maganar da yayi. Takai mintina biyu tana tauna nauyinta. A hankali maganar ke yawata zuciyarta.

Tana gayama duk wani waje daya yarda da fu.ad cewar karyane. Son shi da yake mata na karyane inhar baya son hada jini da ita.

Inna!  Baba!  Yaya!  Usman!  Zuciyarta ke jero mata a hankali.  Duk danginta duk wata rayuwa tata.

Yanda ta fito daga gida tabi fu.ad take gani cikin idanuwanta.  Yanda tabar komai ta biyo soyayyarshi ta karya take hangowa.

Komai karyane. Duniyarshi tashi ce shi kadai. Karya yake dayace ta shigo ciki. A bakin kofa ya ajiyeta saboda babu wani waje a zuciyarshi da duniyar shi sai son kanshi.

Cikin muryar da bata gane tata bace idanuwanta cikin nashi tace.

"Saika baro gidan? Kabar kowa?"

Cikin rashin fahimtar tambayar ta yace.

"Me zan zauna inyi sofi? Bani na zabi in tafi ba?  Abbah ya koreni saboda na zabi tsara rayuwata ba tare da shawararsu ba"

Sai yanzun tagani. Sai yanzun taga fu.ad sosai. Sai yanzun taga babu komai a tare dashi sai son kanshi.

Shi yasa ya aureta. Shi yasa ya yanke musu hukunci kaman shi kadai yake da haqqi akan hakan.

Kallon safiyya yake. Yanda take matsawa baya. Rikota yakai hannu yayi ta ture shi da wani irin karfi.

"Ashe baka sona?!!!....."

Wata guduma yaji ta doka cikin kanshi.

"Ashe karya ne duk kalamanka?"

Wanna karin zuciyarshi ce yaji ta rabe gida biyu. Dakyar ya iya cewa.

"Sofi....."

Cikin tsawa tana wani dafe kai tace

"Bana son ji fu.ad!!! Waya baka ikon yanke mana wannan hukuncin?

Ka taba tunanin inkai baka son yara ni ina so?

Ashe duk karyane. Duk karyane komai?"

Sauran lemar dake cikin zuciyarshi yaji ta karasa bushewa tsaf. Dariyar takaici yai yace.

"*Akan so*nki nai wanna abin. Saboda bana so ke kiyina jikinki ki cutu.

Ki rasa inda zaki dora darajar sona sai kan karya sofi?"

Girgiza kai take wasu hawaye na bin fuskarta.

"Karka gayamun me kai *Akan so* ni safiyya ya kamata in bada wannan labarin fu.ad.

Nabar komai *Akan so* ashe karya ne baka son hada jini dani"

Kai ya dafe a tsawace yace.

"Enough safiyya!"

Saida ta razana. Ji yake kamar kanshi Zaiyi bindiga. Wai dame zaiji ne. Kallonta yake kaman bai taba ganinta ba. Kamun yace

"I don't do happily ever after. Daga randa kika yarda da soyayyata ya kamata kisan banyi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba.

Ban kama da wanda zai asarar lokaci da soyayyar shi akan yara ba. Inada su haneef. Ina da su pha.iza. A duk sanda naji marmarin ganin yara zanje gidansu inga nasu"

Karasawa tai inda yake ta cakumi wuyan rigarshi. Tana wani kukan dana sani.

"bansan baka da soyayyar bawa kowa ba sai kanka da banyi kuskuren yarda da karyarka ba.

Ka cuceni fu.ad. ka rabani da kowa. Ka sa zuciyata ta yarda dukkan alkawurranka"

Hannunta ya kama yana jin yanda zuciyarshi ke tarwatsewa. Bai taba zaton safiyya zatai mishi haka ba.

Cikin idanawa ya kalleta yace.

"Baki san me kike fada ba sofi. Zamuyi magana in kin nutsu"

Wucewa yazo yi ya fita daga gidan dan yadan sha iska ta riko shi gam. Wata irin tsanar shi da bata san cewar akwai irinta ba a duniya na ziyartarta.

"Bana son ganinka wallahi. Bana son sake ganinka"

Kafafuwanshi yaji suna wani irin rawa. Rike hannayenta yai muryarshi na rawa yace.

"Sofi....."

Kai take girgiza mishi tana wani irin kuka.

"Nasan ba zaka taba iya bani soyayyarka ba saboda ban taba ganin mai son kai irinka ba.

Ba kuma zaka iya bani yaran dazan sami soyayarsu ba?

Na rabu da iyayen da suke sona na biyoka bayan baka da abinda zaka bani"

Kallonta yake. Kallonta yake sosai yana auna maganganunta yana ganin tsantsar sonkan dayai mata.

Hannu yasa yai cupping fuskarta dam. Kwacewa take so tayi saidai bata da karfin hakan.

"Ina sonki sofi. Wallah ina sonki"

Kallonshi take hawaye ba sake bin fuskarta.

"Kabani yara. In har kana sona da gaske ba karya kake ba"

Numfa shin shi dake kokarin kwacewa yake kokarin kamawa. Zai iya bata yara ne ta hanya daya.

Kallota yake yana girgiza kai. Sai lokacin wasu hawaye suka zubo mishi. Sosai yake girgiza mata kai.

"Kabani yara in kana sona fu.ad......."

Lumshe idanuwanshi yai wasu hawayen suka sake zubowa yana jin dirarsu tare da dukkan zuciyarshi.

A maimakonta wani irin abu na maye gurbin data bari. Dakyar ya iya fito da kalaman da suke shirin kashe shi har lahira.

"Na sake ki saki daya sofi......."

Kwacewa tai daga hannunshi tana yin kasa. Saboda yanda kafafuwanta suka kasa daukarta.

Baya son sake kallonta karya kasa tafiya. Karya kasa bata abinda ta nema saboda yana da son kanshi kamar yanda ta fada.

Wani irin gunjin ihunta ya daki kuncin shi.

"I hate you fu.ad. Bana fatan sake ganinka a rayuwta."

Wani numfashi yaja ya na takawa zuwa waje

"Mayaudari......!"

Takawa ya sake yi 

"Na tsaneka fu.ad nayi dana sanin kaddarar da duk tasa na fara ganin fuskarka a rayuwata....."

Kofa ya bude batare daya juya ba. Ko kalamanta basu kashe shi ba sun kashe abinda yai saura ba zuciyarshi.

Motarshi ya bude ya dauki jakar system dinshi. Komai da yake bukata yana ciki. Fita yai daga gate din gidan ya miki hanya yana jin shi kaman bashi ba.

Ya fita titi baima kula da motar lukman ba sai da yai parking ya fito ya biyoshi ya dafa shi.

Juyowa yai. Gaba daya a firgice yake. Lukman yace.

"Yanzun haneef ya kirani. Fu.ad me kayi?"

Murza kanshi yai kamun ya kalli lukman sosai.

"It is my life saboda me kowa zai kasa fahimtata"

Fu.ad yake fadi cikin hargowa.

Girgiza kai lukman yakeyi cikin ganin wauta da rashin hankalin abinda fu.ad din ya aikata.

"Wallahi duk yanda kake fadar rashin son haihuwa ban taba kawo wa yai kamari haka ba fu.ad. Ban kuma taba zaton cewa a zamanmu zaka yanke hukunci irin haka ba tare daka shawarce ni ba"

saima kaji abinda na sake yi zakai mamaki tunda rayuwa tace bata wani ba. Fadar fu.ad din cikin ranshi a fili kuma yace.

"Na saki sofi!!!"

Lukman baisan sanda ya dauke fu.ad da wani irin mari ba. Fuskarshi dauke da wani yanayi daya girmi tsana da kyamata yace

"Fu.ad anya baka haukace ba? Ko dai makiya sun maka asiri?

Na dauka akan auren sofi kawai Allah ya gama jarabtarka.

Na dauka ka gama girbar mugayen halayenka"

Wata irin dariyar takaici fu.ad yai hadi da fadin.

"Zan bar muku kasar gabaki daya. I have set her free. Ta auri wanda zai iya bata yara. Kaima bankwana nazo inyi maka"

Kallonshi lukman yake. Ya zo ya rabashi yana wucewa. Murya a dake yace.

"We are done fu.ad. Banga me ya rage ba. Be safe"

Kallonshi kawai fu.ad yayi ya wuce abinshi. Yana ganin motar lukman din tazo ta wuce shi fuuu.

Wata irin dariya fu.ad ya kwashe da ita yana jin cewar ya samu matsala. Dariya yake sosai kamar mahaukaci..............!!!"

*

*21/02/2017*

Yanzun ma dariyar ya kwashe da ita sabo da baiga haukan da ya sake tako da kafarshi nigeria ba bayan shekaru sha daya............!

*#TeamAS*

No comments:

Post a Comment