Thursday 4 May 2017

AKAN SO 12


*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

          12

"Wani ya sake trying mun number din fu.ad please"

Haneef ya fadi muryarshi a gajiye. Sunkai mintina wajen talatin suna neman wayar fu.ad a kashe.

Lukman na shirin sake dialing kira ya shigo.

"Hamza ne..... "

Yace yana dagawa da fadin.

"Hello ina jinka hamza"

Wani numfashi hamza ya sauke sannan yace.

"Please karka fadama fu.ad. promise me sunana bazai fito ba cikin maganar nan"

A kagauce lukman yace.

"Wallahi bazai taba jin daga bakinka maganar ta fito ba. Trust me nasan fu.ad bazan so saka cikin rikici dashi ba"

Sai da ya dan tauna maganar jim sannan ya nisa yace.

"Ya sani na dauko masa yan sanda har mota uku. To be frank bansan abinda zai dasu kenan ba. Yasa an tattara wata yarinya da family nata sunkai su sha biyu.

Yanzun haka muna dawanau. Mun kusan shiga cikin gari. Please kuzo abin is getting out of hand. Akwai yara kanana"

Haneef lukman ya kalla. Jikinshi ko ina bari yake yi.

"Wallahi fu.ad ne haneef........"

Abinda hamza ya fada masa ya maimaita musu. Daga haneef har pha.iza salati suke.

"Wallahi bansan inda fu.ad ya kwaso wannan halayyar tashi ba. Babban yaya nada zafi amman ba irin wannan ba"

Cewar haneef da yake jin kaman ya juya ya koma wajen zaman makokin shi.

Ya gaji da halin fu.ad da rigingimun shi. Shisa har baya so yace zaizo. In yana can kasar waje hankalinsu kwance yake.

Daga pha.iza har lukman sun kasa cewa komai. Mumyn su kawai taima text cewan tana tare dasu haneef zasu je gida su dawo.

*

Suna zuwa police station din ya tabbatar an tura su cell an kulle gaba dayan su.

Aka dauki statement din shi cewar yana filing charges akan assault. Ya shiga motarshi ya tafi gida abin shi.

Alwala ya dauro ya fito ya tafi masallaci yai sallar magrib. Sannan ya dawo.

Baibi takan wayarshi ba. Yana sane ya kashe ta dan baya son su haneef su dame shi.

Mota yakoma ya dauko sauran burger dinshi da pizza ya dawo babban falo ya kunna t.v yana kallon aljazeera sport.

Kallo daya zakai masa kagane idanuwanshi ne kawai akan t.v din. Sam hankalin shi na wani waje daban.

A lokutta da dama inyai rashin mutunci irin wannan yana bashi wani satisfaction na daban.

Yanajin cewar ya isa. Yanajin cewar an masa ya rama. Sannan bacin ran yakan guje daga zuciyarshi.

Dakyar ya karasa tura burger din ya bi da fresh milk saboda yasan jikin shi na bukatar abinci.

Yana saurin burning calories. Amman yau bayajin yunwar sam. Ga zuciyarshi ta mishi wani iri.

Jikin kujerar ya koma ya kwanta sosai. Ya lumshe idanuwansh. Ba abinda ke masa yawo sai fuskar safiyya da kalar kukan da take yi.

Baisan dalilin dazaisa hakan ya dame shi ba. Kukan ya tsaya masa a rai. Yanayin da yake ji bakon abune a wajen shi.

*

Bayan da haneef bai ba da yan sanda su saki su safiyya amman suka ki sauraron shi.

Sun kuma tabbatar masa inba fu.ad bane ya janye case din da kanshi ko bail ba zasu bayar ba.

Kallon su safiyya yake da suke rakube cikin cell din mata sunata kuka.

Dayan cell din kuma mazane ciki matasa guda biyu duk zasu kai sa.anin haneef din. Sai magidanta.

Haneef ya gane dayan magidancin shine wanda sukai karo da danshi a safiyar ranar.

Ranshi bace yace ma lukman.

"Muje gida kawai. Nasan fu.ad nacan"

Jiki a sanyaye lukman ya bishi suka samu pha.iza zaune cikin mota inda suka barta.

*

Suna parking motar haneef ya bude ya fita. Ko rufe murfin motar baiba saboda ranshi a bace yake.

Ko sallama baiba ya shiga gidan.  A falo yaga fu.ad zaune jikin kujera ya rufe idanuwanshi.

Wani irin kallo yake masa mai cike da fassarori daban daban. In akwai abinda ya tsana a duniya bai wuce wulakanta dan adam ba.

"Fu.ad......."

Ya kira muryarshi can kasa. Sai lokacin ya dago ya sauke idanuwanshi da sukai wani duhu kan fuskar haneef.

"Yanzun zaka kira kasa a sake su. Bana bukatar jin me ya hadaku. I want them out of that hell hole"

Kallon haneef kawai yake. Ya dauke idanuwanshi zuwa kan su pha.iza da lukman da suka shigo dakin da sallama.

Lukman ya karasa inda yake ya zauna. Muryarshi a sanyaye yace.

"Fu.ad bansan meke damunka ba. Me yake......... "

Katse shi yai da fadin.

"Cut it please"

Mikewa tsaye yai ya kalli haneef da har wani huci yake. A hankali ya karasa dab dashi. Cikin fuska ya kalle shi yace

"Ka fita daga maganar nan. Babu ruwanka"

"Wallahi wannan karin abbah zan fada ma. Wannan mugayen halayen naka nagaji da boye su. Dan kana da kudi sai ya zama menene?

Abbah bashi da kudi?  Wa kaga ya taba wulakantawa?"

A tsawace fu.ad yace

"Saboda me zata sa hannu ta mareni?  Wallahi sai marina ya fita a jikin gaba daya yan gidansu"

Pha.iza dake gefe tace

"What? Mari?  Waya mareka bro?"

Hankalinshi ya maida kan pha.iza yace

"Wata kucakar yar kauye. Ta daga kazamun hannunta ta mareni"

Rai a bace pha.iza tace

"Ashe ma sune da laifi. Waye uban ta da zata daga hannu ta mareka"

Kallon haneef yai dake fassara 'kaga ita ta gane karatun. Saura kai'

Muryar haneef can kasa yace

"Bana son jin me ya hadaku. Kawai ina son ka sa a sake su ne"

Kai yake girgiza masa alamar abinda bazai yiwu bane kamun yace.

"Yanda ta mareni saina wulakan ta su sai......... "

Mari haneef ya dauke shi dashi. Daya sa iskar dake dakin kanta ta tsaya.

Hannu yakai kan kumatun shi cike da mamaki. Pha.iza ta rike baki. Lukman kanshi bai taba zaton haneef zai iya marin fu.ad ba.

Cikin bacin rai yace

"Kai harka isa ka wulakanta wani? Me kake dashi?  Nawa ne a account dinka?  Yaushe su abbah suka gama daukar dawainiyarka? Fu.ad kai hankali da duniya wallahi"

Idanuwanshi cike da wasu hawaye daya ki bari su zubo. Hannun shi har lokacin yana kan kuncin shi.

Tun yarinta yafi shakuwa da haneef fiye da kowa. Duk wata rashin kunya. Duk wata fitsara dazaiyi haneef na shanye wa.

Babban hukuncin dazai masa shine yaki kula shi. Ko fada ba ko yaushe haneef yake iya mish ba.

Haneef ya sha hada kudin break dinshi na makaranta ya bar ma fu.ad saboda yai mita nashi sun mishi kadan.

Yau haneef din nan ne ya mare shi saboda wasu talakawa. Ba akan wani abu ba akan yan kauye.

Wani daci yake ji a zuciyar shi. Tunda yake duniya bai san ciwon wani abu ba irin na yanzun.

Baima taba zaton akwai randa zaiji son zubda hawaye kan bacin rai irin na yanzun ba.

Baice komai ba yasa hannu ya zaro wayarshi daga aljihu. Ya kunna ta.

Number din inspector din dayai saving dazun yai dialing. Ringing daya ya dauka.

"Nai dropping charges din gabaki daya. A sake su"

Baima jira amsar dazai bashi ba ya kashe wayar shi. Kusa da haneef dake tsaye yana kallon shi ya karasa.

Saida yasa idanuwanshi cikin nashi yace.

"Bakai karya ba. Ina alfahari da abinda na tara. Saboda kafi kowa sanin bakar wahalar dana sha kamun inje inda nake a yanzun.

Kafi kowa sanin clubs da adadin wasannin danai playing. Kana tare dani a duk zaman asibitin danai in na samu ciwuka.

Kana tare dani lokacin da na fara wasa da kano pillars. Kana tare dani lokacin da mack ya fahimci zan iya zama wani abu.

Kana tare dani a duk wata wahala tawa. Yau kaine ka daga hannu ka mare ni akan wasu banzaye.

Yau kaine hannunka ya taba fuska ta saboda anci zarafina nai kokarin ramawa"

Wani numfashi fu.ad ya dauka kamun ya juya da gudu yahau benen zuwa dakin shi.

Suna jin karar datso kofar dayai kaman maison karyata. Lukman ya tashi ya bishi.

Wani irin kallo pha.iza take ma haneef dake nuna rashin jin dadin abinda yayi.

Muryarshi can kasa yace mata

"What is with the look?"

Kallon shi tai cikin fuska

"Wata ta mare shi kabarshi yaji da abu daya. Ba saika kara mishi ba.

Na yarda yana da halaye marassa kyau. But he is our brother. Na dauka yan uwa suna goyon bayan yan uwansu ne..... "

Hannu haneef ya daga mata alamar tai masa shiru. Saida ta kalle shi na tsayin mintina biyu sannan ta wuce abinta.

Kujera ya samu ya zauna ya dafe kanshi da hannuwa biyu dan baisan me ya kamata yayi ba.

****

"Kukan nan ya isa haka safiyya"

Inna ke fadi ta dora da

"Kije ki kwanta kinji. Komai yazo karshe ai"

Cikin kuka safiyya tace

"Duk ni naja muku inna duk....... "

Baba ne ya katse ta da fadin

"Bakiyi laifi ba safiyya. Nama ga hakurin yunusa dabai masa komai ba.

Ko da yake duniya ce tafi bagaruwa jima"

Tashi safiyya tai ta koma dakin su ta shimfida tabarmarta da zannuwa tasa pillow dinta ta kwanta.

Wani abu ya tsaya mata a wuya. A bangare daban tana jin tsanar fu.ad. Wani bangare kuma dauke da yanayin da bata san fassarar shi ba.

*Washegari*

Jikinta babu karfi tagama ayyukan gidan tsaf. Taja ruwa tai wanka.

Haka tasha tsuran ruwan koko saboda sam bata jin dadin komai. Jikinta saikace wadda zazzabi ke shirin kamawa.

Usman ne ya shigo ya kalle ta yace

"Yaya Ado na kira. Yana waje"

Ji tai yanayin da take ji ya karu. Kallonta ta kaida kan inna da ta kafeta da idanuwa.

Tasan fassarar kallon ta sauke numfashi tace ma usman

"Kace gani nan zuwa"

Hijab dinta ta dauka. Fuskarta a dakune ta fita. Dakyar ta iya mishi sallama.

Yana ganinta ya wani wangale baki.

"Amarya ta nan da wata uku in shaa Allah"

Ado ya fadi yana kara fadada murmushin shi. Abinda ke tsaye wuyanta taji ya kara girma.

Tasan ko sauran kwanaki nawa aurensu ba saiya tuna mata da bakin shi ba.

Har yanzun tana jimamin yanda zata zauna da ado a matsayin miji baya bata son shi ko kadan.

Ko fara.a take taganshi sai taji ranta ya baci. Babu yanda zatayi ne kawai. Dakyar tace masa.

"Lafiya dai ko?"

Ya girgiza kai yace

"Lafiya kalau. Baba ne yake fadamun ashe wani tsautsayi ya fada gida kuma. Shine nace bari kamun in wuce gona in biyo in muku jaje"

"Allah sarki. Aikam mungode sosai. Bara in shiga in fada ma inna sai ka shigo ku gaisa ko?"

Safiyya tace tana koma cikin gida ba tare data jira amsar shi ba.

Bata jima ba ta fito tace masa ya shigo. Cikin fara.a da mutunci suka gaisa da inna yai musu jaje.

Dazai tafi ya kawo dubu daya yaba inna wanda dakyar ma ta karba.

****

Safiyya itace yarinya ta biyu cikin yaya uku kacal da malam audu da zainabu suka mallaka a duniya.

Kasancewar duk yaran da suka haifa har hudu basa shige kwana arba.in a duniya Allah ke karbar abinsa.

Sai akan saminu da shine babba a yanzun. Sai safiyya sai usman.

Da malam audu har zainabu yan nan asalin garin bichi ne.  Mutanene masu karamci da gudun rikici.

Talakawa ne sosai sai dai Allah ya azurta su da wadatar zuci. Duk yan uwan malam audu sun dan fishi dan abin hannu.

Dan shi gonar shi daya yar karama. Ita yake noma yake rufa ma kanshi asiri. Sai dai bai taba damuwa da halin rashi da yake fama dashi ba.

Haka rayuwarsu take tafiya. Saminu kuwa. Yunusa kanin malam audu ya samu yan kudi ya siya mishi babur na hannu.

Yake acaba dashi. Hakan ba karamin rage ma malam audu wahalhalu yai ba.

Domin yanzun haka saminu shi ya biyama kanshi kudin jarabawar aji shidda sakandire. Kuma yake daukar dawainiyar karatun usman.

Duk da saka mata a makarantar boko ba damuwar zuri.ar su malam audu yai ba.

Hakan bai saka shi kin saka safiyya a makaranta ba. Lokacin da tazo aji uku tai jarabawa bataci ba.

Hakan ba karamun damunta yaiba dan har ranta tana da kwadayin karatu. Lokacin Ado dan mai unguwar su ya fara zuwa wajenta.

Kasancewar ya fito daga gida na mutunci gashi yaro mai hankali da girmama mutane. Ya fara ginin shi.

Manyan shi na zuwa da maganar neman auren safiyya malam audu ya amince. Ba a wani saka abin da nisa ba. Wata hudu kacal aka saka.

Abinda ba su sani ba shine biyayya ce kawai ta saka safiyya amsa su lokacin da malam audu yazo da maganar da kuma karin bata kula kowa sai ado din.

Amman ko kadan batajin sonshi a ranta. Duk da bashi da makusa.

No comments:

Post a Comment