Thursday 4 May 2017

AKAN SO 33

       *💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

      33

*Shout out to mutanen nan biyar. Dimples remember how much i don't like you. Ummie jay #IfYouKnowYouKnow. Miemiebee i want to be like you when am matured. Biebie Isa #AnaTare. Anty sis Nagode da dukkan karamci*

Wani sama sama yake jinshi. Karar motocin dake wucewa can yake jinsu nesa. Saboda abu dayane kwakwalwarshi ke iya processing a yanzun.

'Yar' shi na da cancer'. Can sama sama yake jin kamar muryar sofi na kiranshi. Bai ko bi takanta ba saboda bata gabanshi a yanzun.

Komai na rayuwarshi a gefenshi yake a ajiye. Nana ce kawai ya rike gam tun daya sauke idanuwanshi akanta.

Da gudu safiyya ta karasa bata damu da mutanen dake wurwucewa ba. Tasha gabanshi. Kallonta yake ya daquna fuska alamar bai fahimci me take yi ba.

"Badan na damu ba. Nana ta farka tana tambayarka........"

Jin sunan nana yasa shi ware idanuwanshi akanta sosai. A tsorace yace.

"No bazan iya ba. Bazan iya facing dinta ba.........."

Kallonshi safiyya take yanda yake girgiza kai yana daga hannuwa. Lokaci daya taga girman da fu.ad yayi a jikine kawai da fuska.

Har yanzun zuciyarshi akwai yarinta fal a cikinta. Sosai ta kalle shi.

"Shisa nace karta sake ta saka a zuciya dan bakata da wajenta....."

Wani abu yaji tun daga yatsan kafarshi ya taso mishi har cikin kirji. Safiyya na son kule shi ya kula. Baice mata komai ba ya juya ya na komawa hanyar asibitin.

Dan karamin murmushi tayi tabi bayanshi. Har suka shiga cikin asibitin. Yana zuwa bakin kofar dakin da Nana take ya rike handle din yai tsaye.

Gabanshi faduwa yake sosai. Nan safiyya ta karaso ta same shi. Kallonta yai kaman zaiyi kuka.

"Em' scared sofi......."

Sauke ajiyar zuciya tayi. Tana jin yanda duk inda ta cika da tsanarshi a zuciyarta ya fara gogewa. Sauke idanuwanta tayi.

Ta karasa ta raba gefenshi ta tura kofar ta shiga tabarshi anan tsaye. Kaman mai ciwon wuya yadan zira kai ya leqa.

Nana na zaune kan gadon suna hira da Ansar dake gefenta.

"Mai katon kan nan bai tafi ba kenan......"

Ya fadi kasa kasa. Shiga yai a ciki. Sai lokacin nana ta ganshi. Wani murmushi da tai mishi baisan lokacin daya mayar mata da martani ba.

Karasawa yai har inda Ansar yake zaune kan kujera. Hannuwa yasa bayan kujerar yaja ta baya ji kake wani qiiiiiiiiii.

Dariya ce ta kusan kubce ma safiyya ganin yanda Ansar ke ware idanuwa. Da alama ya tsorata sosai dajin yanda fu.ad yaja shi.

Yarinta nacin fu.ad har yanzun. Bata kuma san ranar dazai girma ba. Ko kallon su fu.ad baiba ya zauna gefen gadon Nana.

Hannu yasa yai cupping fuskarta yana kallon ta da murmushi a fuskarshi.

"Na dauka ka tafi. Mum tace mun kana nan. Na kasa yarda ne kawai. Kayi hakuri bani da lafiya ranar daka zo...."

Da sauri ya girgiza mata kai hadi da fadin.

"Shhhhh Nana. Wani abu na miki ciwo? Em' here now. Komai zaiyi dai dai. Ni da ke zamu yaqi ko menene kina jina ko?"

Wani irin tsalle zuciyar safiyya tayi jin kalmar nan ta 'ni da ke'. Mikewa tai da sauri ta karaso inda fu.ad yake. Cikin idanuwa ta kalle shi.

"Ina son magana dakai"

Ta buqata. Wani yatsina fuska yayi.

"Ina jinki."

Hanyar waje ta nuna masa da dan yatsanta idanuwanta cike da masifa. Kallon Nana yayi yace.

"Yanzun zan dawo......."

Ya karasa yana mikewa hadi da watsama Ansar kallon karka soma matsowa kusa da ita. Sannan suka fice shida safiyya.

Tana jan kofar a hasale tace mishi.

"Karka sake yi mata alkawurranka da babu komai a cikinsu sai karya.

Zan iya yin komai akan yarinyata. Koda hakan na nufin nisantata dakai"

Kallon da yake mata zai tsorata duk wani wanda baisan shi ba. Kamun yace.

"Kinji me kike fada kuwa? Nisantata dani ai kin riga da kin gama. Bazan yafe miki ba inhar wani abu ya sameta.

Akan me zaki boyemun ita?"

Kallon shi take da mamaki. Har yana da bakin tambayarta dalili kenan.

"I don't do happily ever after. Daga randa kika yarda da soyayyata ya kamata kisan banyi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba.......!

Ka tuna ko saina karasa maka?"

Ta fadi tana jin wasu hawaye na son zubo mata. Dafe kai yayi.

"Damn it sofi. Zaki rikeni akan maganar danai shekaru goma sha daya?

Me kike dauka? em' noh' gonna accept her. Sofi me kika sha ne?"

Kallon fuskarta yake. Yanzun kan wannan maganar da yayine zaisa ta boye masa yarinyarshi. Ji yake in baibar ganinta ba komai zai iya faruwa.

Tambaya daya ce a ranshi yanzun. Dayaji zai bar mata wajen nan. Zai bar kallonta yana jin yanda zuciyarshi keyi kaman ta kama da wuta.

"Akwai hope?"

A hankali ta daga mishi kai. Bai jira komai ba ya juya ya shiga dakin. Yana shiga Ansar ya mike domin ana kiran magrib.

A wajen ya samu safiyya yace mata zai wuce gida. Tai mishi godiya sosai sannan ta shiga ta samu fu.ad zaune gefe yana magana da Nana tana ta kyalkyalar dariya.

"Bara inyo sallah in dawo"

Mikewa yai saida ya watsa ma safiyya hararar data zabi tai biris da ita sannan ya fice. Ajiyar zuciya ta sauke.

Cikin sanyin murya Nana tace.

"Kome ya shiga tsakaninku yana da kirki sosai mumy"

Shiru tayi ta kyale Nana dan wasu maganganun intana yi hankalinta ya girmi shekarunta.

Itama alwala tayo ta dawo ta shimfida dankwalinta ta tashi sallah dan basu dauko komai ba garin sauri.

*

Tunda ya idar da sallah gabaki daya addu.ar shi ta yau babu kowa a cikinta banda Nana. Allah yake roqo daya hukunta duk laifikanshi ta wata hanyar yabawa Nana lafiya.

Yana nan akai sallar isha.i sannan ya bar masallacin ya koma asibitin. Nana tana bacci. Baiko kalli safiyya ba balle tai tunanin zaice mata wani abu.

A hankali tace.

"Dan Allah ka duba mun ita inje gida in dawo........"

Batare da ya kalleta ba ya amsa da.

"Ba saikin tambaya ba"

Bata ce komai ba ta wuce ta tafi. Hannun nana ya sa cikin Nashi ya hada kanshi da gadon zuciyarshi na mishi wani irin nauyi.

Tun randa ya cika shakaru ashirin da biyu a duniya kamar wata takarda ce yasa hannu akai. A duk lokacin dayai tunanin ya samu farin ciki sai wani abu ya gifta mishi.

Yana nan zaune har safiyya ta dawo. Ko sallamar datai bai amsa ba. Kanshi na hade da gadon Nana. Dan zatonta ma bacci yake.

Abinci ta zuba tadan ci. A hankali taga ya dago. Wani plate din ta samu daban ta zuba mishi hadi da fadin.

"Ka sakko kaci abinci"

Sai lokacin ya kalleta. Kai ya girgiza mata. Tunanin saka ma cikinshi wani abu a halin dayake ciki ma neman saka shi amai yake.

Kaman wadda tai mishi dole ya kara daquna fuska ya girgiza kai.

"Naji ka da farko ai"

Ta fadi tana maida abincin cikin warmer. Matsalarshi ce ko yaci ko karya ci bawai don ta damu bane ta bashi.

"Daka tafi dare yana yi........"

Kallon dake fassara kin samu tabin hankali yaima safiyya ya kauda kai gefe. Bashida lokacin asara akanta yanzun.

"Kana jina fa"

Runtsa idanuwa yai alamar ta takura shi sosai sosai kamun yace.

"Karki sake batamun rai sofi. Bazai mana kyau ba wannan karin. Badon ke nake zaune anan ba.

Saboda yarinya tane"

Shiru tai ta kyale shi kawai. Ya mayar dakanshi jikin gadon ya kwantar hannun Nana na rike da nashi.

Bata san koyai bacci ba ko baiyi ba. Shimfida ta gyara ta kwanta da mayafinta. A karo na farko da bacci ya dauketa in har suna asibiti da Nana.

Dan zuciyarta a nutse take ta wani fanni daya bata mamaki.

****

Saida tagama hada musu breakfast sannan. Ta dafa ma umar indomie ta soya mishi kwai ta sa mishi a warmer dinshi ta hada komai a basket ta ajiye mishi.

Wucewa tai ta shiga wanka tabar atika ta shirya mata umar din. Sanda ta fito jabir na zaune yana danne danne da wayarshi.

Bata bi takanshi ba ta cigaba da shirinta. Gaisuwa ce sunyita tun dazun. Saida ta gama shiri tsaf sannan ta karasa inda yake zaune.

Fuskarshi ta rike cikin hannuwanta ta sumbace shi a gefen fuska hadi da fadin.

"Ka kula da kanka please."

A sanyaye yace mata.

"kema haka. Ina sonki ki rike wannan"

Murmushi tayi tana wucewa. Saida takai kofa sannan tace.

"Allah ya bada sa.a ya tabbar da alkhairi........"

Kasa jiran amsar jabir tayi tai saurin fita taja kofar. Bakin kofar ta tsaya hawaye suna siraro mata. Hannu tasa ta goge su tana karanto du addu.ar data zo mata.

Sannan tasa glass dinta ta fice.

****

Kitso akai mata bayan an wanke kan. Bata son wani kana nan kitso duk da wadatar gashi da Allah yai mata.

Guda sha biyu akayi mai kyau sosai. Ta rasa meke damun nawaf. Yanda ya birkice jiya bata taba ganin hakan ba.

Duk abinda yake bai taba zaginta ba. Amman yana yin bacci jiyan ma ya tashi shikenan. Kaman mai aljanu haka ya tashi garas.

Sauke ajiyar zuciya tayi. Ta bude purse dinta ta biya kudin wankin kai da kitson da akai mata ta fito.

Gicci tagani taji zuciyarta ta wani irin dokawa. Tsayawa tai ta rufe idanuwa tana karanto addu.o.i sannan ta bude su taci gaba da tafiya.

Wannan bashi bane karo na farko da take tunanin taga farhan ba. Sai kuma tazo taga tunaninta ne ke wasa da ita.

"Nuriyya......!"

Wannan karin ba da wasa zuciyarta take ba wajen dokawa. Yau abin yayi yawa. Ci gaba tai da tafiya.

"Nuriyya........."

Taji an sake kira a karo na farko. Da sauri ta juya tako sauke idanuwanta kan kyakkyawar fuskar farhan.

Girgiza kai take cike da rashin yarda. Babu ta yanda za.ayi ace farhan ne a gabanta.

Yanda yaga tana kallonshi ya tabbatar mishi da cewar bata yarda shi bane ba. Ta kara girma sosai.

"Nuriyya......"

Da hawaye a idanuwanta ta dafe haba da hannayenta biyu tana kallonshi. Muryarta na rawa tace.

"Yaya farhan......"

Sauke ajiyar zuciya yayi. Yana gayama zuciyarshi da auren wani akan Nuriyya. Lokaci daya ya fara jero neman gafarar Ubangiji.

Sauke murya yai yace.

"Kina lafiya? Baki da matsalar komai dai ko?"

Hawayen da take tarbewa ne suka zubo mata.

"Yaya farhan yaushe ka dawo? Yaushe ka dawo ni bansani ba?"

Da wani yanayi a zuciyarshi mai nauyi da yake kokarin dannewa yace.

"Watana bakwai da dawowa. Ancemun kinyi aure shisa ban nemeki ba. Baki da matsala dai ko?"

Ya karasa tambayar da damuwa sosai a muryarshi nason jin ko tana lafiya.

Kai ta ke daga masa. Alamar eh. Lokaci daya taga ya sauke ajiyar zuciya kamar wanda aka sauke ma wani nauyi mai girma.

"Ki zauna cikin farin ciki. Shine kawai burina. Bai kamata mu tsaya anan ba. Naganki ne bazan iya jure kin miki magana ba......."

Ta kasa cewa komai banda hawayen da take wani nabin wani. Ganin farhan ya mata dadi. Don tana yawan tunanin ko yana raye ko akasin hakan.

Murmushi tai mishi tasa hannu tana goge fuskarta. Kaman ance idonshi yakai kan gefen fuskarta da har lokacin hannayen nawaf na kwance rudu rudu a wajen.

Ga wani jini dayake kwance a saman goshinta. Cike da tashin hankalin farhan yace.

"Dukanki yai nuri?"

Cikin hanzari ta girgiza kai. Karshen abinda zata so shine nawaf yama ji taga farhan.

Idanuwa a kankance farhan yace.

"Ki fadamun idan yana dukanki. Karkiji tsoron komai"

Kai ta sake girgiza masa idanuwanta cike da hawaye. Dubawa yake gefe gefe ya hango wani kanti.

"Ki jirani anan. Ina zuwa......"

Da gudu ya karasa wajen shagon ya siyo biro da littafi. Ya yagi takarda ya rubuta mata number din wayarshi sannan ya dawo.

Mika mata yayi ta karba. Ya kalleta sosai cikin fuska yace.

"Ban damu dako dan waye ba. Ko waye shi. In ya tabaki ki kirani."

Kai ta daga mishi. Dakyar ya iya juya ba tare da ya sake ce mata komai ba saboda inhar zai tsaya ya kara ganin wannan kwanciyar jinin a fuskarta za.a iya samun matsala.

*

Ganin ya dawo da wuri yasa shi son suprising nuriyya yaje ya daukota a saloon. Ya hangota tsaye da wani da baisan kowaye ba.

Wani irin duhun kishi ya lillibeshi. Nuriyya tashi ce shi kadai bata kowa ba. Yana cikin mota yaga wancen ya wuce.

Ita kuma ta karasa bakin titi ta tare napep ta shiga. Jan motar yai da gudun gaske ya wuce.............!

****

Shiryawa take maganganun Abbah na mata yawo.

"Kina son saka yaron nan a ranki. In muna ranshi aida ya waiwaye mu. Kinsan bazan hanaki ba idan kina son zuwa kije. Allah shi kyauta"

Sauke numfashi tayi. Ta saka hijab dinta. Haneef ta kira a waya ringing din farko ya daga hadi dayin sallama. Ta amsa mishi ta dora da.

"Haneef ka sake fadamun address din gidan fu.ad yanzun zan tafi......"

"Banida wani aiki sosai momma. Ki jirani sai inzo in kaiki"

Ta amsa da.

"To shikenan Allah ya kawoka"

Ta kashe wayar bayan ya amsa ta da amin. Ta zauna tana jiranshi.

****

Lukman na zuwa office ya kira hamza a waya. Dan haneef ya fada mishi duk me ya faru.

"Hello...."

Hamza ya fadi ta dayan bangaren.

"Hamza ya gidan da iyali duka?"

"Alhamdulillah ya naka?"

"Duk suna lafiya. Daman abin nan ne daka turomun. Ban samu na kira ba sai yau......"

Da hanzari hamza yace.

"Wallahi abin yana raina. Ina son ka tabbatar mun ne tukunna"

Dan gyara zama lukman yayi kamun yace.

"Yar shi ce da gaske hamza. Yanzun haka maganar da muke yana gari"

Yanajin numfashin da hamza yaja kamun yace.

"Akwai damuwa. Ni ta yanda zan fadama hussaina ne matsalar. Nafison taji daga wajena"

Yar dariya lukman yayi. Rigimar hussaina da fu.ad banbancin su kadanne.

"Kunfi kusa. Daman abinda zan fada maka kenan"

Sake sauke numfashi hamza yayi.

"Ba damuwa. Nagode......."

Wayar ya ajiye. Shi kanshi inba ganin yarinyar nan yayi ba hankalinshi ba wani kwanciya zaiyi ba.

Wasu yan ayyuka ya karasa da suke gabanshi sannan ya tashi yaje yai report cewar bayajin dadi zai tafi gida.

Haneef ya kira yake fada masa shima yanzun ya dauko momma gidan zasuje. Suka tsayar da magana cewar su hadu acan din.

****

Tunda safe yana yin sallar asuba ya dawo baice ma safiyya komai ba ya dauki mukullin motarta dayake ajiye a gefe ya fice.

Hotel din ya koma yai wanka ya sake kaya. Ko awa daya baiyi ba yagama komai ya fito. Rasa me zai siyawa Nana yayi.

Hakan yasa shi siyo mata gasasshiyar kaza da fresh milk da alkawarin zai tambayeta mai ta fiso.

Hakan kawai ya wani tokare masa a wuya. Yarshi baisan me tafi so ba. Kawai dan safiyya ta boye mishi ita duk shekarun nan.

Haka ya koma asibitin da sake sake da yawa a zuciyarshi. Doc din Nana ya samu tazo. Tace musu zata duba wasu marassa lafiyan.

Zatai magana dasu nan da awa daya. Safiyya tai mata godiya ta fice. Idanuwa fu.ad ya sauke a kan safiyya hadi da fadin.

"Bata tashi ba har yanzun?"

Kai ta daga mishi ta amsa tambayarshi da.

"Alluran da akai mata ne. Zata tashi dasun sake ta"

Waje ya samu ya ajiye ledojin dake hannunshi. Ya zauna kan kujera ya zubama Nana idanuwa.

Safiyya bata san lokacin da ta tsinci kanta da cemishi.

"Ka karya?"

Kai ya girgiza mata alamar a.a kamun yace.

"Bana jin yunwa ko kadan"

Lumshe idanuwanta tayi ta ware su akan fuskarshi da take kan Nana kaman kallon da yake mata ne zaisa ta bude ido tace.

"In har kana son kula da ita kana bukatar lafiyarka. Kaci wani abu saboda ita"

Kai ya girgiza mata. Kanshi ciwo yake mishi. Baya son cin komai. Bata bi ta kanshi ba. Haka ta zuciyarta dake son ja mata matsala.

Tea ta hada mishi mai kauri. Ta mike tsam taje ta ajiye a gabanshi. Takoma ta zauna. Binta yai da kallo sannan ya maida hankalinshi kan cup din tea din.

Ya dauka ya soma kurba a hankali. Dakin shiru kamun wayar sofi ta dauki ringing. Yana kallonta ta daga hadi da yin sallama.

"Wallahi bama gida. Muna asibitin imzad......"

Shiru yaji tayi kamun ta sake cewa.

"Eh shi...."

"To ba damuwa. Allah ya kawo ku"

Ta sauke wayar. Ta kalli fu.ad daya zuba mata idanuwa. Duk da bai tambaya ba tasan bayani yake jira tai mishi.

"Momma da su hanif ne. Suna hanya"

Lumshe idanuwa fu.ad yai yana ajiye cup din tea din gefe hadi da fadin.

"Fuck........"

Kallonshi sosai safiyya tayi tana jin wani sabon mamaki na kamata.

"Fu.ad......."

Ta kira a hankali. Kallonta yai yana daga girarshi duka biyun.

"Karka cemun suma........"

Kasa karasa tambayar tayima dan batasan ta ina zata fara ba. Ya fahimci so take taji in har su momma ya bari duk shekarun nan.

Cike da takaici yace.

"Me kike tsammani? Bakwa son ganina ku dukanku"

Dafe kai tayi tana salati a ranta. Tun zuwan haneef ta karanci hakan tadai ki yarda ne kawai da zarginta sai yanzun.

To meye na damuwa tunda ma kowa nashi yabari. Har yan uwanshi dan ita yabarta ba tare da juyowa ba sai me.

Bata jin komai game dashi sai kudin da yake turowa account dinta lokaci lokaci. Wanda tunda ta samu aiki bata kara tabawa ba sai da Nana ta soma rashin lafiya.

*

Ta wani fannin fu.ad yaji dadi sosai. Saboda tun jiya su yake bukata. Shi bai saba kalar wannan tashin hankalin ba.

Daurewa kawai yake yi yana dannewa a zuciyarshi. Karin abin jiya sofi tace mishi akwai hope. Suna nan zaune doc jana ta leko tace su bita office.

Ganin safiyya ta wuce ya sa shi mikewa hadi da fadin.

"Ita kadai zamu bari?"

Ya karasa maganar yana kallon Nana. Doc jana tai murmushi tace mishi.

"Karka damu. Ba zata farka dan yanzun ba."

Shikam duk da haka bayason barin wajen Nana kona minti biyar. A haka yabisu har office din doc jana.

Suna zama ya kalleta yace.

"Bana son all nasihar nan da dogon zance. Kawai ki fadamun abinda ake bukatar yi. Koma menene"

Kallon safiyya tayi tadan daga mata kai alamar babu damuwa kawai tai mishi magana.

Cikin nutsuwa take mishi bayani da kuma stage din da cutar Nana takai. Ji yake har wani zafi zafi jikinshi yakeyi mishi.

Bayason bayanin nan. Muryarshi can kasa ya katse doctor jana da fadin.

"Do mi' a favour. Muje wajen maganar solution....."

Sauke ajiyar zuciya doc jana tai sannan tace.

"Hemotopoietic stem cell transplantation (HSCT) sai dai yana da hadarin gaske ga wanda zai donating din.

Sannan a stage din......."

Hannu ya daga mata hadi da fadin.

"Kawai ayi komenene. Kome kuke son cirewa a jikina. Kawai ta warke shine bukatata"

Kallonshi safiyya keyi zuciyarta na wani irin yawatawa. Komai na kwance mata. Bata taba zaton fu.ad zai damu bama dahar zai baro duk inda ya tafi yazo.

Da yazo bata taba zaton zai kalli nana ba ballantana tayi tunanin zai bada hadin kai.

Muryar doc jana ta katse ta da fadin.

"Zamuje dakai yanzun. Za.ai running wasu tests mugani ko zaka zama match"

Bawani bata lokaci fu.ad yabi doc jana suka bar safiyya nan da mamaki matuka a fuskarta da zuciyarta duka.

Tana sake jin yanayin nan na jiya dake goge mata tsanarshi a wasu bangarori data adana na zuciyarta.

Mikewa tai ta fito daga office din kenan wayarta ta kama ringing. Tana dubawa taga haneef ne.

Fita tai waje batare da tayi picking ba dan tasan sun isone shisa suke kiranta. A waje tagansu su uku.

Momma da haneef da lukman. Da fara.a a fuskarta ta karasa inda suke ta gaishe dasu.

Momma ta amsa ta da.

"safiyya daman kina nan?"

Shiru safiyya tayi tana sadda kanta kasa. Sai yanzun take ganin rashin kyautarwa abinda tayi. Koba komai momma ta nuna mata kauna da karamci.

Amman a lokacin bata son ganin su ne. Gaba daya laifin fu.ad ya shafesu. Tuna hakan kawai taji tsanar shi na sake dawo mata.

Dafata momma tayi tace.

"Abinda ya wuce ya wuce. Muje inga jikata"

Babu musu tai gaba suna binta a baya har dakin da Nana take. Momma ta zauna zuru tana kallon Nana da yanda kamaninsu suka baci da fu.ad.

Ta rasa me zatace. Addu.a tai mata ta mike ta kalli haneef tace.

"Haneef ka mayar dani gida. Mun dawo anjima........"

Ta karasa muryarta na rawa. Dan ganin Nana ya karya mata zuciya sosai. Ga kewar dan nata data addabeta.

Lukman ne yace.

"Ina fu.ad din?"

Sannan yazo ma momma data tambaya. Suka zuba mata idanuwa su duka ukkun.

"Yana wajen......."

Bata karasa ba ya turo kofar da sallama. Idanuwanshi suka tsaya kan momma da itama ta zuba mishi ido.

Wata irin kewarta da muryarta kawai da yakeji lokaci lokaci bata cike mishi ta taso. Wani irin abu yakeji da baida kalmomin dazai dora shi akai.

A hankali kafarshi ke takawa har ya karasa inda take. Hannuwanta ya kama ya dumtse cikin nashi. Ya kasa magana saboda yanda yakejin wani abu na shake mishi wuya.

"Fu.ad."

Momma ta furta a hankali tana jin yanda wasu hawaye ke taruwa a idanuwanta. Ya kara girma ya zama babban mutum.

Hannunta yakai bakinshi ya sumbata har lokacin ya kasa magana. Saidai idanuwanshi dake fada mata yanda yai kewarta.

Yanda rashinta yafi tabashi fiye dana komai. Idanuwanshi suka bar fuskarta zuwa cikin dakin. Haneef yagani tsaye ya jingina da bangon dakin yana kallonshi.

Wani irin dokawa zuciyar fu.ad takeyi. Hannuwan momma ya saki ya taka kafafuwanshi kaman anyisu da dutse saboda nauyin da sukai masa.

Gaban haneef ya karasa. Duk yanda yake gayama kanshi baiyi kewar dan uwanshi ba ya karyatu a yanzun.

Kauda kai haneef yai gefe. Fu.ad din ya matsa inda ya mayar da fuskarshi. Ya sake kaudata gefe alamar baya son ganinshi.

"Haneef........"

Ya fadi kaman zaiyi kuka. Sai lokacin ya ware idanuwanshi kan fu.ad din. Yana neman duk wani haushin shi da yake ji yana rasawa.

Hannuwanshi yakai ya kama kunnuwanshi yanda yakanyi insuna yara sosai yama haneef din laifi.

Ganin yai kasa yana shirin tsugunnawa yasa haneef saurin dagoshi. Da sauri fu.ad ya kalle shi.

"Please........"

Ya fadi da take tattare da wata irin kauna da ban hakuri da yakeji har ranshi. Hugging dinshi haneef yai suna sake ajiyar zuciya.

Lukman kallonsu yake. Yanzun ya tabbatar ko dan uwanshi da suka hada jini iya kaunar daza mishi kenan. Ba kadan yai kewar abokantakarsu da kaunarsu ba.

Karasowa yai kusa da lukman da wannan murmushin yana daga mishi gira duka biyun. Wani irin naushi lukman yakai mishi ya tare da hannu.

Yarfe hannunshi ya shigayi yana dakuna fuska.

"Wannan na rashin bawa kowa zabi ne....."

Haneef ne ya fara dariya kamun fu.ad din sannan lukman. Ba karamar kewarshi sukeyi ba.

Muryarshi na rawa yace.

"Kuncika son kanku. Shine ko sau daya baku taba kirana ba"

Wannan karon har haneef ne ya taho da niyar kawoma fu.ad din naushi ya ruga ya boye bayan momma.

Girgiza kai tayi tace.

"Ku kyalemun yaro mana"

Zama sukai su dukansu. Sai yanzun yakejin shi wani iri. Kaman an rage mishi wani irin nauyi a zuciyarshi.

Fada musu yake Nana zataji sauki dan doc tace mishi jibi zasu dawo su karbi result din. Safiyya dai na gefe tana ta kallonsu.

Karo na farko tun da nana ta fara rashin lafiya da bataji ta ita kadai ba. Hamdala takeyi a zuciyarta. Muryar Nana sukaji tace.

"Mumy....."

Gabaki dayansu suka tashi suka zagayeta. Daya bayan daya take kallonsu.

Haneef taima murmushin nan nata.

"Nasanka"

Dariya haneef yayi. Ya ja mata hanci a hankali.

"Inye ashe kina gane mutane haka. Kinsan sunana?"

Kai ta dan girgiza.

"Uncle haneef."

Ya kalli lukman dake gefe yace.

"Wannan kuma uncle lukman"

Wani gagging sound fu.ad yai dayasa haneef harararshi. Taya za.ace fu.ad nada yarinya baya shi kanshi yarinta na cikinshi.

Kallon haneef momma tayi tace.

"Kanku kawai kuka sani ko?"

Dariya sukayi. Nana na kallon momma tace.

"Granny......."

Fu.ad yai dariya hadi da fadin.

"Momma an tsufa. Kinga tagane ki babu wani introduction"

Safiyya bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba. Tayi kuskure sosai data boye musu Nana.

Jibi yanda suke nuna mata kauna kaman su karbe mata ciwon dake jikinta. Son kanta ne yasata boye musu ita.

Ca sukai zasu tafi da alkawarin zasu dawo da yamma in ba.a sallame su ba. In an sallamesu zasu zo gida.

Iya kofa fu.ad ya rakasu dan yanda Nana ta farka bayajin zai iya matsawa ko ina. Safiyya ce ta tafi ta rakasu.

Fu.ad ya koma gefen Nana ya zauna yana ce mata:

"Sannu. Banson mai kike so ba ina son siyo miki dazun dana fita"

Dariya Nana tayi dayaji har sautinta har zuciyarshi.

"Ni komai inaci fa. Kaban labari"

Yadanyi shiru kaman yana tunani kamun yace.

"Wanne iri?"

Yanda ta daquna fuska yaji zuciyarshi har wani tsalle tsalle take.

"She is so damn cute"

Ya fadi a zuciyarshi kamun Nana tace.

"Kowanne iri. About you and mum"

Ware idanuwa yai sannan yai kasa da muryarshi yace.

"Amman sirrine fa"

Dariyar ta sake yi. Ta mika mishi karamin yatsanta hadi da fadin.

"bazan fadi mata ba i promise"

Dariya sukai su duka sukaji safiyya ta turo kofar. Su dukansu suka ware idanuwansu akan ta iri daya.

Hade fuska tayi.

"Gulmata kuke ko?"

Kallon juna sukai sannan suka girgiza kai. Wani irin sama taji numfashinta yayi. Komai nasu iri dayane.

Karasawa tayi ta zauna daga dayan gefen gadon. Ta sumbaci goshin nana. Dariya nana tayi kadan dan tasan so take taji ko da zazzabi a jikinta.

"Zakici wani abu?"

Kai Nana ta daga mata alamar eh. Ta dora da fadin.

"Nagaji sosai. Ina anty jana mu tafi gida"

Kai safiyya ta girgiza mata tana hade rai. Fu.ad ya kalleta yace.

"wacece anty jana?"

A dake safiyya ta amsa shi da.

"doc dinta"

Mikewa fu.ad yayi haryakai kofa safiyya tace.

"ina zaka?"

Kallonta yai da yake fassara da gaske tambayata kike. Kamun yace.

"Bakiji me Nana tace bane? Gida take son zuwa"

Da mamaki safiyya tace.

"sai kuma akace abinda take so shi za.yi mata. In lokaci yayi zasu sallameta ai. Rigima ce kawai"

Tabe baki yai alamar wannan bai dameshi ba.

"Gida take son zuwa. Bandamu ba koda hakan na nufin a kwashi duk abinda ke cikin asibitin zuwa gida."

Bai jira me zatace ba ya fice abinshi. Nana tai mata wani murmushi har hakoranta suka fito hadi da fadin.

"I love him......."

Harararta safiyya tayi.

*#TeamAS*

*#AnaTare*

No comments:

Post a Comment