Thursday 4 May 2017

AKAN SO 2

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

          02

*19/02/2017*

Da kanta ta sauke Nana makaranta sannan ta wuce wajen aiki. Ko jakarta bata ajiye ba taji an kwankwasa kofa.

"Shigo"

Ta furta cikin sanyin murya. Kaman yanda ta zata ansar ne. Murmushin nan nashi yai mata.

Duk da yanayin nauyin da zuciyarta take dauke dashi bai hanata mayar mishi da murmushin ba.

Zama tayi kan kujerar office din. Shima ya samu wata kujerar ya zauna.

"Ina kwana..."

Ta gaishe dashi ya amsa da

"Lafiya kalau sofi. Kin tashi lafiya? Ya nana?"

Ta langabar dakai gefe daya tace

"Alhamdulillah. Kawai dai bana son ganin dokin dake cikin idanuwanta ne. And yau zanga doctor dinta kan test din da akai last week"

Jinjina kai ansar yai cikin alamar fahimtar halin da sofi din take ciki.

"In shaa Allah za.a ganshi"

Wani murmushin takaici tayi.

"Ansar idan anganshi bazai donating bafa? Baima son da zamanta ba. Bama na zaton ko da yaji zai dawo tunda baya son yara and........"

"please......"

Ansar ya katse ta yana ci gaba da fadin.

"Babu wanda zaiga Nana bai so ta ba. To hell with him not wanting children. Zai donating indai da zuciya a kirjin shi"

Shiru sofi tai. Dan kuwa ita take da tabbacin zuciyar dake manne kirjin Fu.ad. Kaman yanda a duk kallon da nana zatai mata. Cikin idanuwanta take kara ganin zuciyar fu.ad

Mikewa Ansar yai yace.

"Ina office dina if you need me"

Kai kawai ta iya daga mishi saboda wani abu daya dunqule mata a makoshi.

Tana kallon shi ya fice daga office din yaja mata kofar. Kanta ta dora kan table din tana maida numfashi.

****

Hankalinta nakan rigar da take kallo sam bataji shigowar shi dakin ba.

"Me kike yi haka?"

Maganar nawaf ta dawo da ita daga tunanin da take. Cikin sauri tai kokarin kauda rigar gefe.

"Ba....babu komai"

Ta amsa a daburce. Rigar dake gefenta yazo dauka ta rigashi tana rike rigar sosai a jikinta.

Hannu yakai ya riko rigar.

"Har yanzun baki daina tunanin shi ba ko?"

Ya tambaya rai a bace. Rigar ya fisge daga jikinta ya mike daga kan gadon yana nufar hanyar waje.

Da sauri ta karasa inda yake ta riko masa hannu tana fadin.

"Nawaf wallahi ba haka bane ba. Dan Allah kabani rigar"

Hankade ta yai ta fadi. Duk da zafin da taji bai hanata tasowa ta sake riko shi tana magiya ba.

Kamata yai yai mata wani irin riko kaman zai karyata.

"Duk ranar da na sake ganin wani abu nashi a kusa da gidan nan zan baki mamaki wallahi"

Hawaye cike fal idanuwanta saboda azabar rikon dayai mata. Muryarta na rawa take fadin.

"Kayi hakuri. Dan Allah kayi hakuri. Amman kaban rigar zan ajiye bazan sake fito da ita ba"

Sakinta yai yana girgiza kai. Baisan meke damun nuriyya ba. Bata san yanda yake ji idan ya kalleta yai tunanin wannan banzan farhan din yana yawo a kanta ba.

Duk bai isheta ba sai ta dinga dauko abubuwanshi tana tusawa gaba tana kallo.

Wucewa yai har yakai kofa. Ta matso ta sake rike mishi kafa. Tana magiya ya bata rigar.

Dagota yai daga jikin kafarshi yai mata wani irin mari da saida taga walkiya. Kamun ta gama wartsakewa ya sake dauketa da wani marin.

Wannan karin saida ta fadi. A fusace yace.

"Ina farhan yake lokacin da na hana ai miki fyade? Ina farhan yake lokacin dana dauko ki daga cikin kunci da kangin rayuwa? Da abinda zaki sakamun kenan nuriyya?"

Kuka take sosai. Tasan ya taimaketa. Ba kuma tace bata gode ba. Sai dai babu wanda zai iya rabata da tunanin farhan.

Ko kaddara data rabasu da kanta tabar mata farhan a zuciyarta da tunaninta. Duk da ikirarin nawaf.

Tana kallonshi ya jefar da rigar ya fita daga dakin. Kukan da take bai hanata rarrafawa ta dauko rigar ba.

Fuskarta ta rufe da rigar tana wani irin kuka da zaka san bashi da alaka da marin da nawaf yai mata.

****

*01/01/2010*

"Zan dawo Nuri. Daga lokacin dana tsaya da kafafuna. Mutuwa ce kawai zata hanani dawowa wajenki"

Kuka take sosai. Ta dago da jajayen idanuwanta ta kalle shi.

"Yaya Farhan ya rayuwa zata zame mun babu kai? Ta ina zan fara?"

Wani irin daci yake ji har kasan zuciyarshi. Bai taba zaton akwai yiwuwar ka tsani mahaifinka ba.

Amman ya tabbata da za.a bashi wani zabi zaice a dauke mahaifinshi ne. Ya daina ganinshi ya huta.

Daurewa yai dan shi kanshi yana gab da soma kukan.

"Na biya miki kudin makaranta gaba daya. Ga wannan....."

Ya zaro ATM daga aljihunshi da wasu takardu ya miko mata.

"Ki boye su. Duk sanda kike da bukatar kudi. Ki cire. Kudin dana zuba miki basu da yawa. Su kadai suka ragemun Nuri"

Kasa tsayuwa tai. Durkushewa tai gabanshi tana wani irin kuka daya karya masa zuciya.

Shi kanshi baisan ta yanda zai fara cikakken numfashi babu Nuriyya ba. Sai dai dole yabi mahaifinshi subar kasar.

Yana bukatar ya karasa karatunshi. Ya tsaya da kafafuwanshi yanda zai dawo ya cire Nuriyya daga wannan kangin.

"Yaya farhan bana bukatar wannan. Wallahi kai nake so a kusa dani"

Lumshe idanuwanshi yai da suka sake launi saboda tashin hankali sannan ya bude su yana saukewa akan Nuriyya.

Tsugunnawa yai. Yana son ya riko ko da hannuwanta ne ya nuna mata cewar bashi da wani zabi.

Yana tuna exact maganar da babanshi ya fada mishi jiya da dare.

"Ko kabar yar gidan karuwar nan kabi ni mu tafi. Ko kuma ka zauna da ita anan ka manta cewar kana da wani mahaifi.

Amman wallahi zan janye duk wani taimako na akanka. Saboda bazai yiwu kana zubda mun kima da daraja a idan duniya ba"

Yasan babanshi sarai. Ya kuma san zaiyi fiye da abinda ya fadama. Kuma yana da tabbacin zai ci gaba da saka masa ido yaga ko ya yanke alaka da nuriyya.

Cikin sanyin murya yace.

"Nuri banda wani zabi. Zai tafi da khadee ne....."

Cikin sauri nuriyya ta goge hawayen fuskarta. Taya ma zata fara son kai har haka.

*

*19/02/2017*

Turo kofar da taji ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fada. Cikin bala.in sauri ta boye rigar.

Nawaf ne. Tanajin shi ya tako ya karaso har inda take zaune shima ya zauna.

Kallonshi take taga ko yasha wani abu. Idanuwanshi na nan da kalarsu. Bataga alamun yasha komai ba.

Yanda tayi da jikinta ya taba mishi zuciya. Tsoronshi take. Ya dafe kai yana jan iska ta bakinshi.

Hannuwanshi yakai ya kamota. Taki kallon fuskarshi. Sosai ya matso da ita jikinshi. Yana ganin sahun hannuwanshi kwance kan fuskarta.

Abinka da farar fata. Wani tsanar kanshi yaji. Laifin nuriyya ne tasan shi sarai. Tasan idan ranshi ya baci baya iya controlling din kome yake yi.

Kwantar da ita yai kan kirjinshi. Tana ta sauke ajiyar zuciya. Taji kuka tagaji. Yasa hannuwa ya shafi kumatunta duk biyun.

"Ki yafemun please......"

Ya fada cikin kunnenta. Shiru tai mishi. Dan tsoron yin magana take ji. Lokutta da dama tsoron shi take.

Tanaji ya matse ta a jikinshi.

"Please nuriyya. I love you. Ai kinsan haka ko? Kinsan ina sonki sosai"

Kai kawai ta daga mishi. Tanajin shi ya sauke ajiyar zuciya. Ya mike tare da ita a jikinshi.

Toilet yakaita ya wanke mata fuska da kanshi. Yasa towel ya goge mata inda ruwa ya bata. Ya kamo hannunta ya fito da ita.

Kan gadon ya kwantar da ita. Da ido kawai take binshi. Ganin yana shirin hawowa gadon yasata fadin.

"Takalmi nawaf. Please......."

Murmushi ya kwace masa. Ba mantawa yai da takalmi a kafarshi ba. Bai damu daya cire bane kawai.

Inba nuriyya ba wa ya isa ya saka shi canza dabi.unsa. Takalmin ya cire yabar socks din. Yahau gadon ya kwanta bayanta ya rikota jikinshi.

Bata damu ba dan tasan bai taba takura mata dan biyan bukatarshi ba. Lokutta da dama bata gane kanshi.

Jikinta ya kwanta. Har kanshi a bayanta yake. Ya wani nanike mata kaman karamun yaro.

A haka barci ya dauke shi. Yanajin son nuriyya har cikin fatar shi.

****

*19/02/2017*

Mikewa tai da shirin fita daga office din zuwa asibiti ganin karfe sha daya tayi.

Don sunyi da Doc.jana zata shiga amsar result din wajen sha biyu. Gara ta fita da wuri.

Wayarta taji ta soma ringing. A zatonta ma doc.jana din ce ta kirata.

Tasa hannu ta lalubo wayar daga cikin jaka. Zuciyarta taji ta wani doka da karfin gaske.

Bango ta dafa ta nemi waje ta zauna. Number din principal din makarantar su Nana ne.

Addu.ar duk da tazo bakinta ita takeyi. Ta daga hadi da sallama tana jiran jin abinda tafi tsoro. Ko jikin nana ne ya tashi.

A daddafe suka gaisa cikin harshen turanci.

"Akwai wasu yan jarida da suka zo tun misalin awa daya daya wuce. Sunki tafiya suna son magana ne da Nana. So nasan zaki so ki sani."

Lumshe idanuwanta tayi ta sauke wani numfashin. Dan wannan mai sauki ne.

"Karku barsu su je ko da kusa da itane. Gani nan zanzo school din yanzun"

Tana kashe wayar ta kira Ansar dan tasan ba zata iya wannan aikin ita kadai ba.

Last warning na Doc.jana shine kar a dora ma nana wani stress komin kankantar shi.

A halin yanzun yan jaridar can ba karamun stress bane a wajenta......!

No comments:

Post a Comment