Thursday 4 May 2017

AKAN SO 3

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

        03

*19/02/2017*

Farar suit dinta ta dora saman kayan jikinta sannan ta sanya qaramar hijab itama fara.
 

Tayi matuqar kyau. Ta dauki qatuwar jakarta sannan ta manna glass fari mai ratsin zaiba.
          

"Honey J zamu fita tare ne?" Ta buqata.

Tun jiya yake sha mata kamshi. Tayi lallashin duniya. Yauma sanda ta tashi tagama hada komai.

Tabar Atika ta karasa shirya mata umar dan yasir ya iya komai da kanshi.

Bai jirata ba yai breakfast dinshi. Gaisuwarta ma dakyar ya amsa.

Idanuwansa da suke dagula mata lissafi ya kafa mata.
A daburce tace

"alright bara na wuce kawai may be........."

Katseta yai da fadin

"Jana wato rayuwar wasu tafi maki muhimmanci akan tamu right?"

Ta lumshe idanuwanta ta budesu sannan tace

"Na dauka mun gama maganar nan fa"
  

Saukowa yai daga kan gadon yazo inda take ya tsaya suka fuskanci juna.

Idanuwansa ta kalla sosai yauma rikici yake ji ita kam ba zata biye masa ba.

Juyawa tai da niyyar tafiya ya janyo hannunta hadi da fadin

"Jana kina da hankali kuwa?"

Zuciyarta ke wani irin dokawa duk da hakan ba baqon abu bane in har jikinsu zai hadu ita dashi.
     

"Ikram ce kwance a daki"

Ya furta a dake.

Saida ta hadiye miyau dan bakinta ya bushe sannan tace masa

"Nayi mata komai da take buqata bacci ma take and Honey J ikram ba qaramar yarinya bace dan qaramin zazzabi duk ka wani damu"

Kallon da yake mata yasata yin shiru. Har wani huci yake,muryarsa daqyar take fita yace

"Karamin zazzabi? Jana kin daina damuwa damu ko? Aikinki yafi maki muhimmaci? Good!"

Kamin tace wani abu ya fice ya doko qofar da qarfi.

Wasu siraran hawaye suka zubo mata.

Ta cire glass dinta ta sa hannu ta goge su.

Ji take zuciyarta duk bata mata dadi. Tasan yanzun haka patients nacan sunata jiranta.

Fitowa tai zuwa falo. Ta samu Jabir zaune kan kujera. Tazo wucewa ta kalle shi ya watsa mata wani kallo.

Har takai qofa taji ikram tace mata

"Mami yauma fita zakiyi?"

"Ya Allah"

ta furta cikin ranta ta bude baki zatai magana jabir yace

"ikram dakin koma kin kwanta ni zan zauna tare dake."

"Thank you pa"

Ikram ta fadi tana wucewa.
Jana ta kalli jabir da ya dauke fuska yana ta dacin rai.

Addu.a tai sannan ta fita daga cikin gidan zuwa inda motarta take.

*

Kafa yasa ya ture table din dakin yana fadin.

"Damn it"

Wayarshi ta soma vibrating cikin aljihu. Ya dauko ya duba.

Ayna ce. Ya daga hadi da fadin

"Hello"

Cikin sanyin muryarta dayake burge shi tace

"Assalamu alaikum"

A hankali ya amsa sallamar. Dabi.ar aina ce bata amsa hello. Tafi gane kai mata sallama.

"Zanji ya jikin ikram ne. Naga baka shigo office ba"

Murmushi ya kwace masa. Zai iya karantar kunyar da take ji daga muryarta.

"Taji sauki. Aiki yama jana yawa a office shine nace zan dan zauna da ikram din"

Ya amsa cike da jin dadin kulawar data nuna.

"Allah ya bata lafiya. Sai anjima"

Batama jira amsarshi ba ta yanke wayar. Ya cire wayar daga kunnenshi yana zuba mata idanuwa.

Yasani. Kallon jana kawai na saukar mishi da kwanciyar hankali. Babu karya a soyayyarta da take zuciyarshi.

Abinda yafi rikita mishi kai shine yanda yake jin matsayin ayna a zuciyarshi.

Gani yake kaman yinin da jana take wajen aiki. Shi ya bada gap din shigar wata zuciyarshi.

Shi kanshi yasan a satin nan. Dalilin fada kawai yake nema da jana.

Dan hakan ne kawai zaiji kaman baici amanarta ba daya bari son wata ya shigar mishi zuciya.

Kwanciya yai ya lumshe idanuwanshi.

****

Kwance yake kan kujera. Kanshi na kan cinyar zainab da yake ta danne danne jikin wayarshi.

"Zee saikin cinyemun chargy ko?"

Lukman ya fadi yana mika hannu zai karbo wayarshi. Hannunshi zainab ta ture tace.

"Dagamun cinya nima. Sai in baka wayarka"

Gyara kwanciyarshi ma yai. Ta ture masa kai cikin sigar wasa.

"Maza karyamun cinya."

Dariya yai.

"Nikam kin budemun data. Sakonni nata shigowa ko"

Dariya zainab tai. Neman rigima ne kawai yasata daukar mishi waya. Whatsapp dinshi ta shiga.

"Bara na dinga karanto maka sakonnin saika fadi reply din da kake so in rubuta"

Zaro idanuwa yai yace

"Idan kuma babyna tamun sako fa?  Saikinga sirrinmu"

Murmushi zainab tayi. Tanajin dadin yanda akwai yarda da fahimta mai karfi tsakaninta da mijinta.

Shekarunsu na biyar kenan da aure. Da yaransu guda daya ga na biyu nan a cikinta.

Amman kullum soyayyarsu da yarda karuwa take. Sam bata da shamaki da wayarshi.

Tasan lukman ko da wata tace tana sonshi saiya fada mata.

Tun tana kishi harta hakura. Don tasan inya tashi kara aurenshi bata isa ta hana ba. Kuma ba boye mata zai ba.

Wani sako ne yaja hankalinta. Da wani yanayi a muryarta tace.

"Dee fu.ad ba abokinku bane?"

Jin sunan fu.ad a bakinta ya sashi mikewa babu shiri. Wayar ya karbe daga hannunta yana fadin.

"Fu.ad???"

Da mamaki karara a muryarshi. Hamza ne ya turo masa wata wasika ta wata yarinya.

Daga kasa yace.

"Lukman anya wannan ba yar Moh bace?"

Kanshi yaji ya wani bala.in sarawa.

Zainab ta taba hannunshi a tsorace ganin yanda fuskarshi take dauke da tashin hankali.

"Dee?  Lafiya kuwa?  Meke faruwa?"

Iya saninta fu.ad wani bangare ne na rayuwar lukman da baya so a fada.

Ta rasa gane alaqarsu. Tasan cewar abokinshi ne da dadewa. Hakanma wani hotonsu ne data gani ta tambaya.

Koda ta bukaci ko fu.ad din na ina yanzu cayai mata tabar maganar. Saboda bai taba boye mata komai ba sai fu.ad yasata girmama rokonshi.

Banda yau bata sake maganar ba kaman yanda shima bai kara ba.

Lukman wani juyi yaji kanshi nayi. Babu yanda za.ai ace fu.ad nada yarinya.

Ta ina?  Ta yaya?  Wacece ita. Ya dauka sofi tabar garin da jimawa saboda ya gwada nemanta bai ganta ba.

Zainab ya riko jikinshi ya rungumeta sosai.

Rike shi tai itama. Sumbatar gefen wuyanshi tai.

Ta janye jikinta dashi tana hada bakinta da nashi da wani salo na kokarin mantar dashi koma menene.

A hankali take aika mishi sakonni saida taga yadan nutsu tukunna tace.

"Dee meke faruwane wai?"

Numfashi ya sauke. A nutse yace.

"Zan fada miki. Right now zanje inyi wani abu tukunna"

Tare suka mike ta rakashi har bakin kofa.

Saida ta sake tallabo fuskarshi ta sumbace shi sannan tace.

"Allah ya dawomun dakai lafiya. Ka kula sosai dee"

Kai ya daga mata. Ya tsugunna ya sumbaci cikinta sannan yace.

"In shaa Allah. Ki kulamin da kanku. Zan kiraki"

*

Address din makarantarsu nana ya sake dubawa da hamza ya aiko mishi dashi.

Makarantar crescent bata mishi wuyar ganowa ba. Kasancewar bata shiga lungu ba.

Kai tsaye office din principal ya wuce. Suka gaisa sannan ta tambaye shi ko ta ya zata iya taimaka mishi.

"Wata yarinya nake nema. Nana bansan ko da wanne suna take amfani ba dai. But anan makarantar take"

Kallonshi principal din take. Yanayin nutsuwarshi da kamala shi yasa ta cewa.

"Eh nan makarantar take. Amman gaskiya kayi hakuri.
Saboda mamanta ta mana kashedin cewar karmu bar dan jarida ko daya yai magana da ita"

Sauke numfashi lukman yai zuciyar shi na wani dokawa.

"Badan jarida bane ni. Abokin babanta ne. Kuma ba sainai magana da ita ba. Ko daga nesa ne ki taimakamun in ganta"

Saida ta dauki mintina tana tauna maganar tukunna ta mike tace ya biyota zuwa cikin makarantar.

Kafafuwanshi har rawa suke. Baima san kalar addu.ar da yake yi ba. Bai kuma san yanayin da yake ji ba.

Ta window din ajin suka tsaya. Tace masa kaganta can a front sit.

Kaman nana tasan ita suke son gani dai-dai dagowar fuskarta tana dariya akan wani abu da kawarta tace.

Kafafuwanshi kasa daukar shi sukai. Bangon wajen ya dafa ya tsugunna yana karanto.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un"

Babu adadi. Idanuwanta. Idanuwanta sak irin na fu.ad ne. Yanayin dariyarta.

Yarshi ce. Fu.ad yana da yarinya. Ko ina na jikinshi kyarma yake.

Wayarshi ya dauko.

Lambobin fu.ad da a duk tsayin shekarun nan ko saving dinsu baiba dan kar tsautsayi yasa ya gwada kira ya shiga sakawa.

Dan zaune suke daram cikin kanshi. Ta london ya fara gwadawa bata zuwa.

Ta europe ya saka. Bugu daya ta shiga........!

****

*19/02/2017*

Aikam tasan ba karamun taimako Allah yai mata ba data taho da ansar.

Yan jarida ne cike bakin kofar makarantarsu nana. Dakyar ya ture su suka shiga ciki.

Ba karamar godiya taima principal din ba da bata ko bari nana tasan da zuwansu ba.

Bata kuma nemi wani karin bayani ba. Tadai bama sofi tabbacin cewar indai babu yardarta ba zata ma bar kowa yaga nana ba.

Fitowa sukai. Cikin yan jaridun harda Yusra fari. Tana zaune a gefe hakan yasa sofi cema ansar ya bata mintina biyu.

Sallama taimata. Cikin fara.arta din nan dake burge sofi ta amsa suka gaisa. Ta fada mata itace mahaifiyar nana.

Sosai Yusra taji dadi. Dan a yanzun babu labarin dayaja hankalin mutane da social media gabaki daya irin na Nana.

Kowa so yake yaga yarinyar.

"Da zaki taimaka mana ko da mintina biyar ne. Muyi magana da ita kila zai taimaka wajen gano babanta.

Abin ya kara jan hankalin mutane jin cewar baban nana dan wasan kwallon kafa ne"

Cewar yusra. Wani
murmushin takaici sofi tai sannan ta amsa da.

"Hakan ne yasa bana son nana tai magana daku. Kema dan kina burgeni yasa nai miki magana"

Cike da tausayawa yusra tace.

"Nagode sosai. Ba lallai ki yarda da cewar akwai mutane da dama da kaunar yarki ne yasa su son ganinta ba. Bawai son jin labarinta ba"

Jakarta yusra ta bude ta dauko katinta tace.

"Please ki kirani idan kin canza shawara. Nagode sosai."

Karba sofi tai sukai sallama ta koma wajen ansar. Shi ya sauke ta asibiti dan da motarshi ma suka fito.

*

Tunda doctor jana ta soma bayaninta babu inda baya rawa a jikin sofi.

Tama kasa tambayarta wani abu. Ansar ne ma dake zaune yai karfin halin cewa.

"Options nawa muke dashi doc?"

A nutse doc jana tace.

"Option dayane kawai ansar. Shine transplant idan an samu match"

Cikin rawar murya sofi tace.

"Idan ba.a samu match bafa?"

Shiru doc.Jana tai. Cikin aikinta babu abinda tafi tsana banda wannan bangaren.

Kallon mutane a kullum lokacin da zaka fada musu mutuwar wani nasu. Ko lokacin da zaka tarwatsa musu burinsu da magana daya.

Cikin wani karfin hali sofi ta sake cewa.

"Wata nawa muke dashi da ita in ba.a samu match ba?"

Muryar jana can kasa tace.

"Rayuwa a hannun Allah take safiyya. Zan iya cewa kasa da wata shidda. Idan Allah yai karfin ikonshi shekara daya"

Mikewa sofi tai. Gaba daya kanta taji wani abu yai shiru. Bata jin duk kiran da ansar yake mata.

Tafiya kawai take badon tana gane inda take saka kafafuwanta ba harta fita daga asibitin.

Ita kanta ba zatace ga yanda akai ta gane motar ansar ba. Ta bude ne kawai ta shiga ta zauna.

Gida ansar ya sauke ta. Saida ya tabbatar ta bude ta shiga tukunna ya koma office da wani nauyi a zuciyarshi.

No comments:

Post a Comment