Thursday 4 May 2017

AKAN SO 23

  *💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ
     
      
          23

Ya riga safiyya tashi. Sai da yai wanka yai alwala ya fita mota ya dauko kayan da zai sake.

Baya son ya ajiye su cikin gidan sam. Dan in son samun shi ne kar su wuce yau ba su koma gidansu ba.

Komawa bedroom din yayi. Yanda safiyya ke baccin ta hankali kwance yasa yaji kaman kar ya tashe ta.

Gefenta ya zauna ya zuba mata idanuwa. Baya son hannunshi yakai jikinta saboda alwalar dayake da ita.

Gefen gadon yadan bubbuga. Ta bude idanuwanta cike da bacci ta sauke su akanshi.

"sofi sallah"

Ya fadi da murmushi yana mikewa daga kan gadon. Saida ta gama addu.ar tashi daga bacci sannan ta mike zaune.

Tana kallon fu.ad ya fice daga dakin. Dafe kai tadanyi. Duk da yau zuciyarta a shirye take da tashi tare da fu.ad bai hanata jin wani iri ba.

Ga kewar su inna. Mikewa tai ta shiga bandaki. Saida ta fara yin brush da fu.ad ya ajiye mata sannan tai alwala.

Sallah ta gabatar. Addu.a sosai tayi bayan ta idar na Allah ya bama su inna zuciyar yafe mata ya kuma basu zama mai inganci da fu.ad.

Dan shi kadai yasan me yake shimfide kan titin kaddarar daya dora su. Tana nan zaune kan kafet fu.ad ya dawo daga masallaci.

"Ina kwana"

Ta gaishe dashi. Cikin fuska ya kalleta.

"Kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah. Kaifa?"

Dariya yadanyi.

"Kina kusa dani. Komai dai dai sofi"

Kunya taji ta sadda kanta kasa. Fu.ad din ya dora da fadin.

"Yau ba wanka da ruwan sanyi ko?"

Dariya tai.

"Yanzun ma zanyi wankan ai"

Kallonta yai yana wani ware idanuwa. 'Yana da kyau' zuciyarta ta fadi.

Sake dakuna fuska yai alamar bai gane abinda ke sata murmushi ba.

Hakan ta karanta yasata mikewa. Kamun tai wani abu maganar zuci ta kubce mata.

"Kana da kyau"

Hannu tasa ta rufe baki. Dariya ta bashi sosai. Da gudu ta nufi bandaki ta rufo yana fadin.

"Sofi dawo nan......zaki fito ki maimaita mun in sake ji"

Dariyarta ya jiyo daga bandakin. Fita yai daga dakin saboda baya son abinda tunanin tana wanka yake mishi.

Yau akwai abubuwa da yawa da yake sonyi. Ga ball yana son zuwa amman yasan bashida wani lokaci. Dole zai hakura zuwa gobe in komai yai settle.

Yana nan kwance bacci ya dauke shi.

*

Wata doguwar rigar ta sake mayarwa. So take ta wanke kayayyakinta amman ta rasa sabulun wanki. Wankan ma da wani abune cikin roba da batasan ko meye ba.

Sai kamshi ga kumfa yana dashi. Fita falo tayi ta duba fu.ad bata ganshi ba. Daya daga cikin bedroom din ta tura.

Don tana bukatar sabulun wanki. Ganinshi tai kwance yana bacci. Har zata fice taja masa kofar idanuwanta suka hango kayan kan wani table.

Karasawa tai cikin dakin. Kayanshi ne duk daya cire daga zuwansu zuwa yau. Dauko su tayi ta ja masa kofar a hankali.

Bandakin bedroom din ta koma. Dabara ta fado mata. Tunda dai babu bokiti. Ruwa ta tara a bathtub din ta zuba shower gel din ciki ta kada yai kumfa.

Kayan fu.ad ta soma wankewa. Duk rigunan ma fararene. Harda singlet dinshi da boxers. Saida ta wankesu ta dauraye.

Sannan ta wanke jeans din da three quarter daban ta dauraye suma. Nata ta wanke da tazo dasu da hijab dinta sannan ta wanke dogayen rigunan datai amfani dasu.

Karfen data gani cikin bandakin ta shiga yarfe kayan tana shanyawa akai.

*

Ya jima da tashi. Wata kasala dai yake ji yasa shi kin sakkowa daga kan gadon. Wayarshi ya lalubo ya duba agogo.

Takwas da rabi. Mikewa yai safiyya na manne a zuciyarshi. Baisan sanda bacci ya dauke shi ba.

Daga dan hutawa kamun gari yadan waye ya fita ya siyo musu abin da zasuyi breakfast da.

A hankali kaman wanda bayaso ya sakko daga kan gadon. Haka ya tako zuwa falo bao ganta ba.

Bedroom din da yasan tana can ya nufa. Da sallama ya tura kofar ya shiga.

Tana cikin bandaki tsaye tana yarfe hijab dinta. Da mamaki yace

"Sofi? Me kike yi haka?"

Da sauri ta juyo. Ta lumshe idanuwanta ta bude su akanshi. Tsoro yadan bata saboda bata ji shigowarshi ba.

A sanyaye tace.

"Allah yasa dai banyi barna ba. Babu sabulun wanki da wannan ruwan nayi"

Girgiza kai fu.ad yai yana sauke numfashi sannan yace.

"Banna bama karama ba"

Rau rau tayi da idanuwa. Shisa da kaman tabari ya tashi daga bacci. Dan dai tana zaune ba wani aikinyi.

Amman tasan wannan ruwan da tsada da ganinshi. Murya na rawa tace

"Kayi hakuri dan Allah. Wallahi babu sabulu shisa. Bansan da tsada ba amman......."

Katse ta yai da fadin.

"Damn the shower gel. Bannar da kikamun kinsa hannunki a ruwa.

Kina so kiyi mura ne sofi?  Duka yaushe zazzabi ya sake ki? Kinzo kina wani wanki"

Ajiyar zuciya ta sauke. Ta dauka barna tayi.

"Ba abinda zaimun. Wankin ma ba yawa"

Karasawa yai sosai bandakin. Zaro idanuwa yayi ganin harda kayanshi.

"Haba mana sofi. Harda kayana fa. Za azo a wanke ai"

Shiru tayi dan batasan me zata ce masa ba. Ita a wajenta wannan ba wani aiki bane. Ko dauda kayan basu dashi.

Yanda fu.ad din yakeyi saikace ta wanke kaya kala talatin ba kwarori ba. Hijab dinta ta karasa shanyawa.

Karasawa yai gefen gado ya zauna yana wani bata fuska. Baiji dadin ganin tayi wanki ba sam.

Kawai jiyai bayason tayi kowanne aiki. Yafison komai ayi mata. Ta zauna ta huta karta wahala.

Fitowa tai daga bandakin. Muryarshi can kasa yace.

"Bana son ki kara yin wanki sofi. Bana so"

A sanyaye tace.

"Na daina. Kayi hakuri"

Kai ya daga mata kawai ya mike yana fadin.

"Bara in siyo mana abinda zamuci"

"Allah ya tsare hanya"

Ta ce. Ya amsa da amin yana ficewa. Gyara zama tayi ta sauke numfashi. Kawai yanda yanayinshi yayi bataji dadi ba.

Duk kokarin da yake akanta. Karshen abinda zatayi shine ta bata mishi rai.

*

Take away ne yayo musu na kwai da dankalin turawa sai yoghurt. A bedroom sukai zamansu suka ci.

Sannan yace mata zai fita ya karasa siyayyar komai. Saida suka je falo ya kunna mata kallo sannan yai pecking dinta a goshi ya fice.

Ganin maigadi ya bude masa gate ya tuna mishi da cewar yana bukatar maigadi shima. Da kuma yar aiki.

Kasa yai da glass din motar yai masa nuni da hannu da alamar yazo. Da sauri ya karaso.

Cike da ladabi duk da a haife ya haifi fu.ad din yake masa magana.

"Bawani abu bane. Ina son maigadi ne a gidana. Da kuma yar aiki haka.

Zuwa gobe ko jibi ma in an samu saikamun magana"

Da fara.a maigadin yace.

"In shaa Allah za.a samo"

Fu.ad bai amsashi ba ya ja glass din motarshi sama ya fice.  Yana hanya ne ya kira pha.iza.

Ringing daya ta daga da fadin.

"Bro. Ina kwana. Ko dayake ma fushi nake. Hussaina kawai kake nema"

Murmushi yayi.

"Haba sisto. Kina raina. Thank you da bakiyi fushi ba."

Yanajin dariyarta kamun tace.

"oh no. Ni banyi fushi ba. Abinda kai super cool bro. Allah kaman a mumbai. So romantic irin......"

Katse ta yai yana dariya hadi da fadin.

"Gidanku pha.iza...."

Dariya take sosai. Muryarshi ya dai daita sannan yace.

"In momma zata barki. Ki shirya yanzun please. Flash me zaki rakani yin abu ne"

Bata ko tsaya jiranshi taji meye zata taya shi dinba tace.

"Be right back"

Ta katse wayar. Ko minti biyar ba aiba tsakani ta mishi text da.

"Done bro. Call me daka zo kawai"

*

Kofar gida ya tsaya da motar duk yanda yake so ya shiga su gaisa da momma kuwa. Nan ya kira pha.iza ta fito.

Bude motar pha.iza tayi ta shiga hadi da fadin.

"Morning bro"

Da yar fara.a a fuskarshi ya amsa da.

"Pha.iza. Ya momma?"

Kallonshi tai tana rufe murfin motar sannan tace.

"Tana nan lafiya. Me yasa ba zaka shiga ku gaisa ba?"

Girgiza kai yayi yana tayar da motar.

"Um um fa. Ba yauba"

"amman....."

Daga mata hannu yai da ya sata yin shiru. Yaja motar kawai suka nufi gidan daya siya.

Dole shi ya sauke yaje ya sa key ya bude gate din sannan ya koma ya shigo da motar. Suka fito shida pha.iza.

Ya bude musu suka shiga cikin gidan sannan ya kalleta yace.

"Kinga gidana pha.iza. Meye babu? Me ya rage insa. Tun jiya muke tunani da lukman mun rasa"

Dariya pha.iza tayi. Tana karema gidan kallo. Ba wani babba bane ba amman yayi kyau. Furnitures din sun mata kyau sosai.

"pha.iza ba dariya ba. Ki fadamun"

Dariyar ya kara bata kamun tace.

"Really bro? Yanzun ku baku ga babu labulaye bane ko daya?"

Ware idanuwa yai kamun yai yar dariya yace.

"Yeah. Kai wallahi sam fa. Munata tunani. Haba shisa komai yake mun wani iri"

Tare suka zagaya da pha.iza tana rubuta duk abinda yake bukata a gidan a wayarta. Musamman kayan amfani na kitchen.

saida suka biya bank ya ciri kudi tukunna suka wuce kasuwa. Shi kanshi mamakin kudin daya kashe yayi.

Pha.iza ma catai mishi dan furnitures din ma na karfe ne. Dana katako ne sunfi tsada sosai.

Duk wani abu da suke bukata suka siyo. Har bayan mota shake yake da kaya. Lokacin da suka dawo gidan suka zauna suna hutawa.

Wayarshi ya dauko ya kira safiyya da ringing daya ta dauka da sallama ya amsa yana dorawa da.

"Nabarki ke kadai ko?"

"Ba komai fa. Inata kallo ne"

Ta amsa. Zai rantse yaji murmushin kunyar nan da take cikin muryarta.

"Yanzun zan taho in shaa Allah. Ki hada kayanki na nan waje daya. Dana zo zamu taho"

Ta amsa shi da.

"Bari in tashi to. Allah ya dawo dakai lafiya"

Ya amsa da amin yana sauke wayar. Pha.iza ke kallonshi tana wani murmushi. Dariya yai hadi da fadin.

"Go away....."

Dariya ta kamayi tace.

"So cute. Muje tare please kaga bamu gaisa ba"

Kai ya daga mata. Tare suka mike suka fita ya kulle gidan. A mota ne take ce masa.

"Bro kayan abinci kadai ya rage maka"

Daquna fuska yadanyi hadi da fadin.

"Zan siyo pha.iza. Itama bansan meye na mata take bukata ba. May be in baki kudi sai kuje tare.

Na siyo mata dogayen riguna dai. Bata fadamun me take bukata ba kuma"

Jinjina kai pha.iza tai alamar yarda da abinda fu.ad din ya fadi.

*

Kayan data wanke ta dauko. Nata da na fu.ad din ta linke su tsaf. Ta saka cikin ledojin da sukayo siyayya. Sai kayan wankansu duka a wata leda.

Ta koma dayan dakin ta dauko jakar fu.ad ta hada masa kayanshi a ciki. Ta tattara waje daya. Ta koma ta zauna tana jiran dawowarshi.

Har mamaki take wai kwana biyu ne kacal ya wuce rabon data saka inna a idanuwanta. Wani nauyi taji kirjinta yayi da tunaninsu.

Dakyar ta samu ta yakice tunanin gefe saboda bata son fu.ad ya dawo yaganta cikin damuwa.

Sallamar shi taji. Ta amsa tana dorawa da.

"Sannu da zuwa...."

Karasawa yai falon sai lokacin ta kula da pha.iza data shigo da sallama itama. A sanyaye safiyya ta amsa hadi da cema pha.iza.

"Ina wuni...."

Dan bude idanuwa pha.iza tai tana kallon safiyya. Tace.

"anty aini zan gaishe dake. Ina wuni. Ya gida?"

A kunyace safiyya ta amsa da.

"Lafiya kalau."

Wani dan shiru ya biyo baya. Zama pha.iza tai kan kujerar dake gefe. Ta kasan ido take kallon safiyya.

Ta kasa ganin ta inda ta dace da fu.ad dan banda idanuwanta bata ga abu me kyau a jikinta ba. Hancinta dai ba wani dogo ba.

Dan pha.iza ma gani tai doguwar rigar dake jikinta daban. Safiyyar ma daban. Ga fuskarta wani tas.

Safiyya kam duk jinta take wani iri. Haka kawai bata son kallon da take jin pha.iza na mata. Sai take jin ta duk tabi ta tsargu.

Fu.ad dake zaune jikin kujera yana dan hutawa saboda ranar da suka sha da pha.iza ya dago kai ya sauke kan pha.iza.

Lokaci daya ranshi ya baci. Ganin kallon rashin amincewa da safiyya dake kan fuskarta. Idanuwa suka hada yai narrowing mata nashi.

Ware nata tai tana son gaya masa yanda safiyya batai mata ba sam sam. Baya son yin wata magana gaban safiyya dan haka ya mike tsaye yace.

"Ku tashi mu tafi pha.iza. Kinsan fa akwai sauran aiki"

Mikewa pha.iza tai da fadin.

"Gida zani bro. Kun karasa aikinku ai na muku kokari ma"

Safiyya a sanyaye ta mike ta dauki hijab dinta dake gefe ta saka. Pha.iza tabi kokakken hijabin da kallo kawai.

Rayuwa kenan. Datai duba da yanda fu.ad ko abincin da atika ta girka bayaci sai abin duk ya sake daure mata kai.

Nesa ba kusa ba atika daya ke wulakantawa tafi safiyya komai. Har kyau ta fita. Gashi yanzun yanda suka jata ajiki wayewa ta fara shigarta.

Pha.iza ta fara yin gaba tana kallon hararar da fu.ad yabi ta da ita. Ta dakuna fuska tana son gaya mishi ai gaskiya ta fadi bataga inda suka dace da safiyya ba.

Kayayyakinsu ya tayata dauka suka nufi bakin kofa. Takalaman data saka yabi da kallo. Silifas ne duk sun koke. Tana bukatar takalmi zai fada ma pha.iza.

Motar ya bude ya sassaka kayansu ciki. Ya zagaya ya bude gaba yace ma safiyya ta shiga. Babu musu ta shiga ya maida kofar ya kulle ya karasa wajen pha.iza dake tsaye.

Idanuwanshi cike da masifa yace mata.

"what is wid' dah' look da kike mata? Bana so pha.iza"

Sauke numfashi pha.iza tayi.

"Ni na isa inja ne da abinda Allah ya kaddara? Dan batai mun ba bro baya nufin ina rike da wani abu kan aurenku"

Bude idanuwa yai. A kufule yace.

"Rashin kunya zakimun pha.iza?"

Kai ta grigiza masa.

"Ni na isa bro. Yi hakuri. Barin wuce gida zan hau napep"

Dafe kai yadanyi sannan yace.

"Muje in dropping dinki sai mu wuce"

Ta bude baki zatai magana yace.

"Bana son wata gaddama. Ranki zai baci"

Wucewa tai ta bude bayan motar ta shiga. Shima ya zagaya ya shiga. Daya karasa gate saida suka sake magana da maigadi sannan ya wuce.

Suna hanya ya kalli safiyya da tai shiru cikin kujera ta hade hannayenta tana wasa dasu.

"Yunwa ko?"

A kunyace tadan daga mishi kai. Dan tun dankalin safe sai ruwa da shima robar na jiya taje bandaki ta bude fanfo ta tarba ta sha.

Ya lumshe idanuwanshi ya bude su kan titin dake gabanshi. Yace mata.

"Bari in sauke pha.iza tukunna sai mu biya mu siya abinda zamuje"

Kai kawai ta daga masa. Pha.iza dake zaune a baya tana jinsu. Text taima momma ta fada mata duk abinda sukai da fu.ad din.

Reply momma tai mata. Sannan tace ma fu.ad.

"Bro momma tace ku shiga"

Sitiyarin motar yadan doka hadi da fadin.

"What dah' fuck pha.iza. Me kikayi? Ni bana son wani fada yanzun fa"

pha.iza ta amsa shi da fadin.

"Abbah fa baya nan. Yau da sassafe ya tafi abuja"

Bai sake cewa komai ba har suka karasa gidan. Shiga yai da motar ciki sukai parking.

Da kanshi ya zagayo ya bude ma safiyya. Pha.iza kam harta wuce ciki abinta. Kallonshi safiyya tai a tsorace.

Tsayawa yai yasha gabanta. Cikin idanuwa ya kalleta.

"Ki yarda dani. Babu abinda zai faru kina jina ko?"

Kai ta daga mishi. Ya ce.

"Good..."

Sannan ya wuce gaba tana binshi a baya har cikin gidan. Tare sukai sallama.

Hussaina dake zaune falon ta tashi da gudu ta karasa inda yake ta riko hannunshi fuskar nan cike da fara.a.

"Inata missing dinka. Yanzun fa nake ce ma momma nikam zanje inda ka koma tunda kaqi zuwa"

Dariya yai sosai.

"Nima nai missing dinki ai. Thank you for dah' text lil sis"

Ta amsa da.

"You welcome....."

Tana sakin hannunshi ta karasa wajen safiyya tana riko nata hannun.

"Anty. Sannu da zuwa. Amman kwana zakuyi ko?"

Fu.ad safiyya ta kalla. Ya daga mata kai dake nuna cewar kar taji komai zata iya magana da hussaina ba wata damuwa.

Da fara.a a fuskarta tace.

"Umm........"

Kaman tana tunani. Hussainata shagwabe fuska.

"Bro bazai bari ba ko? Ni nasani"

Cikin falon ya karasa inda momma ke zaune. Takalman kafarshi ya cire ya ajiye gefe sannan yaje gab da ita.

Tsugunnawa yai wajen kafafuwanta. Ya rike kunnuwanshi kaman wani dan karamun yaro.

"momma nayi laifi babba. Dan Allah a yafemun......"

Ajiyar zuciya ta sauke. Ta kalli fu.ad. Allah sarki tsakanin da da mahaifiya sai Allah.

Tun a shekaranjiya yana ranta. Ko abinci kirki bata sakama cikinta ba tunanin halin da dan nata yake ciki.

Sai da haneef yaje ya dawo ne ma jiya ya fada mata yana nan lafiya tukunna tadanji hankalinta ya kwanta.

Dan shi kanshi fu.ad din har yanzun bukatar kulawa yake ballantana ace ya kula da kanshi ya kuma kula da safiyya.

Zatai magana safiyya suka karaso da hussaina. Har kasa safiyya ta durkusa gefen haneef. Zuciyarta na wani dokawa ta gaishe da momma.

Da fara.a tace.

"Lafiya kalau. Kuna lafiya dai ko?"

"Alhamdulillah"

Safiyya ta amsa a darare. Momma ta maida hankalinta kan hussaina.

"Kuje da ita dining. Ki hada mata abinci da komai taci"

Hannunta hussaina ta kama ta ja. Suna barin fu.ad a nan.

"Momma nima yunwa fa"

Ya fadi. Ta dan harare shi. Yar dariya yai dan ya rigada yasan ta yafe mishi. Da wahala yake laifi a idanuwan momma.

A nutse tace masa.

"Fu.ad kayi kuskure babba. Bakai nake jiba. Yarinyar can nakeji saboda yanda iyayenta sukai fushi sosai.

Na tabbata zasu jima basu sauko ba. Kuma ko nice iya abinda zanyi kenan. Dan Allah ka rike yar nan.

Duk macen da zatai maka abinda tai to ba karamin so take maka ba. Duk idan kuna da wata matsala ina nan.

Sannan ka kira abbanka ko bazai daga ba. Shima nasan a hankali zai huce"

Shiru yai yanajin nasihar da take ma tana wani shigar shi. Da sanyin murya yace.

"In shaa Allah momma bazan baki kunya ba. Allah ya kara girma"

Murmushi tayi.

"Amin fu.ad. Allah yai maka albarka"

Da murna ya amsa da amin yana mikewa tace masa.

"Pha.iza tace mun ka siya gida ko?"

Da sauri yace.

"Eh mumy takardun suna wajen haneef ma. Sauran kayan ne muka siyo da pha.iza yau. Kayan abinci ne kawai ya rage yanzun"

Jinjina kai tayi.

"Shike nan. Allah ya sanya alkhairi. Yanzun sai insa a dibar muku kayan abincin a store. Abinda babu saiku siya ko?"

Shisa soyayyar momma bai hadata da komai ba a zuciyarshi. Badai ta fada amman yasan kaunar da take masa tafi ta kowa a gidan.

Godiya yai mata sannan ya wuce dining inda safiyya ke zaune hussaina nata cika ta da surutu. Sai juya cokalin take cikin abinci yasan kunya ce ta hanata ci.

Hussaina ya kalla.

"em starving fa hadamun komai. Kuma kin cikata da surutu hussaina ya zatayi taci abincin?"

Dariya hussaina tayi tace.

"Hira muke yi ne........"

Ta mike tana zubama fu.ad abinci. Hada idanuwa sukai da safiyya. Sai lokacin ta danji wata yar nutsuwa ganin fu.ad din.

"Ki ci abincin kar yai sanyi"

Ci ta soma yi a hankali. Dambun shinkafa ne yaji kayan hadi da miyar ganye. Sosai taci abincin dan ya mata dadi ba kadan ba.

Fu.ad plate biyu yaci yasha lemo. Sannan ya mike yace ma safiyya ta tashi su tafi.

Ta mike a falo suka sami momma. Ta kalle su tace.

"Fu.ad pha.iza zata zo. Sai suje wajen mai mana dinki akwai wasu atamfofi suna nan. Sai a dinka mata"

Sosai fu.ad yaji dadi dan kamar ta shiga zuciyarshi.

"You are dah' best momma."

Murmushi kawai tai masa sukai mata sallama. Safiyya tai mata godiya cike da ladabi. Momma ta amsa.

"Ku gaida gida. Dan Allah a kula kunji ko"

Fu.ad ne ya amsa dan safiyya kunya take ji sosai har suka fita.

No comments:

Post a Comment