Thursday 4 May 2017

AKAN SO 32


*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

              32

*Seriously ina feeling kaunarku. #AnaTare*

Yana sauke khadee makaranta ya wuce gidansu. Tun daga yarinta shi fu.ad yake bari da goge daudar barnar da yayi.

Ba bakon abu bane wannan. Saidai rabon da maganar fu.ad ta gifta cikin gidansu ma an dauki shekaru. Momma na kokarin yi musu tun yana gidan.

Sai suyi shiru su dukansu. In abinci akeci bamai kara magana har a gama. Sai tabari. To yanzun dinma shi fu.ad ya bari da zuwa yiwa momma bayanin safiyya na nan.

Bata bar garin ba kaman yanda suke dauka. Tana nan daram kuma harda yarinya. Yar fu.ad.

*

Da sallama ya shiga gidan. Dai dai fitowar Hassan daga shi sai 3 quarter da singlet. Da fara.a ya amsa sallamar hadi da fadin.

"Yaya haneef ina kwana"

"Antashi lafiya? Babu aikine yau?"

Hassan yadan sosa kai.

"Akwai fa. Yanzun naketa shiri. Yasu anty ummie da khadee?"

Kallonshi haneef yayi sosai.

"Khadee ai tayi fushi. Tanata tambayarka"

Dariya hassan yayi.

"In shaa Allah zanje in daukota tai mana weekend."

"Allah yasa. Momma ta tashi ne?"

Dan yamutsa fuska yai kamun ya amsa da.

"Tun asuba da muka gaisa. Bansan ko ta koma bacci ba. Ka kira wayarta mana"

Kai haneef ya daga masa yana lalubo wayarshi daga aljihu. Wucewa hassan yayi abinshi.

Waje ya samu ya zauna ya kira momma a waya yace mata yana babban falo. Ko mintina biyu ba aiba ta fito.

"Ina kwana"

Haneef din ya gaishe da ita a ladabce. Saida ta karaso inda yake sannan ta amsa shi da.

"Lafiya dai ko haneef?"

Dago kai yai hadi da fadin.

"Lafiya kalau....."

Shiru yadanyi yana tunanin ta inda zai fara mata maganar kamun cikin sanyin murya yace.

"Akan fu.ad ne........."

Wani irin dokawa zuciyar momma tayi. Saboda yau kwana uku kenan bata samun wayar fu.ad din. Kuma bai kirata ba kaman yanda yakanyi.

Tanata tunanin ko lafiya. Babu dai wanda zata tunkara da maganar ne shisa tabarma ranta abin. Jin sunanshi a bakin haneef yau ba karamun tayar mata da hankali yai ba.

A kagauce tace.

"Eh meya faru?"

Ganin yanda ta tsorata yasa haneef girgiza kai da saurin fadin.

"Jiya ne lukman yazomun da wata wasiqa da take ta yawo a labarai da yanar gizo gabaki daya.

Akan wata yarinya Nana da take neman babanta. Cewar yana tunanin yarinyar yar fu.ad ce........"

Ware idanuwa momma tayi akan haneef cike da rudanin jin maganar da yake yi kamun ya ci gaba da fadin.

"Nayi kokwanto sosai ko da ya fadamun yaje makarantarsu yarinyar yaganta. Shine nai tunanin ko safiyya na garin nan.

Shine jiya da yamma bayan mun rabu da lukman din naje tsohon gidansu da fu.ad din. Momma tana nan.

Ta boye mana ne saboda bata son alaka da duk wani wanda ya hada jini da fu.ad bayan abinda ya faru.

Nakuma ga yarinyar. Nana din. Yar fu.ad ce babu ko musu a ciki........"

Cike da tashin hankali momma ke kallon haneef. Dakyar ta samu kanta da fadin.

"Ta yaya? Nakejin fu.ad ga abinda yayi. Bazai taba samun yara ba?"

Rausayar dakai gefe haneef yayi. Dan shi kanshi baisan yanda akai ba. Koma dai ya akai yarinyar fu.ad na nan. Sauke numfashi yayi. Momma ta gyara zama sosai.

"Wallahi na rasa ta cewa ma. Yanzun ita safiyyar ta kyauta mana kenan? Babu neman da bamuyi mata ba......."

Da sauri haneef yace.

"Banga laifinta ba Momma. Tasan ko gabaki dayanmu irin halin fu.ad ne damu?

Bama wannan ba. Duk mai sauki ne yanzun. Ita yarinyar......."

Katse shi tai da fadin.

"In dai yar fu.ad ce kaman yanda kace tana bukatar dangin babanta. Tana kuma bukatar babanta.

Oh Allah!"

A sanyaye yace.

"Tana bukatar babanta ne fiye damu. Inhar zai sauke son kanshi ya dawo. Saboda bata da lafiya. Bata da wani lokaci mai tsaho......."

Da wani sabon tashin hankali momma ke kallonshi. Yar murnar da zuciyarta ta fara yi tana birbishewa.

"Tana da cancer. Fu.ad ne karshen hope dinsu akan rayuwar yarinyar...."

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un. Wai meke faruwa ne a rayuwar fu.ad? Wannan yaro Allah kadai yasan abinda ya boye kan kaddarar shi"

Sauke numfashi haneef yayi.

"Wallahi dakyar nai bacci jiya. Idan kika ga yarinyar..... Kika ga safiyya din........"

Kasa karasawa yai saboda yanda zuciyarshi ke karyewa da tunanin yanayin damuwar dake cike idanuwan safiyya.

Da kuma yanda tunda yake a rayuwarshi bai taba ganin yarinya mai dauriyar Nana ba. Kalar kaunar daya gani tsakaninta da safiyya bai taba ganin irinta ba.

Cikin wata nisantacciyar murya momma tace.

"Yau zan magana da abbanku. Zan maganar da yai shekaru sha daya yana kaucema dashi.

Zan kiraka anjima koya mukai dashi. Ka tashi ka tafi aiki"

Mikewa yai. Dan so yake yadan fita ko iska yasha yaji saukin abinda ke zuciyarshi.

"Sai na dawo"

"Allah ya bada sa.a....."

Har yakai kofa ta kira sunanshi ya juya.

"Ka kira kaninka"

Runtsa mata idanuwa kawai yayi ya bude su ya juya ya fice.

****

Kwance yake kan kujera tana zaune kasa dai dai kanshi suna kallon wani film a tablet din nawaf din 'wrong turn'.

A tsorace take saboda horror film ne. A hankali nawaf ya lallaba hannu ya ja mata kunne. Kara ta saki tana neman yar mishi da tablet.

Dariya yake sosai.

"Nur tsoranki yayi yawa wallahi."

Hararshi tayi a wasance. Hannunshi ya dora kan kafadarta yana dariya. Rikota yai yana doro kanshi gefen nata.

"Ina sonki sosai. Ki rike wannan ko da wata rana bana nan. Ki yafemun......"

Da sauri ta gyara zamanta ta fuskance shi. Kanta ta dora a jikin kujerar gaf da fuskarshi.

"Wacce irin magana kake yi haka?"

Lumshe idanuwanshi yayi.

"Kawai inajin wani irin ne Nur. Inajin kaman bazan jima ba......"

Da sauri tasa hannu ta rufe bakinshi dan har idanuwanta sun kawo hawaye taf. Babu inda zashi yabarta. Zata iya tuna lokacin data fara sanin wani abu dadin rayuwa.

*

Bazata manta ranar farko data fara haduwa da farhan ba. Ranar da yunwa ta isheta. Tun safe take jin yunwa amman Anty kaman yanda take kiran mahaifiyarta ta hanata abinci.

Asalima catai sai taje unguwa da wani mutum da bata san shi ba tukunna. Itakuma tace ba zata je ba.

Akwai wani lokaci da anty tace tabi wani unguwa. Sukaje tun cikin motarshi ya dinga tabata. Taita zunduma ihu. Dole a hanya ya sauketa.

Hakan yasha faruwa. Tun anty na jibgarta kaman jaka harta hakura ta kyaleta. Reza gareta koyaushe a jikinta bata rabo da ita. Ko kusa.

Tunda ta illata mutum hudu suke shakkar tabata ko yaya. To yanzun saidai anty ta hanata abinci. Cewarta ba zata zauna tana ci da ita a banza bata morarta da komai ba.

Ga makaranta tana son komawa tun da sukai jarabawar gama primary kawayenta duk sun ci gaba anty tace ba zata biya mata ba tunda ta rainata.

Tsaye take kofar gida tanata kuka. Shikuma yazo wucewa yake tambayarta komenene. Yanayin shi lokaci daya taji ta yarda dashi.

Kukan da take kaman ranta zai fita yasa shi riketa jikinshi yana lallashinta. A tsayin shekarunta tara a duniya farhan ne mutum na farko daya taba nuna mata irin wannan kulawar.

Ranar farko ta juye masa matsalarta tas. Tun a ranar ya tambayeta ko tasan inda ake siyar da abinci a unguwar ta daga mishi kai.

Dubi uku ya bata yace ta boye ta dinga siyen abinci. Haka kuwa akai yai tafiyarshi.

Ba afi sati biyu ba batasan ya akaiba ya sake dawowa. A haka rayuwar ta ci gaba da tafiyar musu. Har wata irin shakuwa ta shiga tsakaninsu da farhan din.

Randa ya kamata ya mayar da ita makaranta anty ta fito zatai masa karnukanci suka dibi yan kallo. Farhan yace zai kwaso mata yan sanda ya tona mata asiri.

Dolenta ta kyale shi. Haka farhan ya zamarma Nuri wani haske cikin duhun dake rayuwarta.

Bata taba sanin akwai wata rayuwa mai nutsuwa ba sai da ta hadu da farhan.

*

Hannun nawaf ta kamo ta dumtse cikin nata.

"Bana son kana mun irin wannan maganar sam. Bana so"

Mikewa zaune yai. Sumbatarta yai a goshi ya mike.

"zafi nake ji barin dan watsa ruwa....."

Binshi tai da kallo saboda akwai Ac a dakin ga fanka amman yace zafi yake ji. Sauke numfashi tayi harya shige bedroom din yabarta nan falon zaune.

Sallama taji. Da fara.a ta amsa. Makociyarsu ce Maimunatu. Tace ta shigo ta zauna sai dai a tsorace take.

Saboda tasan yanda nawaf ya tsani maimunatu. Saboda wata rana daya kamata tana fadama Nur din cewar ya akai ta auri nawaf.

Ai ta san yan gidansu tun tuni. Mahaukaci ne dan shaye shaye. Kaca kaca yai mata ya koreta. Yanzun ma batasan wanne tsautsayi ya shigo da ita ba.

Suna gama gaisawa sun zauna jim. Kawai nawaf ya fito. Maimunatu ya kalla dake zaune yana jin wannan duhun dake rufe mishi kai ya bayyana.

Karasowa yai yaja hannun Nur yai bedroom da ita. Dan bazai manta warning din dayai mata kan maimunatu ba.

Wani irin mari ya dauke ta dashi.

"Jakar ina ce ke? Bance miki bana son kara ganin waccen matar a gidana ba???"

Azabar marin da takeji baikai ta zuciyarta ba. Ga wani tsoro daya rufe ta.

"Dan girman Allah nawaf kayi hakuri wallahi..........."

Wani marin ya sake wanketa dashi da sai da taga wani haske ya gilma mata. Kunnenta yadan daina jin iska sosai.

Wani mugun kallo ya watsa mata yace.

"Just two minute na baki ki fita ki sallameta ki dawo ina jiranki......."

Da gudu Nuri ta fice daga dakin. Tsayawa tadanyi ta goge fuskarta sannan ta karasa. A dake tace ma maimunatu.

"Ki tafi dan Allah. Ki tafi karki jamun matsala......."

Bata jira amsarta ba ta juya abinta. Inda ta bar nawaf ta same shi a tsaye. Idanuwan nan sun sake launi.

Gefe takai kallonta. Wani gwangwani ne a ajiye sannan ta dawo da hankalinta kan nawaf a tsorace tace.

"Nawaf me kasha?"

Wani shakar iska yayi.

"Bana son yawan tambaya. Ki kyaleni! Kaina ciwo yake mun!"

Ya fada a tsawace yana wani daddafe kanshi. Ja da baya Nuri tayi dan tasan ba cikin hankalinshi yake ba.

Allah kadai yasan abinda ya hadama cikinshi. Ficewa tai daga dakin kamun ya illatata.......!

****

Girgiza kai yake ya kasa dauke idanuwanshi daga kan Nana. Ta ya ya samu ya'? Ta ina? Neme neme ya shiga yi cikin akwati nan da suke binne a kanshi.

Possibilities yake nema na cewar Nana yarshi ce. Wata dariyar takaici safiyya tayi tana kallonshi. Tasan dole yai mamaki.

"Ka dauka zaka iya tsarama kanka rayuwa ne? Saboda kai kake da iko da ita ko?"

Bai damu da yanayin muryarta ba. Da tambayar da take masa da gayya. Ba ita bace a gabanshi. Yarinyar nan ita zuciyarshi keta dauka hotuna tana adanawa wajaje daban.

A hankali yana sassarfa ya taka har inda nana ke tsaye da manyan idanuwanta irin nashi tana kallonshi cike da wani irin abu cikinsu.

Kaman tana tsoron karasawo inda yake karya bace. Zai iya karantar shekarun datai tana jiran irin wannan ranar cikin idanuwanta.

Kallonta yake. Baisan lokacin daya tsugunna kan gwiwoyinshi ba. Hannunshi na rawa ya dagashi ya taba kuncin Nana yaji ko ta gaske ce.

Yaji ba rayuwa bace ke son yin wasa dashi kaman yanda ta saba. Ba wani rubutun kaddarar bane da yake tunanin kan dutse yake sai daga karshe gogewar shi ta zama tamkar akan ruwa.

Ba wani farantin cike da farin ciki bane kaddara keson miko mishi saiya saka hannuwa biyu ya karba ta fisge hadi da mishi gwalo ba.

Dumi yaji a hannunshi. Sosai ya dago dayan ya tallabi fuskar Nana. Yan hannuwanta ta sa akan nashi tana tabawa.

Muryarshi a dishe can kasan makoshi yace mata.

"Em real....."

Saboda yanda yaga tana tsoron taba shi. Yan yatsunshi ta kama cikin nata ta dumtse. Wata irin ajiyar zuciya ta saki.

Kamun ta saki yatsun nashi ta kai hannunta kan fuskarshi ta tallaba kaman yanda nashi yake a fuskarta.

Rankwafawa tai ta hada goshinta da nashi tana kallonshi cikin idanuwa. Fu.ad zai iya rantsewa bai taba sanin wata nutsuwa kamar wannan ba.

Zai iya rantsewa an halicci zuciyarshi ne kawai dan ta buga tazo dashi wannan lokacin ya tsinci kanshi da kaunar wannan yarinyar.

Zai iya rantsewa babu farin cikin dayakai na ka dora idanuwanka kan halittar data fita daga jikinka. Safiyya dake tsaye gefe ta rike baki.

Wasu hawaye ne suka zubo mata. Abinda take gudu kenan. Shine yake faruwa a gaban idanuwanta. Tana ganin yanda daga kallo daya fu.ad ya sace zuciyar Nana kaman yanda yaima tata.

Tana tsoron abinda ya faru da ita ya faru da Nana. Domin iya wahalar duniya a shekarunta tagansu. Bata son ta hada da ciwon zuciyar rashin kaunar fu.ad.

Dan tafi kowa shaida yanda radadi da rashinta suke. Tafi kowa sanin zafin abin. Ta kuma fi kowa sanin bashida zuciyar kaunar kowa banda kanshi.

Nana kuwa tasha tunanin me yasa za.ace itace zata mutu bayan ga tsofaffi nan. Da duk wani hankali nata tayi tunani ta kasa gane kalar zabe na mutuwa.

Tsoronta daya. Kar ta dauketa bata saka M a idonta ba koda sau dayane. Bata san dalilinshi na barin rayuwar mumynta ba. Bakuma ta damu ba.

Abu dayane a zuciyarta a yanzun. Kaunar M wadda ta linka ta da da ganinshi. Sai take jin duk abinda ta rasa ta samu yanzun.

Cikon kaunar da bata samu ba. Batasan lokacin da wata dariyar farin ciki ta kwace mata ba.

Fu.ad jiyai zuciyarshi ta bude tana maraba dajin sautin dariyar Nana. Baisan dalilin dariyarta ba amman ta saka shi farin ciki marar misaltuwa.

Shima baisan lokacin da dariya ta subuce masa ba. Sosai dariya suke su duka biyun kaman wanda suke cikin wani irin farin ciki.

Girgiza kai safiyya take saboda batasan me fu.ad yake nufi da wannan abin da yake yi ba. Zata iya komai akan Nana ciki harda kareta daga fu.ad in har zai zama barazana ga farin cikin yarinyar.

Duk da yanda zuciyarta ke mata wasi wasi da kokwanto da yawa bai hana yanayin su fu.ad saka zuciyarta wani matsewa ba.

Cikin kanta take fadin.

"Dan Allah karkimun haka. Karki budemun kofar da na dade da rufewa"

A hankali sautin dariyarsu yake ragewa. Su ci gaba da kallon juna. Hannu nana tasa ta kara tallabar fuskarshi har lokacin goshinta na hade da nashi.

Muryarta ta saukar dai dai kunnenshi.

"Na dauka bazan taba ganinka ba"

Wata irin iska yaji tana fita daga zuciyarshi. Kamun wani irin daci ya ziyarce ta. Janye goshin shi yai daga na nana ya maida kallonshi kan safiyya dake tsaye ta zuba musu idanuwa.

Sannan ya sake kallon Nana. Lokaci daya ya tuno randa rabon Nana ya gifta. Randa zai tafi da suka hada gado da safiyya babu kariya.

Wani irin duhu duhu yake ji na lillibe mishi zuciya da bacin rai. Shekaru goma sha daya ta boye mishi wannan abin.

Yasan bata san ganinshi. Ta tsane shi. Nana ya ke kallo sosai. Amman ta boye mishi Nana abune da bazai iya yafe mata ba.

Kula yai Nana na yamutsa fuska kamar wadda take cikin wani mawuyacin yanayi. Kallon fuskarta yake yana manta damuwar komai banda abinda ke sata yamutsa fuska haka.

"Are you okay?"

Ya bukata cikin taushin muryar da bai taba amfani dashi ga kowa ba sai ita.

Wani irin numfashi take shaqa da sauri sauri kamun jini ya fara biyo hancinta idanuwanta su fara wani kakkafewa.

Jiyai zuciyarshi na shirin tsayawa. Riketa yai dam a rikice ya kalli safiyya data karaso inda suke tsaye da gudu tana karbar nana daga hannunshi.

Data riga da ta suma tun kamun karasowar safiyya. Girgizata safiyya take tana kiran.

"Nana........"

Hannunta fu.ad ya riko yana kallon safiyya a rikice yanajin zuciyarshi na wani irin dokawa.

"Meya sameta?"

Shiru tai ta kyale shi tana dube dube. A tsawace yace.

"Damn it sofi magana nake miki. What the fuck is wrong with my daughter?"

Kallonshi take tana jin yanda yake kure managing hakurinta. Akan Nana zaice zai mata ihu? Ashe ma me yake damun yarshi.

A kufule tana kara jan Nana jikinta tace.

"Da gaske kake? Ka ji me kake fadi kuwa? Yar' kafa kace fu.ad? Anya baka sha wani abu ba?"

Dai dai shigowar Ansar. Ganinsu tsugunne yasa shi karasowa da sauri. Basu kula dashi ba suna watsama juna wani irin kallo dake nuna mintina kadan suka rage su farma juna.

Bai ko bi takansu ba ya janye Nana daga jikin safiyya yana sabarta akan kafadarta.

"Me kika tsaya yi haka safiyya. For goodness sake kin manta warning din Dr.Jana ne. Mtswwww.........."

Da gudu Ansar ya fice da Nana. Safiyya ta dauki mayafinta zata bi bayanshi taji an riko mata riga an fizgota.

Kallon shi tai a fusace.

"Bana son neman rigima. Kabarni ya'ta tana bukatata......."

Mikewa tsaye yai hannuwanshi kan kugu ya na kallon safiyya cikin fuska. Har wani huci yake saboda bacin rai.

"Shekaru goma sha daya. Komin tsanar da kikaimun zaki iya fadamun ina da yarinya?"

Bata da lokacin yin wannan rigimar. Tana juyawa ya sake shan gabanta.

"Meke damunta da wancan mai katon kan ya sani ni ban sani ba?"

Hade hannyenta tai waje daya muryarta na rawa. Idanuwanta cike da hawaye tace.

"Please and please ba yanzun ba......"

Da gudu ta fice daga dakin yabi bayanta. Ansar ya riga yai tafiyarshi. Bude motarta tayi ta shiga. Fu.ad ya bude gefe ya shiga.

Bata da lokacin tsayawa masifar shi dan tasan ita yake ji. Dukan sitiyarin motar tayi ta bude ta fice da gudu ta koma cikin gida tana dauko mukullin motar.

Ta dawo ta tasheta taja ta fita daga gidan. Can kasan makoshi batare daya kalleta ba yace.

"A karo na ukku zan sake tambayarki meke damun yarinyata? And bana son yanda wancan ya dauketa kaman yanda iko akanta"

Hankalinta nakan titi tace.

"Mintinanka nawa da bayyana cikin rayuwarmu da har kake tunanin kana da wani muhimmanci a ciki? Ko kaga alamar na damu da abinda yai maka da wanda bai maka ba?"

A fusace ya kalleta. Gaba daya ta canza.

"sofi kar kice zakimun rashin kunya. Bance mun gama maganar nan ba......"

Shiru tai ta kyale shi. Batai parking ko ina ba sai bakin asibitin. Bata jira fu.ad ba ta fice abinta. Binta yai shima.

Ansar suka samu a waiting area yana tsaye yana ta kai kawo. Yace ma sofi.

"Dr.Jana ta tafi gida. But Dr.james ke dubata. Basu cemun komai ba tukunna"

Kallon su fu.ad yake. Yanda Ansar keyi zaka rantse shine baban Nana. Wani irin karyewa yaji zuciyarshi nayi. Shi ya kamata ace yana abinda yake ba wannan mai katon kan ba.

Duk laifin safiyya ne. Ya dauka kara tabbatar da ta tsane shi zai masa ciwo sosai. Sai yaji baiji ciwon shi kaman yanda yake jin ciwon maye gurbinshi da wannan yayi ba.

Safiyya ta cuce shi data boye mishi Nana. A hankali ya taka inda suke tsaye suna magana ita da Ansar. Tsakiyarsu ya shiga ya fuskanci Ansar.

"Excuse me. In ba zata iya fada maka ba ni zan fada maka. Mungode sosai da karamcinka da kawo Nana asibiti.

Family time yanzun. Ko zaka dan bamu waje"

Kallon shi Ansar yake. Daga yanda yaji labarinshi baiyi mamakin maganganunshi ba. Badon shi yake tsaye anan ba. Ba kuma dan safiyya ba.

Kaunar dayake ma Nana Allah ne kadai yasani domin shi ya halitta mishi ita. Murmushi yaima fu.ad yadan dafa kafardarshi sannan ya kalli safiyya yace.

"Barin siyo wannan allurar in dawo...."

Kasa cewa dashi komai tayi harya wuce. Wani kallo ta watsa ma fu.ad hadi da fadin.

"Fadanka dani ce babu ruwan Ansar a ciki"

Tabe baki yayi. Dr. james jana ta hango da sauri ta karasa wajenshi. Fu.ad na binta. Kallon safiyya yayi yace.

"Na ba dad dinta ya kawo wata allura. She is stable yanzun. Zamu riketa anan gaskiya"

Da sauri fu.ad yace.

"He is noh' her dad. I am...."

Da mamaki Dr. James ke kallon fu.ad. Kamun yace wani abu safiyya ta harare shi tace ma doctor din.

"Karka damu dashi. Zan iya shiga in ganta?"

Kai ya daga mata yace.

"Eh amman banda hayaniya"

"Nagode sosai....."

wuce yai yana fadin.

"Call me in an kawo allurar"

Dakin da aka saba ajiye Nana safiyya ta nufa. Juyowa tayi taga fu.ad na biye da ita. Tsayawa tai ta lumshe idanuwanta ta ware su akanshi.

"Bata bukatar kowa a kusa da ita sai family dinta......."

Hannu fu.ad ya daga mata dan in taci gaba da magana zai iya kwada mata mari. Zagin da take masa ya ishe shi haka.

"Wallahi a shirye nake da in birkita asibitin nan da duk wanda yake son gayamun bazan iya ganin ya'ta ba.

Kaman yanda nake a shirye mu hau sama mu fado ni dake akan boyemun ita da kikayi.......

Ki wuce muje kamun inyi abinda zamuyi dana sani sofi."

Wani miyau ta hadiye. Tasan zai iya yin fiye da abinda ya fada. A hankali ta tura dakin. Nana na kwance kan gado jikinta jone da Na.urori.

Da alamun bacci take. Yanzun da idanuwanta suke a rufe ramar datai ta sake fitowa sosai.

Tsaye fu.ad yayi bakin kofar yana kallonta. Kaman ba ita bace ta gama dariya mintinan da suka wuce. Wani irin abu zuciyarshi take mishi.

Baya sonta akan gadon nan. Baya son ganinta ko kadan. Yafison ganinta kaman yanda yaganta dazun. Kaman mai ciwon kafafu haka yake takawa harya karasa bakin gadonta.

Zuciyarshi na rawa sosai. Tsugunnawa yai. Ya kama dan yatsanta guda daya a hankali saboda karin ruwan dake jikin hannun.

Idanuwanshi dauke da wani yanayi mai nauyi ya kalli safiyya. Abinda tagani a fuskarshi bata taba ganin kalarshi ba a iya lokacin data sanshi.

"Please sofi........."

Lumshe idanuwanta tayi tana kokarin mayar da kukan da ke shirin kwace mata. Tun dazun take daure yanda ganinshi ya karya mata zuciya.

"Leukemia take dashi........"

Girgiza kai fu.ad yake yana so tace masa bata gaya mishi yarshi na dauke da cancer ba. Bata gaya mishi ya makara ba.

"Akwai chemo sofi..........."

Hawayen da take tarbewa ne suka zubo. Tasa hannu ta goge su kamun cikin raunin murya tace.

"Sau uku ana mata chemo therapy. Ta rokeni saboda ba zata iya daukar wani ba......"

Ta karsa maganar wasu hawayen na sake zubo mata. Mikewa yai ya fice daga dakin bai damu daya rufe kofar ba.

Tafiya kawai yake batare daya san inda yake saka kafarshi ba. Baya ganin komai a gabanshi sai ciwon dake shirin rabashi da yarinyar dako cikakkiyar awa daya baiyi ba da saninta.

Mutanen dake wucewa sai dai su su kauce masa dan baya ganinsu. Ansar ne yaganshi. Kafadarshi ya dafa yana fadin.

"Lafiya?........"

Baiko kalle shiba ya cire hannunshi daga kafadarshi ya wuce. Baya bukatar kowa. Baya bukatar kowa sai momma. Baya son gayama kowa damuwarshi sai lukman.

Baya son kowa ya gaya mishi yayi kuskure sai haneef. Baya son kowa ya lallashe shi sai momma.............!!!

*#TeamAS*

No comments:

Post a Comment