Thursday 4 May 2017

AKAN SO 24

 *💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ
    

            24

*To MRS.DOUCHE aka dimples*

"Mama na da karamci sosai"

Safiyya tace masa muryarta da wani sanyi. Wani murmushi yayi. Yana so a yabi momma.

"Momma bata da matsala sofi. Ni nasan zata soki daman"

Langabar dakai tayi kawai. Tana tunanin randa nata iyayen zasu so fu.ad.

Ita kanta a yanzun bata san matsayin nata son a wajen su ba ballantana tayi tunanin zasu so fu.ad.

Hannunshi taji kan nata. Ya riko hadi da dumtsewa. Bata san yanda yake gane tana bukatar hakan ba.

Idanuwanshi nakan tuki yace mata.

"Muna cikin wannan tare. Ni da ke. Komai zaiyi daidai"

Nashi hannun ta sake dumtsewa tana jin laushin hannun da wani dumi dake ratsa ko ina nata.

A hankali ya zame hannunta daga cikin nashi ya ci gaba da tukin da yake yi.

*

Gidan take ta kallo. Bai kai na hotoro girma ba. Daga wajen kawai zata iya gane hakan. Amman ya fishi kyau.

Fu.ad ya karasa yaje ya bude sannan ya dawo ya bude bayan motar yana fito da kayan abincin da momma ta jibgo musu.

Kwalin taliya safiyya ta dauka. Fu.ad ya wani fito da idanuwa.

"Sofi ajiye da nauyi"

Dariya tayi tace mishi.

"Zan iya dauka ai"

Kallonta yake harta shiga dashi cikin gidan. Tsayawa tai tana jiran fu.ad ya shigo taga inda zasu kai kayan.

Kitchen ya nufa tabi bayanshi. Haka tare suka dinga dibar kayan suna kaiwa. Saida suka gama tsaf sannan ya bude lockers din kitchen din suka jera komai.

Haka kayan kitchen din da suka siyo da pha.iza suka jera inda suke sonsu.

Kallon safiyya yai. Da hijab din jikinta take ta aiki. Ko zafi bata ji. Bai dai mata magana ba.

Wayarshi ya dauko cikin aljihu ya duba. Hudu daura minti biyar. Yadan ware idanuwanshi yana fadin.

"Muje muyi sallah sofi. Lokaci yayi"

Bata ce komai ba suka wuce tare har bedroom din. Shi ya fara shiga ya fito sannan ta shiga itama tayo alwala.

Fitowa tai ta same shi cikin dakin.

"Ba zakaje masallaci ba?"

Ta bukata. Ya girgiza mata kai tafe da fadin.

"Lokaci na tafiya. Gashi ban ma san inda zan gano masallacin ba"

Kai tadan daga alamar ta fahimta. Kan kafet din dakin yaja musu sallar la.asar.

Bayan sun idar suna zaune shiru. Can ya nisa yace

"Gobe in Allah ya kaimu zamu je makaranta"

Cikin idanuwanta ya fara ganin murmushin kamun ya bayyana a fuskarta.

Wani irin squeezing yaji zuciyarshi tayi da rabon dayaji shi tun farkon ganin shi da ita.

"Allah ya kaimu goben"

"Amin sofi"

Shiru suka sakeyi. Dan kalamanta nemarsu take ta rasa inya zuba mata idanuwan nan nashi.

"Kinsan yunwa nakeji. Cikina kaman banci komai ba"

Dariya safiyya tayi. Tana mamakin inda fu.ad ke kai abinci. Hakan ya karanta a fuskarta ya sake cewa.

"Ki shirya girki da yawa sofi. Ina cin abinci sosai sosai"

Murmushi tayi ba zatai masa karya ba dan haka tace.

"Gashi ban iya abinci masu yawa ba.  Banma iya duk kalar wanda naga kaci ba"

Jinjina kai yayi hadi da fadin.

"Sai ki koya. Akwai makarantu na koyan girki. Sai in kaiki"

Kallon shi tadanyi. Yana son saukaka mata komai. Wani sonshi ya cika mata zuciya.

"Nagode sosai"

Girgiza mata kai yayi.

"Ni da za.a dafama ai nine da godiya"

Tunawa tai tana son ya koya mata yanda ake tura sako a wayarta. Mikewa tai ta wuce falo yana binta da idanuwa.

Wayar ta dauko ta dawo ta zauna inda ta tashi.

"Ina so fa ince ka koyamun tura sako na manta"

Da fara.a a fuskarshi yace.

"Dawo nan to"

Yana nuna mata gefenshi. Matsawa tai ta zauna inda ya nuna mata. Tana jin har kamshin turarukanshi cikin hancinta.

Wani numfashi ta ja ta fitar dashi. Kallonta yai sosai. Muryarshi na sauka kasa sosai yace.

"Ya dai?"

Kai ta girgiza masa. Wayar ya karba daga hannunta ya shiga nuna mata yanda zatayi.

Sannan ya mika mata yace tayi. Yanda take duba keypads din kamun ta danna ya sa shi bushewa da dariya.

"Sofi........."

Dariya yake sosai.

"Awa nawa zakiyi kamun kiyi layi biyu"

Itama dariyar tayi. Ta mika masa wayar.

"Jeramun ABCD din su koma dai-dai"

Dariya ya sakeyi. Ganin fuskarta da gaske take ya jera mata su koma dai dai.

"Haka suke ai sofi"

Girgiza masa kai tai tana sake duba keypads din wayar sannan ta kalle shi tana wani dakuna fuska.

"Ba daidai suke ba. Duba kagani"

Kara matsawa tai sosai kusa dashi ba tare data kula bama.
"Kaga A anan ko. To kallininda B take fa. Nace maka nawa ba dai dai suke ba"

Dariya yake.

"Sofi please. Sai cikina yayi ciwo?"

Dariya tadanyi. Ita kam bata gane wannan malatsai ba. Karbar wayar yayi daga hannunta.

"Haka suke na kowanne waya sunan su qwerty......."

Jinjina kai tayi. Bata dai ga dalilin dazai sa a jirkita abu ba ga yanda yake.

Hannu ta mika tana karbar wayarta daga hannunshi. Ya rike hannunta. Tsayawa tai tana kallonshi.

Wayar ya karba ya ajiye gefe ya kamo dayan hannunta ya saka nashi yana ware tafin hannunta.

Dogayen yatsunta sun masa kyau sosai. Hannu daya ya kama da nashi duk biyun yana kallon kunshin ta.

Bai taba sanun yana son kunshi ba saida yaganshina hannunta.

Gaba daya jikinta yayi wani dumi. Idanuwanta nakan nashi hannayen. Zoben dake jikin hannunshi na haggu take kallo.

Fuskarta ya kalla kamun yabi inda idanuwanta suke kafe.

"Haneef ya saimun....."

Maganar dayai ta sa safiyya dago da kai ta kalle shi.

"Zoben da kike kallo. Shi yaban gift dana cika shekara sha takwas"

Kallon zoben ta sakeyi kamun a hankali ta furta.

"Yana da kyau sosai"

Zoben ya sake kallo yasa dayan dan yatsan shi yana murza shi.

"Ban taba cirewa ba tunda na saka"

Ta kula akwai kauna mai girman gaske tsakanin shi da haneef da lukman. Duk da ya fada mata basu hada jini da lukman ba.

Zata iya ganin baya banbanta su da haneef. Kusan waje suke a zuciyarshi. Cikinshi yaji yayi kara alamar yunwar dayake ji.

Hannunta ya ja zuwa cikinshi yana dakuna fuska. Dariya tayi jikinta da wani nauyi na daban.

Sakin hannunta yayi yana mikewa.

"Tashi mu siyo abinda zamuci. Mun huta kingani"

"Daka barni kaje ka dawo"

Tunda ta bude baki yake girgiza kai.

"Tashi. Ina zan barki babu mai gadi babu komai. Tashi mana"

Mikewa tayi dole suka fita tare ya kulle gidan. Bama suyi nisa ba yaga wani karamun bakery ya tsaya sukai siyayyarsu anan suka koma gida.

Suna shiga yaji kaman kiran sallar magrib. Saurarawa yayi ledojin ya mikama safiyya yana fita harabar gidan da sauri.

Kiran sallah ne aikuwa. Ciki ya koma yayo alwala ya fito falo ya sameta a zaune.

"Taso ki kulle kofar. Karki bude in bakiji muryata ba"

Kai ta daga masa da murmushi a fuskarta. Yanda yake mata bayanin zaka rantse yar shekara takwas ce ko kasa da haka zai bari cikin gidan.

Itama alwala taje tayi. Falo ta dawo tai sallar anan dan kar fu.ad ya dawo yaita kwankwasa wa bataji ba.

Nan tai zamanta tana danne danne waya. Ta shiga nan ta fito. Gani tai ya dade sosai bai dawo ba.

Ganin karfe takwas harda kwata ya sata tashi tai sallar isha.i tana idarwa taji kwankwasa kofa.

Da sauri taje ta bude. Fuskarshi a hade yace.

"Haka nace fa in bakiji muryata ba karki bude"

Dariya tadanyi.

"Ai nasan babu wanda zai kwankwasa sai kai shisa"

Sake bata fuska yayi hadi da fadin.

"Still. Ki tambaya waye kamun ki bude"

Ta amsa da

"In shaa Allah. Kazo kaci abincin tun dazun kake kiran yunwa"

Karasawa yai. Ta dauko ledojin ta ajiye su a gabanshi. Bude musu yai. Shawarma ya fara ci.

"Kici sofi"

Kai ta girgiza masa tana daukar burger. Abinda zata iya ci tun daga idanuwanta zata iya gane shi bama saita wahalar da harshenta ba.

Dibowa yai da cokali.

"Sai kin tasting fa. Ina kallon ki shekaranjiya ma...."

Janye fuska tayi tana girgiza masa kai.

"Bazan iya ci bane"

"In baki dandana ba ya za.ayi ki gane ko da dadi ko babu"

Hannunshi ta kama ta karbi cokalin. Dakyar ta hadiye tana wani yamutsa fuska daya bashi dariya.

Sosai ya ci komai ya sha exotic. Yai hamdala ya na komawa kan kujera.

Dakyar ta cinye burger din hannunta. Ruwa ta dauka ta bude tasha. Fita fu.ad yayi yai addu.a yasa ma gate dib mukulli.

Sannan ya dawo cikin gidan ma yai addu.a ko ina tana kallonshi sannan ya sa mukulli ya kulle ya zaro shi ya karaso ya ajiye kan kujera.

"Taso muje muyi wanka mu kwanta. Nagaji ko banyi bacci ba so nake inji ni a kwance"

Binshi tai har bedroom din. Saida ya bude jakarshi ya dauki wata T-shirt marar nauyi da gajeran wando sannan ya shiga wanka.

Bai wani dade ba ya fito sanye da kayan daya dauka. Kallo daya safiyya tai masa bata kara na biyu ba.

Wata kunya ta lillibeta ga wani dokawa da zuciyarta ke mata.

Wucewa tayi ta shiga wanka itama.  Ta fito yana zaune kan gado ya kalleta.

"Rigar nan tayi girma. Ya zaki iya bacci a ciki. Ki dauko wani marar nauyi"

Ita kanta tana jinjina kwanciya cikin rigar. Jakarta ta bude ta dauko atamfarta data zo da ita.

Fu.ad ya lumshe idanuwanshi ya bude su. Tana bukatar abubuwa da yawa.

Saukowa yayi. Ya bude jakarshi ya dauko mata wata riga loose ya mika mata. Karba tayi ta koma bandakin ta daura zaninta.

Ta saka rigar da ya bata. Tsahonne kawai yazo mata jar wajen cinya. Amman rigar tadan kamata.

Kunya sosai ta keji tun kamun ma ta firo daga bandakin. Dadi taji data fito hankalinshi nakan wayarshi.

Da sauri ta samu waje kan gadon ta dayan gefen tahau. Shikam fu.ad text yaima pha.iza na list din abubuwan da zata kara cikin wanda safiyya ke bukata.

Kafafuwanshi ya hawo da kan gadon. Wani shagwabe fuska yai kaman zai kuka. Dazun da suka siya zannuwan gado shaf ya manta da blanket.

Safiyya ya kalla fuskarshi a shagwabe.

"Babu abin lillibewa. Ko muje gida mu dauko"

Kallonshi tai sosai.

"Dare yayi fa"

Sake shagwabe fuska yayi hadi da fadin.

"Bana iya bacci inba lillibe kafafuwana ba"

Sauke numfashi safiyya tayi. Mutane kala kala.

"A kware zanin gadon mana. Saika lillibe dashi"

Kai ya girgiza.

"Inba shimfida ma haka bazan iya bacci akan gadon ba"

Lumshe idanuwa safiyya tayi ta bude su kan fuskarshi da ya bi ya shagwabe cike da rikici.

Saukowa tai daga kan gadon.

"Bara in kwaro zanin gadon wani dakin in akwai"

Kallo ya bita dashi harta fice. Yana tunanin gaskiya hada gida yafi komai wahala.

Dawowa tai da zanin gado a hannunta ta mika masa. Ya karba yana yatsine fuska.

"Wannan fa na shimfida ne sofi. Abin lillibewa nake so bashi ba"

Kallon shi take. Rigimarshi na da yawa sosai. Yanzun take ganinta.

"Kayi hakuri da wannan din iya yau kawai. Kawo kagani in linka maka ya kara kauri"

Mika mata yayi. Ta karba ta gyara zanin gadon ta linka shi gida biyu. Inba rigima ma da kaurinshi sosai.

Mika masa tayi. Maimakon ya karba saiya ja jiki ya kwanta yana fadin.

"Ke kikace zaiyi. Saiki rufamun"

Dariya ma ya bata. Lilliba mishi tai taja masa har zuwa ciki sannan ta zagaya ta kwanta gefe.

Addu.a tayi ta tofa. Tana gyara kwanciya. Juyowa yai fuskarshi na kallon tata. Duk da da yar tazara a tsakaninsu.

"Shine ni bakimun addu.ar ba sofi"

Dariya ta sake yi.

"Naga kayi kaima ai"

Wani shagwabe fuska yayi.

"Ni dai kimun. Kuma kin matsa can karshen gado saikin fada. Ki matso kaman zan cijeki"

Shiru tai masa. Inda take dinma duk jikinta a sane yake da kusancin shi balle ta matsa.

Kadan tadan kara jan jiki. Addu.a tayi tadan tofa mishi iskar.

Son jinta yake kusa dashi kaman yay me. Ganin bata da niyyar matsowa ya sashi matsawa sosai gab da ita yana share yanda ta wabi rintse idanuwa.

Peck mai taushi ya manna mata a goshi hadi da fadin.

"Saida safe"

Bata bude idanuwanta ba. Zuciyarta wani irin dokawa take. Tanaji ya kamo hannunta ya rike cikin nashi.

A haka bacci ya dauke su su dukansu.

*

Tana idar da sallar asuba ta shiga bandaki tai wanka. Tunawa tai fu.ad yace karta kara wanki.

Dan haka ta cire kayan jikinta ta linke su ta dauko wata doguwar riga light purple ta saka. Ta koma kan gado tai zamanta.

Bata damu da jimawar fu.ad ba dan ya gaya mata zai motsa jiki koda taga ya dade bai dawo ba.

Kiranshi taji a wayarta. Bata dauka ba dan yace daya zo zai kirata. Tashi tai ta fita ta bude masa gidan.

Duk ya hada zufa. Yana wani maida numfashi yake kallonta ta masa kyau. Kanta daure da dankwalin rigar.

Yana son ganin fuskartan nan fayau haka.

"Sannu"

Ta ce masa. Kai kawai ya iya daga mata yana wucewa ciki.  Kan kujera ya zauna yana kokarin daidaita numfashin shi saboda gudun dayai.

Hannunshi yakai ya bayan kanshi ya taba. Runtse idanuwanshi yai yana cire hannunshi. Ciwon na mishi zafi har yanzun.

Sai lokacin ma ya tuna da wasu su ado da abinda ya faru. Murmushi kawai yayi dan yagama rama abinda sukai mishi tunda ga safiyyar nan zaune a gabanshi.

Saida bugun zuciyarshi ya koma dai dai tukunna ya mike ya tafi bedroom. Wanka yayi ya sakko kaya ya fito.

Kallonshi safiyya take. Wandon jikinshi yaga ce a jiki kusan daga gwiwarshi har kwauri.

Blue ne mai haske sai riga ja a jikinshi. Yayi kyau matuka waje ya samu ya zauna.

Tunda ya tashi cikinshi yake ji wayam ga gudun dayai ya kara kona calories. Wata yunwa ke cinshi. So yake bakwai da rabi tayi su fita gabaki daya.

Baima san makarantar daya kamata yakaita ba. Da yai tunanin yakaita FAAN inda su hussaina suke. Sai kuma ya fasa.

Tunani yazo masa. Yakai ta crescent kawai inda pha.iza ta gama. Ya yarda da makarantar tana da kyau sosai.

"Sofi dauko hijab dinki mu tafi. Sai mu ci wani abu a hanya ko?"

Tashi tayi ta nufi daki. Cikinta a wani kulle. Tunanin komawa makaranta na mata dadi ta wani fannin kuma yana bata tsoro.

Bata san ya zata tsinci kanta a makaranta ba. Gashi ko turanci bata ji. Sai dai ita bamai girman kai bace ta wannan fannin.

Tunda ta dauko hijab dinta take ma kanta alkawarin zata tsaya sosai ta maida hankali kan karatunta.

*

A hanya yai musu takeaway na dankalin turawa da kwai da fresh milk. Ya samu waje yai parking suka ci. Sannan suka wuce.

Tun daga gate din makarantar taji ta karaya. Duk kwarin gwiwar data fito dashi ya kara wargajewa da suka shiga cikin makarantar.

Ga wani irin girma tana dashi. Kayan makarantar kansu abin kallo ne. Sai dalibai ko ina suna kai kawo.

Daka gansu kasan yayan masu hannu da shuni ne. Tsaf dasu. Bata san lokacin da ta kama hannun fu.ad ta dumtse gam cikin nata ba.

Yasan a tsorace take. Hannunta ya rike sosai cikin nashi suka wuce office din principal din.

Saida suka samu wajen zama sannan ya saki hannun safiyya yana maida hankalinshi kan principal din.

Safiyya na zaune tana ta zare idanuwa. Kanta a kasa tana jin yanda fu.ad din suke magana cikin harshen turanci.

Bayanin komai yai masa. Da matakin data tsaya a karatu da kuma cewar bata jin turanci gashi bata da takardu ko daya sai dai ya siya mata na nan.

Shawara principal din ta bashi cewar safiyya ta fara dafa jss1 fur fu.ad yace baisan wannan ba. Baya so ko kadan matarshi taji kaman an rainata.

Kudi shi zai biya. Daga ss1 yake so ta fara. A samu malamar da zai biya ta dinga zuwa gida tana koya mata.

Extra lesson komai da ake bukata dan a taimaka mata. Amman ba za.a nuna an raina karatunta ba.

Shawara ce taba fu.ad yaki ji. Makaranta ce ta kudi. Kuma sune suke magana. Nan take akai masa lissafin komai daga kan kudin makaranta zuwa na uniform zuwa litattafai.

Nan ya biya komai. Da sunce saiya je bank. Ya bada dubu daya yace su aiki wani yakai.

Uniform aka duba kala biyu aka ba safiyya. Tasa wata malama ta rakata inda zata cire na jikinta ta gwada wa.annan.

Kallo daya zakai mata kasan a tsorace take. Saida ta kalli idanuwan fu.ad yadan daga mata kai da cewar babu matsala sannan tabi matar.

Kaman an aunata haka uniform din ya zauna mata. Ta sakko hijab din ta fito. Da kayan data cire a leda malamar ta sakko mata.

Kallonta yake da murmushi a fuskarshi tayi kyau sosai. Yace a kara mata kala biyu uniform din. Ca sukai yabar safiyya sai karfe hudu ya dawo ya dauketa.

Inyaso zasuyi magana kan wadda zata dinga zuwa gida tana koya mata. Gabansu ya kama hannun safiyya ya jata gefe.

Kallonta yai sosai.

"Nasan zaki iya sofi. Karki ji tsoron komai kina jina ko? Ga dubu daya kici wani abu. Ina wayarki"

Mika masa tayi. Ya karba ya kashe yasa a aljihu ya bata dubun.

"Anjima zanzo in dauke ki. Kiyi karatu sosai kinji"

Kai kawai ta daga mishi tanajin kamar karya tafi yabarta. Hannu yasa yadan cupping fuskarta yace mata.

"I love you"

Murmushi tai ta sadda kanta kasa a kunyace kamin ta wuce ta koma inda malamar ke jiranta.

Kara kallonta yai sannan ya fice daga office din.

*

Yana mota ya kira lukman yace masa yana school su hadu acan. Buk ya wuce saida ma yadan jira lukman din ya fito lecture karfe goma.

Mota ya bude ya shiga. Kallon fu.ad din yake ya masa wani haske.

"Ya naga kayi wani fresh?"

Lukman ya tambaya. Dariya fu.ad yayi.

"Bana son iskanci lukman. Sofi nakai makaranta shine na biyo ta nan"

Wani murmushi murmushi ne fuskar lukman.

"Did you?....."

Naushi fu.ad yakai masa a kafada fuskarshi nayin wani ja. Girgiza kai fu.ad yake yi.

"Inalillahi lukman. Kai bakinka bashi da tsarki. Idan nayi ne ma fada maka zan......"

Dariya sosai lukman yai ganin yanda fuskar fu.ad din ke kara yin ja.

"Ashe akwai abinda kake jima kunya?"

Dariya shima yakeyi.

"You are gross lukman"

Tashin motar yayi yana juyata. Lukman dake dariya yace.

"Kai ina da lectures fa karfe sha dayan nan"

Ai kamar ma fu.ad baiji shi ba ya ci gaba da jan motar.

"Da gaske nake maka"

"You are skipping tunda ba test bane. Yawo zamu"

Dariya kawai lukman yayi. Fu.ad rikici.

*#TeamAS*

No comments:

Post a Comment