Tuesday 9 May 2017

AKAN SO 43

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

www.Loobnerh.blogspot.com

Wattpad: LubnaSufyan

                   43

*#AnaTare*

*Babu abinda yakai dan uwa dadi. Babu abinda yakai zumunci muhimmanci. Saboda me zamu cika zuciyarmu da kiyayya bayan zamu iya cika ta da kauna?*

*Saboda me zamu riki junanmu bayan zamu iya bayyana laifin junanmu mu yafi juna komai ya koma dai dai?*

*Saboda me zamu zabi jin haushin junanmu bayan zamu iya bata lokacin mu kan bayyana murmushi a fuskokin juna?*

*Na yarda da kauna. Na yarda kauna abu ce mai girma. Na yarda na zabi farin ciki sama da akasin shi. Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa. Amin thumma amin*

"Fu.ad idanuwanka kenan?"

Dan sosa kai yayi yana murmushi. Anty fatima ta sauke numfashi hadi da fadin.

"Ka kyauta"

Sai lokacin tun zamanshi falon ya dago idanuwanshi ya sauke su kan anty fatima da duk wata nadama dake cikinsu.

Saukowa yai daga kan kujerar dayake zaune ya saka gwiwoyinshi kan kafet din dakin ya hade hannayenshi waje daya. Muryarshi a dakushe yace.

"Nayi laifi anty. A yafemun dan Allah. Kaunarku a gareni tafimun komai muhimmanci a yanzun. Bazan taba iya dawo da shekarun nan ba. Amman zan iya gyara na gaba.

Ki yafemun"

Kallon shi take. Tabbas fu.ad ya musu laifi su dukansu. Tana kallonshi yasa hannu a aljihunshi ya ciro wani abu.

Kallonta yai yana mika mata hannunshi dake dumtse kamun daga baya ya bude shi. Agogo ne na hannu. A ko ina taganshi zata gane shi.

Idanuwanshi ya saka cikin nata. Da wani irin yanayi a muryarshi yace.

"I want mi' sister back. Ina son sister dina data koyamun yanda zangane wannan agogon na hannuna.

Ina son sister na da muke shiga kitchen hada salad tare. Ina son sister na da take tare dani lokacin da nake sneaking zuwa ball.

Anty fatima please......"

Ya karasa maganar yana sauke muryarshi kasa idanuwanshi cike da hawayen dayake rike dasu. Komai na dawo mishi kaman lokacin ya faru.

*
Kitchen suke da anty fatima tana yanka kwan da ta dafa zata hada musu salad. Yana tsaye gefe tace mishi.

"Fu.ad karfe nawa. Ga agogona nan kusa dakai"

Daukar agogon yai. Ya tsura mishi idanuwa. Babu lamba ko daya a jiki. Dakunq fuska yai yadan daga girarshi hadi da fadin.

"Yazan ingane? Babu number ko daya a jiki"

Dariya anty fatima tayi hadi da fadin.

"Karka cemun baka iya reading wannan agogon ba fu.ad"

Cije lebenshi na kasa yai yana ware mata idanuwanshi. A kunyace yace.

"karki fadama haneef. Zaita tsokana"

Fuskarta babu alamar wasa tace mishi.

"Bazai ji ba. Zan koya maka"

Murmushi yai.

"Really?"

Kai ta daga mishi.

"You are the best sis kinsani ko?"

Dariya kawai anty fatima tayi hadi da fadin.

"Gashi na matane dana bar maka"

Da sauri yace.

"Ban damu ba. Ina so sai insa a aljihuna"

Kallon fuskarshi tayi. Da gaske yake son agogon yake in tabar mishi.

"You can have it. Karka zo wajena in wani ya tsokane ka da agogon mata"

"Zan fasa bakin duk wanda yamun dariya saboda ke kika bani"

****

Hawayen dayake idanuwan anty fatima suka zubo. Hannu tasa ta karbi agogon tana juya shi.

Bata taba zaton fu.ad nada shi ba har lokacin. Bata sake ganinshi dashi ba bata kuma tambaya ba. Hannu tasa ta goge idanuwanta muryarta na rawa tace.

"Kana dashi har yanzun daman?"

Kallonta yayi da murmushi yace.

"Ina mantawa na daura a hannuna. Saina dauko na duba naga ya dainayi nake Tunawa"

Dariya tadanyi.

"Fu.ad......."

Katse ta yai da fadin.

"Please. Please i want her back"

"Ka tashi fu.ad. Komai ya wuce. Your sister is here and always will be"

Murmushi yai cike dajin dadi ya mike ya zauna kan kujerar.

"Har yanzun watermelon eyes ne dake anty fatima"

Dakuwa tai mishi ya kwashe da dariya. Yana jinshi wani light. Mikewa yai yana fadin.

"Bani agogo na nikam in wuce. Yamma nayi sosai"

Mika mishi tayi hadi da fadin.

"Saura mu sake nemanka mu rasa"

Dariya kawai yayi yana wucewa.

"Nikam sai munyi waya"

"Ka gaishemun dasu momma"

Ya amsata sannan ya fice.

****

A hanya yai sallar magrib sannan ya koma gida ya samu hassan zai maida su khadee gida saboda washe gari duk yaran suna da islamiya.

Kiran hassan yayi ya zaro credit card dinshi yaba hassan hadi da fadin.

"Ka biya dasu ka siya musu ko chocolate. Ice cream. Kome dai suke so"

Karba hassan yai. Harya juya fu.ad yace mishi.

"Ka siya duk abinda kake so"

Girgiza kai hassan yai.

"Ina aiki bro. Ka manta"

Dariya fu.ad yayi.

"Ka girma ko?"

Dan daga mishi kafada hassan yayi sannan ya wuce abinshi. Falon ya karasa ya samu Nana na kwance kan kujera tayi pillow da cinyar momma tana bacci.

Ya samu waje ya zauna yana sauke ajiyar numfashi. Gaba daya jinshi yake a gajiye. Ba irin gajiya ta ciwon jiki ba. Jinshi yake emotionally drained.

Kallon momma yayi tai mishi murmushi.

"Mungama magana da abbanku. Da yace kuje yauma. Nace abari zuwa gobe tukunna da safe in Allah ya kaimu.

Saika kira safiyya ka fada mata ko"

Jinjina kai yayi.

"Allah ya kaimu. Bara inje sallar isha.i in dawo"

Ya karasa maganar yana mikewa.

"Allah ya karba mana"

Ya amsa da amin yana ficewa.

**

Yana dawowa daga sallar isha.i abinci yaci ya wuce dakinshi ya watsa ruwa sannan ya sake kaya yasa wata T-shirt marar nauyi da three quarter loose.

Kasa ya sauko zuwa falo. Yana shirin kiran momma yaji ya Nana sai gata ta fito jikinta sanye da rigar bacci pink sai hular dake kanta ma pink.

Wani irin dokawa zuciyarshi take yi da kaunarta. Murmushi tayi mishi ta karasa inda yake ta kama hannunshi. Kujera suka samu suka zauna.

Nana ta kalle shi tana ware idanuwanta kan fuskarshi. Tun kamun ta furta ya karanci tambayarta cikin idanuwanta.

Dan haka ya hutar da ita ta hanyar amsa ta da fadin.

"Ni da mumynki. Zamu koma da aurenmu gobe in Allah ya......."

Bai karasa maganarshi ba yaji ihun murnar Nana ta fada jikinshi ta zagaya hannuwanta kan bayanshi ta kankame shi.

Yanajin dariyar da takeyi. Shima dariya yayi. Farin cikinta na kara mishi wanda yake ji. Dakyar ya samu ya banbare ta daga rikon datai mishi.

Ta make kafadarta tana sake komawa ta kankame shi. Kyaleta yai saidata gama murnar da kanta sannan ta dago daga jikinshi ta gyara zamanta kan kujerar.

Kanshi ta tallabo da hannuwanta duka biyun ta hada goshinsu tare. Ji take yagama mata komai na duniya.

"Nagode dady. I love you so much. Nagode sosai"

Cikin idanuwa yake kallon yarta shi yana jin kaunarta har cikin jininshi. Yanajin kaunarta ta yanda bazai iya fassarawa ba. Wannan son is priceless. Kalar kaunar dabance da wadda yake ji akan safiyya.

"Ina mumy yanzun?"

Muryashi can kasa yace mata.

"Tare da mumyn ta da dadynta"

Sake ware mishi idanuwa nana tayi. Tana sauke murya tace.

"Suna nan?. Sauran grannies na suna nan? Mumy ba ita kadai bace yanzun?"

Kanshi dake jikin nata yadan daga. Yana kallon yanda ta lumshe idanuwa wata nutsuwa na sauka kan fuskarta.

Idanuwanta a lumshe har lokacin goshinta na hade da nashi tace

"Na taba tambayarsu. Mumy taita kuka ban sake ba. Me ya faru dasu?"

Raba goshin su yayi ya tallabi fuskar Nana cikin hannuwanshi. Wani irin nauyi yake ji cikin zuciyarshi.

Amman yafison wannan gaskiyar ta fito daga bakinshi. Yafiso ya fadama Nana da kanshi. Saidai wanne irin bayani zakaimq yarinya yar shekara sha daya.

Cikin sanyin murya tace.

"Ba saika fadamun ba in baka so. Naji dadi da mumy take tare dasu. Shi kadai ya isheni"

Wani abu ne yai masa tsaye a wuya. 'She is so fucking matured' ya fadi a ranshi a fili kuma yace mata.

"No zan fada miki. Bansan ta ina zan fara ba"

Daga mishi gira tayi dake nuna itama batasan ta inda ya kamata ya fara ba. Ya sauke ajiyar zuciya.

"Ina da shekaru ashirin da biyu Nana. So young and stupid. Nayi wani kuskure da bai kamata inyi ba.

Bazan iya fada miki kuskuren ba. Amman abune marar kyau sosai. Hakan ya bata komai. Ni da mumynki da kowa namu"

Kai ta jinjina mishi alamar ta fahimta. Bata son ganin yanda idanuwanshi suke. Kaman abinda yake fada yana mishi tsananin wahala da ciwo.

Hannunshi dake fuskarta ta ture tana kama shi cikin nata ta dumtse. Muryarta a tausa she tace.

"Bana son ji dady"

"Why?"

Ya bukata yana tsare ta da idanuwana.

"It is hurting you. Nikuma bana so"

Hugging dinta yayi. Yanayin na karya mishi zuciya. Wannan yarinyar daban take a cikin mutane. Bai taba ganin irinta ba.

Muryarta cike da kaunarshi tace.

"Ka gyara komai ko dady? Komai ya wuce yanzun?"

Muryarshi a dakushe da yanayin da yake ji yace mata.

"Yeah. Komai ya wuce thanks to you"

Dariya tayi tana dagowa daga jikinshi.

"Kira mumy in mata good night"

Ba musu ya dauko wayarshi ya duba. Tinawa yayi bashida number din safiyya ma.

Yai wiki wiki da idanuwa yanajin wata yar kunya ta kamashi. Sosai nana take dariya. Ya dakuna mata fuska.

"Ka fada inji dady"

Kai hannu yayi yaja mata hanci ta ture hannunshi tana dariya sosai. Karanto mishi number din safiyya tayi.

Ya kira bugu daya ta dauka da sallama. Nana ya mikama. Ta karba suka gaisa.

"Mumy bani su mu gaisa please please please"

Dariya safiyya tayi daga dayan bangaren tace.

"Sun kwanta nana. Kema ki kwanta kice dadynki ya kawoki gobe sai ki gansu ok"

Turo baki nana tayi ta kalli fu.ad daya daga mata gira da tambayar lafiya?

"Wai sunyi bacci gobe ka kaini"

Tace ma fu.ad ya daga mata kai. Safiyya dake dayan bangaren tace.

"Kikace me nana?"

"Nida dady ne"

Bata jira amsar safiyya ba ta mikama fu.ad wayar. A dan daburce yace.

"Hello"

Shiru tadanyi da alama itama ta tarasa abinda zatace mishi. Kamun tace.

"Komai lafiya dai ko?"

"Lafiya kalau. Tana lafiya"

Shiru suka sake yi kamun tace.

"Saida safe kenan?"

Dasauri yace.

"No. Zamuzo dasu abbah gobe"

"Allah ya kaimu. Ka kula da ita"

Yadan daga kai kaman tana ganinshi ya mikama nana.

"Good night mum. Take care. Love you"

"Love you too princess"

Ta fadi tana kashe wayar.

Kallon fu.ad nana tayi.

"That is awkward"

Ware idanuwa yai yana mamakin yanda Nana taji turanci haka. Sai kuma yai tunanin jss1 akace mishi take kuma da alama makarantarsu nada kyau sosai.

Kuma gaskia ta fada. Wayarsu da safiyya is kinda awkward. Dariya yayi. Hamma nana ta fara ta kalle shi.

"Na gudu wajen granny dady bacci nake ji"

Kai ya daga mata.

"Sleep well. Banda snoring"

Ta wani dakuna fuska kaman ya fadi kazanta.

"Ewww dadyyyyy!"

Dariya sosai fu.ad yake. Nana ta soma dire kafafuwa.

"Ni bana snoring. Ka tambayi mumy"

Dariya yake. Saida yaga yanda nana ta dakuna fuska ya samu ya tsayar da dariyarshi.

"Go and sleep"

"Bana snoring"

Ta fadi tana dora hannuwanta kan kugunta. Dariya fu.ad yayi.

"Bakya snoring. Na yarda"

Murmushi tayi ta matsa kusa dashi ta sumbaci kumatunshi.

"Good night dady. Love you"

"Love you more"

Wucewa tayi. Yanajin tana fadin.

"Nooooo i love you moreee"

Yai dariya kawai yana sake shigewa kan kujerar. Dakyar ya iya mikewa ya tafi dakinshi. Yana addu.a bacci mai nauyi ya dauke shi cike da mafarkin sofinshi.

****

Tana zaune gaban mudubi tana shafa powder a fuskarta. Hannuwanshi ta fara ji kan kafadarta sannan ta sauke idanuwanta cikin nashi ta mudubin dake gabanta.

Murmushi yai yana sumbatar gefen fuskarta. Lumshe idanuwa yayi.

"Ina son kamshin turarukan nan naki jana. Bana gajiya dajin su"

Dariya tayi ta dora hannuwanta kan nashi hadi da ture su.

"Nikam kabarni in shirya"

Dakuna fuska jabir yayi.

"Ke yanzun saiki barni gidan nan shiru? Yara duk sun tafi islamiyya"

Dankunnenta take kokarin sakawa ya karbe daga hannunta yana makala mata ta amsa shi da.

"In banje ba yau banda lokaci sosai. Rabona da gidan hajiya anfi sati hudu fa honey j"

Langabe fuska yai yana daukar dayan dan kunnenta ya saka mata hadi da jan kunnen. Dukan hannunshi tayi tana fadin.

"Wayyo. Da zafi fa"

Daga mata gira yayi.

"Nikam banajin zama ni kadai"

Juyowa tayi ta fuskance shi. Idanuwan shi cike suke da rikici. Yau kwana uku kenan da fada mishi zataje gidan hajiya yanzun kuma zai rigime mata.

"Kai dan zaman majalissar da maza suke bakayi balle ince ka fita"

Hannu yasa ya mintsinan mata kumatu yana matsewa. Ta ture shi tana shafa wajen.

"Kinsan babu abinda na tsana banda zaman majalissa. Me suke banda gulma da kallon matan mutane"

Ta shagwabe fuska. Hannunta nakan kumatunta inda ya mintsina.

"Shine saika mintsine ni"

Ya daga mata kai.

"Kisan yanda zakiyi dani. Muje in kaiki gidan hajiyar ma ko? Sai mu gaisa"

Girgiza kai take yi.

"No. I mean in caps. Wallahi nagode. Ni sai bayan azahar zan dawo idan naje"

Tasan halinshi da wuya yabari suyi minti sha biyar.

"Honey j. Kaga ka kyaleni in shirya"

Hannuwanshi ya hade kan kirjinshi ya zuba mata idanuwanshi masu rikita mata lissafi. Da sauri tace.

"Kaje wajen ayna"

Dan batason yanda fadar hakan kawai yake saka zuciyarta wani irin tafasa.

Ya karance ta tsaf. Karasawa yai inda take yasa hannuwanshi ya tallabi fuskarta. Cikin idanuwa ya kalleta kamin ya manna mata sumba mai taushi.

"Saikin dawo. Babu inda zanje. Zan kwanta inyi bacci"

"I mean it honey J. Ka....."

Kallon dayai mata yasa ta rufe bakinta ya jinjina kai.

"You are doing enough. Nasan me kike dannewa *Akan so* na jana. Basaikin kara da abinda zai cutarmin dake ba.

Bana so kinajina. Karki kure hakurinki"

Kai ga daga mishi a sanyaye tace.

"Thank you"

Da hannuwanshi dake fuskarta yake nuna mata yanda muhimmancinta yake a wajenshi.

"Ki kulamin da kanki"

Ta daga mishi kai tana sa hannunta ta cire nashi dake fuskarta saboda yanda yanayin kallon da yake mata da komai da take karanta cikin idanuwanshi suke saukar mata da kasala.

Cikin kanta take kirga satikan da suka rage musu. A kasan zuciyarta tana addu.a kar komai ya canza musu. Kar soyayyarsu ta girgiza.

Da wannan tunanin a ranta ta karasa shiryawa. Saida ta karasa inda yake zaune kan gado ta sumbace shi sannan ta fice.

****

Zaune take kasa. Ta dora kanta kan cinyar hajiyarsu dake zaune kasa. Kuka take mai cin rai.

Gabaki daya abinda take dannewa ne a zuciyarta a kwanakin nan take ture shi gefe ya bude mata daganin hajiyarsu.

Hannu hajiya ta dora kan jana da tana shigowa falon ta karaso ta zauna gabanta ta dora kanta a cinyarta tana wani irin kuka.

Da jabir baizo har gida ya fada mata ba. Da yanayin kukan janar ya daga mata hankali. Batai kokarin hanata ba. Kawai ta dora hannunta a kanta ne.

Cikin son nuna ma yar tata tana tare da ita a koda yaushe. Dago fuska jana tayi da harta kumbura ta kama hannuwan hajiya tana wani gogasu kan fuskarta.

Cikin kuka take fadin.

"Bana bakin ciki da auren da jabir zaiyi hajiya duk da na kasa hana zuciyata zafin kishin shi.

Babu wanda zan gayama inajin tsoron auren na saike. Babu wanda zan nunama rauni na ya fahimta hajiya.

What if tazo ta tarwatsa mana komai?"

Cikin idanuwa hajiya ta kalli jana murya a tausa she tace.

"Na fahimci tsoranki murjanatu. Na fahimta wallahi. Nakuma jinjija ma kokarinki. Ina alfahari da karfin halin da kika nuna.

Koni bance zan iya irinshi ba. Ki godema Allah wannan baiwace daba kowacce mace yaima ba.

Naji dadi da yanda bakiyima kaddara gardama ba duk da kina tsoranta. Abu biyu zuwa ukku zan fada miki"

Kai jana ta daga tana sauraren hajiya kaman gabaki daya duniya bata da wani aiki da ya wuce hakan.

Har ranta tanajin yanda ruwan da take ciki yakawo har bakinta. Bata da abin kamawa ta fito daga cikin shi daya wuce shawarwarin mahaifiyarta.

Hajiya taci gaba da fadin.

"Karki yarda zafin kishi ya canza kaunar da tausayin dake tsakaninki da mijinki.

Karki bari addu.a ta kubce miki a kowanne hali da kika tsinci kanki.

Ki zauna da ita da zuciya daya. Ko zata cuceki Allah zai zamana yana tare dake saboda babu mugun abu a zuciyarki.

Ko koma gidanki batare da tsoron nan a zuciyarki ba murjanatu. Kaddararki ta jima da bushewa. Tsoro ko rashin hakan bazai canzata ba.

Hanyoyi na Ubangiji suna da girma. Kiyi addu.ar alkhairi. Ki mika ma Marubucin kaddararki komai naki. Zai nuna miki hanya idan kin rasa ta"

Wata irin nutsuwata daban jana take ji a cikin zuciyarta. Hannu tasa ta goge fuskarta. Ta sake kwantar da kanta kan cinyar hajiya. Muryarta a dishe saboda kukan da tayi tace.

"Madallah da mahaifiya irinki hajiya. Madallah da mahaifiyar datake kama hannuna a koda yaushe zuwa hanyar gaskiya.

Ina kaunarki hajiya. Allah yabarmin ke"

Dariya hajiya tayi.

"Ke dai kice Allah ya hadani da mahaifinku a aljanna. Ita nafi bukata"

Murmushi jana tayi tana ma mahaifinta addu.ar samun Rahma a zuciyarta. Kamun ta sauke numfashi.

****
****

Da safe wajen karfe goma duk sun gama shiryawa daga shi har abbah. Lukman da haneef ma sunzo gidan.

Nana da camera a hannunta su haneef sun biye mata sai shiririta suke. Kar lukman yaji labari. Fu.ad ya kalle su ya girgiza kai.

Gaba daya nana ta mayar dasu yan yara. Har ya juya ya maida hankalinshi wajen abba ya sake juyowa da sauri.

Kallonsu yake sai yake tunanin shima kenan haka yake zama yaro in yana tare da ita kenan?

Ya bude baki zai magana yaya babba ya shigo. Su duka gaishe dashi sukai shikuma ya gaishe da abbah da momma.

Fu.ad ya kalla. Jeans ne blue a jikinshi da riga fara sal da ita. Ya girgiza kai hadi da fadin.

"Kai haka zamuje gidan surukai dakai da kananan kaya?"

Sosa kai fu.ad yai yana ware idanuwa hadi da fadin.

"Banda ko daya ne"

Haneef babban yaya ya kalla.

"Kayanka ba zasuyi ma fu.ad ba?"

Girgiza kai haneef yayi. Dan fu.ad ya fishi tsayi yanzun kam. Na lukman kuma daga tsayin har girman ya mishi kadan.

Sauke ajiyar zuciya babban yaya yayi.

"Allah ya rufa asiri to"

Abbah da momma kam dariya suke musu. A hankali nana ta mike ta taka har inda babban yaya yake. Kallonshi take.

Sai lokacin ya kula da ita.

"Ina kwana baba babban yaya"

Tace mishi dan haka taji suna kiranshi babban yaya. Lukman ya fara kwashewa da dariya kamun si haneef su dauka.

Har babban yaya saida ya murmusa. Kallonsu nana take cikin rashin fahimtar me suke ma dariya.

Kamo hannunta babban yaya yayi.

"Rabu dasu nana. Kina lafiya?"

"Lafiya kalau nagode"

Ware idanuwa yai da dan mamakin wayan yarinyar. Kamun ya kalli su haneef yace

"Muje ko?"

Ba musu suka mike. Lukman ne ya kama hannun Nana suka fice. Momma na musu Allah ya bada sa.a.

Mota daya suka shiga da babban yaya da abbah. Su kuma su haneef suka shiga mota daya. Fu.ad ke tuqin dan shi yasan gidan.

*

Kofar gida suka tsaya fu.ad ya sake kiran safiyya yace musu suna kofar gida.  Ko mintina biyar ba ai ba tsakani ta kira tace su shiga.

Kwace hannunta nana tayi daga na lukman ta ruga da gudu cikin gidan lukman yace.

"Au nana dan munzo ko? Zaki fito ki same ni"

Bata juyo ba dariya kawai tayi. Suka shiga ciki su dukansu. A falon da suka shiga jiya aka tare su. Ware idanuwa fu.ad yake ko zaiga safiyya amman babu alamar ko Nana ma balle yai tunanin zai ga safiyya.

Inna ma suna gaisawa dasu abbah ta  kawo musu lemuka da ruwa da fice daga dakin. Su dukansu ruwan kawai suka sha.

Babban yayane kawai ya fasa lemon exotic guda daya ya sha. A nutse suke magana tsakanin abbah da baba.

Fu.ad kam bayajin me suke fada kwata kwata saboda hankalinshi ba akansu yake ba. Zuciyarshi bata tare dasu.

Tana wajen safiyya a yanzun. Mamakin yanda rayuwa ta canza musu lokaci daya yake. Canji tai musu me kyau.

Kaddararsu ta sauya su daga duhun data jefa su zuwa haske mai ban mamaki. Lukman ya zungure shi. Da sauri ya dago kai ya kalle shi.

Ware mishi idanuwa yai alamar ya dawo da hankalinshin kan maganar da ake yi dan ya kula baya tare dasu.

Yanajin su abbah suka tsayar da magana cewa ranar za.a daura aure karfe hudu. Saboda a samu damar sanarma mutane.

Babu ma yanda basuyi da baba ba akan ya karbi sadakin ya rike yace aa kawun safiyya ne zai amsa sai an kira shi tukunna.

Mikewa sukayi akai sallama gabaki daya. Su abbah suka fara ficewa. Fu.ad ya kalli haneef daya zare mishi idanuwa alamar ya wuce su tafi.

"Bara in kira safiyya ta turo nana"

Tura shi haneef yayi. Kasa kasa yake fadin.

"Ba wata Nana. Kabarta anjima inmun dawo mun tafi da ita"

Hakoranshi fu.ad ya bude haneef gabaki daya saikace mai tallar abin goge hakori hadi da fadin.

"To ko nima in zauna anjima in kunzo saiku tafi dani"

"Fu.ad!"

Lukman ya fadi. Daga kafada fu.ad yai yana ware idanuwa yace ma lukman.

"What? Meye dan kun barni?"

Swatting dinshi haneef yai a bayan kai ya tsugunne yana fadin.

"Ouchhhh me nai ne wai ku?"

"Wuce mu tafi"

Haneef ya fadi yana hade fuska. Turo baki fu.ad yai kaman yaron da aka kwace ma sweet. Ya wuce yana fadin.

"I so don't like ku biyun nan"

Dariya sukai suna tusa shi gaba haneef na fadin.

"We so don't care!"

*#TeamAS*

No comments:

Post a Comment