Thursday 4 May 2017

AKAN SO 20

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

  
     20

*Thank you for all the love and support. I feel you guys oceans and galaxies. To team FU.AD*

Fu.ad ne yai kanta. Zama yai ya kamata yana jijjigawa.

"Sofi. No please. Sofi ki tashi....."

Gabaki daya ya wani gigice. Momma ce kawai ta karasa kusa dashi. Tana janyo sofi jikinta tace

"Pha.iza miko mun ruwa gashi can.... "

Jiki babu kwari pha.iza ta mikoma ta ruwan. Zubawa tadanyi a hannunta ta murza sannan ta shafa ma sofi a fuska har sau biyu.

Fu.ad kam ya tattara gabaki daya hankalin shi ya mayar kanta.

Wani dogon numfashi taja ta bude idanuwanta a firgice. Janye jikinta tai daga na momma ta matsa ta hade sa bangon.

Wani irin kuka ta saki. Karasawa fu.ad yai kusa da ita yakai hannunshi. Yanda ta janye jikinta da hanzari kaman wadda taga miciji yasa shi fasa tabata.

Muryarshi can kasa yace.

"Hey look at me. Sofi nine. Muna tare fa. Komai zaiyi dai-dai"

Kaman daga sama sukaji muryar abba yace

"Ko wani zaimun bayanin abinda ke faruwa a wajen nan? Naka sa ganewa"

Fu.ad ya dauke idanuwanshi daga kan sofi ya sauke su kan momma yana rokonta data fahimce shi.

Saidai ita tama rasa me take ji a lokacin. Mamaki? Bacin rai ko me? Gaba daya kanta ya wani daure.

Haneef dake tsaye yace.

"Kai muke jira fu.ad"

Kallon haneef yai hadi da fadin.

"Wacce kalmace baka gane ba cikin maganata ta dazun?"

Girgiza kai kawai haneef yai. Rashin kunyar ta dawo kenan. Da magana cikin gatsali da isa.

"Wacce maganar banza ce kakeyi haka fu.ad. Me ka fada da zamu gane?"

Abbah ne ke fadar hakan rai a bace.

Tausasa murya fu.ad yai.

"Ya zanyi ne abba? Daukota nai mukaje aka daura mana aure"

Karasawa inda yake abbah yai ya dauke shi da wani mari da yasa har iskar dakin ta daina watayawa na wani lokaci.

"Sake maimaitawa muji!"

Hannunshi rike da kunci yace.

"Abbah aure mukai. Wallahi ba karya nake ba"

Wani marin ya sake dauke shi dashi. Daya sa safiyya dake gefe kara rike jikinta tana kallon abba.

Nadama da kuskuren abinda sukai din na mata yawo a duk jikinta. Balle da taga abbah ya juyo da hankalinshi kanta.

Ta sake takurewa da bango kaman zata shige ciki. A fusace abba yace mata.

"Idan shi bashida hankali ina kika kai naki?  Kinsan darajar sa Allah yai miki kuwa? Kinsan halin da kika bar iyayenki ciki kika bi namiji aka daura muku aure?

Ya Rabb. Wannan wanne irin hauka ne kukayi? Kina da tabbacin zai darajaki? Zai zauna dake har abada? Zai soki fiye da yanda iyayenki suke sonki?

Wanne tabbaci kike dashi na bazai gujeki ba?......"

Da sauri fu.ad ya katse abbah da fadin.

"Wallahi zan rike ta abba. Bazan wula....... "

Momma abba ya kalla yace

"Idan yaron nan bai fitarmun daga gida ba zan ji masa ciwo. Ku fita dashi bana son ganin shi"

Momma ta mike tana girgizama abba kai. Karasowa tai inda yake a tausashe tace.

"Dan Allah alhaji ka kwantar da hankalinka abi a tsanake......"

Safiyya kam wani irin kuka take mai sauti. Abba ya kalle ta yace.

"Kukan me zakiyi?  Namiji ne gaki gashi nan"

Har wani daci yake ji. Zuciyarshi na masa wani irin radadi. Ganin safiyya yake kamar pha.iza.

Ji yake kaman ya batar da fu.ad ya daina ganinsa. Yaushe fu.ad din yai hankali?  Harda zai rabo yar mutane daga gidansu bada sanin iyayenta ba.

Sam baya son ganin fu.ad. Muryarshi na rawa ya ke kallon su haneef.

"Ya fita bana son ganin shi."

Fu.ad dake zaune ya mike. Dan baiga zaman da yake ba. Akan me abba bazai fahimce shi ba.

Laifin shi daya bai gaya musu zaiyi aure ba. Yau abbah ya daga hannu ya mare shi har sau biyu.

Ya dauka shi kadai ya isa hukuncin laifinshi a wajensu. Abbah bai yarda dashi ba yana ganin zai ci amanar sofi ne.

Kuma ma aiba cayai ya rabata da iyayenta ba. Zai kaita suyi musu bayani basu da wani zabi.

Safiyya ya kalla. Kukanta na kara mishi zafin dayake ji kanshi nayi. Dan tun dazun yake jin har wani jiri jiri ke dibarsa.

"Taso mu tafi"

Yace mata. Ware idanuwa tai cike da hawaye. Tana rokon Allah yasa komai ya juye ya zama mafarki.

Mikewa tai da sauri. Kila in suka fita daga gidan nan hankalinta ya dawo jikinta.

Kowa kaman an dasa shi a wajen. Lukman mamaki ya hana shi tunanin komai.

Kallon su kawai yake. Haka yan biyu ma. Sunfi maida hankalinsu kan safiyya. Kayan dake jikinta. Komai nata suna mamakin wannan abu.

"Ina kake nufin zaku tafi?"

Cewar momma da a yanzun take jin kaman ta rufe su da duka dan takaici.

Bata san banbancin halayyar fu.ad din da sauran yayanta na da yawa ba sai yau.  Kanshi a kasa yace

"Idan abbah ya huce saimu dawo."

Numfashi momma ke fitarwa tana jan wani a hankali. Dan gab take da loosing dan sauran control dinta.

Wanda take da bukatarshi dan ta kwantar ma da abbah hankali. Kallon abban tai dake tsaye dafe da goshi tace

"Muje muyi magana dan Allah...... "

Bai musa mata ba ya wuce. Ta juya ta kalli fu.ad

"Ka tsaya inda kake. Wallahi zakaga bacin ran da baka taba zato ba na fito na samu baka nan"

Kai kawai ya daga mata. Ta bi bayan abbah. Sai lokacin haneef yace

"Why?"

Ya bude baki zai amsa haneef lukman yace

"Haka ake zaman tare?  Yanke hukunci babu shawara da kowa?"

Toshe kunnuwa fu.ad yai yana wani rintsa ido. Ya saki hannuwanshi yana fadin.

"Ya isa!  Ku kyaleni please. Akan me kowa zai dinga digamun ayar tambaya ne wai?"

Kallon shi safiyya keyi wasu hawayen na sake wanke mata fuska. Duk da ba hayaniya yake ba yanayin yanda yake maganar ya mata wani iri.

Oh Allah na take fadi a ranta tana tambayar kanta. Me tayi haka?  Wacce wauta tabari zuciyarta ta aikata mata.

*

"Dan Allah alhaji karkai haka. Wallahi harda rashin hankali yake damun fu.ad.

Dan Allah kazo muje dani dakai. Dasu gaba ki daya mu sami iyayen yarinyar nan"

A gajiye abbah yace.

"Da wanne ido zan kalle su? In pha.iza ce a matsayin waccan yarinyar bansan me zan ba wallahi......."

Ita kanta tasan abinda fu.ad yai babbane. Su dukansu ya taba mutuncin su. Duk da ta kula maganar bata ma gama zama dai dai da abbah ba.

Tunda bai fara hango maganganun mutane in maganar ta fita ba. A tausashe tace

"Hakan na dora shisa nace muje. Nasan duk inda hankalinsu yai dubu a tashe yake wallahi...."

Jinjina kai abbah yai. Saboda yarinyar kawai.

"Dauko mayafinki mu tafi. Amman fu.ad yabar falon nan kamun in fita"

Da hanzari momma ta wuce ta dauko hijab dinta. Ta fita falo wajen su fu.ad.

"Haneef. Lukman ku tafi a mota daya kai da su fu.ad din. Gamu nan zamu biyo bayanku yanzun."

Wani dan sanyi fu.ad yaji. Yana godema Allah. Gara ma suje ayi komai yau a kare. Tunda dai sofi ta zama tashi bashida matsala da kome zai biyo baya.

*

Motar shiru banda kuka da ajiyar zuciyar da safiyya ke faman yi. Ta wani hade jikinta da kujerar. Ta sa kanta cikin hijab tana kuka.

Kallonta kawai yakeyi. Zai barta tai kukanta iya yau. Zai bata iya yau kawai tai abinda take so.

Duk yanda kukan yake damunshi. Daga yau ba zatai kukan nan ita kadai ba. Bama yajin zai barta tai komai ita kadai.

Wannan shine tabbacin da ya dinga bama kanshi da mafarkai da yawa.

A hanyarsu ta zuwa bichi yake tsara yanda zasuyi rayuwarsu shida sofi. Daga ita sai shi.

Zai nuna mata yanda zai yi komai *Akan so*nta.

****

Inna ce tsaye tana kallon kofa tana sharar kwalla. So take taga ta ina baba zai bullo.

Yama za.ace an nemi safiyya an rasa?  Ina zataje haka?  Kuma wani abin takaicin shine ko wanda yaga giccinta babu cikin gidan.

Maganganun safiyya ke ta dawoma inna. Addua ta shiga yi kar abinda take zato ya zama gaskiya.

Ko wani yaima safiyya asiri. Dan tun yaushe take kula kaman bata cikin hayyacinta.

Yin komai take kamar wadda aka sakama battery. Shisa ta matsa da tambayarta ko lafiya sai tace bakomai.

Duk gidan anyi jugum jugum ana jimamin wannan ikon Allah. Tun suna fama da inna ta zauna har suka hakura suka kyaleta.

Ita ina taga zama batasan halin da yarta take ciki ba. Ganin shigowar baba yasa inna tarbarsa da hanzari tana.

"Anganta?"

Girgiza mata kai yayi. Ta rushe da wani kuka tana kiran Allah daya kawo musu dauki.

Shi kanshi baba kallo daya zakai masa ka gane tashin hankalin da yake ciki. Yasan yanzun kam ya kamata yaje ya sanar gidansu ado.

Kasa cema inna komai yayi. Yasa kai yana ficewa.

*
Dai dai kofar gidansu safiyya sukai parking. Gaba dayansu suka fito.

Safiyya taji wani sabon tashin hankali. Jikinta ya dauki bari. Batasan da wanne kafa ma zata shiga gida ba.

Fu.ad hankalinsa nakanta. Ganin yanda ta sake rikicewa ta a neman shidewa yasa shi kallonta cikin idanuwa.

"Breath in....... "

Yace mata ganin kaman ta manta yanda ake jan iska. Kula yai bama ta gane me yake nufi ba.

"Sofi. Kinga ki kwantar da hankalinki. Kiyi numfashi. Kija iska..... "

Can sama take jin muryar fu.ad. Sai da yai mata magana sannan ta tuna numfashinta ne take rike dashi.

Shisa take jin duniyar tayi tsaye. Haka ya dinga mata sai da yaga numfashinta ya dai daita tukunna.

Hankalinshi ya maida kan abba da yake tsaye shida momma kofar gidansu safiyya. Suna yanke shawarar momma ta shiga.

*

Yana fitowa yaga mutane tsaye kofar gidanshi da motoci guda biyu. Gabanshi ya sake faduwa.

A mutunce suka gaisa da abba. Ya dora da fadin.

"Mai gidan nan muke nema"

A dadare baba yace.

"Nine Allah dai yasa lafiya"

Dan sam baima kula da safiyya dake can gefe tana boyewa bayan fu.ad data hango shi.

"Alhamdulillah dai. Magana zamuyi"

Sauke numfashi baba yai.

"To amman dai ina sauri ne. Saboda hankalina ba a kwance yake ba....."

Da hanzari abba yace.

"Nasan yanda alaka ne da yar wajenka ko?"

Cike da mamaki baba ke kallonshi. Abba ya dora da fadin.

"Maganar data kawo mu kenan"

Juyawa yai. Yaima haneef nuni dasu karaso. Shikam baba ya tsayane yana kallon ikon Allah.

Su haneef dake tahowa yake kallo. Safiyya na bayansu dan haka baima hangota ba.

Su ukkun dai ya gane su. Musamman fu.ad dayasan fuskarshi ba zata mantu a wajenshi ba.

Yaron nan ne daya mare shi. Wanda sukai rikici da iro. Yaron nan marar tarbiya da akanshi ya soma sanin menene tsanar mutum.

Haneef kuwa sai yanzun ya tuna shi. Tun randa suka zo neman auren safiyya yake masa kallon sani.

Mamaki ya sake cika baba. Ko wani sabon neman auren safiyyar suka zo?  Yake tambayar kanshi.

Mamakin shi ya karu da suka karaso yaga safiyya bayansu kaman wadda aka koro.

Gabako daya ta wani firgice. Wani abu yaji na neman tsayawa cikin kanshi. Saboda baya so yai connecting abinda yake son yai tunani.

Bazai taba ma yiwuwa ba.
Momma ya kalla.

"Ku shiga ciki da ita ko"

Hannun safiyya momma ta kamo. Ta jata suka rakube baba dake binsu da ido suka wuce ciki.

Da sallama mama ta shiga gidan da yake cike da mutane ga mamakinta.

Da gudu inna ta karaso ta rungume safiyya tana sakin wani irin kuka tare da yima Allah godiya.

Yan gidan ma hamdala kowa yake. Wasu kuma na tofa albarkacin bakinsu.

Sakin safiyya inna tadanyi yana kallonta dan ta tabbatar da ita dince. Itama kuka take sosai.

Innar ma haka tana fadin

"On Allah mungode maka"

Hankalinta ta maida kan momma dake tsaye kawai. Tana tunanin ta inda zata fara gaya ma inna maganar data kawo su.

*

A nutse abbah ke ma baba bayanin abinda ya kawosu. Da kuma iya abinda ya sani.

Ai yana karasa fadin cewar an daura musu aure da fu.ad kaman yama baba wata allura ne.

Da hanzarin gaske yai cikin gida..........!

*

Inna ta kalli momma dake tsaye. Ta bude baki zatai magana baba ya shigo a fusace.

Safiyya dake rike hannun inna ya kama ya wurgar gefe daya tana dakin wani irin ihu.

Gaba daya gidan mamaki suke. Safiyya ya kalla yana fadin.

"Wallahi na yafeki safiyya. Ko ke kadai nake da ita yau na hakura da ke ballantana ina da wasu........!"

Da rarrafe safiyya ta taso taba rike kafafun baba tana wani irin kuka mai taba zuciya.

"Baba......!"

Tureta yai. Inna dake gefe ta kamata tana kallon baba. Riketa safiyya tai tana wani irin kuka kaman ranta zai fita.

"Ki sake ta kawai. Kinsan me yarinyar nan tai mana kuwa?

Kinsan guduwa tai da wani suka daura aure?

Safiyya wai. Safiyya fa"

Baba ke fadi yana jin kaman ya hadiye zuciya ya mutu ya huta da fuskantar wannan abin kunyar.

Ture safiyya inna tai daga jikinta tana jero inalillahi......... Tare da wasu cikin yan gidan.

Sulalewa inna tai ta fadi. Da sauri safiyya da wasu sukai kanta. Safiyya na riketa tana ihun.

"Inna....inna ki tashi. Dan Allah ku yafemun........"

Janye safiyya baba yayi daga kan inna. Tana kwacewa yana ihun kuka.

Ya jefar da ita gefe.

"Ai baki damu da halin da zaki sakamu ba kika biye san zuciyarki.

Ki kyaleta. Ki kyakemu kibi wanda kika zaba akanmu"

Tare da momma aka yayyafa ma inna ruwa ta farfado. Tana kallon safiyya ta rushe da kuka.

"Safiyya wanne abin kunya kika ja mana?

Gobe daurin aurenki. Inama kika san yaran da kika bi?

Waye shi?"

Ta kasa magana sai kuka da takeyi. Baba ne ya amsa ta da fadin.

"Yaron da ya daga hannu ya mare ni ne.

Yaron daya sa aka kullemu gabaki dayan mu. Shine ta zaba akanmu"

Girgiza kai inna take tana kallonsu. Tana so su karyata maganar da baba ya fadi.

Ture mutanen dake kusa da ita tayi ta karasa inda safiyya take ta kamata ta jijjiga.

"Ki ce mun hakan bai faru ba safiyya. Kice mun baki gudu kin auri wani ba.

Dan Allah kice mun baki auri yaron daya wulakanta mu ba"

Kuka kawai safiyya keyi. Saida inna ta sake girgiza ta sannan dakyar tace

"Nayi inna..... Wallahi nayi babban kuskuren rayuwata. *Akan so*........"

Bata rufe baki ba inna ta ture. Tsaye ta mike tana zubda wasu hawayen takaici.

"Ki fitar mana daga gida. Wallahi ni bazan miki baki ba. Zan barki da bacin ran da kika saka mu kawai....... "

Mikewa tai tana nufar inna. Da sauri taja baya.

"Zan miki baki in kika karaso inda nake wallahi. Kije gurin wanda kika zaba.

Na hakura dake. Malam ka fitar mun da ita....."

Momma ta karasa wajen inna ta kamata tana fadin.

"Dan Allah da Annabinsa ki tsaya abi abin nan a hankali. Nasan tayi kuskure.

Karku dora laifin nan akanta kawai. Harda danmu.

Mu zauna a gyara kuskuren nan"

Girgiza kai baba yakeyi.

"Kije da ita. Zuwan da kukayi ya tabbatarmun da danku bai biyo halayyarku ba.

Kaman yanda tamu tasa kafa tai fatali da duk wani mutuncin mu.

Da duk wata kauna da muka taba nuna mata"

Safiyya ya kamo dake tsaye yamika ma momma yana fadin.

"Nabar muku ita kyauta. Wallahi na yafe muku ita. Kaman yanda mahaifiyarta ta fada.

Ba zamuyi mata baki ba. Sai dai zan tsine mata duk ranar da ta zomun gida"

Kamo safiyya momma tai tana jin wasu hawayen tausayama yarinyar na zubo mata.

Wannan wanne irin bala.ine fu.ad ya jama yar mutane. Kankame momma safiyya tai tana wani irin kuka numfashinta har sama sama yake yi.

Hakuri momma ke kokarin basu amman kaman ma tunzura su take kara yi.

Dole haka taja safiyya tana tirjewa suka fita. Dan taga alamar sam ba zasu ji wata maganar fahimta ba.

*

Wani irin kallo abbah kema fu.ad dayake cike da fassarori kala kala.

Balle dayaga momma ta fito rike da safiyya dake wani irin kuka. Itama hawaye take ta kalli abba tace.

"Gobe daurin aurenta......... Fu.ad......"

Kasa karasawa tai saboda kukan da yaci karfinta. Wannan wanne irin abune.

Girgiza kai abba yake yana fadin.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un"

Me fu.ad yai haka. Me wannan yaran sukai haka. Kallon shi ya mayar kan fu.ad da yake tsaye can gefe.

Sannan ya kalli momma.

"Ki saketa ta tafi wajen shi. Bana son ganin shi a gidana. Kar su zomun gidana......."

Fuskarta ta goge tana sake rike safiyya.

"Ina kake so suje? Dan Allah kabari muje gida. Karka yanke hukunci cikin fushi"

Cikin idanuwa ya kalleta sannan yace.

"Inhar naga fu.ad cikin gidan nan zan iya yanke kowanne hukunci cikin bacin rai.

Su tafi gidana na hotoro..."

Bata son yi masa musu. Da kanta ta kama safiyya taje ya bude mota ta sakata. Ta dawo ta kalli haneef.

"Ka sauke su gidan abbanku na hotoro. Idan na lallabe shi....."

Fu.ad dake gefe ya katse ta da fadin.

"Kibar shi kawai momma. Ina da wajen da zamu zauna"

Cike da wani takaici ta kalli fu.ad.

"Bacin ran da muke ciki bai isheka ba ko?"

Wani daci yake ji ga kanshi na ciwo.

"shisa nace ina da wajen da zamu zauna. Abbah baya son ganina.

Saboda me zan zauna masa gida?"

Wucewa kawai momma tayi batace komai ba. Batason ya kara bata mata rai. Addu.ar shiriya take ma fu.ad din.

Haneef ma wucewa yai dan ya tabbata in ya tsaya zasu kwashi yan kallo ne da fu.ad din.

Lukman ya kalle shi.

"Really?"

Lumshe idanuwanshi yai ya bude su yana saukewa kan lukman.

"Banda kai ma please. Abin zai mun yawa"

"Banda kana da concussion babu abinda zai hanani punching dinka"

Wani gajeran murmushi kawai yai daya tsaya iya fuskarshi ya wuce ya bude motar ya zauna kusa da safiyya dake kwance luf jikin kujera.

Yasan lukman sarai. Ya masa fushi amman zasu shirya. Kaman yanda yasan zasu shirya dasu abba.

Komai na bukatar lokaci.

*

Kofar gidan haneef yai parking. Budewa yai ya fita yace ma safiyya ta fito.

Babu musu ta fito saboda jinta take wani sama sama. Ga wani zazzabi daya saukar mata.

Koya ta rufe idanuwanta sai taga yanda baba ya banbareta daga jikinshi ya cillar.

Yanda inna ta tureta take fadin bata son sake ganinta
Wani irin radadi take ji. Ga kirjinta na mugun zafi.

Zagayawa yai yace ma haneef.

"Motata please. Credit cards na and......."

Wani mugun kallo haneef yai masa. Baice komai ba ya fisgi motar yana yin reverse. Sauke numfashi yayi.

Zai kira lukman. Yasan bazai qi kawo masa ba. Beside ba zama zai gidan nan ba. Baya son komai na abba sai ya huce.

Hannun safiyya ya kama. Yanajin yanda take kiciniyar kwacewa yaja ya tsaya. Cikin idanuwanta da har sun kankace saboda kuka ya kalla yace.

"Ki kalle ni sofi. Zan dai dai ta komai. Ban miki alkawari zuwa yaushe ba. Amman na miki alkawari komai zai wuce.

Ni da ke ne cikin wannan abin. *Akan so*n da mukewa juna ne komai yake faruwa.

Ke kadai nake da yanzun. Ni kadai kike da. In baki tayabi ba taya kike so mu gyara komai?"

Yanayin sanyin muryarshi taji yana mata wani tasiri na daban. Ta gasgata kalamansa. Ta karbi alkwarinsa.

Hawaye suka zubo mata. Kai ta daga masa. Yasa hannu ya goge mata hawayen dake fuskarta.

Wani sanyi yaji ya ratsa shi na daban. Kama hannunta yai zuwa cikin gidan. Wajen mai kula da gidan ya karbi keys.

Ba wani girma gare shi ba. 3 bedroom flat ne. Budewa yai. Ya tsaya bakin kofar yana addu.a.

Kallo safiyya tabishi dashi. Saida ya gama sannan yaja hannunta suka shiga ciki. A falo ya zaunar da ita da kanshi ya shiga kitchen ya dauko cup.

Fridge din dake kitchen din ya bude. Bakomai ciki. Numfashi ya sauke yana fadin.

"Great.....!"

Fanfon kitchen din ya bude ya dibo ruwa ya kawo mata. Ta girgiza masa kai. Bata son shan komai.

Lukman ya kira. Wajen sau biyar yaki picking. Text yai ya roke shi daya kawo masa motarshi da wasu abubuwa.

Text din na shiga da yan mintina ya sake kiran lukman. Picking yai da fadin.

"Karka dame ni. Nake jin abinda ka ga dama kake yi?  Tam nima sai naga dama"

Sauke numfashi yai.

"Lukman please. Gidan bakomai fa. Badan ni ba. Ko dan sofi....."

"Naji....."

Ya amsa yana katse wayar. Murmushi yai ya maida kallonsa kan sofi da taja jiki ta kwanta kan kujerar.

Zazzabi take ji sosai a jikinta. Kula yai jikinta kaman yana rawa. Da sauri ya karasa inda take.

"Sofi..... Menene?"

Dakyar ta iya ce masa.

"Kaina ciwo... "

Hannunshi yasa a fuskarta yaji wani zafi. Ya dauka dazun daya rike hannunta zafin dayaji wani abinne daban.

"Damn...."

*#TeamAS*

No comments:

Post a Comment