Thursday 4 May 2017

AKAN SO 15

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

         15

*Just wanna say a big thanks to SOFTIE for all the prayers and for being #1 fan of Akan So. May Allah be with you sweetheart and the other fans. Love you all.*

"Lukman magana nake maka fa"

Fu.ad ya fadi ranshi a bace. Waje lukman ya samu yai parking. Ya maida hankalinshi kan fu.ad.

"Anan kake nufin zamu tsaya. Ko da kafafunmu zamu karasa wai........ "

Shiru yai ganin yanayin fuskar fu.ad din. Tsoro ne a bayyane. Dan sai lokacin nauyin yanayin daya hadasu da safiyya yake danne shi.

"Mu koma. I can't, what am i going to say to her"

Fu.ad yake fadi a rikice. Yana running hannun shi kan fuskarshi saboda wata zufa da yake ji a jikinshi.

Dafa mishi kafada lukman yayi.

"Hey. Ka manta ba saika mata magana ba. Kawai ko ganinta kayi. Kabari mu karasa wajen gidansu mu tsaya ko zata fito"

Tunda ya fara maganar fu.ad ke girgiza kai alamar bai yarda ba. Gaba daya ya wani birkice.

Abin har tsoro ya soma bama lukman. Shikam indai haka so yake ya fara gudun ya kama shi.

Kalli yanda gaba daya fu.ad ya wani fita hayyacin shi. Ya kasa samun nutsuwa.

Shikam fu.ad jiyai iskar dake cikin motar ta mishi kadan. Da sauri ya bude murfin motar ya fita.

Jingina bayanshi yai da motar. A hankali ya zame ya tsugunna yana wani maida numfashi da sauri sauri.

Sama sama yake jin lukman na fadin.

"Fu.ad? Fu.ad wai lafiyarka kuwa"

Dakyar ya daga mishi kai. Ganin yaki tashi yasa lukman kallon shi sosai yace

"Ka taso to ka dawo cikin motar"

Dago kai yai.

"Iskar dake ciki nake jin tamun kadan"

"Okay sai mu sauke glass ko abar murfin a bude"

Mikewa fu.ad yai yace.

"No ka jirani. Barin dan taka in dawo"

Da alamun rashin yarda lukman yace.

"Anya kam. Kabari dai mu tafi tare"

Wani guntun murmushi yai yace

"Karka damu banajin a yanayin da nake ciki zan iya wani tashin hankali. Kawai zan ganta ne in dawo"

Kai kawai lukman ya daga mishi. Ya kama hanya ya mike. Tun kamun kafafuwanshi su karasa zuciyarshi ke hango gidansu safiyya.

*

Tsaf ta gama shirinta. Ta dauki jakarta ta duba duk abinda take bukata yana ciki.

Kasancewar yau asabar tun karfe biyu sun shiga islamiyya. Allah ya mata tsoron bulala.

Shisa dakyar ta tsaya taci abinci. Shima dan inna nata fada ne. Fitowa tai tace

"Inna saina dawo"

"Allah ya tsare. A dai kula safiyya"

Ta amsa da

"In shaa Allah"

Ta fice. Tana ta sauri. Kawai jitai gabanta na faduwa bata kuma san dalili ba.

Ita dai sauri take ta karasa islamiyya ta samu asiya ta biya mata karatun da akai na sira ranar laraba.

Tana can tana tunani bataji komai ba. Sam bata kula da mutum ba saida suka zo gab.

"Ya Rabbi...."

Ta fadi tana kaucewa da hanzari dan sun kusan cin karo. Kaman ance ya dago.

Wani irin tsalle zuciyarshi tai kamun yaji ta dai daita a mazauninta. Amman ta wani matse saida ya fitar da wani numfashi.

Kwanaki sittin da takwas. Amman jinsu yake kaman watanni sittin da takwas.

Ita kanta safiyya kallo daya zakai mata kaga tsantsar razanar dake fuskarta.

Hannu tasa ta shafa fuskarta. Dan ta kasa tabbatar da gaskiyar dake gabanta. Gani take kaman mafarkin daren ne ya biyota da ranar nan.

Wani rauni ya ziyarci zuciyarta. Lokaci daya ta rasa kome take ji. Ko me ya kamata taji.

Kallonta kawai yakeyi. Idanuwanta ta sauke cikin nashin nan da kalar su ke bata mamaki.

Idanuwan da ta kasa mantasu. Idanuwan da suke farautarta duk dare tun da ta gansu.

"Sofi..... "

Ya kira da wani yanayin da zuciyarta kadai ta fahimta. Inalillahi ta shiga jerowa a zuciyarta. Ba wanda ya taba kiranta da sunan daya kirata.

Idanuwanta ta sauke daga cikin nashi ta kafe su a kasa. Ji take kaman kasa ta bude ta hadiyeta.

Ga kafafunta ta kasa ko da daga su. Ji take ma kaman sun daina aiki. Dan ta kasa motsa su.

So yake ta dago ta ci gaba da kallon shi. Zai iya rantsewa yanajin dawowar abinda ya rasa da duk numfashin da yake saukarwa.

"Sofi.... "

Ya sake kiran sunanta. Kaman da kanshi kadai yake magana. Saboda sanyin muryar dayai amfani dashi wajen kiran sunan nata.

Aman taji shi. Ba kiranshi kadai taji ba. Har kusancin shi da ita. Taki dagowa ne saboda tana ta neman inda ta adana tsanarshi ta rasa.

Fatan da taje ya tabbata yau. Kuma fata take wani abu da zai kauda shi yazo. Saboda yanayin da take ji ya girmi wanda take zaton tanaji a baya.

Jitake zuciyarta kaman ruwa ce ba tsoka ba. Tanajin yanda take narkewa tana mata yawo a wajaje da ba zasu fadu ba.

Dakyar taji ta iya cira kafarta. Ta motsa dayar kafar dan ta tabbatar basu daina aiki ba.

Gani yai tana shirin rabashi ta wuce. Yaji zuciyarshi ta wani yawata tana son binta. Da hanzari ya tare hanya.

"Karki tafi. Kimun magana inji"

Ji take kaman ta toshe kunnuwanta ta daina jin muryarshi.

Wani irin tasiri take mata naban mamaki. Wucewa ta sake zuwa zatayi ya tare hanya. Dakyar cikin muryar da ita kanta bata gane ba saboda rauninta tace

"Ka matsa dan Allah"

Ajiyar zuciyar daya sauke yasa ta dagowa cikin hanzari. Suna hada ido tai saurin sauke nata saboda abinda kw cikin idanuwanshi suna neman jan zuciyarta inda bai kamata ba.

"Keep talking. Kice koma menene"

Kanta a kasa tace

"Me kake yi anan?  Duk abinda kaimun bai isheka ba saika biyo ni?"

Lumshe idanuwanshi yai. Ya sake bude su.

"Banda kalaman dazan dora abinda ya faru akai. Karki dauka da zabi na nazo nan. Inda wani zai hangomun yanayin nan bazan taba yarda ba"

Idanuwanta cike taf da hawaye tace

"Ka kyaleni. Dan Allah kabarni kawai"

Yanayin yanda muryarta ke rawa ya taba shi. Da sauri yana daga hannuwa yace

"Zan kyaleki. Ina so muyi magana ne kawai. Kiban number din wayarki"

Bata son hawayen da suka cika mata ido su zubo. Bata son ta nuna wani rauni a gabanshi fiye dana yanzun.

Ita ina taga waya. Koma tana da ita akan me zata dauki number dinta ta bashi. Taga alama in ba amsa ta bashi ba bazai kyale ta ba.

"Ni bani da waya. Ka tafi kawai dan Allah"

Hannuwanshi ya hada duka biyun waje daya alamar rokonta sannan yace.

"Zan tafi. I promise."

Aljihunshi ya laluba. Ya dauko nokia dinshi. Sim din ciki ba amfani yake dashi ba.

Pha.iza ta siya mai double. Ta bashi daya. Sai ma yazo Nigeria ne yake bude wayar. Kuma dayar wayarshi ma akwai etisalat.

Mika mata nokia din yai yace.

"Zan kiraki a wannan wayar sai muyi magana"

Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi. A tsorace take girgiza masa kai.

"Aa. Ni ka kyale ni kawai"

Kanshi yaji ya soma ciwo nan take. Shikam bai san yanda zai ba. Ya dauka zuciyarshi zata gamsu da ganinta kawai.

Yanzun kam yaji yana son jin muryarta. Kuma taki karbar wayar.

"Zan dawo gobe to"

Ji take kaman ta rusa ihu. Me yasa bazai gane bane. Bata so ya dawo gobe. Ba taso ya dawo jibi. Bata ma so ya sake dawowa kwata kwata.

"Karka dawo......"

Kallon dayake mata ya makalar da sauran kalaman. Muryarshi a dake gashi ya kafeta da idanuwan nan yace

"In kika karbi wayar mukai magana inba haka ba bansan yanda za.ai in kasa dawowa ba"

Ganin tai shiru yasa shi cewa.

"Ki kalleni sosai. Da ina da wani zabi ba zaki ganni anan ba"

Itama da tana da wani zabi da ba zata ko tsaya inda inuwarshi take ba. Ballantana ma ta saurare shi.

Amman rashin zabin ne yabarta da tsayuwa take jin abinda yake fadi. Bayan duk abinda yai musu.

So yake tace wani abu. Shi kanshi zuciyarshi ke magana.

"Sofi..... Ki karba"

Kai take girgiza mishi. Ganin hankalinshi nakan ta karbi wayar ne yasa ta yin saurin raba shi ta wuce.

Rufe idonshi yai ya bude su yana fadin.

"Damn it..... "

Binta yai. Ganin sun jera suna tafiya. Ta kuma tabbatar dasun kara gaba mutane na zaune majalissa.

Bayan hakan kowa zai iya zuwa wucewa yagansu. A koma ace an ganta ta jero da wani.

Tsayawa tai. Hawayen da take ta tarbewa suka zubo mata. Hannu tasa zata goge su.

Baisan yanda akai hannunshi yai kokarin kaiwa fuskarta ba. Sai ganin ta kauce da sauri yayi.

"Kar hannunka ya sake kokarin kawowa kusa dani"

Safiyya ta fadi tana share hawayenta. Jin yanda ranta ya baci yasa shi saurin cewa

"Kiyi hakuri..... "

Kalmomin ya sake maimaitawa a zuciyarshi. Yanda suka fitona saukake ya bashi mamaki.

Zai iya kirga mutanen daya taba ba hakuri a rayuwarshi. Amman yau gashi ta fito a saukake kan laifin da baiyi bama.

Ture wannan yai gefe. Yana cikin kananun abubuwan da basu bane a gabanshi. Kallonta yake. Wasu hawayen suka sake zubo mata.

Wani kunci yaji ya lullube shi. Baya son kukan nan. Bai taba zaton kukan wani zai dame shi ba sai yau.

Ba damunshi kadai yai ba. Tokare mishi zuciya yai.

"Ki daina. Ki bari. Banason ganin kukan nan..... "

Sai taji ma kaman dayai magana sake bude ma hawaysn hanya yai. Wasu nabin wasu haka suke zubo mata.

Dakyar cikin kuka tace

"Nace ka tafi. Sai wani yaganni tsaye dakai?  Me kake so inyi?"

Ja yake da baya. Dan yanayin zai iya jure komai banda kukanta.

Da baya baya yake tafiya. Yace mata

"Na tafi. Na tafi sofi. Banda zabi ne...... "

Tana kallo ya juya da gudu ya tafi. Sai taji tana son ya juyo ko da sau dayane ta sake ganin fuskarshi.

Ko hakan zai zama na karshe a rayuwarta. Wani irin abu takeji da ta kasa samo masa kalma.

Waje ta samu jikin bango ta karasa. Hijab dinta tasa ta goge fuskarta. Tasan ba zata iya zuwa islamiyya ba.

Juyawa tai ta koma gida. Da sallama ta shiga muryarta a dakushe tana kokarin boye kome take ji saita shiga daki.

"Safiyya?  Lafiya dai ko?"

Kanta a kasa tace

"Inna kaina ke ciwo sosai. Shine na dawo gida"

Cike da kulawa inna tace

"Subahanallahi. Sannu. Kije ki kwanta. Ko usman inya shigo yaje ya siyo miki magani"

Bata amsa inna ba ta shige daki. Jakarta kawai ta ajiye ta kwanta.

Dunkule jikinta tai waje daya. Ko hijab bata cire ba. Wani irin kuka marar sauti ya kwace mata.

Ji take yanda kukan ke fitowa daga zuciyarta kaman fu.ad ne zai fita.

Amman ina. Yau ya sake dasa mata abubuwan da tasan ba zasu gogu ba. Kuka tai har bacci ya dauketa.

*

Yana karasawa ya bude mota ya shiga. Yaja murfin ya rufe. Kanshi ya hada da gaban motar yana jin wani irin yanayi.

"Fu.ad menene?  Lafiyarka kuwa?"

Lukman yake tambaya cike da kulawa. Batare daya dago ba yace masa

"Muje gida"

"Bangane muje gida ba. Me ya faru wai?  Kaganta ne?"

Dagowa yai a kufule.

"Do me a favour. Shut the fuck up"

Dariya lukman yai.

"Easy sharukhan. Karka kawomun cizo. Daga tambaya. In masifa kake ji ka sauke ta wa zuciyarka ba lukman ba. I am just trying to help"

Kauda kai kawai fu.ad yai gefe. Baice komai ba. Kilan inyai banza ya kyale shi yagane cewar bayason magana ne gaba daya.

Aikam hakan akayi. Wakama lukman din ya saka. Da gangan yasa duk wakokin dayasan fu.ad na cewa baya so.

Ya kula baima san yanayi ba. Tunda ya jingina kanshi da kujera ya kalli gefe bai juyo ba.

*

Ko parking bai bari lukman yayi ba ya bude murfin motar ya fita. Da gudu ya shiga gida yahaura sama zuwa dakinshi.

Maida kofar yai ya kulle. Sannan ya zare takalmin dake kafar shi. Nan inda yake tsaye ya cire kaya. Daga shi sai boxers ya shiga toilet.

Ruwa masu sanyi ya sakarma kanshi. Yanajin yanda sanyin ruwan baya kaiwa inda yafi bukata.

Lumshe idanuwanshi yai. Zuciyarshi na wani irin abu. Fuskar safiyya na masa yawo cikin idanuwanshi.

Kunnuwanshi najin muryarta. Komai ya sake cakude mishi. Bai san iya minti nan daya dauka a bandakin ba.

Sanda ya fito ya sake kaya. Kwanciya yai dan ji yake kaman wanda akai ma dukan tsiya.

Wani ciwo ko ina na jikinshi yake yi da bashi da alaka da gajiya.

Kwankwasa kofar yaji anayi. Yai niyyar sharewa. Jin muryar haneef ya sa shi tashi dakyar ya je ya bude kofar.

Komawa yai ya zauna kan gadon. Haneef ya karasa ya zauna kusa dashi.

"Fu.ad?"

Muryarshi can kasa yace

"Haneef bansan yazanyi ba ni. Taki karbar wayar muyi magana. Kuma tace in tafi bata so in dawo. Bazan iya ba..... "

Yana maganar yana watsa hannuwanshi alamun komai ya kwance masa. Ganin haneef din ya nutsu yana saurarenshi ya sashi sauke numfashi kamun ya nuna kanshi da hannun shi yace

"Kalle ni. Kaman wanda ya zautu. Em' clueless....."

Gyara zama haneef yai hadi da fadin.

"Kamun magana yanda zangane fu.ad. Menene?  Wacece?"

A hankali yace

"Sofi..... Safiyya. Yarinyar nan ta bichi....."

Hannu haneef ya daga mishi yana girgiza kai.

"Don't. Please fu.ad karka cemun son ta kakeyi. Karka fara......"

"Too late. Abinda nakeji yafi so"

Fu.ad ya fadi yana dafe kanshi cikin hannuwa. Haneef kam ya rasa abinda zaice.

Kawai abu dayane yake a bayyane. Ko shine a matsayin iyayen safiyya. Ko zata mutu ba zai bata yaron daya wulakanta su ba.

Sau wajen hudu yana bude baki zai magana. Amman ya rasa me zaice.

"Hmm... "

Fu.ad yace yana kauda kai. Dayake nuna cewa ya fahimci haneef kanshi na hango rikicin dake tattare da hanyar da kaddara ta dora shi.

A nutse yace.

"Munje dazun nida lukman. Kuma gobe ma zan koma saboda ina bukatar sake ganinta"

Sai lokacin haneef yace

"Karka yi fu.ad. karka sake zuwa ka kara complicating ma kanka abubuwa. It will not work and you know why"

Cikin idanuwa ya kalli fu.ad.

"Issue dina da ita ne ba da family dinta ba"

Kallon baka da hankali haneef yake mishi.

"Waye zai baka yarinyar? Kaga fu.ad ka hada kayanka gobe ka koma. Zaifi ma kowa kwanciyar hankali"

Fito da idanuwa yai.

"Kana nufin in barta?"

Kai haneef ya daga masa.

"I can't. Bazan iya ba haneef. Ka tafi kabarni kawai...... Just go!"

Sanin halin fu.ad yasa haneef tashi ya fita. A yanayin dayake bazai saurari wani abu ba. Inya dan nutsu sunyi magana.

Yana fita fu.ad ya kwantar da fuskarshi cikin pillow yanajin gaba daya duniyar ta masa wani irin kunci.........!

No comments:

Post a Comment