Saturday 6 May 2017

AKAN SO 42

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

www.Loobnerh.blogspot.com

Wattpad: LubnaSufyan

              42

*Tabbas duk wata daukaka bata zuwa ma bawa babu jarabawa a cikinta.*

*Da yawan kusancinka da Mahaliccinka da yawan kaddarar dq zaka fuskanta. Allah ya bamu hakurin zama da juna. Allah ya bamu juriya da kauda kai daga zagin da muke sha a kullum*

*Habibtee Allah ya kara daukaka. Allah ya kara hakurin zama da mutane. Ki kauda kai. Ki toshe kunnenki.*

*#AnaTare*

Hannun Inna safiyya ta kara kamawa ta rike cikin nata. Dan gani take kaman zata bace kowanne lokaci. Dayan hannun ta kamo mayafinta tana goge hawayen da suke zubo mata.

Muryarta a dishe saboda kukan da takeyi tace.

"Inna kun yafemun da gaske?"

Kwalla Inna ta share tana daga ma safiyya kai. Ta mayar da kallonta zuwa wajen baba dake zaune yana kallonta ciki  da wani yanayi.

"Baba...."

Girgiza mata kai yayi alamar tayi shiru.

"Mun yafe miki safiyya. Duniya da lahira. Kema ki yafe mana bacin rai ne yasa muka ko....."

Da sauri safiyya tace.

"Baba kabari. Bakuyimun komai ba. Wallahi bakumin komai ba...."

Kasa karasa maganar tayi saboda wani abu daya tsaya mata a wuya. Kokarin hadiye shi tayi ta kasa.

Muryarta kasa kasa tace.

"Ina yaya?"

Wani murmushi Inna tayi da safiyya taji tana son ace itace sanadin bayyanarshi. Murmushi ne dake cike da alfahari.

Irin murmushin da kowanne da zaiyi farin ciki ace shine sanadin bayyanarshi a fuskar mahaifanshi kamun tace mata.

"Yana nan lafiya safiyya. Yana aiki a gidan radio. Da matarshi da ya'ya biyu"

Murmushi safiyya tayi kamun lokaci daya wani abu na daban ya maye gurbinshi. Har ranta take jin shekarun data rasa tare dasu da bazasu taba dawowa ba.

"Zanso ingansu"

Ta fadi a sanyaye komai na dawo mata.

"Zaizo ya kawo su anjima da yamma"

Baba ya fadi da kalar murmushin dake fuskar inna. Hade hannayenta safiyya tayi tana son taga sun kalleta da irin alfaharin nan.

"Kinbar mijinki a waje. Ba zakice ya shigo ba"

Inna ta fadi. Kallonta safiyya tai da sauri hawaye na sake taruwa cikin idanuwanta. Girgiza ma inna kai take wani kukan na kwace mata.

Ranar da fu.ad yabarta na dawo mata kaman lokacin abin ya faru.

****

Kofa take kallo tana son ta gasgata da gaske fu.ad yasa kafa ya fice bayan furta mata kalmar data wargaza duniyar da suka gina.

Kalmar dake barazanar tsayar mata da bugun zuciyarta. Mikewa tai hannuwanta na rawa take kallonsu. Kamun ta mayar da kallonta zuwa ko ina na dakin.

Da sauri ta karasa wajen kofa ta kama handle din ta bude jikinta na rawa. Kallon hanyar waje tayo taga ko alamar fu.ad bata gani ba.

Ya tafin da gaske. Zame jikinta tayi wajen kofar tana zama. Wani irin kuka ta saki daya fito tun daga zuciyarta da take jin tana tarwatsewa.

Sautin kukanta ne ya shigo da mama indo data zo wucewa taji ta. Ganinta durqushe tana wani irin kuka yasa mama indo karasowa inda take da sauri.

"Subahanallahi. Safiyya lafiya?"

Kamata mama indo tayi. Safiyya ta makale jikinta tana wani irin kuka mai taba zuciya.

"Safiyya menene? Ko wani ya rasu?"

Ta kasa magana jikinta bari kawai yake da karfin kukan da take. Da wani ya rasu zaifi mata sauki saboda wannan abune da ka riga da ka san zai faru.

Abinda fu.ad yai mata ko da wasa bata taba hango shi ba. Dago kai tayi muryarta na rawa tace.

"Ya sakeni............ya tafi. Komai ya..... Komai ya kare......bani da kowa"

Fadar datai ya sake tabbatar da abinda yake faruwa. Da gaske bata da kowa. Babu su inna. Fu.ad kadai ya rage mata shima ya tafi abinshi.

Numfashinta taji yana wani irin daukewa saboda tashin hankali. Bata da kowa. Bata da inda zataje a wannan duniyar da batasan kanta ba.

Tanajin yanda mama indo ke girgiza ta. Saidai sam ta kasa dai daita numfashinta dake daukewa. Wani irin duhu taji ya mamaye kanta kamun daga bisani duhun ya zo har cikin idanuwanta.......!

****

"Safiyya!!!"

Inna ta fadi tana girgizata da katse mata tunaninta.

"Safiyyaa....!"

Da sauri tana ware idanuwanta kan Inna tace.

"Na.am"

"Lafiyarki kuwa?"

Ta girgiza kai. Ita kadai tasan abinda zuciyarta ke mata. Nauyin da take ji a cikin. Wasu zafafan hawaye na sake biyo fuskarta tace ma Inna.

"Alhaki bai barmu mun samu farin ciki ba. Rashin albarkar iyaye a auren mu ya sa baiyi nisa ba. Ya sakeni shekaru sha daya da suka wuce"

Daga inna har baba wani shocked Expression ne dauke a fuskarsu. Safiyya tai wani murmushi cike da takaici.

"Karkuyi mamaki inna. Babu dan dazai ga dai dai babu albarkar iyaye a rayuwarshi......."

Cikin nutsuwa take basu labarin yanda komai ya faru. Take basu labarin nana. Yanda inna ta rikota jikinta cike da kauna da tausayawa ba karamin taba zuciyar safiyya yayi ba.

Cikin kuka take fadin.

"Nana din ma ba mai tsahon kwana bace ba inna"

Baba ne ya jinjina kai yace.

"Hakika rayuwa wani abu ce mai cike da darussa kala kala. Dabara daya ce mai rai zaiyi. Shine kokarin gyara lahirarshi"

Cike da yadda da abinda baba yace inna ta karbe da fadin.

"Babu komai da yake da tabbas a zaman duniya. Dawamammen farin ciki na tare da wanda ya cika da imani"

Sake kwanciya safiyya tayi jikin inna. Dumi da kaunar mahaifiyarta na saukar mata da wata nutsuwa ya daban. Kamun baba yace.

"Da kun maida aurenku safiyya. Kaddarar data hadaku mai girma ce. Allah ne kadai yabar ma kanshi sanin abinda ke tattare da rayuwarku"

Mikewa zaune safiyya tayi zuciyarta cike da nauyin maganganun da baba yayi. Ba auren fu.ad bane matsalarta. Ba rashin haihuwarshi bane damuwarta.

Dan daga randa ta san tana da cikin Nana ta fahimci haihuwa kyauta ce ta Allah. In ya rubuta maka samu baka isa ka canza hakan ba ko min kinka kuwa.

Da nisantaccen yanayi a muryarta tace.

"Baba bana son sake rasaku. Na dandana hakan yafi komai ciwo da daci. Tunanin rasa Nana baikai tashin hankalin tunanin kin sake ganinku ba"

Sauke numfashi baba yayi.

"Ba zaki rasamu ba safiyya. Mutuwa ce kawai zata rabamu in shaa Allah. Muma munji rashinki wallahi"

Ta rasa daga inda sabbin hawaye ke sake zubo mata. Muryarta na rawa tace.

"Bazan sake abinda babu albarkarku a ciki ba. Komenene"

Jinjina kai baba yayi. Ya mike da fadin.

"Ina zuwa"

**

Zaune yake cikin mota ya lumshe idanuwanshi. Baisan iya lokacin daya dauka ba a haka. Babu tunanin komai a ranshi banda na safiyya da nana.

Su kadai yake gani cikin zuciyarshi da idanuwanshi. Hadata da iyayenta shine abu na farko dayake alfahari da bata shi.

Ko ba komai ya dawo mata da wani bangare na rayuwarta dayai silar salwantar dashi. Ya samu nutsuwa daya kasa samu na tsayin lokaci.

Bazai taba manta abinda yagani cikin idanuwanta da kan fuskarta ba lokacin datai tozali dasu inna.

Kaman yanda bazai manta yanayin dayaji ba lokacin daya rike hannuwan abbah bayan lokaci mai tsayi. Kauna kenan.

Wannan itace kaunar dake tsakanin mahaifa da yayensu. Kaunar da Allah ne ya dasata shi kadai yasan girma da nauyinta.

Abinda yake ji akan Nana babu kalaman da zai amfani dasu wajen fassarawa. Yasan zafin kaunar iyaye. Yasan darajarsu bazai taba bari su sake kubce masa ba.

Ji yai an kwankwasa glass din murfin motar. A nutse ya dago daga jinginar dayai da kujera. Ganin baba ne yasa shi bude wa ya fito da sauri.

Zuciyarshi na wani irin dokawa dan ya dauka wani abune ya samu safiyya yace.

"Baba lafiya dai ko?"

Murmushi baba yayi yace mishi.

"Ba abinda ya sameta"

Wata kunyace ta lullube fu.ad ya sadda kanshi kasa ganin baba ya karanci manufar tambayarshi.

"Muje ciki sai muyi magana a nutse"

Ba musu fu.ad ya rufe motar yabi bayan baba har cikin gidan. Daki suka nufa. Kan safiyya dake lafe jikin inna fu.ad ya sauke idanuwanshi.

Nutsuwar dake kan fuskarta ya saukar mishi da wani nishadi na daban. Waje ya samu kasa ya zauna duk da kujerun dake cikin dakin.

Wata kunyace ta kamashi dayake tuna girman laifukan daya aikata musu. Baisan ta inda zai fara ba.

Kanshi a kasa yace.

"Wallahi bansan ta inda zan fara ba. Ni mai laifi ne a gareku inna. Inajin nauyin rokar yafiyarku saboda laifina mai girma ne"

Shiru fu.ad yai kanshi a kasa yanajin yanda laifukanshi ke danne shi. Baba yace.

"Allah ma ana mishi laifi ya yafe ballantana dan adam. Mu suwaye da zamu rike ka da abinda kai nadama akai?

Abinda ya faru ya rigada ya faru. Bai kamata muna duba baya ba. Mukam mun yafe duniya da lahira. Allah ya yafe mana gabaki daya"

Inna ce ta amsa da amin. Dan fu.ad ya kasa magana. Yana jinjina ma karamcin su baba ne. A nutse baba yace.

"Safiyya ta fada mana komai. Kaman yanda na fada mata san sake fada maka. Ina tunanin kaddarar data hadaku tana da girma.

Dakun yafi juna kun maida aurenku kodan yarinyar dake tsakaninku. Ku kula da ita a tare zaifi"

Da sauri fu.ad ya dago ya kalli safiyya. Sosai yake duba idanuwanta yaga ko zaiga tsanar shi ko kin yarda da maganar baba.

Ya kasa karantar komai. A tsorace yace.

"Baba bansan me zance ba. Bana son sake yima kowa laifi......"

Ya karasa maganar yana ware idanuwanshi kan baba. Murmushi yayi.

"Babu damuwa. Kuyi shawara a tsakaninku. Karku dauki lokaci. Rayuwar bamai tsayi bace ba. Yar'ku na bukatarku"

Cikin sanyin murya fu.ad yace.

"Banda shawara nikam. Ina son yin komai dai dai ne. Ina son gyara komai saboda ban samu nayi daga farko ba.

Zan magana da abbah yau in shaa Allah"

Kai safiyya ta sadda kasa hawaye ba zubo mata. Oh rayuwa kenan. Albarka inna da baba suka saka musu hakan ya musu dadi sosai.

Shiru yadan gifta na wani lokaci cikin dakin. Kowa da abinda yake sakawa cikin zuciyarshi. Fu.ad hamdala yake ta jerowa.

Yasan bai cancanta a sake bashi auren safiyya ba. Saboda bashida abinda zai bata. Saidai bazai iya hana zuciyarshi son sake aurenta ba.

Ya sake tabbatar da sonta da yake yana nan daram. Babu inda yaje. Muryarshi ya sauke kasa sosai yace.

"Baba zan tafi. Zan kirata in fada mata idan munyi magana dasu abbah"

"Allah ya bada iko ya tabbatar mana da alkhairi"

Fuad yana mikewa ya amsa da.

"Amin baba. Inna nagode sosai. Allah ya kara girma"

Safiyya ya kalla. Yana jin nauyin yai mata magana gabansu inna yasa kai ya fice daga dakin. Inna tace ma safiyya.

"Kije ko zakuyi magana"

Dakyar ta iya mikewa jikinta ya mata wani irin nauyi. Yanajin takunta ya juyo da sauri. Tsayawa yai harta karaso inda yake bakin kofar da zata fitar dashi soron gidan.

Ta rasa ta inda zata fara mishi magana. Kome zatace. Abubuwan da take ji suna da yawa yau.

Ganin tayi shiru yasa shi fadin.

"Tunda Nana na gida. Saiki kwana wajen su inna kema ko?"

Taji dadi sosai. Dan ko bai fada ba batai niyyar binshi su koma ba. Saidai yaune rana ta farko data rabu da nana.

Da zata kwana a wani waje ba tare da yartata ba. Ba zatai ma kanta karya ba. Har kewar nana ta fara damunta. Ga tsoron kar aki kula da ita yanda ya kamata.

Gani take kaman wani abin zai faru. Idanuwanta cike da tsoro tace ma fu.ad.

"Kar a bata madara da yawa. Na bata magungunanta duka da zatai amfani dasu.

Karka barta taje wajen ruwa. Ko tasha abu mai sanyi sosai. Ka taba jikinta duk minti sha biyar kaji ko da zazzabi.

Daka ga tayi shiru ka tambayeta. Bata son fada in wani abu na mata ciwo. Karta kwana ita kadai and kuma dakaga matsala dai ka kirani please......."

Murmushi fu.ad yayi. Wani burge shi take yanda duk ta daburce sai lissafo mishi ka.idoji take. Ganin kallon da yake mata yasa tadanyi murmushi itama.

"Ka kula da ita sosai dan Allah"

"Karki damu. Babu abinda zai same ta in shaa Allah. How bouh' in kira kuyi magana lokaci lokaci"

Taji dadi sosai. Ta daga mishi kai alamar hakan ya mata. Harta juya yace.

"Sofi....."

Juyowa tayi ta zuba mishi ido. A raunane yace mata.

"Banda abinda zan baki sofi. Kinsani ko?"

Batace komai ba. Shiru tayi tana son fahimtar maganarshi. Ya dora da fadin.

"zan fahimta idan bakya son sake aurena. Wallahi zan fahimta duk da zuciyata ba zata so ba"

Gaba daya ya karasa kashe mata jiki. Ita yanzun burinta yagama cika. Ta ga su inna ta samu yafiyarsu. Shi kanshi haushin da yake bata ta neme shi ta rasa.

Duk da ba zata iya tsayar da abinda take ji a kanshi ba.

"In har baba ya hango kaddararmu mai girma ce banida bakin musu."

Da sauri yace.

"Farin ciki nake so ki samu. Ko da ba tare dani bane ba"

Sauke numfashi tayi.

"Na same shi a yau fu.ad. Nagode da cikamun alkawarin nan"

Wani kasalallen murmushi yai mata.

"Hmm sofi. Alkawarin daya daukeni shekaru"

Kallonshi tayi.

"Bance ga ranar dazan cika miki alkawarin nan ba. Amman komin dadewa zan gyara komai.

Wannan shine kalamanka a gareni. Ko harka manta?"

Wannan karin murmushin dayai har cikin zuciyarshi yakai.

"Ban manta ba. Ban manta komai ba"

Jinjina mishi kai tayi. Ta juya tanajin shi ya furta.

"Nagode. Nagode sosai sofi"

Bata juyo ba. Da murmushi a fuskarshi ya fice daga gidan.

*

Daki safiyya ta koma ta zauna gefen inna. Sai yanzun abinda ke manne a ranta ya fado mata.

"Inna ina usman?"

Ta bukata. Kaninta mai sonta. Usman da lokutta da dama in nana tayi wani abin takan tuna mata dashi.

Hada ido taga inna da baba sunyi kamun suyi shiru kowa na sadda kanshi kasa. Wani irin bugawa taji zuciyarta tayi.

Lokaci daya tsoron da ta kasa fadar kalarshi ya rufeta har tsikar jikinta ta tashi. Muryarta a sarke tace

"Innaa"

Kauda kai gefe inna tayi. Safiyya ta mayar dashi kan baba.

"Baba ina kanina? Ina usman? Dan Allah ku fadamin"

Cikin wani yanayi baba yace.

"Ya rasu safiyya. Shekara hudu kenan. Ciwon ciki na yini daya...."

Kanta ke juya mata. Girgiza kai take yi tana jin zufar dake keto mata tako ina. Inna ta kama hannunta.

"Sai hakuri safiyya. Allah baiyi zaku sake hada fuska a duniya ba. Yafi kowa jajenki. Babu inda bai nemeki ba"

Wani irin kuka ya kwace ma safiyya marar sauti. Zuciyarta take ji kaman ta ciro ta ajiye gefe tadan samu sa.ida saboda zafin da take mata.

Usman ya rasu. Rufe idanuwanta take tanajin yanda suke mata wani yaji yaji amman hawaye ko daya yaki fitowa.

Tana tuna shi. Tana tuna komai nashi. Yanayin maganarshi. Rikota inna tayi jikinta amman sam safiyya taki.

Matsawa tayi ta hade kanta da gwiwa so take karsu lallasheta. Subarta taji mutuwar usman. Taji rashin kaninta da bata samu ta mishi sallama ba.

Kaninta dazaiji ta manta dashi saboda ko sau daya bata taba aika mishi da sakon addu.a ba tunda bata san ya rasu ba.

Mutuwa na da daci. Dacinta bazai fahimtu ga wanda baisan yanda take ba. Wanda bai taba rasa wani makusancin shi ba.

Allah sarki usman yaron kirki. Yaro nai cike da kauna da fahimtar kowa.....!

****

Bai kokarin hana zuciyarshi tsalle tsallen da take ba. Yana cikin mota ya kira lukman. Bugu daya ya daga.

"Bazawari"

Baisan lokacin daya kwashe da dariya ba. Ya manta rabon dayai kalarta haka. Wai bazawari. Lukman din ma dariya yake.

"Ni yanzun na girma na kusan aurar da junior. So banida lokacin ka dankaji"

Cewar fu.ad din yana dariya. Shima lukman din dariya yake.

"Amman lukman baka da mutunci wallahi. Wai bazawari....."

Yana dariya shima yace

"Gaskiya ce baka so nasani. Yane? Yasu nana"

Komai daya faru ya juyema lukman daya sauke ajiyar zuciya ya na fadin.

"Na yarda kam fu.ad. Kaddararku da safiyya babu mai fahimtarta idan ka duba"

"Hmm. Hakane kam. Yanzun zan tsaya masallaci inyi sallar juma.a in kana free mu hadu gidan yaya babba mana.

Banje bafa tunda na dawo"

Lukman ya amsa da.

"Babu damuwa to. Nima yanzun wanka kawai zan infi to sallar. Zan dai kiraka idan na fito"

"Alright. Godiya"

Fu.ad ya amsa yana kashe wayar .

**

Yana fitowa daga masallacin sarki kanshi tsaye kundila ya wuce gidan babban yaya.

Ya kira lukman shima yace mishi yana hanya yama kusa kaiwa. Bakin kofar gidan ya sami lukman maigadi ya bude musu suka shiga sukai parking motocinsu.

Sunci sa.a babban yaya na gida. Sosai anty sa.a matarshi tai mamakin ganinsu. Musamman fu.ad dan gara lukman wani lokaci sukan zo da haneef.

Bayan sun gaisa ta shiga ciki ta kira musu babban yaya. Yana fitowa ya ware idanuwanshi da mamaki. Duk da momma ta fada mishi fu.ad din ya dawo bai hanashi mamaki ba.

Waje ya samu ya zauna. Suka gaisa da su fu.ad.

"Daman nace zanzo in gaishe dakai ne"

Fu.ad ya fadi yana murmushi. Babban yaya ya harare shi.

"Aikam kai baka da kirki ko kadan fu.ad"

Dan sosa kai fu.ad yayi a kunyace.

"Ayi hakuri babban yaya. Bazai sake faruwa ba in shaa Allah"

"Allah ya kara shirya mana kai. Dan kam bakajin magana fu.ad. Ya jikin nana din?"

A sanyaye yace.

"Da sauqi tana gidan momma ma"

Jinjina kai babban yaya yayi.

"Momma ta fadamun komai. Ina jirankane daman.

Muma mun hada jini da ita ai. Saboda me ba za.a auna mu ba? Ko dan bamu da mutunci a idonka har yanzun?"

Da sauri fu.ad yace.

"Haba mana. Wallahi sam ba haka bane ba. Ko daya wannan tunanin bai zomun ba. Saboda abune mai girma da hadarin gaske.  Dan Allah karkace haka.

Nagane kuskurena"

Kallon shi babban yaya yayi sosai. Lukman dake zaune yace

"Ai hakuri babban yaya."

Jinjina kai yayi.

"Bakomai. Komai ya wuce. Zan magana da kowa tun daga kan su hassan inason kowa yaje a auna shi ranar monday"

Fu.ad shiru yayi. Ya rasa abinda zaice. Ya rasa kalar kaunar yan uwanshi a gare shi. Jiki a sanyaye ya mike.

Dan tsaf zuciyarshi zata iya karyewa. Wani irin yanayi yakeji dayake bukatar ya zauna shi kadai ya jinyace shi.

"Nagode"

Bai jira amsarshi ba da sauri ya fice daga falon. Lukman ya kalli babban yaya yace.

"Abubuwan ne sun mishi yawa. Yana ganin kaman bai cancanci dukkan karamcin da ake mishi ba"

"Menene amfanin yan uwantaka idan babu taimako a tsakani? Zumunci abune mai girman gaske lukman.

Bamu hada jini dakai ba. Iya abinda zan ma fu.ad shi zan maka. Zakumin laifi. Zanyi fushi daku. Zaku gane kuskurenku zan kuma yafe muku.

Wanna shine zama na hakika. Wannan itace kauna ta gaskiya"

Maganganun babban yaya sun shigi lukman ba kadan ba. Ya kara darajta girma na zumunci. Godiya ya sake yima babban yaya kamun suyi sallama.

Sanda ya fito babu motar fu.ad. Tashi ya shiga yai gida abinshi. Yasan zai neme shi in yana bukatarshi.

****

Ya dade cikin mota bayan yai parking bai fito ba. Ya hade kanshi da gaban motar kawai yanq jinjina kalar kaunar da babban yaya ya nuna mishi yau.

Haka ya kamata ace yan uwantaka ta kasance. Haka ya kamata ace an girmama zumunci. Idan ya tuna ranar daya sa kafa yai watsi da wanna kaunar yakanji ciwo marar misaltuwa.

Yakanyi dana sani dashi kadai zai fahimce shi. Bude motar yayi ya fito saboda yanda yake jin iskar dake ciki ta mishi kadan.

Yana kaiwa kofa haneef na fitowa. Da fara.a yace

"Yanzun nake shirin kiranka. Momma tace mun kunje wani waje da safiyya"

Jajayen idanuwanshi fu.ad ya sauke kan haneef daya sashi saurin karasowa ya na dafa kafadar fu.ad din.

"Lafiya? Fu.ad meya sameka?"

Dafe kai fu.ad yadanyi. Ga abinda ya same shi nan. Muryarshi a dakushe yace.

"Ion' deserve dukkanku. Dukkan kaunarku ban....."

Katse shi haneef yai da fadin.

"Daga ina wanna shirmen yake fitowa? Kar in sake ji fu.ad. Inba so kake ranka ya baci ba"

Kama hannuwan haneef din yayi yana tsugunnawa kan gwiwoyinshi. Bai damu da yanda haneef din ke fadin.

"Fu.ad ka tashi. Wai meye haka?"

Hawayen dayake rikewa ne suka zubo mishi. Hawayen farin ciki ne da samun yan uwa irin su. Murya na sarkewa fu.ad ke fadin.

"Hada jini daku alfahari ne a wajena haneef. Kaunarku mai girmace a gareni"

Rike da hannayen fu.ad cikin nashi haneef ya kama shi yana dago shi. Saida ya saki hannunshi daya sannan ya zaro hanky daga aljihunshi ya mika ma fu.ad.

"Saboda Allah ka shiga cikin gida kagani. Su khadee duk suna nan. In kana hawaye haka ai anyi abin kunya.
Bakasan ka girma bane yanzun?"

Langabe kai fu.ad yayi yasa hanky din yana goge fuskarshi. Dakuna fuska yayi.

"Na girma ai. Na kusan aurar da ya'ya"

Sosai haneef ke dariya. Shekaru kam sun ja. Amman akwai bangare na fu.ad dayasan da wahala ya girma. Yanzun haka yanda ya dakuna fuska cike yake da yarinta.

Halittace ta fu.ad wannan. Yana bukatar dukkan kulawarsu duk girman dazaiyi.

"Nikam ina da wajen zuwa. Sai munyi waya ok?"

Kai fu.ad ya daga mishi yana fadin.

"Hanky dinka"

Girgiza mishi kai yayi.

"Ewww waye zai karba? Nabar maka"

Ware idanuwa fu.ad yai kamun ya kwashe da dariya.

"That is gross haneef"

Dariya kawai yayi ya wuce. Shima hanky din ya kalla. Saidai bazai iya cillar dashi ba. Da murmushi a fuskarshi ya shiga gida.

Kaman yanda haneef ya fada gidan a cike yake da yara da suka saka murmushin shi ya kara fadada.

Karasawa yai wajen su. Yana ganin su yassar yagane su. Kamarsu daya sak da pha.iza.

Gaishe dashi sukayi. Nana na zaune ita da wata yarinya mai kyau da yake son gane ko yar wacece. Nana ta kalle shi tana murmushi.

Dayar yarinyar dabaisan sunanta ba tace.

"Kaine uncle fu.ad?"

Dariya yayi ya daga mata kai.

"Zo mu gaisa mana"

Ba musu ta taso tazo wajenshi. Ya tallabi kumatunta duk kaunarsu ta cika mishi zuciya. Bai taba sanin haka kaunar yara take ba sai randa ya dora idanuwanshi kan Nana.

Kaman ta bude mishi wani wajene da baisan dashi ba. Yanzun duk inda yaga yara sai murmushi ya kwace mishi. Biye su yai suna ta shiririta har momma ta fito.

"Fu.ad yaushe ka dawo?"

Kallonta yayi a gajiye.

"Ban dade ba momma. Sannu da hidima. Wallahi yunwa nake ji sosai"

Momma ta daga mishi kai. Mikewa yayi ya karasa inda nana take zaune tayi wani shiru.

"Lafiya dai ko nana?"

Murmushi tayi ta daga mishi kai.

"Na sha magani ne. So yana sani bacci kuma shisa. Ina mumy?"

Dan dakuna fuska yayi.

"Zan baki labari anjima"

Da ido ta nuna mishi ta fahimta. Ya wuce inda momma tabi yabarsu nan. Yana cin abinci yake ba momma labarin komai.

Taji dadi. Tuni take son mishi magana kan auren su da safiyya din sai dai bata son kara mishi tension.

Ya dora da fadin.

"Naje gidan babban yaya ma"

Kai ta daga ta amsa shi da.

"Eh ya kirani kuna fita yake fadamun yanda kukayi. Yakamata kaje gidan antynku ma"

Saida ya hadiye abincin dake bakinshi sannan yace.

"Aikam wallahi. In shaa Allah anjima. Dana gama cin abinci wanka zan indan huta sannan"

Mikewa momma tayi da cewar.

"Allah ya kaimu. Bara inje. Nasan yanzun abbanku zaizo sai in mishi magana aji yanda za.ayi"

"Ba damuwa momma. Allah ya kara girma ya tabbatar mana da alhairi"

Ta amsa da amin tana wucewa. Sosai yaci abincin sanna ya tashi ya nufi dakinshi........!

*#TeamAS*

No comments:

Post a Comment