Thursday 4 May 2017

AKAN SO 31


*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

        31

*Godiya mai yawa ga duk wanda ya bata koda second daya ne ya kalli littafina. To the fans of Akan so. Kusani ana tare. I love you guys*

Fu.ad na nan yanda yake. Bazai taba canza halinshi ba. Ya dauka a shekarun nan ya karanci kuskuren shi.

Saima abinda ya karu. Son kanshi yana nan. Shekaru goma sha daya babu abinda ta canza fu.ad dashi.

Zee ce ta fito da cikinta daya turo. Murmushi yai mata a kasalance. Ta mayar masa da martani.

"Ki bimun yarinya a hankali zee"

Dariya tayi.

"waya ce maka yarinya ce?"

Ta karasa ta dafa cinyar lukman din kamun ta zauna gefen shi. Kanta ta kwantar kan kafadarshi.

"Inaji a jikina ne kawai. Kinsan zuciyata bata mun karya"

Daga mishi gira tai hadi da fadin.

"Ko?"

Sarai yasan me hakan ke nufi. Kan junior har kayan mata yaita kwasowa shi a dole jikinshi ya bashi mace za.a haifo sai gashi ta haifo namiji.

"Wannan karin fa da gaske nake"

Dariya kawai tayi. Tambayar da take son yi mishi na ci mata zuciya. Kamun tasan fu.ad nada wani muhimmanci a rayuwarshi ta dauka haka kawai yasama junior sunan dan yana burge shi.

Sai daga baya ta gane sunan fu.ad din ya mayarma junior. Kuma tun yana jariri baya kiranshi da fu.ad din.

Shi ya fara ce masa junior kamun kowa ma ya dauka. Inba makaranta ba babu mai kiranshi da fu.ad. Tana son jin labarin shi da fu.ad ko yaya ne.

Dan duk abinda ke da muhimmanci a rayuwarshi ta sani. Ya boye mata fu.ad ta rasa dalilinshi.

"Ina son tambayarka ne fa. Amman ina tsoron bata maka rai"

Kallonta yadanyi hadi da fadin.

"Kiyi tambayarki babu damuwa"

Sai da ta nisa sannan tace.

"Nasan ka roqeni kar na zurfafa tambaya. Kawai ina son sanin duk wani abu dake da muhimmanci ne a rayuwarka.

Waye fu.ad a wajenka?"

Wata ajiyar zuciya lukman yayi. Wayar da sukai da fu.ad din yan mintinan da suka wuce na kara yi mishi wani iri. Jin yai shiru yasa zee cewa.

"Kayi hakuri. Bansan ranka zai baci ba wallahi. In shaa Allah bazan sake tambayar komai a kanshi ba"

Kanshi ya jingina da nata dake kafadarshi cikin sanyin murya yace.

"Yau zaki san komai game dani da fu.ad zee.........

****


Kai kawo yake tayi cikin dakin tunda ya dawo aiki. Kira uku yaima nuri wayarta a kashe. Ita da tace mishi ba dadewa zatayi ba. Duk da yasan inda taje bai hana ranshi baci ba.

Wani abu yake ji na mishi yawo cikin kai. Yakan tsinci kanshi cikin wannan halin inhar Nuri tai mishi nisa.

Waje ya samu ya zauna yana running hannuwanshi cikin kai. Kallo daya zakai ma yanayin nawaf kasan yana da matsala ba karama ba.

Jin jirin mota yasa shi mikewa ya karasa jikin window din. Nuri ce gaban mota da wani wanda yake tunanin ya taba ganinshi amman ya rasa ko a ina.

Murmushin da yaga Nuri tamai yasa shi jin wani abu ya soki zuciyarshi. Yana kallo ta bude motar ta fito ta fadi ma matashin wani abu dabaisan ko meye ba.

Amman yaji yana son cire mishi hakoran can dayake ta bude ma Nuri. Kanshi zafi yake. Yana kallo yaja motar yai baya da ita.

Nuri kuma ta yo hanyar shigowa gidan. Da sallama ta turo kofar. Ganin nawaf tsaya yasata sakin mishi wani murmushi.

Fuskarshi a hade yake kallonta.

"Waye wancen Nuri?"

Batare da tunanin komai ba tace mishi.

"Mijin amal ne. Dazan kiraka kazo ka daukeni yace bara ya saukeni ma. Sannu da gida kaga na dade ko?......."

A tsawace yace.

"Shine kike bude mishi hakora? Dan yana mijin amal sai akace ya kawoki gida?

Cike da mamaki Nuri ke kallonshi.

"Nawaf? Karka cemun kishinka har da mijin amal"

Baisan lokacin daya dauketa da mari ba. Wani ihu ta saka tana matsawa da baya rike da fuskarta.

"Babu namijin daya ke da hurumin zama mota daya dake bandani. I don't care ko wanene shi"

Wasu hawaye taji sun zubo mata. Wai meke damun nawaf ne? Ta dauka shaye shaye ne kadai matsalarshi kuma ya daina.

Zata iya rantsewa abinda yake yanzun marar hankali ne kawai zai yishi. Muryarta na rawa tace mishi.

"Kayi hakuri. Bazan sake ba"

Lumshe idanuwa yai. Dana sanin marin dayai mata na ziyartar shi. Karasawa yai ya kamata ya rungume tsam a jikinshi.

"Bana son ganinki da kowa. Baki da kowa sai ni Nuri. Baki da inda zakije sai nan........"

Sake matse shi tai. Tasani. Basaiya tuna mata ba. Tasan bata da kowa sai shi. Bata da inda zataje sai gidanshi.

Bata da inda yafi nan din. Shine bargonta. Shine makangin da take dashi tsakaninta da zama da matar data fi tsana fiye da komai a duniya.

Matar da zata iya bada ranta in za.a canza kaddarar data zo da ita a matsayin yarta. Gara ko wacce wahala da koma ma rayuwa da ita.

Zata iya jure duk wani duka na nawaf indai hakan na nufin rashin komawa rayuwar da ta riga da taima bankwana........!

****

"Dady........."

khadee ta fadi tana rugawa da gudu ta rike kafafuwan haneef. Lumshe idanuwanshi yayi yanajin wani sauqi sauqi a zuciyarshi.

Tsugunnawa yai ya tallabi fuskar yar tashi yana kallonta. Ji yake kamar ya bude kirjinshi ya sakata ciki ya boyeta kar wani abu ya samar mishi ita.

Yau ganin Nana dajin matsalarta ba karamin daga mishi hankali yai ba. Tunanin wani abu ya rabashi da khadee kawai yasa yana jin numfashin shi na wani tsaitsayawa.

Riketa yai a jikinshi yana matseta gam. Fu.ad yayi kuskure. Duk da haushin yanda yabarsu da yake ji bai hana shi hango mishi kuskuren daya aikata ba.

Bai hanashi tausaya ma halin dazai shiga da wannan jarabtar da Allah ya dora masa ba.

A haka ummie ta shigo ta same su tana rike da Alhaji dayake da sunan mahaifinsu haneef din wato Muhammad.

Daukar khadee yai ya karasa inda take tsaye ya hadasu su duka ya rungume yana godema Allah da ni.imar dayai masa ta kyautar iyali masu cikakkiyar lafiya.

Cikin kunnenshi ummie ke cewa.

"Lafiya?"

Dan bata taba ganinshi haka ba. Sumbatar goshinta yai. Sannan ya sumbaci Alhaji dake ta babbaka dariya abinshi. Ya sumbaci khadee ma yana kara rike su jikinshi sosai.

"Ina kaunarku da yawa ummie. Ina sonku. Allah ya kara muku lafiya"

A hankali ta amsa da.

"Amin...."

Tana kara rike shi dan ko bai fada mata ba tasan akwai abinda ke damunshi. Saidai yana da zurfin ciki.

Ko ita bako yaushe take jin damuwarshi ba. Saidai yanayin kaunarshi dabanne a wajen su.

*

Ko da dare fur haneef yace dasu khadee zasu kwana karta kai mishi yara ko ina. Batai musu ba ta kwantar dasu tsakiyarsu.

Hannu yasa kansu khadee kaman wani zau kwace su. Kallonshi take da mamakin shi yau.

"Habeebi ba zaka fadamun damuwarka ba ko?"

Cikin sanyin murya yace.

"Kawai ina bukatar yarana a kusa dani ne ummie. Ko nayi laifi?"

Hannu takai ta shafi sumar kanshi da murmushi hadi da fadin.

"Bakai komai ba. In ba zaka iya fadamun damuwarka ba karkai kokarin nunamun babu ita.

Saboda zan iya karantarka a duk yanayi habeebi"

Murmushin ya mayar mata yana sauke numfashi.

"zan fada miki. Kimun hakurin zuwa safiya. Yanzun ina bukatar jinkune a kusa dani kawai"

Kai ta jinjina mishi.

"Allah ya kaimu goben lafiya."

Ya amsa da.

"Amin. I love you"

Murmushi tai mishi yanda baya gajiya da fada mata yana sonta na mata dadi kamun tai musu addu.a gabaki daya.

Hannunta riqe cikin nashi yaransu a tsakiyarsu bacci ya dauke su cike da kaunar juna.

****

Tunda ta dawo aiki gaba daya batajin dadi. Nana itace marar lafiya ta farko data bari ta shiga zuciyarta har haka.

Har ranta fata take a samu match Allah ya taimaka a ceci rayuwar yarinyar. Bata samu jabir a gida ba sai yaran kawai sun dawo daga makaranta.

Yasir da Umar sunata assignment dinsu. Ikram na kwance cikin kujera tana danne danne da tablet dinta. Umar kadai yai mata oyoyo.

Ta rike shi jikinta. Tayi kewar yaran nata sosai. Yasir ma sannu da zuwa yai mata ta amsa tana zama. Sai lokacin ikram ta dago.

"Sannu da zuwa"

Kallonta tai. Fuskar nan a murtuke. Miskilanci da rikici tsaf na jabir babu wanda ikram ta bari.

"Yawwa ya jikinki?"

"am okay"

Ta amsa a taqaice tana mikewa. Falon tabar musu. Jana ta girgiza kai kawai. Yau ko jabir dinma yazo da rikicin shi bata da karfin jurewa.

Nan tabar su yasir din ta wuce dakinsu. Wanka tadanyi dan gaba daya a gajiye take tayo alwalar magrib.

Tana nan zaune inda tai sallah jabir ya shigo da sallama. Ta amsa tana mishi sannu da zuwa. Gefen gado ya zauna yana kallonta.

Baisan ta inda zai fara ba. Har zuciyarshi abinda yake ji akan jana bai canza ba. Inma bazai karya ba sonta karuwa yake a zuciyarshi.

Kaman yanda son ayna yake daban. Kowanne wajen shi daban. Dafe kanshi yai cikin hannayenshi. Kallonshi jana tayi.

Mikewa tai ta cire hijab dinta ta karasa gefenshi ta zauna. Kafadarshi ta dafa. Hakan yasa shi dagowa ya sauke idanuwanshi kan fuskarta.

"Menene? Gajiya?"

Ta jero mishi tambayoyin lokaci daya. Kai ya girgiza mata. Hannuwa tasa ta tallabi fuskarshi tai kissing kumatunshi gefe da gefe.

"To menene? Bana son ganinka cikin damuwa kasani ko?"

Hannuwanta ya kama ya sauke daga fuskarshi. Bashi yake bukatar lallashi ba itace. Yanda yake kallonta yasata sanin akwai matsala.

A sanyaye tace.

"Honey J kodai kan aikina ne?"

Hannunta ya riko.

"Idan nace eh zai canza ra.ayinki?"

Ya tambaya. Kai ta girgiza mishi dan ba zatayi karya ba. Babu abinda zai canza ra.ayinta kan aikinta.

Tana son mijinta sosai. Kaman yanda yake bangare na rayuwarta hakama aikinta.

A nutse yace.

"Good. Kaman yanda na daina ma kaina karyan cewar rashin samun kulawarki ne yasani jin abinda nake ji..........."

Zuciyarta taji tana dokawa a tsorace. Hannunta ya riko a hankali ya dora kan kirjinshi dai dai inda zuciyarshi take sannan cikin idanuwa ya kalleta yace.

"Kar ki dauka abinda zan fada yanzun ya canza wajen zamanki anan.

Karki dauka sonki zai taba girgiza a zuciyata. Kar abinda zan fada yai sanadin taba zaman lafiyarmu"

A tsorace tace.

"Honey J.........."

Da sauri ya katse ta da fadin.

"Ki barni in karasa please. Ina sonki. Ina sonki sosai babu abinda zai canza haka.

Kinmun halaccin da babu macen da zata taba yimun shi Jana. Bazan manta ba kuma.

Banda iko da zuciyata daban bari tai miki abinda tai miki ba. Ina son wata jana..........!!!"

Wani shiru taji cikin kanta kaman wani ya doka mata guduma a ciki. Lokaci daya taji wani irin kishi da bata taba tunanin tana dashi ba.

Da sauri ta soma jero duk wata addu.a da tazo mata. Sama sama taji jabir ya sake rike hannunta gam cikin nashi yace.

"Ban fada mata ba. Nace zan fara fada miki tukunna..."

Yanda yai maganar cikin rashin makama yasata sake jin wani abu a zuciyarta. Saikace fara fada mata yana son wata bayan ita zai rage mata kishin shi.

Hawayen dake son zubo mata take kokarin controlling. A hankali ta kalle shi. Saida ta hadiye miyau yafi sau biyar kamun ta iya cewa.

"Wacece? A ina take? Yaushe ka fara sonta?"

Kallon fuskarta yake. Ya kasa karantar komai akai. Ya kasa ganin ko ranta ya baci ko bai baci ba.

"Ayna.u mardiyya sunanta. Wajen aikin mu daya. Bansan ko tun yaushe ba jana.

Farko na dauka ko dan bakya zama sosai yasani son wata. Shisa naso kibar aiki ko zan daina ji ban........."

Riko hannunshi tai. Ta sumbata a hankali daya sashi yin shiru. Muryarta na rawa tace mishi.

"Ya isa honey J. Zuciyarka badon ni kadai akayi ta ba. Baka da laifi a cikin son wata.

Ka fada mata. Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Zan roqeka yanzun ko da bazan iya ba nan gaba.

Bazan iya hanaka aure ba. Bazan iya hanaka abinda Allah ya halatta ba. Ina rokonka karka wulakanta ni dan kayi wata....."

Bude baki yai zai magana. Tasa hannunta kan labbanshi tana girgiza mishi kai kamun ta ci gaba da cewa.

"Karka mun alkawari. Bana son alkawari ko daya. Saboda bana son ka dora zuciyata kan abinda zaka zo ka kasa inji kaman kaci amanata.

Allah ya baka ikon yin adalci. I need to be alone please......"

Hannuwanta ya rike ya matse gam yana jinjina ma kokarinta. Wata kima da girmanta na sake cika mishi zuciya.

Daga abokai yasha jin labarin tashin hankali da hauka da matansu keyi in suka zo da maganar kishiya. Yanda jana tai mishi ba karamin daraja ya kara mata ba.

Duk da barinta ita kadai a yanzun shine karshen abinda yake sonyi bai hana shi mikewa ba. Wani light kiss ya manna mata a labbanta data kasa mayar mishi da martani.

Fita yai daga dakin. Tana jin yaja mata kofar ta ja jikinta kan gadon ta dunqule ta saki wani irin kuka marar sauti.

Wani radadi take ji cikin zuciyarta da wanda ya taba shiga cikin irin halin data shigane kawai zai fahimta.

Wanda yasan ya raba soyayyar miji take. Ya tunanin zama da wata yake. Ya raba farin cikin jabir yake. Kuka take sosai.

Ji take kaman taita kurma ihu. A iya zamansu da jabir bata taba hango raba soyayyarshi ba. Ko da wasa bata taba hango kalar wannan ranar ba.

Tasan shi na mace ne har hudu. Sai dai hakan bai rage mata jin abinda take ji ba. Dan dazun ji take kaman ta shaqe shi dayake gaya mata yana son wata.

Ganin datai shedan na shirin saka mata hannu a zuciya yasata mikewa dakyar ta shiga bandaki tayo alwala. Sallar isha.i ta idar.

Wani sabon kukan ta tisa. A hankali takai hannu ta dauko Qur.an din dake ajiye kan drawer din gado. Ta bude.

Tana karantawa tana kuka har wata nutsuwa ta fara saukar mata. A hankali take jin zafin da zuciyarta keyi na hucewa. Sosai tai addu.o.i sannan taja jiki ta koma kan gadon ta kwanta.

Ko yaran kasa fita tayi tai musu saida safe kaman yanda ta saba indai tana gida. Tana nan kwance sai juye juye take taji jabir ya shigo.

Kwan dakin ya kashe. Tana jinshi ya hawo kan gadon. Rikota yai ta bata cikin kunnenta ya shiga rada mata kalaman da sirrinsu ne.

A hankali take jin wani sonshi na kara shigarta. Cikin sanyin murya tace.

"Ya kamata ikram ta sani"

Saida ya sumbaci gefen fuskarta sannan yace.

"Zan fada mata da kaina. Ba yanzun ba. Sai ayna ta karbe ni....."

Da sauri ta juyo ta cije mishi labba. Janye fuskarshi yai yasa hannu yana shafa wajen. Muryarta a dakushe tace.

"Karka sake kiramin sunanta cikin dakin baccinmu. Balle kuma kan gadona. Jikinka hade da nawa honey j.

Suna ne kawai ya kamaci labbanka"

Dariya yai sosai yana hade goshin shi da nata. Tai kokarin tureshi ya riketa gam.

"Gabana harya fadi. Na dauka kin daina sona shi ya hana miki kishina"

Mintsinar mishi hannu tayi. Ya birkitata yana riketa sosai. A hankali ya shiga nuna mata yanda kowacece ta shigo rayuwarshi soyayyarta bata da fargaba.

Da salonshi ya shiga tabbatar mata da har abada akwai inda takai a zuciyarshi da ya girmi hangen ayna.........!

****

Tun cikin taxi abinda ke manne a kirjinshi madadin zuciya ya ke wani numfasawa har suka karasa.

Bakin gidan mai taxi din ya sauke shi. Ya dauko kudinshi yabashi dan saida ya biya wafa dashi yai canzin kudin dake jikinshi.

Hotel ma credit card ya biyasu dashi. Lumshe idanuwanshi yayi ya na jan wata iska data shiga har cikin kirjinshi.

"Sofi......."

Ya furta a hankali. Karo na farko a shekaru sha daya da bakinshi ya bude da sunanta. Sai dai in ya gifta mishi a tunaninshi.

Wani irin zafi yaji a kirjinshi. Yakai hannu wajen ya bude idanuwanshi yana wani yamutsa fuska. Da wani irin nauyin kafa ya taka ya karasa kofar gidan.

Kallon gidan yake. Yana tuna ranar farko daya fara zuwa gidan shi da haneef. Sake yamutsa fuska yayi.

Haneef din daya watsar dashi. Haneef daya yanke alaqa dashi kaman yanda abbah yayi kawai saboda ya nemi tsara rayuwarshi babu shawararsu.

Ji yai ranshi ya wani baci. Baisan wanne hauka yasa ya biyewa lukman ba. Yazo nigeria. Yanzun kuma ya taho nan.

Hannu ya daga zai kwankwasa kofar gate din.

"Na tsane ka.......!"

Yaji muryar sofi cikin kanshi. Kwankwasa kofar yayi yana sake jin maganarta radam cikin kanshi kaman tana gabanshi.

"Bana son ganinka wallahi. Bana son sake ganinka"

Lumshe idanuwanshi yayi. Kirjinshi zafi yake masa sosai sosai. Wani numfashi yake fitarwa da sauri da sauri ko zai ji saukin abinda yake ji.

Bude kofar da maigadin yayi ne ya dan taimaka mishi. Ware idanuwanshi yai kan fuskar maigadin.

Kallon fu.ad yake. Ganin kamannin da sukai sosai da nana ya sashi bude mishi kofar hadi da fadin.

"Alhaji sannu da zuwa."

Ko kallonshi fu.ad baiba ya shiga cikin gida. Wani abu yaji ya kulle a kasan cikin shi. Yai kuskure babba.

Son famo ciwukanshi ne su dawo danyu suna zubda jini yasa shi biyewa lukman. Sai dai ya rigada yazo. Babu komawa baya kuma.

Dakyar kafafuwanshi suke motsi suna taka mishi. Komai na rayuwarshi a gidan ke ta masa yawo cikin kai.

Dakyar ya karasa kofar gidan. Tsayawa yai ya rufe idanuwanshi yana kokawa da abinda yai saura a zuciyarshi.

kwankwasawa yai. Yana jin koma meye a kirjinshi na dokawa da karfin gaske.

*

Dakyar ta iya mikewa daga kan kujerar ta nufi kofa. Tun tafiyar haneef tasha kukanta ta more. Sai take jin jikinta duk babu karfi.

Bata tambayi ko waye ba. Kawai bude kofar tayi. Cik zuciyarta ta tsaya. Idanuwanta suka kafe a kanshi.

Ya kara girma. Jikinshi sanye da normal jeans blue. Sai tshirt ja data kama shi. Banda girma sosai daya kara.

Sai sajen dake kwance a fuskarshi da gashinshi daya rage ma yawa. Tsaye zuciyarta tayi. Tana shirin manta yanda ake shakar numfashi.

Idanuwanshi yawo suke a fuskarta. Baiga ta canza da komai ba. A hankali yake jin abinda ke kirjinshi na budewa.

Yai tunanin bashida sauran zuciya ashe a boye take cikin abinda yake tunanin ya maye gurbinta a kirjinshi.

A hankali take budewa. Sofinshi ce. Ta kara kyau fiye da yanda yabarta. Muryarshi dauke da wani irin yanayi yace.

"Sofi........"

Sai lokacin taji zuciyarta ta numfasa cike da wani abu daya girmi tsanarshi. Kallonshi take tana kokawa da iskar data ke son shaqa saboda yanda ta dauki mintina wajen biyu bata shaqeta ba.

Kofar data ke rike da ita taja tana son kulleta yasa hannu ya rike kofar yana kallonta.

"Kofar gidan nawa zaki kulle a fuskata sofi?"

Wani abu taji ya tokare mata wuya. Ji tai kaman ta kwada mishi mari. Nana ce kawai dalilin daya sa ba zata kira maigadi ya dauke shi ya fitar mata dashi ba.

"Daga randa ka sa kafarka kabar gidan nan kai loosing right din ka na kiranshi naka"

Wani murmushin takaici fu.ad yayi. Ashe shi yai shekara goma sha daya yana kokawa da murmushi duk sanda tunaninta ya fado mishi.

Tana nan ta kara kyau abinta. Baya ranta. Tsanarshin data fadi da gaske ne tana jinta. Cike da takaici yace.

"Ko sofi?"

Bata son sunan nan yanzun. Bata son yanda sunan yake kaiwa zuciyarta yana wani matse mata ita.

"Karka sake kirana da wannan sunan. Sunana safiyya"

Kallonta yake da mamaki. Sofi ta koyi rashin kunya. Sosai shi take kallo cikin ido tana fadama magana babu tausasawa.

Ware idanuwanshi yai a kan fuskarta.

"Kin canza sosai"

Kallonshi kawai tayi. Tana ganin yanda yake nan da halinshi data kasa kallo acan baya.

Ji take daman baizo ba. Saboda bata son yanda Nana ta saka shi a ranta. Tasan kuma ba sonta zaiyi ba.

Babu son kowa a zuciyarshi sai nakanshi. Basu da waje a zuciyarshi. Daga ita har yarta.

Bude baki tai zatai mishi magana ta hango Ansar ya taho. Batasan lokacin da murmushi ya kwace mata ba.

Wani dan guntun murmushi fu.ad yaji ya bayyana a fuskarshi. Yaushe rabon dayaji shi haka har ranshi.

Ta wani kara kyau. Yana son murmushin nan a fuskarta. Ganin hankalinta na wani waje yasa fu.ad juyawa.

Wani abu yaji ya tokare mishi wuya. Waye wannan datake ma murmushi haka. Kallon kallo suke da Ansar da fu.ad din.

Hannu Ansar ya mikama fu.ad dakyar ya karba sukai musabaha. Kanshi tsaye ansar ya wuce zuwa cikin falon.

Safiyya tace mishi.

"Yanzun nake shirin kiranka. Najika shiru"

Da biyu take maganar. So take fu.ad yagane bashida wani muhimmanci a rayuwarta yanzun. Kuma yaji hakan.

In a shekarun nan yana tunanin yayi dana sanin tafiya. Abinda yakeji yanzun ya linka nada. Wani ne zaune a falonsu shida sofi.

Da ido Ansar ke kallon safiyya yana tambayarta. Duk da kamanin daya gani kawai ya tabbatar masa da wannan ne fu.ad din.

Yanayin shi kawai yasan zai aikata abinda safiyya ta bashi labari. Saboda akwai wani attitude tattare da fu.ad dako wanda bai sanshi ba zai karanta a kallo daya.

Sake kallon safiyya yai. Duk yanajin wani irin awkwardness ya baibaye dakin. Ita tana tsaye. Shi a zaune a falo. Fu.ad din kuma yana bakin kofa a tsaye ya kafe su da idanuwa.

Kai tadan girgiza mishi alamar yanzun fu.ad din yazo. Ansar ya bude baki zai magana maigadi ya rugo da gudu.

"Hajiya ga wasu mutane nan su da yawa bakin kofa. Wai sai sun shigo suna son ganin Nana"

Hada ido safiyya da ansar sukai. Kamun Ansar ya mike ya bi maigadin zuwa kofa. Karasawa tai ta dauki mayafinta dake kan kujera.

Tazo ta raba fu.ad dayake tsaye kaman an dasa shi ta wuce tabi su Ansar.

Yan jarida ne cike da kofar gidansu. Ta lumshe idanuwanta tana tunanin yanda akai suka gano gidansu.

Ansar ta kalla da idanuwanta da suke rokonshi da yasan yanda zaiyi da yan jaridar nan. Bata son su ganta a yanzun.

Duk da ta ma Nana alkawari. Ba haka ta shirya fu.ad yaji labarin Nana ba. Tazo ma babu matsala batai tunanin zai karbeta ba.

Ballantana yanzun kuma. Kaman yaji zancen shi take a zuciyarta ya karaso inda take. Saijin muryarshi tayi yace mata.

"Me yake faruwa? Me wannan suke yi anan?"

Lumshe idanuwanta tayi ta bude su hadi da fadin.

"Ba matsalarka bace ba"

Kamun yagama mamaki ta juya tayi cikin gida. Binta yayi da sauri yana fadin.

"sofi........"

Ko tsayawa batai ba balle yaima tunanin zata juyo. Yana ina shekaru sha daya da suka wuce. Sai yanzun zai tambayeta meke faruwa.

Bai tsaya ya tambayi mezai faru da ita ba kamun ya tafi. Ya manta tabar komai *Akan so* bana kowa ba nashi.

Badon Nana da zata iya komai *Akan so*nta ba bai isheta ko kallo ba ballanta har musayar magana. Baida wannan darajar a idanuwanta ko kadan.

Kofa ta tura ta shiga. Tana kokarin tarbe hawayen dake son zubo mata. Ta riga ta ma kanta alkawari tagama kuka akan fu.ad ba tun yanzun ba.

Tana shiga cikin gidan Nana na fitowa daga dakinta. Da alamun bacci a fuskarta tana murza ido.

Ganinta kawai yasa zuciyar sofi wani yawatawa da kaunar yar tata. Zata iya komai saboda ita. Koda kuwa daina numfashi ne indai zatai hakan da sanin cewar rayuwar Nana zata ci gaba.

A shirye take. Cikin abubuwan da zata iyayi harda jure ganin fu.ad da jin muryarshi duk da yanda suke yi mata kaman zuciyarta zata tarwatse saboda ciwo.

Kama Nana tayi tana kokarin janyeta ta mayar da ita daki. Bata son taga fu.ad saiya fara sanin da zamanta tukunna.

"Sofi......."

Taji ya kira. Wani yarr taji duk jikinta. Tsaye tai cak. Sannnan a hankali kaman mai ciwon wuya ta juya.

Nana dake jikinta ta fito ta tsaya tana kallon fu.ad. shi da yake tsaye idanuwanshi kafe kan safiyya sam bai kula da Nana ba.

Safiyya ta mayar da dubanta kan Nana tana ganin yanda ta ware idanuwanta tana kallon fu.ad. Inda yaga fuskar ta tabi da kallo ya sauke kanshi.

Yako yi Nasarar sauke idanuwanshi cikin na Nana. Lokaci daya yaji komai ya tsaya mishi. Kallonta yake da wani irin yanayi.

Kallonta yake saboda yana tunanin bai taba ganin halittar datai mishi kyau ba kamarta. Kallonta yake yana jin yanda komai na jikinshi ke narkewa da kaunarta.

Kallonta yake yana jinta kaman wani bangare na rayuwarshi. Kamun yaji zuciyarshi ta yamutse. Idanuwanta.

Akwai wani abu tattare da idanuwanta da yake son gane komeye.

Kaman wanda aka daka da karfe akai abin yazo mishi. Irin idanuwansu daya sak. Hancinsu da bakinsu iri dayane.

Ba saiya tsaya wahala ba. Wannan yarinyar tamkar an ciro shi ne an ajiye a jikinta. Jiyai ko ina na jikinshi na kyarma.

Wani murmushin takaici sofi tai hadi da fadin.

"Fu.ad ga Nana fa........."

Ya kasa janye idanuwanshi daga kan Nana duk da yaji abinda safiyya tace. Baya son dai kona second daya ya daina kallon fuskar yarinyar.

Nana safiyya ta kalla tace.

"Ga M."

A tsorace Nana ke kallonshi. Tana ganin kaman datai wani abu ba dai dai ba bacewa zaiyi. Tunda tai wayau take jin kaunarshi cike da zuciyarta.

Tunda tai wayon sanin menene mahaifi take jin son ganin shi koda sau dayane a rayuwarta. Wani murmushi ya kwace mata duk da hawayen da suka zubo mata.

"Kaine babana..........."

Bangon dake wajen fu.ad ya dafa saboda yanda yaji kafafunshi na rawa da maganar data fito daga bakin Nana.

"No way........!"

Ya furta yana girgiza kai.

No comments:

Post a Comment