Thursday 4 May 2017

AKAN SO 10

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

          10

Baima yi kokarin kula su lukman ba. Kaman yanda basu ce masa uffan ba haka shima.

Har suka kai gida. Lukman yace ma haneef zaije gida ya kira shi in zasu koma.

"Haneef kaban number din mai gyara ma abbah mota"

Ko inda yake haneef bai kalla ba ya wuce ya shiga cikin gida. Wani abu fu.ad yaji ya tokare masa wuya.

Already bayajin dadin komai. Ga yunwa dake damunshi dan cake din dayaci harya kone.

Cikin gida ya shiga. Atika na hango shi ta rakube jikin bango. Kaf yan aikin gidan ya kula dole ke sawa suna haduwa dashi.

Wucewa yai dakinshi yai wanka sosai. Sanda ya fito jinshi yake wani fresh.

Crazy jeans din dai ya sake maidawa blue. Da farar riga data matse shi. Ya feshe jikinshi da collection din turarukan shi.

Dakin haneef ya nufa. Bai damu da yai knocking ba ya shiga. Yana tsaye yana balle links din rigarshi.

Jikinshi sanye da wani yadi ruwan toka. Ya matukar karbarshi.

"Zan fita. Ba nisa zanba abinci zan siyo in dawo"

Ko kallonshi haneef baiba. Zaka rantse ba dashi yake magana bama.

Matsalolin fu.ad yawa gare shi. Yasan gulmace shi bayacin abincin yan aiki. Kara son tabara shi mumy ke shiga kitchen ko su pha.iza a dafa mishi.

Yau ba sa nan yasan hotel zashi ya kaso dubunnai kan abinci gashi a gida.

A kufule fu.ad yace

"What is with the attitude? Tun dazun nake maka magana ka share ni"

Kallon shi haneef yai cikin idanuwa sannan yace.

"Me kake so ince maka? Abinda kake so ba shi kakeyi ba? Meye na neman ra.ayina kuma?"

Kallon shi fu.ad yai na wani lokaci kamun yace

"Kace in dropping case din kuma nayi. Me kake so inyi again?"

Wani numfashi haneef yaja. Karasawa yai inda fu.ad yake tsaye ya sa idanuwanshi cikin na fu.ad.

"So nake kasan darajar mutane fu.ad. Kaima wata rana uba zaka zama. Zaka so a girmama ka"

Wani murmushin takaici fu.ad yai

"Bana girmamaka?  Bana girmama su abbah? And ban taba hango ni da yara ba. Bana son damuwa"

Girgiza kai haneef yai. Rashin hankalin fu.ad yawa gare shi.

"Just get out of my room!"

Lokaci daya yaji bacin ran da yake ta yawo a kasan zuciyarshi ya samu wajen zama.

"Haneef! Ni kake kora daga dakinka?"

Wucewa yai yaci gaba da hidimar shi. Waje fu.ad ya samu kan daya daga cikin kujerun dakin ya zauna.

Wasa yake da zoben azurfar dake hannunshi. Har haneef ya gama shiryawa yana wajen a zaune.

"Ba yunwa kace kana ji ba?"

Haneef ya tambaya. Shiru yai shima. Bai damu da yunwarshi ba ai. Yafi damuwa da yan kauyen nan da bai ga abinda sukai mishi ba zai dora masa laifi.

Ajiyar zuciya haneef ya sauke. Matsala daya da ake samu kenan. Son fu.ad yana hana shi nuna masa kuskurensa. Dama duka yan gidan.

Kan hannun kujerar ya zauna muryarshi a sanyaye yace.

"Ka tashi kaje ka siyo abincin. In kuma ba zaka koma ba mu tafi da lukman"

Dago fuska yai. Ya wani tabare murya.

"Ka damu da yunwar danake jine. Zaka kama mun fada kan yan kauyen nan"

Murmushi haneef yai.

"Sorry okay. Tashi ka wuce. Kai zamanka kawai zamu koma"

Da sauri yace.

"No zan biku nima"

Kawai yaji yana son komawa kauyen. Bakuma yason amsa ma kanshi dalili.

Mikewa yai ya kalli haneef yace.

"We good?"

Daga masa kai yai tare da fadin.

"Yeah we are good"

Murmushin shi da yakan jima baiba yai ma haneef sannan yace

"Barin je in settling da lukman"

"Kaje ka sa abu a cikinka tukunna"

Girgiza kai yai yana bude kofar yace.

"He is more important"

*

Yana shiga gidansu lukman kanshi tsaye ya wuce dakin su lukman din.

Yana zaune yana cin indomie da soyayyen kwai.

Ko sallama bai mishi ba yace.

"Waya dafa?"

Dagowa lukman yai ya kalle shi.

"Shine sallamar ka kenan?  To ban sani ba"

Dariya kawai fu.ad yai.

"Don't be a jerk. 'Mma hungry"

Saida yai kaman bazai amsa shi ba sannan yace

"Ummie nasa ta dafamun"

Bai cire takalmin kafarshi ba ya karasa ya zauna gefen gadon lukman.

Sanin halin shi yasa lukman ya mika mishi plate din duka. Bai musu ba ya karba.

Saida ya cinye duka sannan ya sha orange juice din dake cikin glass cup da lukman ya zuba bai taba ba.

"I am still hungry"

Ya fadi yana yamutsa fuska. Mikewa yai yana fadin.

"We good?"

Kai kawai ya daga mishi. Yasan pointless ne kokarin saka fu.ad a hanya.

Yana kallon shi harya fice daga dakin.

*

Wannan karon fu.ad bai manta komai ba. Zaka rantse wata tafiyar sati biyu zaiyi kayan daya dauka.

Harda toiletries gaba daya. Yaje ya zuba cikin Range Rover dinshi ya kira lukman a waya yace musu sun shirya.

Haneef da lukman suka zauna gaba. Wannan karin haneef ke tuqin.

*

Suna shiga mamansu ya kira a waya shi yana missing dinta.

"Fu.ad anan ka kwana?"

Ta tambaya cike da mamaki. Da fara.a a muryarshi yace.

"Eh momma muna tare harda lukman fa. Haneef yace sai jibi zamu tafi gida har daku"

Dan jim tayi da alama tana tauna maganar fu.ad kamin tace.

"Please banda rigima. Ka zauna tare da haneef throughout kana jina"

Saida ya tabbatar mata zai kiyaye sannan sukai sallama. A mota yake zaune yana cin burger.

Su haneef na wajen zaman makokin. Bama su gayyace. Shi ba.

Wayar shi tahau ihu. Pha.iza ce ya daga yana fadin.

"Sis... "

"Bro namu mu kadai. Kaga white rice suke dafawa cikin gidan nan...."

Kamun ta karasa maganar yace

"Ki fito ki duba zakiga baqar Range dina. Ina ciki"

Bai jira amsarta ba ya kashe wayarshi. Yana nan zaune pha.iza ta fito.

Leda daya ya bata. Ta juya abinta. Kulle motar yai ya fito batare daya san inda zashi ba.

Headphones dinshi ya kunna wakar Drake-child's play. Ya ci gaba da tafiya zuciyarshi na masa jagora.

Dan bama ya kula da inda yake saka kafarshi. Gaba daya tunaninshi yana wani waje da baisan ko ina bane.

Kanshi a kasa. Hannuwanshi na cikin aljihun hoodie din daya dora da zasu fito bawai don kare sanyi ba. Dan gayu kawai.

Sai ganinshi yai tsaye kofar gidansu safiyya. Ya rasa yanda akai yazo wajen da kuma abinda yake yi.

Kallon kofar gidan yake. Zuciyarshi na masa wani iri. Juyawa yai da niyyar tafiya.

Kaman daga sama yaji muryar safiyya tace.

"Usman kace lami ta jirani. Yanzun zan fito"

Bai san lokacin daya juya ba. Itace a tsaye. Banbancin ta da mafarkin shi hijab da take sanye jikinta.

Kwalliyar fuskarta na nan. Muryar iri dayace.

"WTF......."

Ya fadin jin yanda zuciyarshi ta wani squeezing. Kallonta yake kaman bashida wani muhimmin abu dazaiyi bayan hakan.

*

Safiyya ta rigada tasan lami na iya kin jiranta. Jin datai a jikinta cewar ana kallonta yasa ta juyowa inda fu.ad yake tsaye kaman an dasa shi.

Idanuwanta ta sauke cikin nashin nan da sukai mata tsaye a rai. Ta kasa manta komai nashi.

Zuciyarta taji tana ta dokawa. Ta hadiye wani abu dataji ya tsaya mata a makoshi.

Mai shanu ta hango yanata faman yima fu.ad ihun ya kauce daga kan hanya amman da dukkan alamu baima san yana yi ba.

"Kauce daga hanya zai wuce! "

Ta fadi da karfi. Fu.ad ya wani yamutsa fuska da dukkan alamu bai fahimta dash take magana ko da wani ba.

Hannu yaji saman kafadarshi an ture shi gefe a fusace ana fadin.

"Kurma ne kai kome? Anata magana wa zaka kawoma tsagerancin ku na zamani"

Kafadarshi ya kalla. Sawun hannun mutumin ya fito da daudar da baisan ko ta mecece ba jikon farar hoodie dinshi.

Headphones dinshi ya cire daga kunnuwa ya taka wajen mutumin daya tabbata ya girmi anty fatima.

"Wawan ina ne kai zaka dauki kazamin hannunka ka dora akan kafadata?"

Da bala.in mamaki mutumin yake kallon fu.ad.

"Yaro rashin kunya zakaimun?  Dan gidan uban waye kai da bakasan........ "

Fu.ad bai bari ya karasa ba ya dauke shi da mari. Babu kazamun da zai zagi abbah.

Saffiyya batasan sanda ta karaso wajen ba da sauri. Hannu ta daga ta wanke ma fu.ad fuska da yatsunta biyar.

Kallon shi take tana gefen mutumin daya mara.

"Safiyya?"

Mutumin ya kira da alamun tambaya a muryarshi.

Tata muryar na rawa tace.

"Kawu kabarni. Akan me shine da laifi baiga girman kaba zai daga hannu ya mareka?"

*

Fu.ad hannu yasa ya taba kuncin shi. Ya sake shafawa ya dawo da hannunshi ya kalla.

Sannan ya sake kallon safiyya dake tsaye gefen mutumin dayaji ta kira da kawu.

Kwakwalwarshi ta kasa tauna abinda ya faru. Zuciyarshi ta kasa yarda da cewa abubuwa biyu ne suka faru dashi.

Wani kazamin talaka mai dauke da dauda ya zagi abbah. Wata kucakar yar kauye ta daga hannuwanta a mare shi.

"Marina kikai?"

Yake tambayar kanshi fiye da yanda yake tambayar safiyya. So yake wani ya tabbatar mishi da gaske abin ya faru.

Can nesa yake jin muryar safiyya dake cike da rauni na fadin.

"Eh marinka nai"

Kalar ashar din dayai zaisa ko bamaguje yake wajen kunya ta lullube shi.

Lokaci daya idanuwanshi suka rine saboda bacin rai. Dagowa yai ya sauke idanuwanshi cikin na safiyya.

*

Idanuwanshi take kallo. Lokaci daya duk wani abinda ke motsi a jikinta yake fahimtar kuskuren data aikata.

Bata san lokacin data matsa bayan kawunta ba. Har lokacin idanuwanta na cikin nashi.

Girgiza masa kai take. So take da wannan alamar kawai ya karanci yanda take dana sanin abinda ta aikata.

Shi kanshi kawunta kallon fu.ad yake. Da dukkan alamu yaro ne mai karancin shekaru.

Saidai a yanzun akwai wani abu tattare da yanayin shi dashi kanshi ya tsorata.

Akwai wata isa da tsayuwarshi da fuskarshi kawai ta nuna su.

*

Takawa yake a hankali kaman mai tafiya kan bawon kwai.

Yana kallon yanda jikin safiyya ke kyarma. Ta rike rigar kawunta kaman zata koma cikin shi.

Hannu kawunta ya dago yana shirin tare fu.ad. Muryarshi a dake can kasa yace.

"Kuskure na uku da zaka aikata shine barin hannunka ya karaso ya taba ko da rigata ne"

Da alamu kawu ya karanci gaskiya a maganar fu.ad dan haka ya maida hannunshi inda ya kamata ya tsaya.

Karasawa yai daf da safiyya da ta kasa sauke idanuwanta daga cikin nashi.

Kome yake ji akanta. Kome yake tunanin akwai a cikin idanuwanta. Abinda ta aikata ya girme shi.

Ko wanda yake so yakan nuna masa kuskurensa inhar ya mishi ballantana ita da basu hada komai ba.

Aa a ganinshi na biyu kenan da ita akwai abinda suka hada dabai fahimta ba bakuma ya son fahimta.

"You gonna' regret this. Bake kadai ba. Gabaki daya danginku.......!"

Thanks to *Dimples* for liking fu.ad so damn much. (Wink)

No comments:

Post a Comment