Thursday 4 May 2017

AKAN SO 13

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

         13

Yanajin lukman na kwankwasawa harya gaji ya tafi. Baya son magana da kowa.

Subar shi ya sha iska abin shi. Ai komai yayi su ba dai dai bane ba. Komai yai rashin mutunci ne.

A dakin shi yai sallar isha.i. Yaje ya watsa ruwa sannan ya dawo yai kwanciyarshi.

Yanajin wayarshi na ringing. Ya duba yaga haneef ne. Rejecting yayi.

Ya sake kira ya kara kashewa. Text yaji ya shigo ya bude haneef ne.

"Stop acting like a kid and pick the call"

Share shi yai. Inya gaji ya hakura. Aikam daya sake kira har hudu bai dauka ba wani text din yai masa yace sun koma bichi.

Yana karantawa ya kashe wayarshi gaba dayama. Gara su tafi abinsu subar mishi gidan.

A haka bacci ya dauke shi. Wannan karon ma safiyya ta kutso masa kai cikin mafarki.

Zaune take gaban wata bishiya tana ta kuka. Shikuma yana tsaye a gefe yana kallonta.

Tana dagowa ta kalle shi da fuskarta a kumbure idanuwanta cike da hawaye.

Ya farka da sauri. Wani numfarfashi yake fitarwa. A ranshi yana tunanin wannan yarinyar ko dai mayya ce.

In ba haka ba shi mafarki ma ko yana yinshi to daya farka baya rikewa. Amman karo na biyu kenan da mafarkinta ya hana mishi bacci.

Wanka ya shiga ya sake yi saboda wani iri duk yake jin shi. Daya dawo ya kwanta koya ya rufe idanuwanshi safiyya yake gani.

Dakyar ya samu bacci ya dauke shi.

*Bayan kwana biyu*

Zaune yake dakin shi yana kallo. Gabanshi ledojin snacks ne dayake ci tuli guda da kuma wanda ya cinye.

Lukman ya turo kofar ya shiga hadi dayin sallama. Amsa mishi yai.

"Wai badai baka shirya ba. Karfe tara ne fa addu.ar nan"

"Allah ya jikanta. Na dauka na fada maka babu inda zanje?"

Fu.ad ya amsa shi hankalinshi nakan ball din dayake kallo.

Girgiza kai kawai lukman yai yace

"Sadakar ukkun hajiya babbar ne ba zaka ba fu.ad? Ka kyauta kenan?"

Sai lokacin ya juyo ya kalli lukman.

"Nake jin ance addu.a duk daga inda kayita zuwa take?  Nace Allah ya jikanta ko akwai inda aka wajabtamun zuwa ne?"

"Allah yaye maka"

Lukman ya fadi yana juyawa.

"Amin. Ka jamun kofar Mr. i know what is right"

Bai ko juyo ya bi takan fu.ad ba. Kofar yabari a bude kuma yasan da gangan yayi dan haka ya tashi ya kulle kofar shi.

Lumshe idanuwa fu.ad yai yana sauke wani dogon numfashi da baisan yana rike dashi ba.

Kirga daya zuwa goma yakeyi cikin kanshi yana son ya dai daita bugun da zuciyarshi keyi.

A kwanakin nan biyu a daddafe yayi su. Ga rashin wadataccen bacci.

Ga iya kokarin shi da yake na ganin ya karyata dalilin da yasa yake son zuwa bichi.

Hakan yasa shi ganin yayi duk wani kokarin shi nakin zuwa wajen addu.ar yau. Tunda dare haneef ya kira shi.

Baima daga ba duk da ya huce fushin marin dayai masa. Yana jin share shinne kawai.

Yanzun da lukman ya shigo ya kira bichi ba karamun kara mishi son zuwa yake ba.

Cake din dake hannun shi daya ci rabi ya ajiye saboda ji yai bazai iya karasa cinyewa ba.

Ya maida kafafuwanshi kan kujera ya kwanta cikinta sosai yanajin wata kasala ta rufe shi.

Lumshe idanuwanshi yai duk da ba baccin yake ji ba. Wayarshi yaji ta soma ihu. Yai niyyar share ta ya dai dauko ya duba.

Da sauri ya daga yana fadin

"Hello momma"

"Fu.ad lafiya dai ko?  Haneef yace mun ba zaka zo wajen addu.a ba.  Yanata kiranka ma kaqi dauka"

Kasa yai da murya sosai yace

"Kaina ciwo momma. Bana jin zan iya handling hayaniyar shisa"

"Ayya ka sha magani. Ka kwanta. Muma anjima da yamma zamu taho gaba daya ai. Allah ya kara sauki"

Ya amsa da

"Amin momma. Allah ya dawo daku lafiya"

Ta amsa shi ta kashe wayar. Baya son ana mishi maganar zuwa bichi ko kadan.

*5:30pm*

Yau bayajin zai iya zuwa ball. Dama lukman na nan sai su fita tare.

Babban falo ya fito. Jin cikin shi yake wayam kaman ba dazun ya gama loda mishi burger da milkshake ba.

Sallamar su pha.iza yaji. Ganin harda abba yasa shi karasawa da fara.ar shi.

"Abbah sannunku da dawowa"

Da fara.a suka amsa mishi. Haneef yace

"ya ciwon kan?"

Hankalin shi ya maida kan yan biyu da suke rikici kan waya ya share haneef yace musu

"Ku bakwa gajiya da rigima ne"

Idanuwan hassana cike da hawaye tace

"Hussain ya fasamun screen din waya"

Kallon fu.ad yai yace

"Nafa bata hakuri. Kuma har tawa wayar na bata nace muyi musaya. Tace bata so wai tawa duk ta gurje"

Dariya fu.ad yai. Yasan hassana tana da rikici sosai. Su momma kam wucewa sukai abinsu suka bar su nan.

Wayar hassana fu.ad ya karba yaga dan tsagewar datai bama wata bace can. Shi ya siya musu samsung din wancan zuwan dayai.

"Yanzun ya kike so ayi?"

Fu.ad ya tambaya. A shagwabe tace

"A sakemun screen din. Kuma nasan zaiyi tsada sosai"

Wayar ya mika mata yace

"Kuje da hussain to. Kikai a gyara in zaku karbo sai in baki kudin ko?"

Wani murmushi tai mishi kaman ba ita ke shirin yin kuka yanzun nan ba.

"Thank you bro"

Ta fadi. Murmushi kawai yai ya wuce abinshi.

*

Da dare su duka suka hadu kan dining table sunata cin abinci. Kaman koda yaushe hassana da hussain rigima suke tayi.

Hakan baya nufin babu jituwa tsakaninsu. Sai kayi kokarin taba daya zaka ga yanda suke kaunar junansu.

Pha.iza hankalinta nakan fu.ad tunda suka dawo taganshi wani iri dai. Da yanzun ya damu kowa da tsokana.

Ko yana tambaya wanne abinci ne momma ta dafa da kanta wanne yan aiki suka jagwalgwala.

Saida ta hadiye abincinta sannan tace mishi.

"Bro meke damunka?"

Kafada yadan daga mata sannan yace

"Me kika gani?"

"You are strangely quiet"

Kai kawai ya langabar gefe bai amsata ba. Momma tace

"Da gaskiyar pha.iza meke damunka?"

Yamutsa fuska yai hadi da fadin

"Kawai banajin dadin jikina ne"

"Ka tashi in rakaka asibiti"

Cewar haneef daya ture plate din abincin shi da alamun shirin mikewa.

"Pha.iza mikomun robar ruwan can"

Fu.ad ya fadi kaman ba dashi haneef ke magana ba. Abbah ke kallon su yana murmushi yace

"Fu.ad bakajin haneef na magana ne"

Sake daquna fuska fu.ad yai yace

"Naji shi abbah. Ba saina je asibiti ba"

Mikewa fu.ad yai yace musu

"Nikam saida safenku. Zan kwana a gidansu lukman ne"

Su duka suka amsa shi momma ta dora da

"Ka gaishe da hajiyar su lukman din"

Ya amsa da

"In shaa Allah"

Yana wucewa. Ba abinda ya dauka dan har kayan sawa yana dasu dakin lukman.

*

"Kasan babu abinda na tsana sai a tusani a gaba ana dariya"

Fu.ad ya fadi yanajin kaman ya kwada ma lukman mari. Dariya yake har da rike ciki dakyar ya iya cewa

"Mayu fa kace fu.ad"

Juya idanuwanshi yai yace

"To inba mayu bane suka kamani. Ni banajin dadin jikina and bazan iya cewa ga exact abinda ke damuna ba"

Abin dariya yake bama lukman. Wai mayu.

"Kai ba mai ciki ba balle ince mood swing ka....."

Bai karasa ba saboda pillow din da fu.ad ya jefa mishi akai yana dariya shima.

Babban dalilin dayasa yace gidansu lukman zai kwana kenan. Yasan zaiji shi light ko yaya yake.

Beside baya son magana da haneef. Saboda yana da wani abu a tattare dashi da yake sa kaji kana son gaya mishi dukka abinda ke damunka.

Yasan inya tambaye shi zai iya fada mishi. Lukman kam zai iya fadar wani shirmen suyi dariyarsu.

Lukman ya rigashi yin bacci. Har tsoron rufe idanuwanshi yakeyi kar yaga safiyya.

Amman kaman abin baki. Bacci na dauke shi abinda yake gudu ya faru....!

****

"Da yawan lokutta kaddara kan hada abubuwan da hankali baya dauka"

Murmushi tai tace

"Kaman yanda kaddara ta hada ni dakai"

Kai ya daga mata cikin yarda da abinda tace kamun ya sauke idanuwan nan nashi da kalarsu ke bata mamaki cikin nata.

Bata san lokacin da tace

"Idanuwanka nabani mamaki"

Murmushi yai mata da taganshi har cikin idanuwan shin nan kamun yace

"Yanda kika shiga nan yana bani mamaki"

Ya dafa kirjinshi dai dai inda zuciyarshi take.

*

Bude idanuwanta tai. Muficin dake gefenta ta dauka ta tashi zaune tana fifita.

Amman a banza. Wata irin zufa take da bata da alaka da yanayin zafin da akeyi.

Tagaji da wannan abin. Jan kafafuwanta tai. Ta hada kai da gwiwa wasu hawaye masu dumi na zubo mata.

Wannan wanne irin abune. Sati daya kenan. Da duk numfashin da zata ja ta fitar da tunanin shi a ciki.

Ta ma rasa me take ji game dashi. Saboda wani irin yanayi ne take ji kala kala.

Ko lomar abinci zata kai yana nan cikin kanta. Dashi take komai a manne.

Bata da ikon bacci mai lafiya ba tare dashi a cikin mafarkinta ba.

Gashi wani irin mafarki take yi da duk inta farka sai taji shi kaman gaske. Kalaman da suke ma juna a mafarkin yafi komai daga mata hankali.

Kamata yai ace ko mafarkin shin zatayi ace rashin mutunci yake mata. Yanda taga fuskarshi haka take ganinta a mafarki.

Ko jiya da dare saida tai kuka saboda bata san abinda ya dace tayi ba. Saurayin da tasan ba zata sake ganin shi ba.

Akan me zai manne mata har haka. Saida tai mai isarta sannan taja jiki ta koma ta kwanta. Addu.o.i tai sosai.

Bacci mai nutsuwa ya dauke ta batare da mafarkin komai ba.

*

Jikinta babu wani karfi ta samu tagama sharar gidan. Saida tai wanke wanke sannan taja ruwa taje tai wanka.

Shafa man take yi amman hankalinta na wani wajen daban. Ji tai an tabata da sauri ta dago.

"Safiyya meke damunki ne kwana biyun nan? Sai aita magana bakyaji?"

Inna ke fadi da alamun damuwa. Cikin sanyin murya safiyya tace

"Yi hakuri inna. Banjiki bane shisa"

"Nasan bakiji ni ba ai. Ina tambaya ne ko lafiyarki?"

Saida ta langabar dakai sannan ta amsa da

"Bakomai"

Da alamu inna bata yarda bakomai ba. Tadai kyale ta ne kawai. Da hanzari ta karasa shafa man.

Ta tashi ta dauko wata doguwar riga ta atamfa ta saka. Kasancewar ranar alhamis ne babu makaranta.

Yasa safiyya ta koma kan tabarma tai kwanciyarta. Tunda abincin rana ba lokacin zata dora ba.

Addu.a take sosai ta fatan yanda tasan ba zata sake ganin fu.ad ba Allah yasa ya fita daga tunaninta har abada......!

No comments:

Post a Comment