Thursday 4 May 2017

AKAN SO 5

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

         05

*21/02/2017*

Harya gama bubbuga kofarshi ya tafi bata bude ba. Kuka kawai takeyi. Saida tai mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet.

Ruwan dumi ta hada ta shiga ciki ta dan jikinta ko ina ciwo yake. Yanda nawaf ya janyota daga kan kujera ya jefar kasa.

Ba karamar buguwa tai ba. Zata iya rantsewa wani lokaci nawaf bashi da hankali.

Zaman lafiyarsu na wata biyu ne a shekaru daya da rabi da aurensu. Inhar sunan farhan ya gifta cikin gidan sai an samu matsala.

Ta rasa kalar soyayyar nan ta nawaf. Tasan da gaske yana sonta sosai. Inkuma ya daketa yana duk abinda yasan zai faranta mata.

Nawaf ya mata halacci. Ba zata manta abin daya fara mata ranar farko ba.

****

Ta dawo daga makaranta da yammaci likis. Tafiya kawai take amman da tana da wani waje da zata je da bata koma inda ya zame mata dole ta kira gida ba.

Ta jima sosai tsaye a wajen katon flat house din da yake da bala.in jan hankali daga waje.

Gidan da zaka iya rantsewa mutanen arziqi ke rayuwa a ciki. Ajiyar zuciya nuri tayi sannan ta kwankwasa kofar mai gadi ya bude mata.

Ta gaishe dashi a ladafce tsohon ya amsa cike da tausayinta a muryarshi da yanayin shi.

Tun kamun ta karasa cikin falon take jin shewa da hayaniyar maza da mata.

Duk da hakan ba bakon abu bane a wajenta bai hanata jin sabuwar tsanarshi a ranta ba.

Bata damu datai sallama ba kai tsaye ta karasa falon. Addu.a kawai take ta wuce zuwa dakinta lafiya. Bataki ace babu wanda zai kula da shigarta ba.

Kanta a kasa. Muryar Alh.baushe taji yace

"Nuriyya kin taso daga makarantar"

Bata ko nuna alamun tajishi ba. Zuciyarta sai dokawa take. Ta tsani mutumin nan da za.a bata damar kisa shine na farko dazai fado mata a rai.

Jin takunshi yasata kara sauri dan wucewa dakinta. Caraf ya rike mata hannu da duk karfinshi.

"Ke ina miki magana zaki wuce ni. Ko uwarki bata isa ta wulakantani ba balle ke banza"

Idanuwan nuriyya cike da hawaye take kokarin kwace hannunta. Amman kara janta zuwa jikinshi yake.

Kokawa ta gaske suka shiga yi. Dayake Alh.baushe ba karamin bane. Irin manyan mutanen nan ne ya riga yafi karfin nuriyya ta ko ina.

Allah ne ya bata sa.a ta gartsa masa cizo a kirji daya gigita shi. Da gudu ta nufi hanyar waje tana ihun da tasan bata da mataimaki sai Allah.

Sanin halin gidan da abinda ke faruwa yasa baba maigadi bude ma nuriyya kofa cikin hanzari dan shine kadai taimakon dazai iya yi mata.

Wani matashin saurayi ta hango tsaye jikin wata farar mota. Bandashi ko kare babu a unguwar.

Juyawa tai ta hango Alh.baushe ya fito da gudu ta karasa wajen saurayin tana wani irin kuka.

"Ke lafiyarki kuwa???"

Ya tambayeta.

Cikin kuka tace.

"Ka taimakamun wallahi zai lalatamun rayuwa"

Da mamaki a idanuwanshi yace.

"Bangane ba"

Kamun tai masa bayani Alh.baushe ya karaso inda suke yanata huci kaman mayunwacin zakin da ya kwana bai ci ba.

Ko kallon saurayin dake tsaye baiyi ba yakai hannu zai cafko nuriyya data boye bayan saurayin.

Batare da tunanin komai ba saurayin ya wanke Alh.baushe da wani irin mari.

Hakan yaba nuriyya damar sake labewa bayan saurayin. A dake yace.

"Wallahi ka soma taba ta zan baka mamaki"

Da alamun kallon da alh.baushe yake ma saurayin yaga babu alamar wasa a bayanin shi kuma yanzun yake ji da kuruciya.

Gashi in yaja maganar akai daidai to ni wani yazo wuce wa za.a iya samun matsala. Kallon da yake fassara zaki dawo gidan yai ma Nuri sannan ya juya.

Hankalin shi saurayin ya maida kan Nuri dake wani irin kuka cike da tambayoyi da yawa yace.

"Meye hadinki da wannan mutumin?"

Ta kasa amsa shi wani irin kuka take da yaji yana ci mishi rai. Hannunta ya kama ya bude motar shi ya sakata.

Zagayawa yai ya zauna. Ya dauko ruwa dake gefe ya mika mata hadi da fadin.

"Ungo ki sha"

Batai musu ba ta karba ta sha sosai. Ta bude motar ta wanke fuskarta tana ta sauke ajiyar zuciya.

A sanyaye yace mata.

"Sunana nawaf"

"Nuriyya"

Ta amsa shi muryarta a dakushe.

*

Sallama taji data dawo da ita daga tunanin da takeyi. Kamun ta amsa an sake yin wata. Da sauri ta tsane jikinta ta fito daga ban dakin.

Doguwar riga ta zura ta dauki karamun hijab tasa da sauri ta fito tana amsa sallamar.

A kunyace tace.

"Yaya sannu da zuwa. Wallahi ina wankane shisa kaji shiru. Ina kwana"

Kallon ta t.j yake sosai. Wani jini ne ya taru gefen fuskarta harya soma baqi baqi. Ya girgiza kanshi cike da takaici.

Waje ya samu ya zauna kawai. Nuriyya ta zauna nesa dashi tana fadin.

"Ina anty jidderh?"

Numfashi t.j ya sauke yace.

"Tana lafiya nuriyya. Ya kike?"

"Alhamdulillah"

Ta amsa tana dorawa da.

"Sai dai nawaf din ya fita"

Kallonta t.j yai sosai a nutse yace.

"Gidana yaje nuriyya. Me yasa baki taba ko da kirana kin fadamun nawaf na dukan ki ba?"

Kanta ta sunkuyar kasa. Taya zata fara kai karar nawaf? Tace me?

Gani yai bata da alamar amsa shi hakan yasa shi ci gaba fadin.

"Nuriyya yanda yaimun bayani kaman farhan ke yawan kawo matsala tsakanin ku.

Kinga dai yanda nawaf yake. Kece abu na farko a rayuwarshi data raba shi da addiction din da mu munyi iya bakin kokarinmu mun kasa.

Nuriyya nawaf yana sonki. A kalar nasa haukan. Dan Allah kiyi kokari sunan farhan ya daina fitowa daga bakinki a gabanshi kinji ko?"

Muryarta can kasa tace.

"In shaa Allah yaya. Mungode sosai. Allah ya kara girma"

Mikewa t.j yai yana fadin.

"Bakomai nuriyya. Inya sake dukanki ko ki kirani ki fadamun ko jidderh. Ko kizo gidana kinji ko?"

Kai nuriyya ta daga masa. Yai mata sallama ya fice. Ta sake lafewa cikin kujera.

Ko dan karamcin da yan uwan nawaf suka nuna mata kadai ya isa ta shanye duk wani abu.

Ballantana son dashi kanshi nawaf din yake mata.

****

*20/02/2017*

*EUROPE*

Number din lukman ya sake dialing a karo na babu adadi. Daga zuciyarshi har brain dinshi abu daya suke gaya masa.

Dan haka bai musu gardama ba. Kasancewar suna hutu ya kara saukaka mishi abin.

Kayanshi yake hadawa amman hankalinshi ba kan abin yake ba. Ko menene yasa lukman kiranshi ba karami bane ba.

A karo na farko a rayuwarshi dazaiyi abinda wani ya umarce shi dashi. Bai taba ba yaune zai zama tarihi.

Passport dinshi ya dauka da duk wasu kana nan abu da yasan zai amfani dasu.

Cab ya dauka zuwa airport. Ba abokai gare shi daya damu da susan matsalar shi ba.

Logan kawai yaima text cewan zai je gida wani abu ya taso. Shima yana ganin ya shiga ya kashe wayar gabaki daya.

Shi kanshi bashida amsar tambayoyin daya san Logan din zai masa.

Ba karamar sa.a yaiba da ya samu jirgin dazai tashi cikin awa biyu. Dan haka ya samu waje ya zauna.

Shi kanshi bazaice ga kalar tunanin da yake ba. Saboda babu wani wadataccen nutsuwa a tare dashi.

Shekaru goma sha daya. Yanda rayuwar take tafiya kawai ma ya isa ya baka mamaki.

****

*21/02/2017*

*NIGERIA*

Har jirginsu ya tsaya fu.ad ji yake kaman a mafarki. Wai da gaske ya shigo jirgin zuwa nigeria.

Da gaske kafafuwanshine a kasarshi. Kasar da bai taba zaton zai sake waiwayarta ba.

Yana sakkowa daga kafar jirgin rayuwarshi na gifta masa cikin idanuwanshi.

Tsayawa yai yana kallon airport din. Ya lumshe idanuwanshi yana shakar iskar kasarshi.

Yanajin yanda dumin zafin ranar ke busa shi. A hankali kaman wanda aka kunnama film farkon rayuwarshi ya dawo mishi.............!!!

No comments:

Post a Comment