Thursday 4 May 2017

AKAN SO 18

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

     18

*For those asking. Ina da blog but honestly bana iya managing nashi for now. You can get my stories on wattpad: LubnaSufyan. Thank you for all the support and prayers. Do include a sister Aysher abdullahi in your prayers. May her soul rest in peace. Amin*

Tun daga soron gidan su take jin hayaniyar mutane. Da mamaki tai sallama. Har kasa ta tsugunna ta gaishe dasu, suka amsa.

Mikewa tai ta kasan ido take kallon akwati nan da tasan na lefenta ne. Wani abu ne tsaye a wuyanta da ta kada hadiyewa.

Daki ta wuce. Ko hijab bata cire ba. Bata taba sanin rashin son da take ma Ado yakai haka a zuciyarta ba.

Ta dauka zata iya hakura tai biyayya wa iyayenta ta zauna da ado. Amman yau tunanin hakan kawai yasa numfashinta na wani daukewa.

Wayar dake makale kugunta ta ciro. Ta sa hannu ta shafi screen din wayar. Wasu daga cikin maganganun fuad na dawo mata.

Yakan kirata sau biyune kawai a rana. Da dare sai kuma da sassafe. Daga sun gaisa bata iya cewa komai

Saidai tai shiru tana jin yanda yake gaya mata zai dawo. Kuma zai samar musu hanyar yin rayuwa waje daya.

Sakonni kam saiya turo sunfi goma sha a rana. Haka zata bude taita kallonsu. Fin rabinsu baganewa take ba saboda da turanci yake turowa.

Kalmomin da take tsinta na turanci ba zasu shige goma ba. Inya hada da hausane kawai zata karanta.

Badai ta reply saboda bata iya ba. Inhar tace ga dalilin dayasa take daga wayar fu.ad to tayi karya.

Abu dayane take da tabbaci akai. In har ya kira saita daga. Ko tana cikin su inna ne zata shiga bandaki ta amsa wayar.

Wasu hawaye ne kebin fuskarta tana goge su. Ita kam bata son Ado ko kadan.

*

Tana nan zaune shiru taji alamun mutane na tafiya. Kamun wani lokaci gidan yayi shiru.

Tana jiyo muryar usman da inna suna magana kan lefen cewar ba karamun kokari ado yayi ba.

Akwatina ne hudu. Duk da atamfafin kanana ne sosai. Bakowa ke wannan saar ba a kauyen.

Ita kam bata wani damu da kaya ba. Addu.a take Allah ya bata karfin zuciyar daurewa ayi auren nan ko dan iyayenta.

*

Kaman kullum a kwanakin nan bakwai. Sallama taima su inna ta shige dakinta ta kwanta.

Kiran fu.ad take jira. Yau shiru bai kirata ba. Ba zatace ga adadin lokacin data dauka tana jira ba. 

Sai taji wani irin yanayi mai wahalar fassarawa. Wani daci mai bambanci dana dazun.

Juye juye kawai take baccin yaki bata hadin kai. Ta jima sosai a haka kamun wani wahalallen bacci ya dauketa mai cike da mafarkai.

*

Tun kamun asuba tai wata irin farkawa da batasan ta mecece ba. Wayar ta zaro ta duba.

Ta zuba mata idanuwa kaman fu.ad zai fito ta ciki. Kwancia tai shiru. Kan kunnenta akai kiran sallar Asuba.

Alwala tayo tai sallah. Tana idarwa ta kwashe shimfidarta ta gyara dakin.

Aikace aikacen daya kamata tayi na safe ta gama tsaf. Sannan ta koma daki ta zauna tana jiran kiran fuad dabai shigo ba.

Yinin ranar ji take kaman bata da lafiya. Kaman akwai wani bangare nata dabai cika ba. Saita samu kanta da yima fu.ad addua a duk inda yake ya kasance cikin lafiya.

Ga kwanakin bikinta sun mata tsaye cikin kanta. Duka duka yau saura sati biyu cif.

Dan tun jiya da dare takejin baba nacewa ba zata sake fita ko ina ba. Ko da islamiya ce ma.

****

Matakin rashin kwanciyar hankalinshi ya kara hawa tsakanin jiya zuwa yau da safe.

Ya rasa inda ya yadda wayarshi. Tsakanin wajen training da restaurant din daya tsaya yaci abinci zuwa gida.

*

Wata wayar ya fita ya siya. Ya bada tsohuwar number dinshi aka rufe akai masa wata.

Ko gida bai bari ya karasa ba ya saka number din safiyya yai dialing. A kashe wayar take.

Yasan ko karfe nawa ne lokacin a nigeria. Saidai baisan dalilin dayasa wayarta take a kashe ba.

Kanshi yaji ya soma ciwo na babu dalili. Babban takaicin shi dayane. Hotunan safiyya dayake dasu suna cikin waccen wayar daya yarda.

Gashi yai rashin dubarar saka su a system. Gida ya koma ya rage kayan jikinshi ya kwanta muryarta na masa yawo cikin kai tana rage mishi damuwar dayake ciki.

****

Usman take jira yazo ya karbo mata battery dinta data aika shi yakai chargy.

Daya daga cikin dalilan dayasa take kaunar yaron. Gashi da karancin shekaru amman yana da sirri sosai.

Farkon data bashi yakai mata battery dinta ya tambayeta na wanene. Tace masa nata ne.

Abu daya daya bukata shine inna tasan tana da waya. Ta girgiza masa kai. Bai sake cewa komai ba ya karba yakai mata.

Daga lokacin zai kaimata ya amso mata. Inhar ya sameta da inna baya bata sai su kadai.

Haka yauma yana shigowa ta bashi ashirin yaje ya karbo mata. Dan kudaden makarantarta tara su take. Ita bamai yawan ciye ciyw bace ba.

Battery din ta saka a wayar. Wani sanyi taji da taga sakonnin shi sunata shigowa.  Tasan yana lafiya.

*

Lokacin daya saba kiranta ya kirata yauma. Gaisawa sukai tai shiru. Tanajin yace

"Sofi kinga ban kira ba ko?  Na yarda wayata ne shisa"

A sanyaye ta amsa da

"Allah ya mayar da alkhairi"

"Amin. Barin barki kiyi bacci ko?  Bana so kiyi ciwon kai"

Wani murmushi ya kwace mata. Lokaci daya ya dauke data tuna wannan wayar da suke bata da wani amfani.

Asalima karin matsaloline a wajenta. Ya kamata ace tayi duk wani abu da zai nisantata da fu.ad dan da kusanci da yawan tsanar ado a zuciyarta.

"Dan Allah karka sake kirana. Ina maka fatan alkhairi a rayuwarka"

Da alamun tashin hankali taji yace

"Sofi tsaya..me kike nufi?  Saboda me bazan kiraki ba?  Baki san muryarki kadai ce abinda ke rike mun sauran hankalina ba.

Please karkimun haka...... "

Katse shi tai da fadin.

"An kawo lefe na yau. Sauran sati biyu daurin aurena. Meye amfanin kiran nan da kakemun?

Ka daina daj Allah. Wallahi kana sake rikitamun tunani ne"

Shiru yadanyi kamun yace

"Ba zaki auri kowa ba sofi. Zan dawo kamun lokacin.

Ni da ke are meant to be. Babu abinda zai shiga tsakani kina jina ko?

Kar bakinki ya sake furtamun cewar na daina kiranki. Saida safe"

Kamun tace wani abu ya kashe wayar. Batai kokarin goge hawayen da suke zubo mata ba.

Dan sun dade da kwacewa daga ikonta. Zuba suke duk sanda suka so fitowa.

Duk idan yace ita da shi din nan sai taji wani abu ya yawata mata a zuciya. Tasan babu wani abu wai shi ita da shi.

****

Yau sauran kwana uku kacal a daura mata aure da ado. Saidai babu komai a zuciyarta daya wuce kin auren da fu.ad.

Tun jiya yake kiranta bata dagawa. Saboda bata son yanda kalamanshi suke mata tasiri. Ya turo sakonni sunfi talatin tsakanin jiya da yau.

Duk da inya kira sai tayi da gaske take kin dagawa. Gaba daya ta wani yi zuru zuru. Tun inna na tambaya harta gaji ta kyaleta.

Hidima kawai suke abinsu. Dan ranar ma mutanene cike da gidansu anata hidima za.aje ayi jere.

Su lami da jummai suka kwance mata kai. Ta wanke tas. Jummai tai mata kitso.

Kawai binsu take. Duk yanda sukace mata. Saboda bata da karfin ko yawan magana ma. Su kansu basu dame ta da yawan tambaya ba.

*

Tanajin wayarta na zuu ta sake gyara kwanciya tana wani hade jikinta. Zuciyarta na dokawa da karfin gaske.

Yanda jikinta ke mata har tsoro abin yake bata. Nan da kwana uku ko bata so dole ta cillar da wayar nan.

Ta saba da rashin shi tun yanzun. Tana ta kokarin karyata cewar ta kwallafa ranta akan shi.

Jitai wayar tai shiru nadan wani lokaci kamun taji ta sake daukar view vibrating. Saidai wannan karon na alamar text ya shigo ne.

Wayar ta ciro ta bude. Gajeran sako ne kamar haka.

'Ki na so inyi menene? Na miki wani abu ne?'

Lumshe idanuwanta tai. Hawayen dake son zubowa take kokarin umarta da su koma. Wani sakon ya sake shigowa.

'Yanzun zan taho gida. Kiyi bacci mai dadi'

Wayar ta mayar tana sauke wani numfashi. Baccine ya dauketa cike da mafarkai masu hargitsi.

*

Rashin nasarar wasansu bashi bai dame shi kamar kin daga wayarshi da sofi tayi ba.

Har wani daci daci yake ji. Babu abinda ya tsaya siya. Haka ya dauki jakar system dinshi sai waya da abinda yake bukata yai airport.

*

NIGERIA.

Basu ji wani mamakin ganin fu.ad ba dan suna saka ranshi cikin satin daman.

Daga pha.iza sai momma a gidan. Dan haka suna gama gaisawa yahau sama.

Dakinshi a gyare tsaf. Wanka yai ya shirya kanshi cikin jeans baki da riga simple ja. Gashi ya taje ya fesa turaruka yasa takalma suma jaijaye ya fito.

Lukman ya kira wayarshi taqi shiga. Gidansu ya wuce kanshi tsaye. Hajiyar su lukman take fada mishi yana makaranta.

Bayajin zai iya jiran lukman din dan har wani ihu ihu zuciyarshi take masa.

Daga shi har ita hakurinsu bashida yawa akan safiyya. Balle baiji muryarta ba. Dan haka gida ya koma.

Mukullin mota ya karba wajen momma yace mata zai fita amman bawai jimawa zai ba dan yamma ta fara yi.

Addu.a kawai tai masa ya fice.

*

Tuqi yake. Yanajin zuciyarshi na bugawa har cikin tafin hannunshi saboda wani maiko da suke yi da zufa.

Ac din motar ya duba yaga ko bai kunna ba. A kunne take zufar dayake yi ya daban ce.

Komai da yake ji karuwa yai daya ganshi zai sha corner din da zata kaishi gidansu safiyya.

Inda ya saba tsayawa ya tsaya. Badan komai ba saidan baya son jama safiyya matsala. Baya sonta cikin damuwa dabamai hanashi parking kofar gidansu.

Wayarshi ya dauko yai dialing Number dinta.

*

Zaune suke a daki. Su jummai nata faman hira. Wayarta taji tana vibrating.

Ta lumshe idanuwanta kawai. Tanajin yanda wayar ke wani zuu. Addu.ar duk da tazo bakinta takeyi.

Can wayar tai shiru kamun ta kara daukar vibrating . Danne zuciyarta dake mata ihun ta dauki wayar take tayi.

Sake daukar vibrating tayi a karo na babu adadi. Can tai shiru sai taji alamar sako ya shiga.

Hannu tasa ta lalubo wayar ta gyara zama yanda ita kadai zata iya ganin wayar.

Sakon daya turo ta bude.

'Ina wajen gidanku. Ki zo'

Kamun sakonshi ya karasa isa inda ya kamata a cikin kanta wani ya sake shigowa.

'Wallahi zan karaso idan baki fito ba. Believe me ba zaki so hakan ba'

Wata zufa taji ta lullubeta. Jikinta ya dauki bari. Tasan ba karya yake ba. Karasowa zai gidansu.

Ita yanzun batasan yanda zatayi ba. Wayar ta ci gaba da zuu alamar kiranshi ya shigo. Tasan wannan karin bata da zabi.

Daga wayar tai ta kara a kunne hadi da mishi sallama daya dawo da hankalin su jummai kanta suna mata kallon mamaki.

"Me nai miki?"

Lumshe idanuwanta tai tanajin yanda zuciyarta ke wani numfashi data kwana biyu batai ba.

Har wata iska ta daban taji tana shaka.

"Sofi....ina tsaye tun dazun"

Maganarshi ta dawo da ita hankalinta. Cikin sanyin murya tace

"Kayi hakuri. Bazan iya fitowa ba akwai mutane sosai. Karka sake dawowa. Na fada maka nan da kwana uku aurena kuma.......... "

Katse ta yai muryarshi can kasa dauke da wani irin yanayi da taji ko ina na jikinta yace

"Ion' give a damn da mutanen dake nan sofi. Abu biyu na sani.

Ba a daura miki aure ba. Sannan ina son ganinki.

Idan baki fito ba ni zanzo kofar gidanku ko na shigo har ciki...... "

A tsorace safiyya tace

"Fu.ad........"

Karo na farko da ta dora sunanshi kan harshenta. A zuciyarta take fadarshi ko da yaushe.

Wani abu taji na daban. Tanajin sauke numfashin da yai hadi da fadin.

"Sofi..... Ki fito please. Idan na kara mintina biyar banganki ba zan karaso"

Kashe wayar tai kamun ta amsa. Idanuwanta ta sauke kan su jummai da fuskokinsu ke dauke da tambayoyi kala kala.

"Dan Allah ku taimakamun in fita daga gidan nan. Na yan mintuna banaso kowa ya kula da na fita"

Safiyya tace musu murya na rawa. Jummai ta kalleta sosai.

"Saboda me? Me zakiyi a waje? Dawa kike waya kuma?"

Mikewa safiyya tayi tace.

"Dan Alla ku taimakamun. Wallahi zan muku bayanin duk abinda yake faruwa"

Sai lokacin lami tace

"Ni nasan da akwai wata a kasa. Me zai hana ki fada mana yanzun?"

Jummai ta gyada kai alamar yarda da abinda lami tace. Kallonsu tai idanuwanta cike da hawaye.

"Banda lokaci sosai. Ku taimakamun dan Allah Wallahi zan fada muku.... "

Yanda ta karasa maganar da wasu hawaye da suka zubo mata ya karya musu zuciya.

Mikewa sukai su duka suna tunani. Kamun lami ta basu dabara.

*

Ya kasa tsayawa waje daya. Sai kai kawo yake. Har zuciyarshi yake nufin maganganun daya gayama safiyya.

Inhar bata fito ba zuwa zai. Kome zai faru ya faru bai dame shi ba. Inhar zai ga fuskarta it will be worth kome zai fuskanta.

Hanya yake kallo. Su uku ya hango. Tafiyarta kawai ya gane. Wani lallausan murmushi ya kubce masa.

Ajiyar zuciya ya sauke yana takawa ya suka hade akan hanya. Idanuwanshi kafe suke kan safiyya. Sam baya ganin su jummai da suka zuba masa idanuwa.

Kallonta yake yana cike guraren da sukai kewarta a kwanakin nan. Kanta a kasa tace

"Tunda kaganni ka tafi dan Allah. Wannan ya zama karo na karshe da zaka dawo.

Wallahi zaka iya sakani cikin matsala. Bana son fushin iyayena akanka"

Kallonta yake sosai. Muryarshi da alamar lallashi yace.

"Hey.... Bana nufin na ja miki matsala sofi. Ki fahimceni. Kawai dai ba zaki auri wani bane ba.

Nikuma inyi yaya kenan? In sa kaina ina? Kinsan me nake ki kuwa?"

Jajayen idanuwanta ta dago ta sauke su cikin nashi. Bata da kalaman da zatai amfani dasu.

Kila zai iya karantar halin da take ciki ta idanuwanta. Zai iya ganin yakin da take gabzawa da zuciyarta akanshi.

**

Shi da abokinshi hashimu ne suke tafiya cike da nishadi suke hirarsu. Kamun hashimu yace.

"Ado wata nake hangowa kaman safiyyarka tsaye da wani ko?"

Girgiza kai ado yake da alamun rashin yarda yace.

"Haba dai. Safiyya fa kace."

Da hannu hashimu ya nuna masa su. Wani abu yaji ya tsaya masa a wuya. Safiyya ce kuwa tsaye da wani saurayi.

Da sauri yake takawa ya karasa wajensu hashimu nabin bayanshi.

**

Tsaye suke suna kallon kallo. Kaman daga sama su jummai sukaga ado da har wani huci yake.

"Safiyya me kike a waje? Waye wannan kuma?"

Wani abu taji ya kulle a cikinta. Shikenan abinda take gudu ne ya faru. Dole su inna su sani. Asirinta ya tonu.

Cike da matsanancin tsoro ta kalli ado. A daburce ta soma cewa.

"umm.... Wallahi..... Ado..... "

Fu.ad dake tsaye kallon safiyya yake yanda ta rikice gabaki daya kamun ya maida kallonshi kan ado.

"Waye kai kuma din?"

Ya tambaya yana masa wani kallon wulakanci. Shima adon kallon da yake mayar masa kenan.

"Me kake tsaye da matata?"

Ya tambaya. Wata dariyar takaici fu.ad yake. Me ma sofi zatai da wannan dan kauyen. Kazamin yake tambayar kanshi. A fili kuma yace.

"Ka kama hanya kawai. And kar bakinka ya sake kiranta da matarka"

Ya karasa yana nuna safiyya dake tsaye kamar an dasata. Su jummai kansu baki bude suke kallon ikon Allah.

Cikin bacin rai ado yace.

"Lallai ma. Kaji mun wani karfin hali. Kai asuwa to?  Malam tunda mutuncinka kabar wajen nan wallahi.

Bansan ya akai take tsaye dakai ba. Ba kuma zai sake faruwa ba dan matata....... "

Bai karasa ba ji kake wani tas!  Fu.ad ya kwada masa mari. Ai kam ado ba tsaya jira ba ya kaima fu.ad din naushi a fuska.

Ramawa yai. Hashimu yai kokarin shiga tsakaninsu amman sai fu.ad ma ya sauke masa naushin dayake kokarin kaima ado.

Ko da wasa ba zaka hada girman jiki da karfin fu.ad dana ado shi kadai bama ballantana da hashimu.

Kamun kace wani abu hashimu yai sama da fu.ad ya tiqa da kasa.

Wata kara safiyya ta saki. Shi aka doka da kasa amman ciwon har cikin zuciyarta taji shi.

Dafe fuska tai da hannuwa biyu. Kota ko ina ado da hashimu suke turmusa fu.ad kaman wanda akaima wahayi.

Ganin mutane sun fara taruwa yasa jummai da lami jan safiyya tana turjewa tana wani irin kuka.

Janta suke tana kokarin komawa kaman zata shigar ma fu.ad da yanzun ya daina ma rama dukan da suke masa.

Duk sun fasa masa baki da gefen fuska. Ga shi sun turbuda shi cikin kasa yai futu futu.

Sannan mutane suka fara kula aka taru kansu. Dakyar aka janye ado daga kan fu.ad yana fadin.

"Kai din banza zaka zo har kauyenmu kai mana fitsara.

Wallahi ka sake dawowa sai dai waninka. Safiyya matata ce kana jina!!!"

Wasu ne suka kama fu.ad suka daga shi yana maida numfash. Ciwon dayake ji daban ne dana jikin shi.

Idanuwanshi da guda daya harya soma rufewa da alamar kumbura yake duddubawa baiga safiyya ba.

A firgice yake fadin.

"Sofi......... No.....Sofi......."

Wani mutum ne ya kama shi saboda yanda yaga kaman jini na kokarin dibarshi.

Duba shi yai yaga ya fasa bayan kai. Jini kuma bai bar zuba ba har lokacin. A rikice yace.

"Subahanallah. Dan Allah ku kamashi aje ko chemist ne jini yake zubdawa....... "

Ture shi fu.ad yai muryarshi harta soma canzawa. Hannu yasa ya dafe gefen kanshi yana fadin.

"sofi...... Ta tafi...... "

Wani ya dafa yana tafiya yana hade hanya. Mutane suka kamashi. Kanshi ya saki yana ture su.

Baya son taimakon kowa. Momma yake so. Gida yake son zuwa. Wannan fadan bana shi bane shi kadai.

Dole mutane suka sake shi saboda yanda yake ture su yana fadin.

"Fuck off!"

Wajen motarshi yana nufa. Kanshi ya sake dafewa yana jin wani luu. Da babu motar daya kai hannu jiki daya fadi.

Wani datijjo mai ruwan kamala ya dubi mutanen dake tsaye yace.

"Malam garba ka taimaka ma yaron nan mana. Ko gidansu ya fada a tukashi. Kana ganin yanda jini ke dibarsa"

Dayake malam garba direba ne. Yana jan motoci. Daga shi har datijjon mutanen arziqi ne matuka da ake girmamawa dagani da mutunci a unguwar. Babu musu ya karasa wajen fu.ad.

"Kai kam samari kabari a taimaka maka mana"

Dakyar fu.ad yace

"Ni gida zanje. Kaina...... "

"Sannu kaji. Ka fadamun inda kake sai inje in sauke ka. Ni direba ne"

A yanda yake jinshi kaman ba a duniya yake ba. Yasan bazai iya tuqi ba. Haka ya gayama malam garba inda zai kaishi.

Shi ya karbi mukullin motar. Ya bude ya kama fu.ad ya saka shi a ciki. Sannan ya kalli dattijon dayai magana yace.

"Sai inga wani yazo mu tafi tare. Dan gudun matsala"

Kallon kallo suke an rasa wanda zai bishi dan tunda sukaga motar fu.ad din kowa ya sha jinin jikinshi. Datijjon nan ya taka zuwa inda motar take yace

"Muje..... "

*

Sun nisa sosai. Sama sama fu.ad kejin ringing din wayarshi. Hannu yasa cikin aljihunshi ya zaro wayar da screen dinta ya farfashe.

Kanshi na wani irin juya mishi. Dakyar ma wayar ta dannu ya amsa ya kara a kunne.

"Ina ka shiga haka. Inata kira not reachable"

Dakyar ya iya ce ma haneef.

"Ka so dai dai dawanau. Please ka taho....... "

Cikin alamun razana haneef yace.

"Fu.ad are you okay?"

Da bala.in dauriya ya amsa shi da.

"kazo mana. Ka taho..... "

Yanajin haneef na magana amman bazai iya amsa shi ba
Kanshima wani ciwo yake da duk karar data shiga kunnen shi.

Dattijon dake baya tare dashi ya mika ma wayar da fuska yake rokonshi daya taimaka ya karba.

Karba yai ya kara a kunne hadi da sallama. A razane haneef yace.

"Waye kai?  Me ya same shi ne wai? Kuna ina?"

A nutse ya fara ma haneef bayani da cewa.

"Ka kwantar da hankalinka. Mu taimakon shi mukai. Fada sukayi ne yadan samu raunuka. Kaman yanda yace kazo zamu tsaya dai dai dawanau"

Jin anyi shiru yasa shi mikama fu.ad wayar da yake jingine jikin kujera.

*

"Lafiya wai?"

Momma ke tambayar haneef da duk ya rikice.

"Momma fu.ad.....zan miki bayani...... "

Da gudu ya fita daga falon tana kwala masa kira. A harabar gidan yaci karo da lukman.

"Muje please...... "

Kawai yace suka bude mota. A hanya yake fada mishi iya abinda ya sani.

*

Dai dai dawanau suka hango Range Rover din fu.ad tsaye. Parking yai suka fita shi da lukman.

Wani dattijo suka hango tsaye jikin motar. A kagauce yace

"Yana ina?....... "

Lukman kam baibi takansu ba. Motar ya bude. Hannunshi yakai ya dafe kai. Kwata kwata kamannin fu.ad din sun sauya.

Ga wani numfashi yana ja dakyar. Rasa ina zai kama a jikinshi yai. Dan jinin dayake gani baisan daga inda yake fitowa ba.

Haneef ya zagayo ya ture lukman.

"Ya Rabb......... "

Ya fadi yana zira jikinshi cikin motar ya kamo hannuwan fu.ad ya tallaboshi ya fito dashi.

"Fu.ad......."

Yake kira amman da alamu ma baisan abinda yake yi ba. Daga shi yai cak a kafada ya nufi mota da gudu.

Lukman ne ya tsaya. Ya zaro kudi a aljihunshi ya kamo hannun dattijon nan ya damka mishi hadi da fadin.

"Mungode sosai baba"

Zagayawa yai inda malam garba yake ya karbi mukullin motar dake hannunshi ya ja motar yana bin bayan haneef.

*

Aminu kano suka nufa dashi. Suna karasawa sukai parking.

Haneef ya bude bayan motar. Lukman ya karaso suka tallabo fu.ad.

"Fu.ad....."

Haneef ya sake kira yana taba kumatunshi. Dakyar ya bude idanuwanshi kamun ya sake lumshe su ya wani langabe a jikin haneef din.

Kasa sukai a tare saboda wani nauyi dabai tsammani da fu.ad din yayi.

Lukman ya dafa a rikice yana fadin.

"Call for help........ "

Da sauri lukman ya tashi ya na karasawa cikin asibitin da gudu.

Girgiza shi haneef yake yana fadin.

"Wake up fu.ad.....su waye sukai maka haka?"

Wasu nurses ne suka fito da wheel chair. Kama fu.ad suka saka shi ciki.

Da sauri suka gungura shi. Wata nurse ke cema haneef.

"Ba zamu taba shi ba saida yan sanda gaskiya....... "

Kai kawai haneef ke jijjiga mata. Lukman ne mai karfin halin dauko waya ya kira su momma yake fada musu. Su taho da yan sanda.

Wani numfashi haneef yaja hadi da fadin.

"Am going to fucking end ko waye ya taba fu.ad............!"

No comments:

Post a Comment