Thursday 4 May 2017

AKAN SO 14

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

         14

Agogon shi yake daurawa. A cikin kanshi babu komai sai son barin kasar gaba daya.

Son yabar komai inda ya kamata ya zauna daga farko. Amman abinda yake so a zuciyarshi da kanshi ya sha banban.

A yan kwanakin nan mafarkan da yake sun yawaita. Har idanuwanshi sun fada saboda bashi da wata wadatacciyar nutsuwa.

Komai baya masa dadi. Baya son zama shi kadai. Danma lukman na hutu sai abin yai masa sauki.

Gudun haneef yake dan baya son gaya mishi asalin abinda ke damun shi. Ta ina ma zai fara ce masa shi fu.ad yau tunanin mace ya saka shi a gaba.

Tunanin macen ma kucaka yar kauye. Abin da dan nauyin fada. Tunda shi baisan me yasa ma yake jin abinda yake ji din ba.

Jiyai an turo kofar hadi da sallama. Ya lumshe idanuwanshi ya bude su. Haneef ne ya nemi waje gefen gadon shi ya zauna.

Kallon shi yake sosai daya soma damun shi saboda yasan zai karanci damuwa a fuskarshi. Yace

"Nasan ba fushi kake mun ba. Avoiding dina kake nakuma rasa dalili. Meke damunka?"

Takalmin shi ya wuce ya dauka. Ya dawo ya zauna ya na saka socks. Ciki ciki yace

"Ba abinda ke damuna. Kabarni in shirya a nutse"

Idanuwa kawai haneef ya zuba mishi. Yanata kallon shi harya karasa shiryawa. Wata yar jaka ya dauka.

Hannun shi ya sa cikin gashin shi hadi da fadin.

"Fuck this...... "

"Language fu.ad.....language please"

Haneef ya fadi yana murmushi.

Kai kawai fu.ad ya jinjina ya kalle shi yace

"Kawai wani abune yake damuna. Banajin zan iya magana akai yanzun. Just drop it"

Gira haneef ya daga masa. Yana kallon yanda yake kokawa da kalmar dazai fada. Dakyar ya iya cewa

"Please. Just drop it"

Mikewa haneef yai yana yar dariya hadi da fadin.

"Since you asked so nicely. Muje sai mu biya mu dauki lukman mu rakaka"

Bai ce komai ba ya bude kofar ya fita. Cije lebe yai ya rufe idanuwanshi ya bude su da yake fassara baya son abinda ke shirin faruwa.

Gaba dayan su suna falo tsaitsaye abbah ne kawai baya nan. A tabare yace

"Momma mana. Me yaran nan sukeyi"

Dariya sukai gaba daya. Sunsan baya son bankwana. In da za.a barshi zai sulale kowa bai sani ba.

Pha.iza tace

"Dame kaga ya maka kama?"

Hassan ya amsa da

"Bro dinmu zamu raka airport"

Momma ya kalla idanuwanshi cike da rokonta tace musu suyi zamansu.

Dariya kawai tayi tace

"Allah ya tsare ya bada sa.a. A duk inda kake addini da tarbiyarka suzo farko fu.ad. Karka zubda su domin rudin duniya......."

Fu.ad ya katse da fadin

"Banda abokan banza. Banda dauko al.adar da ba tamu ba.....banda banda banda
...momma na haddace duka"

Haneef ya tallabe mishi kai. Ya dafe yana fadin.

"ouchh that hurt"

Dariya sukai gaba daya. Dole ya yarda su pha.iza suka bisu. Lukman suka kira ya fito suka dauke shi shima.

Har aiport suka raka shi. Su hussaina na jero mishi tsarabun da suke so ya siyo musu.

Ya amsa musu da saiya kira mama yaji suna kokari a islamiyya da boko sannan.

****

*Bayan wata biyu*

EUROPE.

Babu abinda ke taimaka masa sai bacci. Da hannu biyu yake tallabar mafarkan ta yanzun.

Da kanshi yake fatan dare yayi ya kwanta bacci. In da babu su baisan yanda zaiyi ba.

Komai ya jagule mishi a watannin nan. Komai yakeyi kaman wanda akai ma chargy akai masa loading din abinda ya kamata yayi.

Abinci ma timing yai yasa a wayarshi. Da yaga reminder zai tura ma cikinshi komai ya samu badon bakin shi nagane dadin abin ba.

Shi ba abokai yake yi ba. Saidai team mates kawai. Maganar data wuce wadda ta danganci abinda yake tarasu bata hadasu.

Sai ya wuni baice ma kowa komai ba. Fuskar nan a dakune. Bamai shiga harkarshi kaman yanda baya shiga ta kowa.

Da niyyar sai yai wata shidda zai je gida kwana biyu yazo. Amman sam yaga ya kasa.

A daddafe yai wata biyun nan. Ticket dinshi dake kan gado ajiye yake kallo.

Yana son da duk wani sauran karfi dayake dashi yai fada da son zuwa gida da yake yi.

Da duk numfashi da yake shaka yana jin yanda komai ke ruguje masa.

Yana so yaganta. In bai ganta ba zai iya karasa gigicewa. Yana da wasa cikin sati uku masu zuwa da zai iya zama silar ci gaban shi.

Bazai iya yinshi cikin kwanciyar hankali da nutsuwar da yake so ba inhar baije yaganta ba.

Tunda ya tashi damuwa labarinta kawai yakeji. Sai yanzun ne ta iso inda yake.

Tunda ya tashi kunci nisantarshi yakeyi amman yanzun ya samu wajen zama tare dashi.

Tun girmanshi ya ke dauka an damka mishi ikon tsara rayuwarshi yanda yake so.

Yanda ya zanata shine zaikai shekara ashirin da takwas. Zai samu yarinya mai zurfin karatu wadda zata dace da tsarin rayuwarshi ya so.

Zai aurenshi babu wata damuwa. Zasuyi rayuwarsu daga shi sai matarshi.

Zai rayuwarshi da abu biyune.  Zuciyarshi zata kaunaci abu biyune kawai. Daga ball sai matarshi.

Bashi da wajen ajiye wata damuwa. Baisan ya akai kaddara tai masa wannan kamun ba.

Bai fahimci asalin abinda yake ji ba sai jiya da yamma daya zauna yana kallon wani film "Heartbeat" tukunna.

Abinda ke faruwa dashi shine yake faruwa da guy din ciki. Sun kira abinda yakeji da *So* .

Sai dai bai taba dauka cewar *Akan so* zaiji ya rasa farin cikin shi ba. *Akan so* zai kasa walwala.  *Akan so* zai ji ya kasa sakewa yai ball daya taso da ita a zuciya tun yarinta.

Wani numfashi yaja ya sauke hadi da mikewa. Yagama tsaida magana. Gobe zaibi jirgin karfe 8.

Dan haka ya fita ya ga kozai samu abinda zai saima su pha.iza.

****

"Dan Allah ku samamun lafiya lami.  Mutum bashi da ikon yai shiru saikun dame shi da bakar tambaya"

Safiyya ta karasa maganar tana zabga wani tsaki. Su lami kam kallon juna suke.

Saboda sun rasa kan safiyya a watannin nan. Ta canza gabaki daya. Abu kadan zakai mata sai tahau ka da fada.

Sam ba halinta bane. Safiyya nada fara.a da hakuri. Su zasu iya cewa abinda duk ya bata mata rai ba kadan bane.

Amman yanzun kullum cikin kunci take. Babu fara.ar nan. Ga wata rama datai. Takan ga kuskure a duk wata magana da zasuyi mata.

Wani hawaye suka zubo ma safiyya ta sa hannu ta goge su. Cikin tashin hankali lami tace

"Subahanallah. Safiyya kiyi hakuri wallahi ba nufinmu mu bata miki rai har haka ba. Muna tambaya ne kawai dan mun damu"

Jummai ta dafata tace

"Abinda lami ta fada gaskiya ne. Bamu saba ganinki haka ba shisa muke tambaya"

Wasu hawayen taji sun sake zubo mata. Ita kanta halayyarta ta dameta. Sai dai bata da yanda zatayi.

Cikin sanyin murya yace

"Karku damu. Ba ku kuka batamun rai ba. Abinda ke damuna bashi da alaqa da tambayarku"

Fuskokinsu suka nuna alamar jin dadin basu suka bata mata rai ba.

Suna gudun tambayarta ko menene. A haka malamin hadith dinsu ya shigo.

Anata karatu safiyya hankalinta na wani waje daban. In zaka yankata bata san me suke fada ba.

Wannan abinda daya sameta ya isheta. Bata da damar wani kwakkwaran motsi sai taji shi manne da ita.

Wani irin mannewa yai mata da zata iya rantsewa tana jin dankonta har a fatar jikinta.

Da dare mafarkinshi. Da rana tunanin maganganun shi. A zuciya fatan sake ganin shi tunda na son fitar dashi yaki faruwa.

A kwanakin nan abin ya kara tabarbare mata. Ado ne a tsaye a gabanta.

Amman fuskar fu.ad take gani cikin tashi. Magana zai mata muryarshi take ji. Tun inna na tambayarta meke damunta.

Harta gaji ta hakura. Wani lokacin in tana kwance shiru takanji inna ta shigo ta taba jikinta taji ko bata da lafiya ne.

Ta kasa dainawa. Tana son ta tsaida komai kodan mahaifiyarta data damu da ganinta haka.

Bata san taya zakai fada da abinda yafi karfinka ba. Abinda ko dan yatsa ba zaka iya daga masa ba ballantana kai tunanin yaki dashi.

Tabarma Allah komai. Shi ya dora mata koma menene kuma shi yake da ikon yaye mata shi.

****

Hassan na zaune shida hussaina suna kallon wrestling a New World cinema sunata gaddamar da suka saba.

Hassan yace

"Yarinya kiyi hakuri kawai. Bafa yanda john cena zaiyi da yan shield"

Hararar shi tai tace

"Ai dan suna da yawane shisa. Inba tsoro ba ayi da dai daya mana"

Amsa zai bata suka ji sallama. Da gudu suka tashi suka suka rukunkume fu.ad saboda basu zace shi ba.

Da gudu hussaina ta ruga ta na kiran momma data zo ga bro ya dawo.

Hassan kuwa yana tsaye yana kallon shi sosai. Saboda tunda ya tashi bai taba ganin fuskar fu.ad da gashi ba.

Banda kanshi baya tara gashi ko ina.  Amman yau fuskarshi cike take da gashi. Da alama rabon dayai aski tun sanda zai tafi.

Dan ko gashin kanshi haka yake. Ya kara yawa sosai ga babu ko gyaran fuska. Sai yaga duk ya canza masa.

Da sauri momma ta fito. Cikin farin ciki tace

"Fu.ad zuwa babu sanarwa haka"

Da murmushi yace

"Nima fa bansan zanzo ba.  Wai na samu kwana hudu ne shine nace barin zo inyi su a gida"

Kallon shi take itama. Da damuwa a fuskarta tace

"Aikam gara dakazo. Duk ka canza. Fu.ad ji fuskarka. Wai meke damunkane haka?"

Yaji dadin pha.iza data fito tana fadin.

"Wooo bro. Kaine haka kwatsam"

"Nagaji fa. Bara indan watsa ruwa"

Ya fadi.  Hassan ya karbi akwatin shi ya hau masa dashi sama. Ba bata lokaci shima yabi bayanshi.

Saida yai kira lukman a waya bai daga ba.  Yai tunanin ko yana da lectures din asabar. Text yai mishi sannan ya shiga wanka.

Yana fitowa ko mai bai shafa ba. Yasa wani 3 quarter loose da hoodie. Kwanciya yai kan gadon yana jin wata nutsuwa da baisan ta inda take fitowa ba.

Kiran lukman ya shigo ya daga wayar yana fadin.

"Dan Allah kazo muyi magana"

Lukman ya amsa shi da.

"Kazo school ka daukeni. Motata na wajen gyara"

Bai musu ba ya katse wayar ya na sauka falo. Momma ce tace masa

"Kazo kaci abinci"

Yana tafiya yace

"Sai anjima tukunna. Barin zo momma. Ba dadewa zan ba"

"Allah ya tsare"

Ya amsa da amin yana ficewa.

*

"Me ke damunka?"

Shine kalmar farko da lukman ya furta masa yana kallon shi.

"Safiyya"

Ya amsa mishi yana jingina da mota. Shiru lukman yai yana dakuna fuska. Da alama yana tunanin ya taba jin sunan nan. Amman ya kasa tuna ko a ina.

Don haka yace

"Wacece safiyya?"

Wani kallo fuad ke masa dake tambayar yana nufin bai gane ta ba. Hakan ya fahimta ya sa shi cewa

"Ni yazan ingane ta?"

Ba yanda zaiyi ne shisa zai fadama lukman. Amman harya fara hango kalar iskancin dazai masa.

Muryarshi can kasan makoshi yace

"Safiyya ta bichi....."

Kwalo idanuwa lukman yai kaman wanda aka gayama an sace motar dayakai gyara.

"Safiyya daka kulle ma iyaye?"

Kai fu.ad ya daga masa. Shiru lukman yai kmun yace.

"Allahu Akbar. Allahu Akbar. Umn Allahu Akbar"

Da mamaki fu.ad yace

"kabbarar me kake kuma"

Jinjina kai lukman yai yace

"Ina mika yabona ga Ubangijin dake da iko da dukannin halitta. Ubangijin daya dasa maka zuciyarka yake kuma iko da ita"

"Hmm.... "

Kawai fu.ad ya fadi yana kauda kai gefe. Dan ya san gaskiya ne kalaman da lukman yai.

A yan kwanakin nan yagane shi ba komai bane.

"Ni bansan yazanyi ba"

Kallon shi lukman yake. Dan har lokacin mamaki yake. Rayuwa kenan. Bawai dan yafi karfin safiyya ba. Shi ba mai cika baki bane ba.

Amman fu.ad da safiyya. Wani hadi ne da kwakwalwarshi ba zata ko iya dauka ba.

"Wallahi abin nan yamun girma fu.ad na rasa ta ina zan fara ko kuma me zan fada"

"Ni kawai ina so inganta ne. Shi ne kawai abinda ya dawo dani. Ko ban mata magana ba lukman"

Sauke ajiyar zuciya lukman yai yace

"Muje ka aske wannan fuskar. Kadan nutsu tukunna muyi magana"

Girgiza kai fu.ad yai

"Ba aski nake bukata ba. Nutsuwa ta zata samu idan naganta ne kawai"

Wani abu lukman yake ji da bazai fassaru ba. Gabaki daya lamarin duniya ya kara tsorata shi.

Kalli yanda lokaci daya fu.ad ya birkice. Wato mutum yaji tsoron Allah duk inda yake. Ka gode masa in yana tallaba maka.

Zaka gane kai din bakomai bane lokacin da Allah ya saukar maka da kaddarar da zata birkita maka lissafi cikin kankanin lokaci.

"In kana so kaganta. Saika aske wannan gashin fu.ad"

Baya son yawan surutu dajan magana dan haka ya zagaya ya bude mota ya shiga yana barma lukman wajen zaman driver.

Har sukaje shagon mai aski ba suce komai ba. Kowa da abinda yake sakawa a zuciyarshi.

Aski akai mishi. Har yadan nutsu. Sai dai askin saiya fito da ramar dayai sosai.

Daman shi ba wata kibar kirki ba. Farinne kawai sai dogon hanci. Suna mota ne yaga lukman ya dauki hanyar gida

"Ya haka kuma lukman?"

Kallonshi yadanyi ya maida hankalinshi kan tuqin da yake yi.

"Ai dai kabari inci abinci. In watsa ruwa muyi sallar azahar ko"

Hade fuska fu.ad yai.

"Ni da mun tafi yanzun.  Ni bama najin yunwa"

Shiru lukman yai mishi. Yabarshi yaji da abinda ke damunshi ma. Yaga alamun fu.ad din so yake ya rage damuwar dake ranshi ta hanyar jan shi da rikici.

Dole ya hakura suka je gidansu lukman. Yai wanka ya fito. Ba yanda baiyi dashi ba suci abinci yace baya ci.

Jiran shi dai yai yagama ci. Tare sukai alwala suka fita masallaci. Suna dawowa sallar azahar lukman ya tukasu zuwa bichi.

Da duk kusancin su da bichi da yawaitar karin bugun zuciyarshi. Lukman kanshi da yake gefe sai yanzun yake ganin tsantsar wautar da sukayi.

Yana ganin lokacin da fu.ad zaisan menene rayuwa yayi. Lokacin dazai girbi abinda ya shuka.

Sai wani tausayin shi ya kamashi. Saboda yasan ko basu raba wannan abin tare ba. Zai samu nashi kason.

Fu.ad kam ya rasa inda tunaninsa ya kamata ya tsaya. Ya rasa me ya kamata yaji.

Ya dauka farin cikin shi zai dawo daga lokacin da suka dauki hanya. Amman sai yaji banbancin haka.

Saima dayagan su cikin garin bichi. Yaga motar tayi corner zuwa layinsu safiyya.

Yaga da gaske shine a cikin garin bichi. Shine yazo yaga safiyya.

Lokaci daya wata fargaba da tsoro suka cika mishi zuciya......!

No comments:

Post a Comment