Thursday 4 May 2017

AKAN SO 35

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

             35

*Haka Allah yake ikon shi. Lokaci daya sai ya aiko maka da mutanen da zakaji kaman ka sansu tun farkon halittarka. You are not only a friend but a sister. I don't have to mention her name. ALLAH YA SADAKI DA DUKKAN ALKHAIRI SIS YAF*

*Saqon addu.o.inku ya sameni. Nagode. Tabbas #AnaTare*

Kuka take sosai. Can kasan ranta wani abu na fada mata babban kuskure tayi na kiran farhan. Idan kuma haukan nawaf ya hada dashi fa?

Ba zata taba yafe ma kanta ba in wani abu ya same shi ta sanadinta. Daga wani bangaren kuma yana gaya mata kome nawaf yai mata bai kamata ace tabarshi ba.

Yana tare da ita lokacin da take da bukatar taimako itama. Kamun ta karasa tunanin wayarta ta katse ta.

Tana dubawa taga number din farhan ne gabanta ya fadi. Salati ta shiga jerowa hadi da mikewa dakyar.

Wata azaba ta ratsata har tsakiyar kanta saboda zafin da taji a hannunta. Tallabe shi tai sabbin hawaye na zubo mata.

Dakyar ta iya daukar mayafinta ta dan yafashi. Ta riqe wayarta hadi da hannunta da take jinshi ba daidai ba. Tai waje.

Kallo maigadi yabita dashi. Tana fita kofar gida taga motar farhan yana ciki a zaune. Karasawa tayi ya miqo hannu ya bude mata murfin.

Tana shiga farhan ya kalli fuskarta yace.

"Ya Ilahi. Nuri......."

Yama rasa me zaice. Kowaye nuri ta aura zai iya cewa rashin tausayinsu in baizo daya da babanshi ba kadan ya hana.

Inba rashin imani da dabbanci ba. Baiga abinda zaisa ka ware karfi kana ma mace wannan dukan ba. Duk ya fasa mata fuska.

Yanda ta runtsa idanuwa ta sake dafa hannu yasa shi saurin kai idanshi wajen. A tsorace yace.

"Nuri saki hannun nan mugani"

Batai musu ba ta saki hannu. Wani zogi da radadi yasa idanuwanta suka kawo hawaye. Girgiza kai farhan yayi.

Ji yake kaman a bashi bindiga a ajiye mishi nawaf yaita harbi sai yaga babu sauran rai a jikinshi. Ya karyata. Hanunta a karye yake.

Wani daci yake ji a ranshi. Zuciyarshi na hango mishi mamanshi a kwance jini na binta. Yana hango abubuwa da dama na rayuwar shi.

Tayar da motar yayi suka nufi amini kano. Bai tsaya bata lokaci ba ya nemi wani abokinshi dake aiki a wajen. Dan yasan yanayin Nuri ba zasu kula su ba babu yan' sanda.

Shiya tsaya musu aka karbi Nuri farhan ya samu waje ya zauna da wani irin nauyi a zuciyarshi. Abu dayane yake gani.

Ko garin kano zata hade sai ya raba Nuri da wannan azzalumin. Koda zai mutu yana kokari kuwa. Daga kan mamanshi yai rantsuwa sai inda karfin shi ya kare akan masu irin wannan halin.

*

Bai san inda yake ba. Tunda ya dauki mota kawai tuqi yake. Harya samu waje yai parking. Kanshi ya hade da sitiyarin motar.

Zuciyarshi kuna take kaman ana zuba mata garwashi. Da ace yana da tabin hankali sai aima haukan daya sauke kan Nuri uzuri.

Runtse idanuwanshi yayi yana hango yanda ya taka mata fuska. Wani irin ihu ya saki daya fito daga maqoshin shi.

Kanshi ya daga ya doka kan sitiyarin motar. Yana maraba da zogin daya ziyarce shi. Kuka yake saboda komai ya masa zafi.

Gabaki daya duniyar ta hade mishi. Halin dayabar Nuri yake tunawa. Tayar da motar yayi yaja ta da karfin gaske yana hawan titi.

Gida ya wuce kanshi tsaye. Yana parking ko kashe motar bai tsaya yi ba ya wuce cikin gida da gudu.

Jini ne a falon kan tiles din. Bango ya dafa yana jin yanda kafafuwanshi ke son kasa daukar shi. Baisan ya mata wannan dukan ba.

Baisan inda hankalinshi yake ba.

"Nuri!!!....."

Ya kira da wata irin murya. Da bin bango idanuwanshi kafe kan jinin dake kwance kasa kaman wanda zai taso ya kama shi yake tafiya.

Kamun ya juya ya shiga dakin su. Bata ciki. Da karfi ya shiga kwala mata kira. Babu inda bai duba ba na gidan amman bata nan

Da gudu ya fito ya tambayi maigadi ko yaga Nuri yace mishi ta fice. Dafe kai yayi da hannayenshi biyu. Shikenan ya rasata.

Motarshi ya shiga. Ya jata. Yanda ya figi motar har maigadi saida ya tsorata. Yana hanya ya lalubo wayarshi ya kira yayanshi.

Bugu daya ya daga. Yana wani irin kokawa da numfashin shi yake fadin.

"Yaya nuri. Nuriyya ta tafi........"

Magana yayan nashi yake amman bayajin komai cikin kunnuwanshi da kanshi sai kalma daya. Sakin wayar yayi yana jin wani luuu.

Kamun ya saki motar gabaki daya ya dafe kanshi dake wani juya mishi. Hakan yasa motar ta kwace daga hannunshi ji kake wani quuuuuuuu.

Sama nawaf yaji motar tayi. Yana jinta ta dawo kasa dashi. Tana jujjuyawa kamun ya daina jin sautin komai cikin kunnuwanshi.

Wani abu yaji yana bin fuskarshi kamun wani irin duhu mai tsanani ya lillibe komai na duniyarshi...........!

****

Suna parking din motar hassan na fitowa daga gidan dauke da junior saman wuyanshi suna hira. Kallon shi fu.ad yake yi.

Lokaci daya ya hango hassan din daya bari. Ya kalli wannan saurayin dake tahowa. Baxai iya fassara abinda yake ji a zuciyarshi ba saboda baisan komenene ba.

Idanuwa ya dago ya fara sauke su kan lukman da yace mishi.

"Hassan ana ganinka daman"

Sam bai kula da fu.ad ba. Yar dariya yai ya amsa da.

"Ina wuni. Wallahi aiki babu lokaci sosai. Yanzun ma naje gidan yaya haneef nace bara na biyo........"

Kasa karasa maganar yai ganin fu.ad. A hankali duk fara.ar dake fuskarshi ta soma dakushewa har ya zamana babu ita ko kadan.

Junior ya sakko daga kan wuyanshi zuwa kasa. Da gudu ya ruga wajen lukman ya rike hannunshi.

A dakile hassan ya dauke idanuwanshi daga kan fu.ad ya mayar kan lukman.

"Zan wuce. Sai anjima....."

"Hassan......."

Fu.ad ya kira. Banza yai ya kyale shi. Yana karasawa inda machine dinshi yake ajiye ya hau. Kallon lukman fu.ad yayi. Yadan ware mishi idanuwa dake fassara babu ruwana.

Da hanzari fu.ad ya karasa inda hassan yake yana kokarin tayar da machine dinshi. Hannu yasa kan handle din machine din ya riqe dam.

Gefe hassan ya kalla dan baya son sake ganin fuskar fu.ad dinma kwata kwata. Zagayawa fu.ad yayi muryarshi a sauke yace.

"Hassan"

Batare da nuna alamar sanayya ba yace.

"Sannun ka fa"

Yaji yanayin muryarshi sarai. Ya share da fadin.

"Hassan please mana. Ka daina mun magana kaman yau ka fara ganina"

Sai lokacin ya ware idanuwanshi kan fuskar fu.ad din. Ranshi a bace yace.

"Nasanka ne?"

Dan runtsa idanuwa fu.ad yayi ya budesu.

"Harshenka bazai canza matsayina a wajenka ba"

Kallon mamaki hassan ke mishi kamun yace.

"Wanne matsayi kenan?"

Ya wani kankance idanuwa. Fu.ad ya amsa shi da.

"Yayanka"

Wata irin dariya hassan yai. Kamun lokaci daya ya hade rai. Ya hanga mishi lukman dake tsaye rike da junior.

"Kaga wancen shine yayana. Yaya haneef. Babban yaya. Banda su banda wani yaya.

Oh na manta da wanda ya yarda mu kaman bamu taba hada alaqa dashi ba. Now if you will excuse me inada abin da zanyi....."

Kokarin jan machine din yake fu.ad ya riqe dam.

"Saboda me yasa baka kirani ba? Ko da yake ba wannan ba. Kawai zanji ya kake"

Cikin idanuwa ya kalli fu.ad. Da gaske yake tambayar dayai. Yaga alama inya tsaya biyewa fu.ad ranshi kara baci zaiyi.

Shekaru goma sha daya sai yanzunne zai dawo yace zai zama yayanshi. Gaba daya cikin yan gidansu burin hassan bai wuce inya girma ya zama irin fu.ad ba.

Shine role model dinshi. Daga randa yasa kafa ya wargaza duk wata alaqa dake tsakaninsu ya hada da burin hassan din ciki. Machine din ya tayar yaja shi baya. Batare daya sake kallon fu.ad din ba yaja.

Har ya kusa gate ya tsaye. Juyowa yai yaga fu.ad din tsaye yana kallonshi. Da alamar roqo a fuskar shi hassan din yace.

"Do me a favour. Karka je inda hussaina take. Bata bukatarka. Mu duka bama bukatarka.

Bana son ka sake hurting dinta. Akwai wanda suka damu da ita da yawa"

Bai jira amsar shi ba yaja machine din ya fice. Hannuwan shi yasa ya rufe fuskarshi yana sauke numfashi. Yana tsanar yanda zuciyarshi ke fada mishi bai duba halin da kowa zai shiga ba yai abinda yayi.

Lukman yaji ya dafa shi. Hakan yasa ya bude fuskarshi ya sauke idanuwanshi da har sunyi ja saboda bacin rai.

"Bana son maganar please......"

Dan daga mishi kafada kawai lukman yayi. Ya daina saka matasalar fu.ad a rai.

"Ga junior...."

Kallon yaron fu.ad yayi ya shafa kanshi hadi da yi mishi murmushin da baisan ta inda ya fito bama a yanayin da yake ji.

Lukman yace ma junior.

"Ga uncle fu.ad...."

Dariya junior yai yace ma fu.ad.

"Nima dayan sunana fu.ad ne"

Da sauri fu.ad ya dago ya ware ma lukman idanuwa. Murmushi yai yadan daga mishi kai. Alamar yes sunan junior kenan.

Wani irin abu yaji a zuciyarshi. Bayan duk abinda ya faru. Da wani irin yanayi a muryar fu.ad din yace.

"Ion' deserve duk wannan"

Dan yatsa lukman yakai kan labbanshi yana nunama fu.ad din yai shiru kawai hadi da fadin.

"Zumuncinmu naiwa"

Kasa magana yayi. Kawai yaja junior jikinshi ne ya riqe tsam yana rasa abinda zaice ko abinda ya kamata yayi.

"Muje ciki ku gaisa da zainab"

Kai fu.ad ya girgiza mishi. Bazai iya ganinta ba yanzun. Bazai iya tuna abinda ya kamata ace yaima lukman bai mishi ba.

"Zan tafi lukman. Zamu gaisa wani lokaci. Ka kula dasu duka"

Kai lukman ya daga mishi. Gabaki daya yanayin fu.ad din ya bashi tausayi.

"Muje in sauke ka to"

Lukman ya fadi yana kokarin zaro mukullanshi daga aljihu fu.ad yace.

"Karka damu. Zan taka har saina danji dai dai"

Magana lukman zai ya katse shi da.

"Please"

Sauke numfashi lukman yayi. Yama rasa me zaice. Fu.ad din ya shafa kan junior hadi da fadin.

"Boy me kake so?"

Da sauri junior yace.

"Machine irin na uncle hassan"

Yar dariya fu.ad yayi.

"Umm sai ka girma kaman uncle hassan then. Amman yanzun zan siyo maka wanda bai kaishi ba"

Cike da jin dadi junior yace.

"Yeee ina so. Dady uncle zai siyamun machine"

Murmushi lukman yayi. Ya rasa me zaice har lokacin. Fu.ad ya kalle shi yace.

"Zamuyi waya...."

Ya wuce yana fita daga gidan.

****

Lafiya kalau suka ci abincin dare gabaki daya da yaran kaman babu wata matsala.

Jabir na nazarin yanayin jana. Zai iya karantar damuwar da take ta son boyewa. Kishin da take son dannewa nashi.

Yau tare dashi suka raka yaran suka kwanta banda ikram. Dan ji take ita ta girma. Suna kulloma yaran daki ya rike hannun jana.

Sumbatar hannun yai. Tai mishi wani murmushi a kasalance tana zame hannunta. Dakinsu ta wuce yabi bayanta.

Tana zaune kan gado jabir ya samu waje dab da ita ya zauna shima. Wani irin dokawa zuciyarshi take. Yanda komai yake tafiya da sauri na bashi mamaki.

Kaman yanda karbarshi da ayna tayi. Duk da batayi hakan ba saida ta fara tambayarshi ko matarshi tasani. Ya amsa ta da cewar saida ya fara fada mata.

Da saqon janar a wajenta. Sosai ayna taji dadi domin ta fada mishi bata son namijin da bashida adalci ko kadan. Sauke numfashi yai.

"Jana....."

Yaja sunanta. Idanuwanta ta sauke mishi. Sai ya sake jin kwarjininta ya cika shi. A sanyaye yace.

"Ayna ta amince dani. Bana son aja lokaci tunda ni ba yaro bane dazan tsaya wannan abubuwan. In anjima wata uku"

Wani irin numfashi jana taja tanajin yanda zuciyarta take tafasa. Wannan karin ta kasa jure hawayen da take ji. Suka zubo mata a hankali.

Jikinshi jabir ya jata. Tana wani irin kuka marar sauki. Sumbatar kanta yai da duk wani waje inda bakinshi zai iya kaiwa yana dan bubbugata sigar lallashi.

"Jana bazan taba wulaqantaki ba in shaa Allah. Wallahi ina sonki. Ina sonki sosai.

Badan bana sonki zan kara aure ba. Bansan dalili ba nima......"

Jin yanda duk ya rikice yasata dagowa ta hada bakinta da nashi nadan wani lokaci. Sannan ta kalli fuskarshi. Hannunshi ta riqo ta dumtse cikin nata.

"Nasani honey J. Ina sonka nima. Bazan iya hana zuciyata kishinka bane.

Allah ya sanya alkhairi. Ina ma ayna godiya da karbar mijina da tayi. Allah ya bani ikon tayaka sonta.

Allah ya tabbatar da alkhairi ya kaimu wata ukkun"

Lumshe idanuwa yai. Yana ma Allah godiya daya bashi mata kalar jana. Haqiqa ita din alherice a rayuwarshi. Riketa yai tsam a jikishi yana kwantar dasu.

Yanajin yanda take kuka a hankali har ranshi. Sun jima sosai a haka. Kamun ta zame daga jikinshi. Toilet ta shiga ta dauro alwala. Yana kwance yana kallonta ta shimfida kafet ta fara nafila.

Tun yana kallonta har bacci ya dauke shi. Sosai jana take roqon Allah harda kukanta daya bata karfin zuciya ya bata juriya na danne kishin da take ji.

Taima jabir dinma addu.a ta fatan Allah ya tabbatar mishi da alkhairi. Kishin shi bai sata baqin ciki da auren shi ba sam.

Akan kafet din tai bacci. Da wata irin nutsuwa taban mamaki.....! Haqiqa rashin tabewa na tare da duk wanda ya riqi addu.a da kai kukanshi wajen Allah.

****

"Hello....... Hello nawaf wai baka jina ne?"

Ibrahim ke fadi kamun ya kula kiran ya katse. Ajiyar zuciya ya sauke ya mike daga kwanciyar da yake. Jallabiyar jikinshi ya cire yana sake kaya yana kwalama Jidderh dake kitchen kira.

Da saurinta ta karaso

"Afuwan dear. Ban jika bane....."

Ganin yana sa kaya yasata fadin.

"Ina zaka?"

Saida ya balle maballan shaddar shi sannan ya amsa ta da.

"Nawaf ne wallahi. Bansan me yai ba. Yace nuriyya tabar gidan. Kinsan shi dai zai iya yin wani haukan.

Ya kira baya jina. Kuma sai kira nake taqi shiga. Zanje in duba......."

Bai karasa ba wayarshi dake kan gadon ta hau ringing. Ya dauka yana fadin.

"Inaga ma shine....."

Dubawa yai yadan daquna fuska ganin sabuwar number ce. Ajiyewa yai ya karasa saka links din rigarshi.

Jidderh tace.

"Bakai picking ba....."

"Baquwar number ce"

Ya fadi a taqaice lokacin da wayarshi ta sake daukar ringing.

"Bansan sau nawa zance maka ka dinga daga baquwar number ba. Emergency ake gudu wallahi.

Ko wata lalurar ta daban"

Dan daquna fuska ya sake yi alamar ya takura. Kamun wayar ta yanke. Dauka yai yana kallonta da fadin.

"Saina dawo"

Ta bude baki zatai magana ringing din wayar ya sake katse ta. Ta kalli ibrahim da yake fassara. Kaga me nake ce maka ko.

Wayar ya daga ya kara a kunne hadi da fadin.

"Hello....."

Daga dayan bangaren aka ce.

"Please ko waye yazo titin dake zoo road ta wajen masallaci. An samu mummunan hatsari ne kuma wannan shine number na karshe a wayar mai hadarin.

Babu rai a jikinshi. Kazo da hanzari"

Subuce wa wayar tai daga hannun ibrahim. Wani irin jiri yaji na dibarsa
Baisan sanda yai kasa ba. Yana dafa gadon.

Da sauri jidderh ta riqo shi a rikice take fadin.

"Menene? Dan Allah kaimun magana....."

Yana wani irin jan numfashi ya amsa ta da.

"Jidderh nawaf.....nawaf..... "

Girgiza shi take tana fadin.

"Menene?  Me nawaf din yayi?"

Wata zufa yake ji tana fito mishi tako ina na jikinshi.

"Nawaf......yai accident...."

Wani irin kuka jidderh ta saki tana riqe baki. Waje ta samu ta zauna itama ko ina na jikinta na kyarma.

Mikewa ibrahim yayi. Ya dauke wayarshi yana fita daga dakin da gudu. Babansu ya fara kira yana bude mota yana shiga.......!

****

Tunda ta tashi daga bacci taganta wani shuru shuru bata ce komai ba.

"Nana? Lafiya?"

Daqyar ta iya ce mata.

"Cikina ciwo mumy..... Ciwo sosai"

A rikice sofi ta mike. Ta kama nana ta sabe ta a kafadarta. Mayafinta ma a kafada ta dorashi ta dauki mukullan motarta ta fita.

Saida ta kwantar da Nana bayan motarta sannan tazo ta bude gaban ta shiga. Maigadi ta fadama kowa yazo yace suna asibiti.

*

A hanya yai sallah. Ya samu taxi zuwa gidan safiyya da wani irin nauyi a zuciyarshi. Sam baiji dadin abinda hassan yai mishi ba.

Mai taxi din na ajiye shi ya bashi kudinshi ya karasa ya kwankwasa. Maigadi ya ce mishi suna asibiti.

Allah yaso mai taxi din bai tafi ba. Dan haka ya koma ya shiga yana fadin mishi sunan asibitin.

*

Kasancewar ta kira doc jana ta rigada tabar asibitin yasata wucewa emergency da nana. Suna zaune suna dan jira aka shigo da wani yai hadari da gudu.

Idanuwa Nana ta kafe a kanshi. Tana kallon fuskarshi. Duk da jinin dake jiki da yanayin yanda suke wuce dashi bai hanata gane shi ba.

Ganin yanda jikinta ke kyarma ne yasa safiyya kamata tana kokarin boyeta jikinta dan ko ita nata jikin bari yake.

Tureta Nana tayi tana binsu da kallo har suka bace ma ganinta. Sakkowa tai daga inda take zaune. Safiyya ta kamata.

Kuka take. Kuka take sosai tana fadin.

"Mumy shine. Wallahi shine......"

Kamata safiyya tayi tana kokarin lallashinta amman a banza. Tasan zata iya samun matsala. Shocked na komai ko excitement in yai yawa yana iya bata matsala.

Dai dai shigowar fu.ad wajen. Yanata hange hange ya hango su. Da gudu ya karasa. Ganin kukan da Nana keyi yasa shi jin wani abu ya soki zuciyarshi.

Da hawaye cike idanuwan safiyya tace.

"I need to calm her........"

Tsugunnawa fu.ad yai. Ya tallabi fuskar Nana cikin hannunshi yana kokarin hada idanuwanshi da nata.

"Shhhhhhhh. Nana kalle ni"

Kuka take sosai. Har numfashinta na wani sama sama. Sai lokacin ta sauke idanuwanta cikin na fu.ad muryarta na sarqewa tace.

"Shi ya taimakeni na ganoka. Shi ya biyamun kudi...... Shine ya biya aka sa wasiqa ta..... Mutuwa zaiyi ko?"

A rikice fu.ad ya kalli sofi. Dan zancen Nana babu wanda ya fahimta. Dafe kai safiyya tayi zatai magana Nana ta ci gaba da jan wani irin numfashi.

Zaka rantse asthma attack ne ya kamata. Jikinshi fu.ad ya riqota yana kwalama duk wani wanda zai saurare shi kira.

Da gudu kuwa wasu nurses sukayo kansu. Kokarin karbar Nana suke a hannun fu.ad yaqi basu ita. Ji yake kaman zai miqa musu zuciyarshi.

Saida safiyya tace.

"Fu.ad ka basu ita. Taimaka mata zasuyi...."

Sannan ya sakar musu Nana yana binsu da gudu. Dai dai dakin sukai kokarin dakatar dashi.

"She is mi' daughter. Babu hankali a jikin duk wani wanda yake tunanin zai hanani shiga....."

Ganin da gaske fu.ad din shirin bangaje nurse din yake. Likitan dake ciki yace tabarshi ya shigo. Tsaye yai yana dafe da haba yana kallonsu.

Wata allura sukaima Nana. Har lokacin bata daina kokawa da numfashin taba. Kamun tai wani laqwas.

Wani tsalle zuciyar fu.ad tai kaman zata baro kirjinshi. Yaune rana ta farko a rayuwarshi da yasan meye asalin tsoro.

Da gudu ya karasa kan gadon da take yana ture likitan dake kokarin sakama Nana ruwa.

Tsugunnawa yayi. Yasa hannu ya taba fuskarta. Muryarshi a dakushe yace.

"Me kukai mata?"

Dafashi likitan yayi.

"Relax. Allurar bacci mukai mata. Tana bukatar hutu sosai"

Yana nan tsugunne suka gama mata duk wani taimako da take bukata a lokacin. Likitan yace fu.ad ya fito daga dakin dan tadan huta.

Ya ki. Barinshi sukai. Hannun nana da bashida komai ya kama ya sumbata. Ya kamashi ya dora kan fuskarshi yana rufe idanuwanshi.

Tunanin abubuwan daya rasa na rayuwarta ne ke wani irin ci mishi zuciya. Dazai iya daya karbar mata wannan ciwon.

Dan a yanzun ji yake tafi mishi muhimmanci akan komai na rayuwarshi........!

*#TeamAs*

No comments:

Post a Comment