Thursday 4 May 2017

AKAN SO 16

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

      16

*Ina godiya mai yawa ga masu mun fatan alkhairi. Allah ya biya muku bukatunku. Kuna zuciyar Luβπα ako da yaushe*

A daki yai sallar isha.i sannan ya fito ya sauka zuwa falo. Kujera ya samu ya zauna. Kowa nakan dining table suna cin abincin dare.

Hussaina ce tace

"Bro kazo kaci abinci"

Kai ya girgiza mata kawai. Baya son ko bude baki yai magana. Tasowa tai daga inda take zuwa tsakiyar falon.

Hannunshi ta kama tana kokarin janshi. A kasalance yace

"Hussaina ki kyale ni nikam. Em' not hungry"

Girgiza masa kai tayi cewar bata yarda ba.

"Ka taso kawai"

Kanshi yaji ya soma daukar chargy. A tsawace yace

"Wai bakyaji ne. Nace bana ci!"

A tsorace ta saki hannunshi tana matsawa. Kowa ma kallon shi yake. Yana da fada sun sani.

Amman su da wahalar gaske yai musu. Barshi can da yan aikin gidan. Balle ma hussaina da bayaso yaga ta bata rai.

Mikewa yai yanajin wani iri. Ko kallon inda suke baiba. Da gudu ya ke hada steps biyu a lokaci daya yahau sama.

Dakinshi ya shiga ya doko kofar da karfi kaman ita tai masa laifi. Kan gadon shi ya fada a kwance.

Ya rasa me yasa ya kasa controlling abinda yake ji. Bai kamata ace hussaina ta zama punching bag dinshi ba.

Wayar shi ya dauko. Ya nemo num din hussaina yai dialing. Ta dauka cikin sanyin murya tace

"It's okay bro. Kawai kome yake damunka ka fadama momma ko su yaya. Bama son ganinka haka"

Kai ya daga kaman tana ganinshi. Dan wani abu ya tsaya masa a wuya ya hana maganar fitowa. Yanaji tace

"Allah ya tashemu lafiya. Just be safe please"

Jin yai shiru yasa ta kashe wayar. A hankali ya saketa ta fadi gefenshi.

Yau ko kaya bayajin zai iya cirewa. Bacci yake jira ya dauke shi. Yasan mafarkinta zaizo. Zai dan ji sauki.

Amman yau baccin kanshi kokawa suke yi. Kokarin janyo shi yake yi yana kubcewa.

Har karfe biyu yana nan kwance. Juye juye kawai yake. Duk yanda ya kwanta yaki masa dadi.

Ga wani ciwon jiki da yakeji dabai san dalilinshi ba. Iskar dakin har wani kadan take masa. Saukowa yai daga kan gadon ya shiga toilet.

Alwala yayi. Yazo ya shiga sallah. Ita kadaice take samar masa da nutsuwa. Shima daya idar yake sake jin shi ba dai dai ba.

Nan kan daddumar bacci ya dauke shi wajen hudu. Kan kunnen shi aka kira asubah. Ya shiga yai brush ya sake yin alwala sannan ya fita zuwa masallaci.

Koda ya idar nan yai zamanshi. Ji yake kaman karya koma gida. Dan masallacin yana soothing mishi wasu wajaje da suke masa ciwo.

Har wajen shidda da rabi sannan dakyar yaja kafa ya dawo gida. Dakinshi ya shige ya kulle daga ciki.

Wanka ya shiga. Tunani ya masa yawa cikin kai. Yakai minti talatin cikin bathtub banda kafa babu abinda yake wankewa.

Sai da yaji ana kwankwasa mishi kofa sosai sannan ya dawo hayyacin shi. Da sauri ya karasa wanke jikinshi ya dauro towel ya fito.

"Waye?"

Ya tambaya.

"Malam ka bude kofa"

Cewar lukman. Kofar ya bude. Lukman ya shigo. Kallon shi kawai yai.

Idanuwanshi da wani dark circles alamun bacci bai wadace shi ba. Ga fuskarshi sam babu walwala.

Gaisawa sukai da lukman kamun yace

"Wai yane? Kasan ka rage tunani kar wani ciwo yazo ya kamaka"

Murmushi kawai fu.ad yai baice komai ba. Lukman bazai gane me yake ji bane. Daga Allah daya dora masa saishi da abin yake a zuciyarshi.

Ganin yai shiru yasa lukman jan numfashi yace.

"Hajiya ta aikeni katsina. Nace barin zo mu tafi"

"Kaje kawai lukman"

Karo na farko da indai yana gari yaki bin lukman wani waje. Ko ina daya zaije dayan na biye dashi.

Da mamaki lukman yake kallonshi. Fu.ad ya sake cewa

"Banajin dadine fa"

Mikewa yai yace

"Tam shikenan. Allah ya bada lafiya. Saina dawo"

Da sauri fu.ad yace

"You mad at me or something"

Kai lukman ya girgiza masa yai dariya sannan yace

"Kai haba. A.a fa. Nima ba jimawa zan ba in shaa Allah"

"Tam drive carefully. Allah ya tsare"

Ya amsa da amin yana ficewa.

Wani numfashi fu.ad ya fesar ta baki. Yaki bin lukman ne saboda yana son komawa bichi.

*

Sanye yake da 3 quarter loose milk colour. Sai riga fara ta kama jikinshi. Ya taje kanshi.

Sai kamshin turaruka yake. Ya fito. Batare daya hada ido da momma ba yace

"Ina kwana"

Ta amsa da

"Lafiya kalau.... "

Tana nazarin dan nata da ta rasa meke damun shi tsakanin jiya da yau. Gaba daya ya canza.

Ta ma haneef magana yace mata bakomai kawai yace bayajin dadine kuma sunje asibiti jiya da yammaci.

Bata ce sake cewa komai ba. Plantain ya zuba da soyayyen kwai. Da alama tura abincin kawai yake bawai dan yanajin dadin shi ba.

Yana gamawa ya kalli pha.iza yace

"Ki dauko mun akwatin dana zo dashi a dakina"

Bata ce komai ba ta ajiye abinda take ci ta tashi. Ta dauko mishi akwatin ta kawo.

Janshi yai zuwa tsakiyar falon ya zauna kan kafet. Sannan ya bude.

Pha.iza yaba ma system din dayai mata alkawari. Hp ne mai kyau sosai. Ta karba tana mishi addu.a.

Collections ne na turaruka ya kawoma abbah da momma. Ta amsar musu tana saka mishi albarka.

Hussaina sarkin shan zaqi. Wasu irin chocolates ne ya kawo mata. Hassan kuma takalma ne masu tsada da wata hoodie daya ce ma fu.ad din yana so.

Sai kaya masu kyau na yara yaba mama yce akai ma yaran su anty fatima.

Rolex din daya siyo ma lukman da haneef ya kwashe ya ce pha.iza ta dauki akwatin in tana so.

"Ina dasu har biyu fa. Sai dai ummie data ga irinshi a dakina tace mun tana so"

Dafe kai yayi. Sam ya manta da kanwar lukman. Ga yarinyar tana wani girmama shi. Mikewa yai yace

"Ina zuwa"

Dakin shi ya shiga. Samsung Galaxy din daya siya dan yai amfani da ita ya dauko ya dawo.

"Ki bata da wannan. Mantawa nai"

Momma da pha.iza suka tayata godiya. Danko hajiyar su lukman indai ta siya ma ummie wani abu takan hada da pha.iza.

Mutanene masu karamci da sanin ya kamata.

*

Dakinshi ya koma yai kwanciyarshi. Sai lokacin ya samu bacci ya dauke shi wannan karin ko mafarkin safiyya dake dan rage mishi kewarta baiyi ba.

Haka ya tashi ya duba agogo yaga karfe sha biyu har da mintina arba.in. Bai tsaya sake wanka ba.

Alwala kawai yayi. Ya fita masallaci ya tsaya lokaci ya karasa sukai sallah sannan.

Mota ya dauka ya fice zuwa bichi. Yanayi yana duba agogo dan jiya biyu da kwata ne bazai manta ba.

Baya so ta fito ta wuce bai ganta ba.

****

Uniform inna taga safiyya tasaka tace

"Da kin hakura da makarantar ban yau"

"Zanje inna. Ko karatu aka danyi naji sauki sauki"

Jinjina kai inna tayi.

"To ai naga bakici komai ba tun jiya. Gashi kinyi wani zuru zuru"

Murmushi ta kakaro tace.

"Da sauki sosai fa inna. Kuma yanzun ai sai inci ko kadanne"

Innna da kanta ta zubo mata. Taliya ce yar hausa da manja. Tadan ci ba laifi sannan ta wanke hannunta.

Ta sake gyara fuskarta ta saka hijab ta dauki jakarta.

"Inna saina dawo"

Cike da kulawa tace

"Allah ya tsare. Indai kina jin jikin. Ki dawo gida"

Ta amsa da

"In shaa Allah"

*

Tun jiya zuciyarta bata daina dokawa ba har zuwa yanzun. Kaman abinda take ciki bai isheta ba ta hango Ado.

Wani takaici ya sake lullube ta. Da saurin shi ya karaso.

"Safiyya.... "

Ciki ciki tace

"Ina wuni"

Ya amsa da

"Lafiya kalau. Har an fito makarantar kenan"

Bata daina tafiya ba.  Ko zai gane cikin sauri take ya kyaleta. Ga mamakinta shima tafiyar yake yana mata magana.

"Umm"

Ta amsa a takaici. Surutunshi yake. Muryar da kunnuwanta ke jiyo mata daban.

*

Tsaye yake jikin motarshi dai dai inda sukai parking jiya. Yana kallon hanya. Yanda zuciyarshi ta wani doka abin har mamaki ya bashi.

"Sofi...... "

Ya furta a hankali. Wani ya hangota dashi yana mata magana harda dariya.

Jiyai zuciyarshi ta turnuke. Har wani duhu duhu yake gani. Takawa yai yana shirin karasawa inda suke.

Kafarshi har kara sauri take. Sai dai kamun yaje yana kallo harya saurayin daya ga yana mata magana ya juya.

*

Kaman ance ta dago da idanuwanta. Ta sauke su kan fuskar fu.ad dayake karaso inda take.

"Ya Allah.... "

Ta fadi komai na kwance mata. Dawowa yai. Ji tai kaman tasa kuka.

Wai me yake nema da ita ne haka. Saboda me zai zabi takurata da yawa ne.

Yana karasowa daf da ita maganarshi ta farko shine.

"Waye wancan dayai miki magana"

Yanayin muryarshi ya tabata har a zuci. Batare data kalle shi ba ta amsa da.

"Me ya dawo dakai?  Bana ce karka sake zuwa........ "

A tsawace yace

"Dammit sofi. Tambayarki nai ki amsani. Waye shi?"

Duk da ya tsorata ta bai hanata dagowa ba.  Idanuwanta da suke cike taf da hawaye ta sauke masa.

"Ni kaina ba matsalarka bace ballanta na shi. Dan Allah ka kyale ni. Ka fita daga rayuwata ko zan samu sauki"

"Sauki..... "

Ya maimaita yana kwashewa da dariyar da baima san daga inda ta fito ba.

Maganar sauki take yi. Shi zai fita daga rayuwarta ta samu sauki ko ita zata fita daga tashi ya samu sauki.

Kallonshi take yana dariya da yanayin da bata taba gani ba. Sannan yace

"Ki kalleni sosai. Ki kalli idanuwana sofi. Nima saukin nake nema. Ni kaina so nake kibarni ko rayuwata zata koma yanda take..... "

Hannuwanta tasa duka biyun tana toshe kunnuwanta. Bata son jin kalamanshi.

Bata son jin duk wani abu dazai fito bakinshi. Wanda yake a mafarki ma bata da hanyar hana su ne.

Kallonta yake da mamaki yana girgiza kai. Bata son jin muryarshi.  Bata son ganin shi.

Wani abu yaji yana zuba a zuciyarshi da baisan ko menene ba. Saidai yana da ciwo sosai.

Fuskarshi da yanayin shi yana neman sake karya mata zuciya.

"Dan Allah ka tafi. Ni dakai duniyarmu ba iri daya bace ba. Ka zauna a taka kabarni a tawa"

Hannu yasa cikin sumar shi.  Sannan ya kalle ta sosai.

"Taki duniyar ta shigo tawa. Bani na janyo ta ba. Ban kuma san yanda zanyi da ita ba. Saboda me ba zaki bari in koyi zama da ita ba"

Sosai take kokarin tarbe hawayenta.

"Saboda zamansu waje daya bazai yiwu ba. Kana tambayar me wancan yakeyi tsaye dani ko?

Ka saurareni sosai. Ba damuwarka bane ba. Zan gaya maka ne saboda karka kara dawowa.

Shi zai aureni. Satika hudu suka rage. Saboda haka ka kyaleni"

Tana gama magana ta wuce da sauri. Ko juyawa baiba. Saboda duk budar bakinta.

Duk wata kalma da ta fito mayar dashi kaman kusa su kuma maganganun suka zama guduma.

Duk daya kara buga shi take ya shige ciki. Ya kasa motsawa. Ya kasa jin komai.

Wani abu ya lullube zuciyarshi da yake son kare sauran jikinshi daga fahimtar abinda ta fada.

Samu yai ya ja kafa zuwa motarshi. Ya bude ya shiga. Yanda yai corner zai daga maka hankali.

Safiyya dake tafiya gefe taga yazo ya wuce ta da wani irin gudu. Dafa kai tayi.

"Ya salam. Me na aikata...... "

*

Allah ne kadai yakai shi gida dan ko gani baya yi. Haka ya bude murfin motar bai ko rufe shi ba ya fito.

Falo ya shiga. Momma na zaune tana kallo.

"Momma........ "

Kallo daya tai masa. Ta mike. A hargitse yake. Duk yai wabi maiko da zufa. Saikace wanda sabon hauka ya kama.

Wajen da yake ta karasa. Jiri ke dibarshi ta kula. Ta riko masa damtsen hannu taba fadin.

"Fu.ad lafiyarka kuwa? Menene?"

Wani irin numfashi yake ja da alama baya kaimasa inda ya kamata. Dan kokawa take dashi.

"Momma aure zatayi. Ina haneef. I can't..... She can't...... Saboda me zata auri wani?"

Bata fahimtar me yake cewa. Kokarin janshi takeyi ya zauna. Amman kaman an kafe shi a wajen.

Kuma har lokacin kokawa yake yi da numfashin shi. Sai kace wanda yake fama da asthma.

Dai dai shigowar haneef da sallama. Ganin su yasa shi karaso da sauri. Kama fu.ad yai da kaman baya cikin hayyacin shi.

Momma da ta rasa me zatai tace ma haneef

"Wai me ke damunshi ne haka. Sambatu fa yake"

Haneef ya kalla yace

"Haneef kazo muje kai mata magana....aure fa zatai. Taki ta saurare ni. Ina sonta wallahi"

Sai lokacin haneef ya fahimta. Girgiza kai yake. Yau ga fu.ad na girbar abinda ya shuka.

Gashi ya samu matsala kan yarinyar da ya tabbata in a dane ko kallon wulakanci bata ishe shi ba.

Lallai Allah ya dora masa jarabta. Ya nuna masa yanda ya halicci dan Adam ya kuma daukaka shi da daraja mai girma.

Kamashi haneef yai. Yanata surutai. Dakyar yakaishi daki yace.

"Kai bacci. Yanzun zanje muyi magana. Wasa take maka fa"

Da wani yanayi yace ma haneef.

"Ka tabbata?"

Kai ya daga masa. Waje ya samu ya zauna yana kallon shi. A zuciyarshi yana nemar masa sauki wajen Allah.

Bai bar dakin ba saida yaga ya samu bacci sannan ya fito ya ja masa kofar.

No comments:

Post a Comment