Thursday 4 May 2017

AKAN SO 40

  *💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ
   

    40

*"Turomun number dinta inba mamanta mamaki"* 😂😂😂
*Wannan maganar make my day.*

*Ayna.u mardiyya (dimples) Allah yabarki da masu kaunarki. Ba saina fadi matsayinki a wajena ba. #ICDWAWFEY*

*Biebie Isa Allah yabar zumunci. You know #AnaTare*

*To the readers ina godiya da yanda kuke biye dani. Da hakuri da rashin update akan lokaci. ILYA😍*

Kwance yake shi kadai a daki. Ya kira number din nuriyya a kashe. Yau kwana uku kenan da rasuwar nawaf.

Bai samu yai magana da ita ba. Yana son yaji yanda take. Shi kanshi dayaga Nawaf na mintina rasuwar ta bala.in tsaya mishi a rai.

Lumshe idanuwanshi yai. Kaman hoton film rayuwarsu ta wani lokaci ta fado mishi.

*Years Back*

Kitson da ake mata tace a barshi haka, zata zo gobe da Safe a k'arasa mata.

Mai kitso tace

"Maman Farhan da kin bari an gama, saura Kadan a gama."

Tace

"Aa, yanzu maigidana ya shaida min yana kan hanyar gida, kar yazo gida ya iske ba na nan, zan dai dawo gobe"

Da sauri ta saka Mayafinta ta fito daga saloon din ta ja Motarta ta nufi gidanta da ke k'asan layi.

**

    Zaune yake kan Motarshi,  Fuskar shi ba annuri d'aure kamar Lion da ya kwana hudu be ci Abinci ba, tana shiga Gidan Gabanta ya yanke ya fadi ganin shi.

K'irkiro Murmushi tayi ta k'arasa gunshi,

"Welcome Dear you are home Already"

mugun kallon da ya jefeta dashi ne ya sa hanjin cikinta kururuwa.

"Daga gidan Uban wa Kike?"

Dankwalin kanta ta zame, Baki na rawa tace

"daga gidan kitso nake, kuma ai na maka text"

Gashin kanta ya damk'a, Ta sandara ihu Zafi ya sa ta kiran sunanshi,

"Muhammad Don Allah kayi hakuri, you are hurting me"

Be saurareta ba ya jata har Parlo inda ya yasar da ita a k'asa kamar Gabage.

Kuka takeyi sosai, ga Zafin kitson ga kuma na jan Gashi, Belt ya shiga Zarowa, ta san dawan Garin, tayi sauri tashi zata gudu ya sa k'afa ya tande ta, ta fadi k'asa, wani ihu ta saka.

Muhammad be ji tausayin ta ba haka ya shiga lafta mata wannan belt din kamar Allah ya aiko shi sai da ya gaji don kanshi kafin ya barta.

****

Straight Islamiyyar su Farhana ya nufa, ya ci ko sa'a sun tashi, dama abunda baya so ya zo yayi ta jira, da gudu ta k'araso gunshi tana fadin

"YaYa Farhan, ina ta jiranka"

Murmushi yayi yace

"Sorry muje Gida"

*

Tana jin dawowar su tayi saurin tashi don shiga dakinta, bata kai ga shiga dakin ba taji Farhana a jikinta.

"Mummy, me ya sameki?"

Rasa abun da zata ce mata tayi, ta fara kame kame.

Daga nesa Farhan ya k'are mata kallo, fuskarta duk bruises ya matso kusa da ita  a nutse yace da k'anwarshi;

"Farhana je ki cire Uniform dinki"

Ba gardama ta dauki jakkarta tayi daki.

"Mummy, Daddy ya sake dukkan ki ko?"

Ta shiga girgiza kai ta rasa ansar da zata bashi, a fusace yace

"For how long zaki cigaba da enduring dukkan da yake miki?"

Jiki a sanyaye tace

"Kayi hakuri, zai bari"

A fusace yace:

"Till when zai daina dukkanki? Sai kin aurar damu? Mummy shekaru na Sha takwas, tun ina Shekara 4 nake ganin yana Abusing dinki, Allah kadai yasan tsawon lokacin da kikayi cikin wannan halin, Mummy put an end to this please.

Ki kai shi K'ara, befi k'arfin Hukuma ba, akwai Agency na Women Rights and Child Abuse, he's been Abusing us all for quiet a Long time, Mummy i hate seeing you like this"

Murmushin takaicin tayi tace

"Farhan i cannot, Ni ba kowa bace face Marainiyar Allah, banda kowa, banda wanda zai tsaya mun, Kai da k'anwarka ne Farinciki na, i can endure all this for you, so everything is going to be fine"

Takaici ya hana Farhan magana, ya saba jin wannan maganar daga gun Mahaifiyarsa, haushi ya sa shi fita daga Parlorn.

****

Wayarshi datai ringing ta katse mishi tunanin da yakeyi. Ya dauko ya duba. Dan guntun tsaki yaja ganin bakowa bane yan mtn ne saikace zasu bashi wata tsiyar.

Mikewa yai da wani nauyi a zuciyarshi ganin lokacin sallah yayi. Yana son yin wani abu wa matan dake cikin rayuwar domestic abuse saidai baisan ta inda zai fara ba.

Da wannan tunanin a zuciyarshi ya fita masallaci.

****

Yana rike da hannu nana da sallama suka shiga babban falon a tare. Momma ta amsa su.

Kwace hannunta Nana tayi daga cikin na fu.ad ta ruga da gudu tana fadin.

"Granny...."

Da fara.a momma ta riko Nana jikinta. Fu.ad kam yarinyar dake zaune kasa tana wasa yake kallo. Ta mishi kyau ba kadan ba.

Karasawa yai yasa hannu ya dauketa ya kwantar da ita kan kafadarshi. Ya hada fuskarshi da ta yarinyar yana rocking dinsu a hankali.

Yanda tai luf yake jin abin har cikin zuciyarshi. Lumshe idanuwanshi yayi yana jin kamshin yar yarinyar da baisan na menene ba. Powder ce ko turare.

Muryarshi can kasa yace.

"Momma babyn wacece?"

Kallon shi take yanda ya lumshe ido yana jijjigasu shida babyn. Ta kalli nana dake jikinta. Gaba daya sai tausayinshi ya cika mata zuciya.

Da sanyin murya tace.

"Arfat. Yar pha.iza ce"

Bude idanuwanshi yai yana ware su kan momma. Zuciyarshi tai wata irin dokawa. Sauko yarinyar yai daga kafadarshi data soma bacci.

Hakan yasata fara kuka. Kallonta yake sosai.  Yar fara ga wasu kumatu. Jijjigata yake taki yin shiru. Ya bude baki zai magana.

Pha.iza ta fito daga hanyar daya san ta kitchen ce hannunta dauke da feeder tana daure murfin.

Tsayawa tai cak. Idanuwanta kan fu.ad. Shima kallonta yake. Wani miyau ya hadiya. Zaka rantse arfat tasan akwai wani abu dake faruwa daya fi kukan da take muhimmanci.

Shiru tayi. Kallonta yake. Kaman ba pha.izar daya sani ba. Tayi girma sosai. Bude baki yai.

"Pha.iza....."

Baima san maganar bata fito ba. Ita dake tsaye daga nesa zata iya karantar sunanta akan labban shi duk da bai fito ba.

Shekaru sha daya. Ya sa kafa ya fice yabarsu batare daya juyo ba. Wani abu ya tsaya mata a wuya. Mikewa momma tayi ta kama hannun Nana.

"Zo muje....."

Ba musu Nana ta mike tana rike da hannun momma. Dan sam bata kuka da pha.iza ba suka nufi sashin momma a tare.

A hankali pha.iza take takowa tana jin yanda idanuwanta ke cika da hawayen dataqi bari su zubo. Karasowa inda yake tayi.

Hannu ta mika zata karbi Arfat. Ga mamakinsu yarinyar kara makale fu.ad tayi. Dariya yai yana bude idanuwanshi.

Kallon arfat pha.iza tayi ta daquna fuska.

"Baki san uncle dinki bai damu damu ba kike makale shi ko?"

Wani abu yaji a kirjinshi da maganarta.

"Pha.iza......"

Ya fadi da wani irin yanayi. Cikin idanuwa ta kalle shi.

"Shekara sha daya. Ko ka dauka weeks ne?"

Ya rasa me zaice mata. Arfat ta karbe daga hannunshi data soma kuka. Ta samu waje kan kujera ta zauna tana lallashinta.

Gabanta ya tsugunna yana wani dafe kai.

"Pha.iza please......"

Sai lokacin hawayen da take rikewa suka zubo. Muryarta dauke da dacin da take ji tace.

"Da sai wani cikin mu ya rasu zaka dawo? Baka taba tunanin ka waiwaye mu ba ko sau daya. Why? Laifin da mukai maka yai girma har haka?

Da bro lukman bai kiraka ba ba zaka taba dawowa ba ko? Ka manta kana da yan uwa? Ko baka sonmu baka tunanin mu muna sonka? Bro ko......."

Hannunta ya kama da sauri yana katse mata abinda tai niyyar fadi. Idanuwanshi ya sauke cikin nata. Yana so taga nadamar dake cikinsu.

Yana so taga yanda girman kaunarsu yake a zuciyarshi kamun yace.

"Ni mai kuskure ne pha.iza banda abinda zan fada. Ki yarda dani da ina da iko dana koma shekaru sha daya na gyara komai.

Ina biyan kuskuren dana aikata da zuciyata pha.iza............ki yafemun"

Hannunta tasa tana goge fuskarta. Ta riga ta yafe masa. Duk da za.a dauki lokaci kamun ta daina jin dacin laifin shi.

Jin tayi shiru ya sashi fadin.

"Ki yafemun. Bance ki manta ba......."

Katse shi tai da fadin.

"Na yafe maka bro. Ka yafemun nima. Dana kiraka. Dukkanmu muna da laifi.

Yan uwantaka abune mai girma. Zumunci abune dabai kamata bacin rai yai sanadin yankewarshi ba.

Daya daga cikinmu ya kamata ya ajiye bacin rai ya nemi daya. Duk bamuyi ba.

Yanzun sai mu duba gaba....."

Kai yake jinjina mata alamar duk yaji abinda taje dan yaji din. Baya son ko tunanin abindq zaisa ya nisance su yanzun.

Komawa yai kan kujera gefen pha.iza ya zauna. Arfat take kallo.

"She is so cute......"

Mika mishi ita tayi. Ya karbeta. Hannuwanta tasa tana sake goge fuskarta. Da dan murmushi tace.

"Sauran will love to meet you"

Dariya fu.ad yayi.

"Su nawa?"

"Su hudu...."

Ware idanuwa yayi sukai dariya gabaki daya.

"Akwai kabir da muke kira (Amir)  yana da sunan in-law dina. Sai Yassar da yasir. Ridwan sai arfat gata nan"

Da mamaki fu.ad ke kallonta.

"Kina da twins?"

Ta daga mishi kai. Lokaci daya fuskarshi ta canza. Muryarshi can kasa yace

"Nayi missing abubuwa da yawa......"

Yanda yai maganar ya taba mata zuciya ba kadan ba. Cikin taushin murya tace.

"Make sure bakai missing wani abu ba nan gaba okay?"

"Damn right....."

Dariya sukai gabaki daya. Lokacin da suka ji sallama. Su duka suka daga kansu zuwa hanyar shigowa falon.

Hassan ne. Yana ganin fu.ad yai baya zai koma. Da sauri fu.ad ya mikama pha.iza arfat yana binshi da gudu.

"Hassan......."

Bai tsaya ba. Asalima kara sauri yai batare daya juyo ba. Yana jin takun fu.ad din ya karaso inda yake. Hannu yasa kan kafadarshi yana juyo dashi.

Fuskar hassan babu annuri yace.

"Sannunka"

Yana sake juyawa. Lumshe idanuwa fu.ad yayi. Ya sake juyo da hassan. A kufule yace.

"Hit me! Yell at me in kana so. Buh' for goodness sake ka daina mun kaman baka taba sani na ba"

Ture shi hassan yayi da hannuwa duka biyun hadi da fadin.

"Da gaske baka so? Baka son inayin kaman ban sanka ba? Kasa kafa kabarmu? Ko ance ba zuciya a kirjinmu kaman kaine?

Saboda me zaka dawo kasan ba zama zakai ba. Ka tuna mana yanda muke kaunarka ka sake tafiya ko me?"

Har wani huci hassan yake. Komai na rayuwarshi. Tun tasowarshi duk wani burinshi bai wuce na ya zama kaman fu.ad ba.

Shi kadai yasan abinda tafiyar fu.ad tai mishi. Tai musu gabaki daya. Sosai fu.ad ya kalle shi.

"Babu inda zani hassan. Ba inda zan sake zuwa. Kaima ka yafemun mana ko zan ji sauqi a rayuwata"

Wani kallo hassan yake mishi cike da rashin yarda kamun ya juya. Hannunshi fu.ad ya riko.

"Hassan....."

Juyowa yai ya na zame hannunshi daga na fu.ad murya a gajiye yace.

"Ka kyaleni. Please kabarni kawai....."

Girgiza kai fu.ad yake. Yaga abinda kyaliya tai mishi a baya baya fatan tarihi ya sake maimaita kanshi.

"Ba zaka iya yafemun ba hassan? Zan fahimceka in ba zaka iya ba? Ka fadamun cikin idanuwa sai in sani.

Ka fadamun ba zaka iya sake bani daman zama yayanka ba."

Girgiza mishi kai hassan yake fuskarshi dauke da wani yanayi mai wahalar fassarawa. Murya a sarqe yace.

"Kullun har shekara biyu nida hussaina sai mun zauna. Munyi tunanin laifin me mukai maka mu.

Saboda me baka neme mu ba? Laifin abba ne ya shafemu ko me?

Mun kiraka daga farko bama samu. Muka gaji muka daina. Hirarkanma muka bari kaman yanda kaima ka watsar damu.

Kayi hakuri idan bana son ganinka yanzun. Bance bazan yafe maka ba. Amman zaidan dauki lokaci"

Hade hannayenshi hassan yayi waje daya yana dorawa da.

"Please kadan barni tukunna"

Kai fu.ad ya daga mishi badan yaso ba. Badan baiji ciwon maganganun hassan ba. Saidan a kwana biyun nan ya fahimci menene asalin rayuwa.

Ya soma koyan dora bukatar wasu akan tashi. Cikin sanyin murya yace

"Bakomai hassan. Na fahimta koda banso hakan ba. Sai dai ina son kaga Nana.

Inada duk lokacin da nake bukata. Bata dashi....."

Da mamaki hassan ke kallonshi. Dan sam yaki zama ai mishi maganar fu.ad din. Momma ta fara yabar mata wajen saita kyale shi.

"Wacece Nana?"

Dan murmushin nasara fu.ad yai hadi da fadin.

"Muje cikin gida kaganta......."

Ba musu hassan din ya bishi suka koma cikin gida. Tsaye yai bai zauna ba. Fu.ad ya nufi bangaren momma ya taho da Nana.

"Ina su amir?"

Ya tambayi pha.iza.

"Suna gida. Zasu zo muku hutu in sun gama exams ai"

A sanyaye yace.

"Allah ya kaimu"

Dago kan dazai ya sauke idanuwanshi kan Nana. Kallonta yake sosai kamun ya maida kallonshi zuwa kan fu.ad.

Kamanninsu yake gani qarara. Yana tunanin inbai manta ba ance fu.ad bazai iya haihuwa bane ko me? Sanadin hakan ne ma har yabar gida.

Kallon Nana fu.ad yayi yace mata.

"Ga uncle hassan"

Kallonshi Nana take. Ta kallo fu.ad tana ware idanuwa a hankali tace.

"Kuna kama dady"

Murmushi fu.ad yayi.

"He is ma' lil bro"

A hankali ta taka ta karasa wajen hassan. Pha.iza ma kallonta take dan sai yanzun taganta. Labarinta kawai taji wajen su hanif.

Kama hannun Nana hassan yai data miko mishi.

"Ina wuni...."

Shafa kanta yai yana rasa me zaice mata. Gabaki daya abubuwan sun masa yawa cikin kai. Dakyar ya iya ce mata.

"Nana. Zanzo mu gaisa sosai okay?"

Kai ta daga mishi.  Yadan mata murmushi ya saki hannunta yana ficewa daga dakin. Wajen pha.iza Nana ta koma ta gaishe da ita tana tallaban kumatun arfat.

"Ina son kanwa nima. Amman banda ita. Duka yan class dinmu suna da fa"

Kallon fu.ad pha.iza tayi yadan daga mata kafada. Indai Nana ce yanzun ta fara jin maganar da bata da amsarta a bakinta.

Momma ce ta fito daga daki. Fu.ad ya kalli agogon hannunshi ya kalli momma hadi da fadin.

"Yamma nayi momma.  Zamu tafi"

"Dady......."

Nana ta kirashi cike da alamun bata so a tafin. Dakuna mata fuska yayi ta make mishi kafada itama tana daquna tata fuskar alamar bata gaji bafa.

"Ba zaka bari abbanku ya dawo ba. Yana son su gaisa da Nana"

"Zan dawo da ita gobe in Allah ya kaimu. Zata wunin muku anan ma"

Jinjina kai momma tayi.

"Allah ya kaimu. Yar tsohuwa me An dafa miki"

Dariya Nana tayi tace ma pha.iza.

"Anty dan Allah ba granny bace tsohuwa? Kinji wai nice tsohuwa"

Dariya pha.iza tayi.

"Ki kyale granny taga kinfita kyau ne"

Kallon momma Nana tayi tana jijjiga kai alamar kingani nafiki kyau. Dariya ta basu gabaki daya kamun fu.ad yace.

"Taso mu tafi"

Sumbatar arfat tayi a goshi kamun ta mike da fadin.

"Anty zaku zo gobe?"

Girgiza mata kai pha.iza tayi. Langabe fuska Nana tayi.

"A kawo babyn nan to. Ya sunanta?"

"Arfat sunanta. Ai dole ma in kawo miki ita. Kanwarki ce. Kinga in en class dinku sunce suna da kanwa kema kice kannenki da yawa. Su biyar ne"

Rike baki nana tayi cike da jin dadi.

"Suma za.a kawo su?"

Pha.iza ta amsata da.

"Eh suma zasu so suga anty Nana"

Karasawa tai wajen pha.iza tai hugging dinta. Cikin kunne tace mata.

"Nagode anty"

Ta sake pha.iza dake cike da mamakin Nana. Bata taba ganin yarinya cike da kauna irinta ba.

Zata iya rantsewa yarinyar ta dabance a cikin halittu. Jibi yanda ta manne mata a zuciya daga ganinta. Lumshe idanuwanta tayi data tuna abinda ke tattare da Nana.

Tana kallonta harta karasa wajen momma tai hugging dinta hadi da fadin.

"Sai gobe. Zanzo da camera dina muyi video"

Ta saki momma ta ruga wajen fu.ad dake tsaye tasa hannunta cikin nashi. Ya kalli momma da tace musu.

"Ka gaishe da safiyya"

Ya jinjina kai.

"Zataji. Pha.iza sai munyi waya"

Kai ta daga mishi. Yaja hannun Nana datake waige tana daga ma arfat hannu suka fice.

*

Baby dream ya biya da Nana ya shiga kwasar mata kayayyaki daga na sawa zuwa takalma.

Kamo hannunshi Nana tayi ya juyo ya kalleta yana mayar da hankalinshi kan wasu takalma da sukai mishi kyau. Sake janyo hannunshi tayi.

"Dady....."

Dauko takalman yai ya miko mata hadi da fadin.

"Na.am. Sa wannan kigani zai miki"

Karba tayi ta mayar inda ya dauko su. Ya dakuna mata fuska. Ta ware mishi idanuwanta.

"Ya isa haka. Mu tafi gida......"

Girgiza kai yayi.

"Sai mun kara....."

Yana tunanin yanda ya rasa shekaru goma sha daya na siya mata abubuwa. Yasan bazai iya biyansu ba amman yana so ya kamanta.

Sosai Nana ta shagwabe mishi fuska.

"Nagaji dady. Nagaji sosai"

Hannu yasa ya riko fuskarta. Yana feeling goshinta da wuyanta ko da zazzabi. Sauke numfashi yai dayaji babu. Babu shiri yajata da kwandon da suka zuba kaya zuwa wajen biyan kudi.

Tunawa yai da alkawarin dayai ma junior yace ma Nana ta jira shi anan karta je ko ina. Ya koma ciki bangaren kayan wasan yara ya dauko ma junior machine ya dawo.

Credit card dinshi ya bayar dan bashida cash a hannunshi suka cire kudinsu aka daukar musu zuwa bayan mota.

Kiran sallar magrib yaji ya lumshe idanuwan shi. Bude motar yai Nana ta shiga. Yadan tsugunna yace mata.

"Idan nabarki naje nai sallah ba komai?"

Kai ta daga mishi taba lafewa jikin kujerar. Dazun da take cema fu.ad tagaji dan yabar siyayyar da yake yine.

Da gaske gajiyar take ji yanzun. Ko ina na jikinta ciwo yake. Ganin yana tsaye har lokacin yasa tace.

"Really. Kaje ka dawo. I will be okay"

Sumbatar goshinta yai. Ya rufe murfin motar ya wuce masallaci. Acan ya samu buta yai alwala.

*

Sanda ya dawo ya zagaya ya bude motar Nana tayi bacci. Fasa zama yai ya zagayo bangarenta ya dauketa.

Bayan motar ya mayar da ita ya kwantar sannan ya dawo ya shiga ya kunna motar. A hankali yake tuqin dan baya so ya shiga wani rami dazai tsalle ya tashe ta.

*

A kafada ya sabi Nana tana ta bacci. Ya kwankwasa. Safiyya tazo ta bude mishi jikinta sanye da shadda light blue dinkin doguwar riga daya karbi jikinta sosai.

Sauke ajiyar zuciya yai. A dan daburce tace mishi.

"Sannu. Bacci tayi"

Kai ya iya daga mata a yanayin da yake jinshi. Nana tazo karba ya girgiza mata kai.

"Saikin yarda mun yarinya"

Rabata yazo yi. Ta matsa mishi ya wuce tana bin bayanshi.

"Duka Nana din nawa take da bazan iya daukarta ba"

"Oh-Oh yaushe kikai kwarin daukar Nana din? Ke kanki kina bukatar daukar"

Kallonshi take da mamaki. Fu.ad ya rainata. Ya wuce ya kwantar da Nana kan gadon ya cire mata takalma ya gyara mata kwancia.

Zuwa yai ya wuce safiyya ya fice daga gidan. Da kanshi ya shiga kwaso ledojin siyayyar da sukai yana shigowa dasu cikin falon.

Saida ya gama tas. Sannan yace ma safiyya.

"Ki shirya Nana gobe wajen karfe goma zankaita wajen su momma.

Kema ki shirya zamuje wani waje"

Yar dariya tai dake nuna wasa kake ko? Ganin fuskarshi tayi ko murmushi babu. Hakan yasata fadin.

"Wai da gaske kake?"

"Yep"

Ya fadin yana jan P din. Hade fuska tayi.

"Ina da abinyi. Beside banga me zaisa na bika wani waje ba. Nana din dai zan fahimta saboda momma.

Kazo ka dauketa"

Idanuwa ya tsareta dasu dayasa ta fara jin duk ta takura a dake yace.

"Ki shirya karfe goma"

Bai jira amsarta ba ya juya.

"Fu.ad bafa inda zanje"

Ko saurarenta baiba ya fice daga dakin. Ta juya idanuwanta. Taga alama yana jin dadin ganin ranta ya baci. Kayayyakin daya ajiye ya zo ta shiga dubawa.

Kayan sawa ne da takalma lodi guda. Tana mayar dasu kaman daga sama taji Nana na fadin.

"Mumy....."

Juyawa tai takalli Nana dake murza idanuwanta da hannu.

"Ina dady?"

A sanyaye tace.

"Ya tafi ba dadewa"

Dafa kafadar safiyya tayi ta zagayo tana zama.

"Bacci nakeji"

Ta fadi. Murmushi safiyya tayi.

"Baccin kike ai kika tashi Nana"

Muryarta cike da baccin da takeji tace.

"Banyi sallar magrib bafa. Kuma ga isha.i"

Dan shiru safiyya tayi.

"Tam tashi maza. Kiyi sallah saikizo ki ci abinci kisha magunguna ki kwanta"

"Naci dambun nama wajen granny. Banajin yunwa"

Jinjina mata kai safiyya tayi tana maida hankalinta kan kayan dake baje falon.

"Sunyi yawa ko?"

Nana ta tambaya a sanyaye. Shiru safiyya tayi bata san amsar da zata bata ba. Ta dora da fadin.

"Wasu ma bazan saba. Na kasa fada mishi ne saboda naga yanata so ya saimun.

Wai zamu koma a kara. Mumy ko zaki fada mishi sun isa?"

Hannu safiyya takai tadan ja mata hanci saboda yanda take jin idanuwanta na cika da hawaye da gaskiyar maganganun Nana din.

"Oya tashi muje tare. Nima banyi sallar isha.i ba"

Mikewa Nana tayi.

"I love you mum"

Murmushi safiyya tai mata. Suka shiga bedroom din tare.

*

Ja musu bargo safiyya tai tai musu addu.a cikin sanyin murya Nana tace.

"Mumy in roke ki wani abu"

"Kome princess ke so"

Cewar safiyya. Sauke numfashi Nana tayi.

"Bana so in bata miki rai. Kimun alkawari zaki duba magana ta. Ba zaki ji haushina ba"

Da mamaki safiyya tace.

"Nana ki fadamun. Komenene zan duba in shaa Allah"

Juyawa Nana tayi ta fuskanci safiyya sosai.

"Ki auri dady. I mean ki sake auren shi please......"

Wata irin dokawa zuciyar safiyya take yi. Ga kanta da ya sara. Bata taba tunanin wannan rokon daga wajen Nana ba. Ta sake aurar fu.ad?

"Na fada mishi. Yace bashi da abinda zai baki. Nana  bangane ba amman yana sonki sosai mumy.

Please indai zaki aure shi yace zai aureki......"

Katse ta safiyya tai da fadin.

"Nana!  Kinma fu.ad magana?"

A tsorace Nana ta daga mata kai. Tana sake ware idanuwanta kan safiyyar.

"Kiyi hakuri mumy. Please karkiyi fushi. Kawai bana so in tafi inbarki ke kadai.

In da dady zai kula dake. Bana so in barki ke kadai. Bana so......"

Kamota safiyya tai jikinta ta rungume gam. Cikin kunnenta take fadin

"Shhhhhhh......waye yace zaki barni?"

Kuka nana take jikinta har rawa yake. Sai kokarin maida numfashi take.

"Please mumy zaki aure shi?"

Ba zata iya fadin abinda take ji ba. Abinda tambayar Nana take mata. Yanda zuciyarta ke mata wani irin ciwo.

Dakyar ta iya fadin.

"Kiyi bacci Nana. I love you..."

"Mumy please"

Cikin son Nana tai shiru safiyya tace.

"Okay. Okay naji zan duba okay?"

Dariya Nana tayi ta sumbaci kumatun safiyyar kamun ta zame jikinta ta kwanta sosai.

Bata jima ba bacci ya dauketa. Safiyya kam juye juye kawai take. Ta rasa kalar tunanin daya kamata tayi......!

****

Yana shiga gida ya ajiye mota baima karasa ciki ba ya juya ya fice dan yanajin ana kiran sallar isha.i.

Yana kan hanyar dawowa daga masallaci ne yaji wayarshi tai kara alamar text ya shigo.

Ya bude:

"Kurna babban layi. Layin birji gida mai number 85"

Murmushi ya kwace mishi. Fita yai daga text din yasa wayar a key ya mayar aljihunshi. Hamdala yake ma Ubangiji da ya bashi wannan Nasarar har yakai gida.

Ya taka kafarshi zuwa cikin falo yaji ance.

"Kaji...."

Juyowa yai. Hassan ne a tsaye duk ya daburce.

"Hassan lafiya dai ko"

Hannunshi yasa cikin sumar kanshi ya yamutsa. Kamun ya dauko wayarshi dake cikin aljihu.

Fu.ad na tsaye yana kallonshi. Dan yatsa hassan ya daga mishi alamar minti daya.

Dan daga mishi kafada fu.ad yayi. Yana kallonshi yana latsa wayar ya kara a kunne nadan wani lokaci kamun yace.

"Hussaina gashi nan........."

Wayar ya mika ma fu.ad yai tsaye. Karba yai ya kara a kunne hadi da fadin.

"Hello....."

Cikin sauri yaji muryar hussaina na fadin.

"Me yasa ka tafi bro. Nayi kewarka sosai. Kayi hakuri ban maka magana ba a asibiti. Ina fushi ne kawai shisa.

Amman zanzo. Zamu zo nida hamza yace zai kawoni"

Yar dariya fu.ad yai hadi da fadin.

"Lil sis...... Breathe... Yanzun nan"

Yana jin dariyarta kamun tai shiru tana maida numfashi. Har ranshi yake jin kaunar hussaina.

Banda su abbah yafi kewarta akan kowa. Kaunarta dabance a wajenshi. Cikin serious magana yace.

"Ki yafemun kanwata. Nayi kewarki da yawa. Na muku laifi babba. Ki yafemun dan Allah ki........."

Katse shi hussaina tayi da fadin.

"Na yafe maka bro. Tuni fa. Kawai ina danyin fushi ne daman....."

Wani numfashi mai nauyi fu.ad ya sauke yanajin kaman an sauke mishi katon lodi dake kanshi.

"Ki kula da kanki sosai kinji."

"In shaa Allah kaima haka."

Katse wayar tayi. Ya mika ma hassan da wani irin yanayi cikin idanuwanshi. Tsaf hassan ya karanci rokon da fu.ad ke mishi.

Ya kara damke fuska ya karbi wayarshi. Yana kallon yanda fu.ad ya wani langabe fuska ya na juyawa.

"Bro......"

Hassan ya fadi. Da sauri fu.ad ya juyo fuskarshi na tambayar hassan ko da gaske ya kira shi da bro. Kaman yana son amsa tambayar dake fuskar fu.ad yace.

"Bro...."

Rike fuska fu.ad yai da Hannuwanshi duk biyun cike da jin dadi.

"Nagode hassan. Nagode sosai"

Dariya hassan yai hadi da fadin.

"We are good tun dazun. Kawai nabarka ne kadan kara sweating kadan"

Ya karasa maganar yana kashe ma fu.ad ido. Duka fu.ad yakai mishi ya kauce yana dariya. Girgiza kai fu.ad yai ya shige cikin gida.

*

Saida suka ci abinci dasu abbah ya shiga dakinshi ya watsa ruwa ya fito. Ji yake gabaki daya ya gaji. Ya dan kwanta.

Da yana son zuwa yakai ma junior machine dinshi bayajin zai iya. Bacci kawai yake so yayi.

Wayarshi ya dauko ya kira lukman suka gaisa.

"Da gidanka zanzo yanzun fa"

Lukman ya amsa shi da fadin.

"Yawwa ina jira"

"Na fasa ai. Jikina ciwo fa. Zan kawo ma junior machine dinshi ne daman. Ko zaka zo ka karbar mishi?"

"Waye? Tab! Bamai fito dani da daren nan"

Dariya fu.ad yayi.

"Sai ni ne zan fito ko? Hmm. Ka shafamun kan junior. Ka gaishe da madam"

"zasu ji in shaa Allah...."

Lukman ya amsa kamun suyi sallama ya kashe wayar. Gyara kwancia fu.ad yai.

Addu.a yai ya lumshe idanuwanshi. Saidai ga mamakinshi. Babu abinda ke mishi yawo banda fuskar safiyya.

Hakan ba bakon abu bane. Saidai tun randa ya sauke idanuwanshi kan Nana bashida tunanin komai sai nata. Yauma yana tunanin safiyya data addabe shi nada alaqa da rokon da Nana tai mishi.

A haka bacci ya dauke shi........!

*#TeamAS*

No comments:

Post a Comment