Thursday 4 May 2017

AKAN SO 38

💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

          38

*Ina godiya da fatan alkhairi kaman ko da yaushe. Ba sai na ce komai bama kunsan #AnaTare*

Juyawa fu.ad yai safiyya ta dakatar da shi da fadin.

"Please ka dauki mukullin motata kuje gida da Nana. Bazan iya ganinta ba yanzun......"

Ta karasa maganar muryarta na rawa. Kai ya daga mata alamar yaji ya dan kalli haneef da yake masa wani kallo dake kara karya mishi da zuciya.

Sannan ya wuce. Shi kadai yasan yanda yake jin zuciyarshi. Yakai mintina biyar tsaye riqe da handle din kofar yana maida numfashi.

Addu.a yake Allah ya bashi karfin gwiwar fuskantar nana batare da zuciyarshi ta sake karyewa ba. A hankali ya tura kofar yana jin sallamar da yake sonyi tsaye a ranshi taqi fitowa.

Idanuwanshi ya sauke kan momma. Muryarshi a dakushe yace.

"Gida zamu tafi. An sallameta"

Da fara.a momma tace.

"Alhamdulillah. Aikam nima bara na tashi......"

Kai yadan daga mata. Nazarin shi take kwata kwata a birkice yake hankalinshi kaman baya jikinshi.

"Fu.ad?"

Ta kira cike da alamun tambaya. Kallonta yai sosai yana roqonta da idanuwanshi da karta tambaye shi komai. A hankali ya girgiza mata kai.

Shiru tayi tana mikewa tace ma nana.

"To yar tsohuwa nikam zan wuce sai nazo duba ki ko?"

Dariya Nana tayi da sautinta yasa fu.ad jin zuciyarshi ta wani matse kaman zata fashe. Baya son tuna karancin lokacin dayake dashi najin wannan sautin.

"Ni zan zo ai. Mumy zata kawo ni in kwana gidanki"

Murmushi momma tai mata.

"Allah ya kawo ku lafiya. Ya kara sauqi"

Ta amsa da.

"Amin. Allah ya tsare hanya"

Momma na tafiya ta amsa ta da.

"Amin thumma amin"

Raba fu.ad tayi ta wuce batare data ce mishi komai ba. Yaji dadin hakan dan baya jin zai iya wata magana a yanda yake jin shi.

Kayan su ya fara tattarawa dan baya son ko kallon inda Nana take. Saukowa tai daga kan gadon tazo inda fu.ad ya saka warmers dinsu a babbar leda ta kamo hannunshi tana ja.

Sai da ya ja wani numfashi ya sauke shi batare daya kalle ta ba yace.

"Princess ina jinki...."

Sake jan hannun shi tayi. Bata son yanda yake kin kallonta din nan sam. Tasan me hakan yake nufi. In tun yanzun zasu fara mata irin hakan nan gaba bata san me zai faru ba.

A hankali ya juyo ya sauke idanuwanshi da suka sake launi kan fuskarta.

"Ina mumy?"

Ta tambaya tanajin komai baya mata dadi. Bata son ganinsu cikin damuwa ko kadan. Da da yanda zatai ta cire musu da tayi. Dakyar yace mata.

"Sunyi gaba dasu lukman ni dake zamu tafi"

"Hmmm"

Nana ta fadi ta saki hannunshi taje tana saka takalminta da hijab. Sannan ta dawo ta kama hannunshi suka fita tare.

Saida ya bude bayan motar ya zuba kayayyakin ciki sannan ya bude ma nana ta shiga ya zagaya shima ya shiga.

*

"What is wrong?"

Nana ta tambaye shi kaman daga sama. Dan kallonta yai sannan ya maida hankalinshi kan tuqi da fadin.

"Bakomai me kika gani?"

Sake lafewa tai cikin kujerar motar tace.

"Kayi shiru tun dazun"

Shi kanshi bai kula da cewar tunda ya soma tuqin baice komai ba. Yanajin yanda hannuwanshi ke wata zufa duk da AC din motar a kunne yake.

"Bako....."

Da sauri ta katse shi da cewar.

"Please kar kamun karya. Na tsani aimun karya"

Sauke numfashi yai.

"Tsana is not a nice word princess"

Sauke murya tayi tace

"Kayi hakuri"

Kai yadan daga.

"Yau dinne babu dadi shine kawai"

Ba karya ya fadi ba. Gaba daya ranar bata mishi dadi. Tun kamun a fada mishi wannan mummunan labarin.

Hankalinta ta mayar kan titi sosai tana kallo hanya. Da wani irin yanayi mai nauyi da bai taba ji a murya yarinya mai shekarunta ba tace.

"You are not a match ko?"

Motar yaji tana kokarin kwace mishi. Kamun ya samu yadan dai daitata yana rage gudun da yake. Wani irin yawo zuciyarshi take yi cikin kirjinshi.

Wani abu daya tsaya mishi a wuya ya hadiye. Zufa yake ji ta wajaje da dama tana fito mishi. Baya son mafa karya ko kadan.

Saidai baisan ta inda zai fara gaya mata gaskiya ba. Tsoro ne cike fal a zuciyarshi. Koda Nana zata sani baiso daga shi sai ita ba.

Tafi sabawa da sofi. Zata so kasancewa da ita a wannan lokacin bashi ba. Duk da fadar hakan a kanshi kawai ba karamin ciwo abin yake mishi ba.

"Princess......."

Ga mamakinshi gyara zama tai ta zuba mishi idanuwan nan nata iri daya da nashi.

"Ya mumy take? Ya ta dauki hakan? Bata ji dadi ba ko?"

Nana ta jero mishi tambayoyin lokaci daya. Damtse steering wheel din yayi kaman zai karya shi. Tagane. Tasan bai matching ba.

Muryarshi a sarqe ya amsa ta da.

"Pretty bad"

Shiru yai dan baisan kalaman dazai dora yanayin safiyya akai ba. Dashi kanshi. Dan har yanzun jiyake gabaki daya duniyar shi tayi wata irin girgiza da komawarta dai dai abune mai wahala.

Ko yanzun da yake tuqi kokawa yake da zuciyarshi da duk wani abu nashi ya yarda cewar babu abinda zai iya yi ma Nana.

Shiru tai na lokaci mai tsayi. Tukin yake amman ji yake kamar garin zasu bari. Kwata kwata yaki masa sauri. Yama manta da ya rage gudun motar sosai.

Ta gefen idanuwanshi yaga ta cire hijab dinta. Yadan kalleta ya maida hankalinshi kan tuqi yana jin wani irin yanayi da bashida kalaman misaltawa.

Hular dake kanta da tunda ya ganta irin sune a kan ko yaushe bata taba cirewa ba tasa hannu ta fitar.

Kanta ta shafa da babu gashi ko kwara daya. Ya sake juyowa ya kalleta. Ji yake kaman wani abu na matse mishi zuciya. Kirjinshi zafi yake sosai.

"In fada maka wani abu ba zaka fada ma kowa ba? Kayi alkawari"

Kai ya daga mata ya kasa magana. Wannan wacce irin rayuwa ce. Shekararta sha daya. Kamata yai ace tana can tana wasanta tana tunanin wanne Disney movie ne yafi wani kyau.

Wanne riga yafi burgeta. Bawai zaune anan ba da kanta babu gashi ko kadan. Ji yake zai iya bayar da komai dan ta samu hakan ciki harda tashi rayuwar.

"Ina tsoron in mutu"

Jiyai wani abu ya tsane a fuskarshi. Dayake da tabbacin duka jinin dake jikinta ne ya koma wani waje. Kamun lokaci daya wani abu mai yaji ya mamaye mishi idanuwa.

Hannunta ya kamo da nashi guda daya ya dumtse gam dayan nakan steering motar. Yasan shi ba mai yawan kuka bane. Amman wannan yarinyar ta zaune kusa dashi ta taba mishi zuciya.

Yarinyar shi. Jininshi. Yarinya kwal daya da kaddara ta miko mishi kuma yanzun zata sake karbewa. Wasu hawaye ne yana jin taruwar su da ke da wani irin ciwo.

Yana jin yan kananan fingers dinta sun matse mishi hannu gam kamun tace.

"Kar kai kuka. Please. Kawai ina son in samu wanda zan fada ma ne. Bazan iya fada ma mumy ba. Tana cikin damuwa mai yawa bana so in kara mata.....nasan daka zo ta kara sama ranta zan ji sauqi kuma........"

Shiru tai. Saida yadan yi gyaran murya ya hadiye wani yawu yana maida hawayen dake son zubo mishi kamun yace.

"Kuma me?"

Sauke ajiyar zuciya tayi.

"Kawai ina so in fada ma wani inajin tsoro ne ba tare da yace mun komai zaiyi dai dai ba"

Kai yadan daga mata cikin fahimtar abinda take fada din. Shi kanshi a tsorace yake saboda me zai kasa fahimtar nata tsoron.

Sauke murya tai tace.

"Kawai ina son kowa ya zama dai dai ne"

Da sauri ya fadin abinda yasan karya ne.

"Zamu zama dai dai. Kina iya fadamun kome kike so Nana......zamu zama dai dai.... Duk da....."

Saida yaja numfashi a jere yafi sau uku yana fitarwa kamun ya iya karasawa cikin rawar murya.

"Duk da hakan baya na nufin ba zamuyi kewar ki duk rana ba"

Ya juyo yadan kalleta yana jin yanda zuciyarshi ta rabe gidaje da dama. Murmushin da tai mishi sam bai rage masa radadin dake kirjin shi ba.

Da gudi in aka bashi zabi zai karbi cancer dinta. Ya riga da yayi rayuwa. Wannan lokacin daya kamata ace tayi tata ne.

Saidai zuwa yanzun idan akwai abinda rayuwa ta koya mishi shine bai da iko da tsari na rayuwarshi. Alkalamin kaddara ya rigada ya dade da rubuta mishi tashi.

Da wannan tunanin ya karya corner har suka karasa gida. Maigadi ya bude musu. Suna parking din motar safiyya na fitowa tai tsaye bakin kofar shiga gidan.

Kama murfin motar nana tayi tana sauke wani irin numfashi me nauyi hadi da fadin.

"Daren yau mai tsayine......."

****

Kwance take tana juya text din da jabir yai mata tun da yammaci kan maganar ayna. Rayuwa take dubawa.

Ta lumshe idanuwanta. Tasan yana wajen ayna zance ya fada mata. Sai dai maimakon ta hango shi babu komai cikin kanta sai fuskar Nana.

Babu abinda take tunawa sai yanayin tashin hankalin da iyayenta suke ciki. Sai take ganin rayuwa babu wanda tazo ma da adalci irinta.

Babu wanda ke da kwanciyar hankali irin nata tunda har tana da nutsuwar da zata zauna tana kishi. Godiya ta shiga jeroma Ubangiji da kalar ni.imar dayai mata.

Bata san iya lokacin data dauka a haka ba. Sam bataji shigowar jabir ba saida ya hawo kan gadon inda take ya sumbaci kuncinta.

"Honey j"

Ta furta a sanyaye tana bude idanuwanta kan fuskarshi. Murmushi tai mishi. Ya mayar mata.

"Naji kana kamshi. Ko ayna ta feso maka turaren angonci tun yanzun"

Tana kallon yanda sonta ke yawo cikin idanuwanshi. Mamakinta jabir yake sosai. Yana kuma jin tsoro can kasan zuciyarshi kar sai anyi auren ta birkice masa.

Sauke murya yai.

"Jana. Are you okay kuwa?"

Saida ta mintsinar mishi kunci sannan tace.

"Me yasa kake tambaya?"

Gyara zamanshi yayi kan gadon sosai ya kwanta rigingine kaman yanda take. Kanshi yaja ya hada da nata sannan ya soma magana cikin sanyin murya.

"Na kasa yarda cewar bakya bani matsala dan zan kara aure. Ina jin kaman kina boye komai ne a kasan ranki. Ina jin kaman zaki iya birkicemun in anyi auren nan"

Kanta ta juyo ta sa idanuwanta cikin nashi. Takai hannu ta kamo nashi hannun sosai take kallonshi.

"Honey j yau na sake ganin abinda ya kara karyamun zuciya. Yau naga abinda rayuwa take tattare dashi mai muni da kunci.

Ko kamun ingani kishi na dawainiya dani. Kuma har yanzun bai daina ba. Sai dai banida dalilin damuwa inhar ina ganin wannan soyayyar cikin idanuwanka.

Fatana daya kar wani abu ya canza ta"

Sauke numfashi yai.

"Ina sonki sosai jana. Nagode da kalar kaunar da kika nunamun. Allah yasa kece matata har a aljanna"

Sosai taji dadin addu.arshi. Itama tata takeyi musu. Allah ya basu zama na fahimta ya bashi zuciyar yi musu adalci.

Hannunta ta dora kan cikinshi sannan tace.

"Kaci abinci?"

Hannunshi ya dora kan nata.

"Ina zanci abinci naki yana jirana?"

Dariya tayi tana mikewa. Ta sauka daga kan gadon. Ta zagayo.  Saida ta rankwafa sannan ta sumbaci gefen fuskarshi.

Hannu yasa ya kama kanta ya sumbace ta a labba sannan yai mata rada a cikin kunnenta. Dariya tai sosai tana girgiza kai.

"Ka tashi nikam muje muci abinci"

"Duk abinda uwargida take so"

Ya fadi da murmushi. Girgiza kai kawai tai ta wuce da wata kaunar shi mai nauyi a zuciyarta.......!

****

Ya rasa abinda yake masa dadi a zuciyarshi. Sam tunda ya koma gida ummie ma da tazo tana tambaya cayai mata ba komai.

Karantar datai baya son surutun yasa taba shi waje. Ya kuma ji dadin hakan ba kadan ba. Wayarshi ya dauko ya nemo number din pha.iza ya kira.

Ringing din farko ta daga hadi da yi mishi sallama ya amsa mata ta dora da fadin.

"Kowa lafiya dai ko yaya haneef?"

"Hmm pha.iza ya mukai dake?"

Ya bukata yana tuna maganar dayai mata tun jiya. Dan saida ya fara kiran abdulkadir mijinta ya roke shi daya barta tazo asibitin yau kamun ma yai mata magana.

Shiru ta danyi kamun ta ciki ciki ta amsa shi da.

"Kayi hakuri yaya haneef. In shaa Allah zan samu lokaci inzo. Kawai zuciyata ce ta kasa hakura wallahi"

Dafe kai haneef yai. Yau yaga rayuwa ba komai bace ba. Yar yarinya ma kenan da bata da wani zunubi mai yawa Allah ya dora mata wannan ina gasu.

"pha.iza kijini. Gabaki daya rayuwar nan bata da tsaho. Mu dukanmu munyi kuskure da muka zabi mu share fu.ad kaman yanda yai mana.

Daya mutu fa? Ban fada miki yarshi bata da lafiya ba? Yar karama ce. In kika ganta zaki sota sai dai cancer take fama da.

Allah baiyi rayuwarta zatai tsayi ba. Fu.ad na bukatar soyayyarmu ne ba fushin mu ba pha.iza.

Dan Allah ku yafe mishi yaji da abu daya"

Yana jin yanda ta amsa da

"In shaa Allah"

Dakyar sannan ta kashe wayar yasan kuka take. Sauke wayar yai yana tunanin yanda rayuwa zata iya birkice maka cikin kankanin lokaci.

****

Tunda Ansar yazo suke zaune su duka hudun a falon an rasa wanda zai fara magana.

Nufin safiyya su dukansu in Nana tana ganin su zasu iya comforting din ta. Amman abin ya gagara. Rashin iyayenta zafin shi dabanne a zuciyarta.

Bata san asalin ciwon da zuciya zata iya ji ba sai yanzun. Tasan babu wanda zai fahimce ta sai wadda tasan dadin haihuwa.

Sai wadda tasan me rayuwa da d'a yake. Dan daka raina har tsayin shekara goma sha daya. Ki jariri ne ka rasa hakan nada ciwo sosai balle wanda irin wannan shakuwar ta shiga tsakaninku.

Mikewa daga kan kujera nana tai inda take zaune kusa da fu.ad. Yana kallonta ta taka har ta karasa inda sofi ke zaune kan kafet tayi shiru.

Zama Nana tayi ta na matsawa sosai kusa da safiyya. Hannuwanta ta bude ta rungume ta. Sosai ta matse sofi a jikinta.

Wani irin kuka marar sauti ne ya kwace ma sofi. Ita ya kamata tai ma Nana wannan bawai ita ta lallashe ta ba.

Tissue din dake hannun ansar yasa yana goge idanuwanshi da yake jin sun kawo hawaye.

Bazai manta shekaru hudu Kenan da kaddara ta hadashi da safiyya. Taje neman aiki a company din da yake aiki.

Tun daga ranar ta shiga zuciyarshi. Hakan bai karu ba sai lokacin dayaga Nana. Itace sanadin shakuwar su da safiyya har yaji labarinta.

Nana ta hadasu. Bazai manta yarinyar ba da lafiyarta. Yarinyar da duk wanda zai ganta sau daya zai jima bai mantata ba.

Bazai manta shekaru biyu da sanin su dayai ba Nana ta fara wannan rashin lafiyar. Yana tare dasu a duk lokacin nan.

Duk da bai aure da wuri ba. Kuma matarshi har yanzun Allah bai azurta su da samun haihuwa ba tun bayan barin datai bai hana shi jin nana kamar yarshi ba.

Yana kaunar yarinyar har ranshi. Kuma ko shi yasa rai da samun lafiyarta. Sai yau din nan da safiyya ta fada mishi.

Sosai abin ya tabashi. Yanzun kam ganin yanda suke manne da juna da safiyya ya kara karyar mishi da zuciya sosai.

Fu.ad kallon su yake. Yana kokarin tarbe nashi hawayen. Zai zama strong for Nana. Ta roqi hakan daga wajen shi. Bai gaba ganin yarinya mai karancin shekaru irinta ba tunda yake.

Duk dai bawai yaga yara da yawa bane. Yana jin ita din ta dabance ba kuma dan tana jininshi ba. Ansar yake kallo yanda gabaki daya ya birkice.

Sai yanzun yaga tsantsar kaunar da yake ma Nana. Kuma zuciyarshi ba zata taba manta wannan ba. A hankali nana ta janye jikinta daga na safiyya.

Tasa hannu tana goge mata fuska. Kamun ta mike. Wajen Ansar ta nufa da yake kan kujera a zaune. A tsayen da take ta bude hannuwanta shima tai hugging dinshi.

"I love you. I love you so much uncle Ansar"

Take fadi cikin Kunnuwanshi. Kai kawai yake dagawa yana riketa a jikinshi a hankali.

Saboda yanajin kalar ramar datayi ta cikin rigarta. Ji yake daya matse ta sosai zai iya karyata. Dagota yai ya sumbaci goshinta da kuncinta kamun ya sake riketa a jikinshi.

Magana tai mishi cikin kunne yanda shi kadai zaiji.

"Can you do me a favour?"

Muryarshi a dakushe shima cikin rada yace.

"Ko menene ki fada nana"

Sai da ta sauke ajiyar zuciya yana ji kamun tace.

"banida lokaci mai yawa. Ina son maida auren su mumy. Kana son mumy kaima ko?

Nasan ba zaka ji dadi ba"

Yar dariya ansar yayi. Tabbas Nana ta koyar dashi abubuwa da yawa. Ciki har da karfin hali. A hankali ya amsa ta da.

"Umm Nana bazan iya da dadynkin nan ba. Na bar mishi"

Dariya tai cikin kunnenshi daya sa shi dariya shima. Tun daga sanda yasan safiyya ya karanci wajen mutum daya take dashi a zuciyarta.

Koda yana sonta dole zai hakura. Kaunar dayake mata yana jinta kamar yar uwarshi ne. Nana ta katse mishi tunaninshi da fadin.

"You are the best uncle Ansar. I love you"

Lumshe idanuwanshi yai. Rashinta zai bar wani waje mai girma a zuciyarshi.

"I love you more princess din mumynta"

Fu.ad kam ji yake daman shi aka runguma haka. Kota ina bukatar lallashi yake. So yake wani ya lallashe shi har sai ya fitar da dukkan ciwon nan da yake cikin zuciyarshi.

Sai yanzun ya fahimci abin da Nana tace da ta fadi mishi tana tsoron mutuwa. Ba tsoro take ji wa kanta ba.

Tana tsoron abinda mutuwarta zatayiwa wanda take kauna. Zai iya rantsewa Nana ta dabance. Komai nata. Maganganunta da hankalinta ya girmi shekarunta nesa ba kusa ba.

Tana tsoron abinda mutuwarta zataiwa mamanta. She is the strongest girl daya taba gani a rayuwarshi.

Yana kallo tana takowa zuwa inda take. Saidai yasan ko zuciyar da take da kwari irin tata tana bukatar tallabi.

Kokarin saka kanshi yake a matsayinta ya kasa gane me zaiji ace yau yasan a hankali a hankali komai nashi na lalacewa.

A lokaci daya kuma yana jin ya kamata ya zama strong saboda halin da zai saka wanda yake kauna a ciki amman ya kasa fahimta.

Harta karaso kusa dashi kirjinshi kaman an kunna mishi wuta saboda zafin da yake masa. Goshinta ta hada dana shi tana tallabar fuskarshi da hannuwanta.

Yasan kwarin gwiwa take son samu daga wajen shi. Duk yanda yake jin kaman numfashin shi zai tsaya bai hana shi yin alkawarin zai zamar mata abinda take bukata ba.

Bashida wani abu dazai bata. Yana jin hucin numfashinta da take fitarwa akan fuskarshi ya ki yarda su hada idanuwa saboda baya son taga raunin da take dashi.

"Nagaji sosai. Bacci nakeji"

Ta fadi muryarta na wani irin sauka kasa sosai. Bashi bane a matsayinta amman a gajiye yake. Saida yasa hannuwanshi ya dorata kan kafadarshi sannan ya mike da ita.

Dakin dayakaita rannan ya nufa. Bai ajiyeta ko ina ba sai kan gadon a hankali. Ya gyara mata kwanciya. Ya zauna gefen gadon.

Idanuwanta ta lumshe ta dora hannunta kan cinyarshi hadi da fadin.

"Dady!!!"

Saida kalmar ta amsa yafi a kirga cikin kunnuwanshi sannan ta samu wajen zama a zuciyarshi. Wani irin abu yake ji da bazai fadu ba.

Sai maimaita kalmar yake yi. Cikin kanshi yana jin tana zama wajaje da yawa. Baisan yana bukatar jin ta kira shi haka ba sai yanzun.

Da sauri yasa hannu yana goge hawayen da yake jin kaman su fito mishi dan baya son ta bude ido tagani. Jin yai shiru yasa ta fadin.

"Zan iya kiranka dady?"

Da sauri yace.

"zan fi kowa sa.a in kika kirani haka princess"

Murmushi tai hadi dayin hamma. Tai shiru yana kallon yanda numfashinta ya canza alamar bacci ya dauketa. Gyara mata hannunta yayi.

Ya mike ya zuba mata idanuwa na wani lokaci. Baya son fita daga dakin yana son ya kalleta sosai. Yaita kallonta kamun tabarshi.

Saidai a yanzun yana bukatar yadan jinyaci ciwukan dake kirjinshi ko dana yan awanni ne. A hankali ya fice daga dakin yana ja mata kofar.

Baisan yana rike da wani numfashi ba sai yanzun ya sauke shi. Inda yabarsu safiyya nan ya same su. Kanshi a kasa ya nufi kofa sannan yace musu.

"Tayi bacci"

Bai jira amsar da zasu bashi ba ya fice daga dakin........!

*#TeamAs*

No comments:

Post a Comment