Thursday 4 May 2017

AKAN SO 9

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

             09

"A mikomun towel dina"

Fu.ad ya fadi yana daga cikin toilet din.

"waya hanaka shiga dashi?"

Lukman ya fadi. Haneef kam tabe baki kawai yai.

"Wallahi zan fito haka"

Da sauri lukman ya dauki towel din ya kwankwasa ban dakin. Ya mika masa. Yanayin dariyar da yake.

Yasan halin fu.ad babu kunya a idanunshi tsaf zai fito in basu mika mishi towel din ba.

Yana fitowa lukman ya shiga. Jakarshi ya dauka. Banda comb da man gashi bai dauko komai ba. Sai kayan sawa da takalma.

"bani manka indan shafa ma hannuwana"

Vaseline haneef ya mika mishi. Dan shima bai dauko mai ba yace.

"Ga dai na masu dakin"

Ai da sauri ya janye jikinshi kaman ya miko masa miciji. Ajiye robar haneef yayi yaci gaba da latsa wayarshi.

Kaya ya dauka ya sake ya gyara gashin shi da yake ta daukar ido. Kallon shi haneef yai yaga crazy jeans din dake jikinshi.

Yaga duk a gwiwar zuwa kwauri. Har jikin cinya yaga ne. Sai riga fara data bala.in kamashi shi ba wani jikin kirki ba.

Yasan inya masa magana ma fitsara zai sha ranshi ya baci a banza dan haka yai masa fatan shiriya kawai a ranshi.

Dai dai sallamar khalid. Haneef ya amsa da fara.a a fuskarshi.

"Ina kwananku"

Khalid ya fadi yana ajiye kwanan shan daya shigo dashi a hannu.

"Khalid ka tashi lafiya? Ya hidima kuma?"

Haneef ke tambaya yana mikewa daga kwanciyar da yai. Khalid ya amsa shi da.

"Alhamdulillah"

Yana ficewa da sauri. Ya sake dawowa da leda a hannunshi. Kamshin kosai ya cika dakin.

Fu.ad dake tsaye ya wani yamutsa fuska. Dan kamshin koma menene aka shigo dashi yana shirin saka shi amai.

"Ga abin kari"

Haneef yai masa godiya ya sauko ya bude ledar kosan. Gasu manya manya ya dauki daya ya gutsura.

Rabon shi da kosai tun wani azumi da atika tayi musu shi. Hada idanuwa sukai da fu.ad dake masa kallon 'Me kake yi haka?'

Share shi yai ya ci gaba dacin kosan shi suna dan hira da khalid din dake kallon fu.ad lokaci lokaci.

Kayan daya cire ya daga a kyamace yace.

"Ina za.a yadda wannan?"

Idanuwan khalid ya zaro yana kallon kayan da fu.ad ke kira da a zubda.

"Me ya same su?"

Ya tambaya sanin fu.ad bazai kula khalid ba balle har ya amsa mishi tambayar dayai yasa haneef saurin cewa.

"Yadan fita wata ta watso ruwa ya same shi"

"Ayya bara sai na wanke masa su"

Cewar khalid. Rolling idanuwanshi fu.ad yai. Ko ance ma wannan dan kauyen zai iya saka kayan da aka tsoma a bokiti yasa kazamun hannun shi ya wanke.

"Germs"

Ya fadi kasa kasa. Dan bai shirya dogon surutun haneef ba. Zai magana lukman ya fito daga wanka.

"Naji kamshin kosai"

Ya fadi yana dariya. Wani mugun kallo fu.ad yai masa da ko kula dashi baiba ya zauna gefen haneef sukaci tare.

"Ka kawo kayan sai in wanke maka"

Kallon khalid lukman yai. Mutanen karkara akwai karamci da sanin darajar mutane.

A shekaru zai girmi fu.ad amman yana offering ya wanke masa kaya. Ba ruwansu da girman kai.

Da haneef da lukman suka zuba masa ido yanda yake tsaye yana yamutsa fuska. Yason kallon da suke masa. Kaman wanda aka shaqe.

Can kasa kasa yace.

"Ba abinda zan da kayan ne. A zubar"

Tashi khalid yai ya karba yana fadin.

"Kai nikam ina so"

Ya dawo ya zauna. Wani kallo fu.ad yake mishi. Ya rasa meke damun talakawan nan. Harka iya kasa kayan da wani yai using.

Girgiza kai kawai yai. Ya dauko jakarshi. Ya duba. Kudin daya dibo basu shige dubu goma ba dan inba amfani zai da kudi ba ba yake dasu ba.

"Wayake da cash a jikinshi? Like 20k or more"

Ya tambaya yana kallonsu. Lukman ya mike ya dauko wallet dinshi. Dubu takwas ne. Ya girgiza ma fu.ad kai.

"Haneef?"

Ya kira da alamar tambaya a muryarshi.

"Aikin me nake dazan yawo da 20k?"

Haneef ya bashi amsa yana komawa kan katifa. Girgiza kai fu.ad yai yana tuna haneef bai fara aiki ba.

Kuma baya karbar kudi a hannunshi sam. Koya tura masa maida mai yake. Garama mota itama sai da ya nuna masa mugun bacin rai tukunna ya karba.

"ko 5k tam kamun mu shiga gari. Lukman ban na hannunka."

Mika mishi sukai haneef ya bashi 5k din. Ya kirga dubu ashirin. Khalid dai kanshi kasa yana sauraransu.

Lukman ya mikama yace.

"Give him ion wan him wearin' mi used'

Dariya lukman yai ya karbi kudin yace ma khalid.

"Gashi fu.ad ya baka ka siya kaya"

Ya karbi kudin da mamaki a fuskarshi. Allah kenan rabonka baya wuceka.

Godiya ya fara ma fu.ad dako kallon shi baiba ya karasa daura takalmanshi ya dauki key din mota ya fice.

Da khalid baiji yai hausa ba zai iya rantsewa yanda fu.ad ya basar dashi bai gane me yake cewa bane.

A sanyaye yace ma haneef.

"Inata godiya ko baiji ba"

Wata kunya ta rufe haneef yace masa.

"Kayi hakuri. Bai cika son godiya ba shisa kaga yai shiru"

Jinjina kai khaleed yai kawai bai ce komai ba.

**

Cake dinshi ya zauna a mota yaci ya sha fresh milk da sun wani dauki dumi.

Ac ya kunna. Ya zame kujerar ya kwanta. Kanshi wani ciwo yake ya kuma san baccin dabai samu bane.

Dama yasani cikin mota ya kwana. Ya fiye mishi alkhairi da sauro da zafin shagon nan. Wata kewar dakin shi na gida yaji.

Ajiyar zuciya yai. Ya sake gyara kwanciyarshi kan kujerar motar ya lumshe idanuwanshi.

Bacci mai karfi ya dauke shi da wani nauyi a zuciyarshi daya kasa fahimta.

*

Safiyya ce tsaye da kayan jikinta na dazun. Wata kokakkiyar atamfa. Fuskarta duk dige digen kwalli na alamar kwalliyar kauyen dake fuskarta.

Bata cika haske ba sosai. Bata da tsaho. Banda idanuwanta da suke manya tubarkalla babu wani kyau a fuskarta.

Hancinta kaman daga baya akan dan dora mata shi. Ba zaka kirata mummuna kai tsaye ba.

Saboda jikinta nada kyau sosai. Tana da kira da dirin da mata da yawa zasu yi hassada da.

"Fu.ad..........."

Ta kira shi. Mamaki yake dan baisan ya akai tasan sunan shi ba. Baima san me yake tsaye a wajen yana kallonta ba.

Yamutsa fuska yai saboda yanayin yanda ta kirashin baya so. Bayason yanda zuciyarshi ta wani matse.

Hade fuska yai. Baya son wata alaqa tsakaninsu. Shi ba mata yake kulawa ba. Mazan ma ba kula su yake ba.

Ball ce masoyiyarshi. Ita ya runguma. Amanarshi na tare da ita. Ba kuma ya tunanin zai iya hada sonta dana mace shisa basa gabansa.

Beside a shekaru ashirin da biyu wanne shiririta zai kaishi soyayya. Dan haka ya zo wucewa ta gabanta.

Ta riko mishi riga.

"Nima wulakancin zakai mun?"

Ta bukata.

A fusace ya juya ya sauke idanuwanshi cikin nata. Lokaci daya kankarun dake cikin idanuwanta suka soma kashe duk wata wuta dake cikin nashi.

Dukkanin ginin dake kare da zuciyarshi suka soma girgiza. Foundation dinsu na barazanar rugujewa.

*

A firgice ya bude ido yana jan wani irin numfashi. Ac din motar bai hanashi zufa ba. Zaune ya tashi dirshan.

Ya dafe kanshi cikin hannuwanshi. Yana maida numfashi da sauri sauri. Glass din motar ya sauke.

Dan iskar dake ciki ta masa kadan. Ruwa ya dauko ya bude motar. Ya kurkure bakinshi ya wanke fuskarshi sannan yasha.

Ya koma cikin motar ya hada kanshi da sitiyari yana jin yanda numfashin shi ya samu dai-dai ta.

Wannan wanne irin mafarkine. Safiyyar da maganganunta ne kawai mafarki. Amman yanayin da yake ji a cikin mafarkin.

Shi yake ji a yanzun. Rawar da zuciyarshi takeyi saima abinda yai gaba. Wanne irin bala.i ne wannan? Yake tambayar kanshi.

Baiga hadinsa da yar qauye kucaka ba. Yar gidan talakawa da zata kutso masa kai cikin mafarki.

Wani tsaki yaja. Yana mikewa yaji muryar lukman kaman daga sama.

"Dan banza ashe kana nan. Anata kiran wayarka kaqi ka dauka"

Wayarshi a silent take. Shiru yai ma lukman din ya zagaya ya bude motar ya shigo.

Baima kula tare suke da haneef ba saida yaji an bude gidan baya an shiga.

"Lukman karbi tukin nan please"

Bayajin yan gardamar dan haka ya bude motar ya fita. Lukman ya koma inda ya tashi. Baya ya bude ya shiga. Haneef yace

"Me ye haka din?"

A kasalance yace.

"Em noh' in the mood"

Fita haneef yai ya koma gaba. Fu.ad yai luf dashi cikin kujera. Yanajin lukman na maimaita yanayin turancin shi.

Ya rasa me yasa indai zai turanci sai lukman ya maimaita yana mai dariya wai ya zama masu jar fuskar nan.

Yanayin dayake ji bana rigima bane.  Suka dauki hanya. Wayarshi lukman ya jona yasa kida yana dannawa wakokin suna wucewa.

Wata waka ta shigo ta justin biebier (Purpose) harya danna ya canza dan yasan yanda fu.ad ya tsani slow wakoki.

Wai sai kace marassa rai. Da hanzari fu.ad yace masa.

"Bar ta please. Mayar mana"

Mayarwa yai yana kallonshi ta cikin mudubi. Ya fahimci baison surutun yau. Yakuma san akwai abinda yake damunshi.

Yasan da kanshi zai fada mishi dan haka yabar wakar kawai. Fu.ad kam wakar na shigar shi ya kuma rasa dalili.

Bason slow music yake ba. Saidai kawai yaji wakar tayi dai dai da yanayin da bai san ta inda ya fito ba.

Wani mai machine ne ya shigo musu kaman daga sama. Badan a hankali lukman ke tuqinba da munin abin zaifi yanda ya faru.

Parking yai suka fito su duka. Fu.ad ya rike baki yana kallon gefen gabar motarshi ya tashi aiki.

Benz dinshi da yana da wanda suka fita kudi amman yake mugun ji da. Fuskar shi horrified yake fadin.

"Oh no.....oh my God"

Yana girgiza kai. Baima kula dasu haneef dake magana da yaron ba. Juyawa yai rai a bace ya ture lukman ya cakumi wuyan yaron.

Mutane harsun fara haduwa. Tsayi kawai fu.ad zai nuna mishi. Amman ya fishi girma wani wawan mari ya kwada ma saurayin yana kara mishi wani.

Haneef da lukman suka rike shi suna fadin.

"Fu.ad control yourself please ya bada hakuri fa. Machine dinshi ne ba brake"

Cikin hargowa fu.ad ya ture su yana fadin.

"Ciyawa ce a kanshi? Da akace yahau machine ba brake? Kana tunanin ko gidaje da gonakin danginsu za.a siyar zasu biya kudin motata ne?"

Cike da takaici yaron yace.

"Allah ya baka hakuri"

Kallon shi fu.ad yai yanajin kaman ya rufe shi da duka yace.

"Aikin talaka kenan. Bada hakuri. Tunda ka gama mun barna dole kabani hakuri. Daqiqin banza"

Harya juya yana sake kallon motar shi. Matashin saurayin yace.

"Arziqi dai ba hauka bane ba. Allah daya baka muma talakawan zai iya bamu"

Tunda ya bude bakinshi haneef da lukman suka karanci kuskuren hakan. A hankali fu.ad ya juya muryarshi can kasa kaman mai magana da kanshi yace.

"Me kace?"

Haneef ne ya dafa kafadarshi yace.

"Forget it fu.ad muje please"

Ture hannun haneef yai ya karasa daf da saurayin. Muryarshi very controlled da abinda yake ji yace.

"No ya maimaita abinda yace"

Shiru saurayin yai. Cikin jama.an wajen fu.ad yace ma.

"akwai police station a kusa?"

Hakuri suka shiga bashi yace wallahi sai ya maimaita maganar daya fada. Sai yasa an kulle shi.

Bai gama balbalin ba. Ashe tun farkon rikicin wani yaga abin zai wuce gona da iri yai saurin karasawa police station din dake nan kusa kusa ya kai report.

Nan suka rankaya zuwa police station din. Haneef da lukman na kokarin shawo kan fu.ad din dako saurararsu yaqi yi.

Filing report yai yace yana son a biyashi barnar da akai masa jikin mota. Dan yasan basu da kudin biyan shin. Wulakanta yaron yake so ayi.

Saboda babu wanda ya isa ya gaya masa magana ko ya fishi kudi basuyi shari.a ba ballantana wannan kazamin talakan.

Dukan shi yan sanda suka shiga yi zaka rantse da Allah kayan wani ya sata. Wani abu sai kasata nigeria.

Gefe haneef yaja fu.ad.

"Wai meke damunka ne? Wallahi kasa su kyale shi ko na kira abbah na fada mishi"

Lukman na gefe dan yagaji. Fu.ad ba saurarsu zai ba. Wani dattijo ne ya shigo police station din a rikice.

Yan sandan suka kira fu.ad ya karasa inda suke. Kallon dattijon yake akwai inda ya taba ganin shi.

Lokaci daya abin yai clicking masa. Shine tsohon da anty fatima ta mare shi saboda. Wannan kazamin tsohon.

Shima kallon fu.ad din yake. Yagane shi sarai. Ya rausayar dakai gefe kawai. Nan yan sanda suke kara ma zancen fu.ad gishiri.

Ya bude baki zai magana haneef yace.

"Fu.ad na taba rokon alfarma a wajenka?"

Yai shiru kawai. Haneef ya ci gaba.

"Fine ban taba rokon wani abu a wajenka ba. Indai har ina da wata daraja a wajenka. In jini daya ne yake a jikinmu zakai dropping case din nan yanzun"

Shiru yai kaman baiji abinda haneef din yace ba. Harma ya dauko waya zai kira abba yaji fu.ad yace.

"Fine. Ina son babanshi yaban hakuri"

Ya fadi yana kafe idanuwanshi kan dattijon. Haneef yai masa kallon kana cikin hankalinka kuwa.

"Allah ya baka hukuri ya huci zuciyarka da kuskuren da yarona yai maka"

Cewar dattijon muryarshi na rawa. Haneef fita yai daga police station din lukman na rufa mishi baya.

Saboda kunya yake ji. Yaji ya muzanta da abinda fu.ad yayi. Shikam wani murmushi ya kwace masa.

Sauran kudin aljihun shi ya zaro yaba yan sandan sannan ya fita wajen su haneef.

Su duka babu wanda yace masa uffan har suka tsallaka wajen motarsu suka shiga lukman ya tuqa su zuwa gida.

No comments:

Post a Comment