Thursday 4 May 2017

AKAN SO 21

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

         21

Wayar shi ya dauka ya sake kiran lukman. Bai dauka ba. Jirin mota yaji. Hakan ya sa shi barin safiyya ya fito da sauri.

Parking lukman yayi. Ya bude ya fito. Ko kallon fu.ad baiba ya juya ya taka yana nufar gate.

"Lukman....."

Fu.ad ya kira. Ko juyowa baiba har ya fice. Numfashi ya sauke. Komai dayake bukata yana ciki.

Dauka yai ya shiga dasu ciki. A falo ya ajiye komai. Safiyya na kwance. Karasawa yai ya dan rage tsahonshi yace mata.

"Bara inyi sallah. Ko zuhr banyi ba kar laifin yai mana yawa"

Dakyar ta mike saboda yanda take jinta. Muryarta a dakushe tace masa.

"Nima sallah zanyi. Banyi ba"

Batai musu ba daya kama hannunta suka shiga daya daga bedrooms din. Toilet din ya nuna mata ya zauna gefe yana jiranta.

Duk da yanda take jinta bai hanata karema bandakin kallo ba. Sai dai bata ga ko cup ba balle buta. Har azo ga maganar inda bokitin ruwa yake.

Yana zaune yaji kaman tana jijjiga kofar. Mikewa yai ya murza handle din yadan tura kadan.

Kamawa tai ta bude. Idanuwanta ta sauke cikin nashi. Yanda yake kallonta yai mata wani iri. A dan daburce tace.

"Banga ruwa ba. Kuma ba buta"

Ga mamakinshi dariya yaji ta kubce masa. Harya manta when last yai dariya.

Daquna fuska safiyya tai. Dan bataga abinda dariya a maganarta ba. Sai dai duk abinda take ji.

Duk yanda fuskarsa ke dauke da raunukan da yaji shekaranjiya bai hana dariyar yi mishi kyau ba.

Tura kofar ya karasa yi ya budeta duka. Ya raba gefenta ya wuce ciki. Fanfo ya bude mata ya zo ya wuce.

Yana nan zaune ta fito. Har yakai bandakin tace masa.

"Ina ne gabas din?"

Dan ita inhar tabar gidan su bata gane gabas a ko ina sai an nuna mata.

Nuna mata yai sannan ya shiga. Sai da yai wanka tukunna. Sai lokacin ya tuna abinda yake bukata a gidan nada yawa.

Ko dan ba zama zai ba. Wannan alkawari ne dayai ma kanshi. Abinda bai taba ba yayi. Kayan daya cire ya mayar a jikinshi ya fito.

Safiyya na zaune inda tai sallah gefen gado. Da alama tai nisa cikin tunani dan ko karasawar shi bata ji ba.

Gefenta ya raba. Ya gabatar da sallar azahar. Sannan ya maida la.asar yana jin shi wani iri saboda hada sallar dayai lokaci daya.

Kuma duka biyun ba.akan lokaci ba. Sai daya gama addu.o.i da yima Allah godiya daya bashi safiyya duk kuwa da hanyar da hakan ya faru.

Magana yai bata ji ba. Dan haka yadan taba ta. A firgice ta juyo.

"Tunanin me kike haka?..."

Kai kawai ta girgiza masa. Ya dora da.

"Tashi muje asibiti. A dubamun ke. Sai muzo mu siya abinda muke bukata.

In shaa Allah zuwa jibi zamu barma abbah gidanshi"

Ita kam tagaji da laifuka haka. Bata son fushin iyayenshi ya tsananta a kanshi kaman ita. Hakan yasa ta ce masa.

"Kabari mu zauna anan din. Kar laifukan suyi mana yawa"

Kallonta yai sosai.

"Sofi bazan zauna a gidanshi ba yana fushi dani.

Nafison komai namu a yanzun. Nawa da naki. Mu kadai kaman yanda suka ware mu"

Bata san me zatace ba kuma. A sanyaye tace.

"Ba saimun je asibiti ba....."

Katse ta yai da.

"Karki karasa maganar nan. Asibiti zamu je. That is final"

Mikewa yai tsaye ya mika mata hannunshi alamar ta kama ya dagata.

Dan jim tai tana kallonshi. Kamun tayi abinda ya bukata. Suka fita tare. Asibiti ya kaita ya bude mata file.

Kasancewar private hospital ne basu samu wani layi ba can. Sosai aka duba safiyya. Doc ta ce masa stress ne yai mata yawa tana bukatar hutu sosai.

Hankalin safiyya bai tashi ba sai da taga fu.ad ya siyo magunguna ya kawo ma likitar data dubata.

Taga an bude an dauko allura ana gyarawa. Tunda take bata taba cutar data kaita asibiti bama. Sai dai ko in ta raka inna.

Balle azo ga allura. Sosai tsoronta take yi. Kallon fu.ad tai tana rau rau da idanuwa.

Shi kanshi ganin yanda duk ta tsorata ji yake kaman yace a fasa allurar. Sai dai yana son lafiyarta sosai.

Doc din ta kama safiyya suka shiga dan wani waje da aka kebe. Gaba daya a tsorace take.

*

Biyawa yai da ita ta wani karamun bakery ya siya musu milkshake,burger da shawarma dan wata irin yunwa ke cinshi.

Sanda suka karasa stop and shop ana kiran sallar magrib. Parking yai. Yabar safiyya a mota yaje yai sallah ya dawo.

Tai kwance abinta. Tasan bata san komai akan fu.ad ba. Asali ma wulakancin shi ne abu na farko da zata bada shaida akai.

Sai yanzun daga yanda ta karanta zata iya cewa yana kula da addinin shi sosai. Tana nan ya dawo yace mata.

"Fito mu siya kayan sawa"

Sai lokacin ta tuna bata da kowanne kaya sai na jikinta. Bata da sauran hawaye tasan da sun zubo.

Sai wani abu daya tsaya mata a wuya. Dakyar tace masa.

"Ka siyo ka dawo ina nan"

Girgiza kai yayi.

"Yazan gane sun miki?  Ki zo ki zaba da kanki"

Kaman zatai kuka tace.

"Ka siyo kowanne. Koma wanne iri ne zaimun"

Baya son a takura shi. Hakan yasa baya son ya takura wani.

"What is ya' size da height kuma?"

Kallonshi take dan bata gane abinda yace mata ba. Dan haka tace masa.

"Ban gane ba"

Yadan daki kanshi. Makaranta ya kara cikin jerin abinda suke bukata sannan yace.

"Tsayin ki. Da kuma size. Ni bansan yanda zance ba"

Kafada ta daga masa. Alamar itama bata sani ba. Numfashi yaja ya sauke shi a hankali. Bai ce mata komai ba.

Dogayen riguna ne ya kwaso mata. Kawai ya kiyasta tsayinta ne. Ya siya toiletries da mayuka sannan ya biya.

Ya dauko ya fito. Bayan mota ya bude ya zuba komai. Ya dawo yaja motar suka nufi gida.

*

Yana parking din mota. Ya kira mai aikin gidan yazo ya kwasar musu kayan zuwa ciki ya fito.

Sallar magrib safiyya ta shiga tayi tabar fu.ad din nan falo a zaune.

Wayarshi ya dauko dan sai lokacin ya tuna da wani friend dinsu isma.il da babanshi ke aiki a housing co-operation.

Magana sukai ta fahimta kan gidan da yake so ya siya. Ya turo masa hotunan wasu guda biyar da kudaden su.

Jin safiyya shiru ya sashi daukar kayan cin da suka siyo ya bita bedroom din. Tana zaune kan kafet. Jikinta na jingine da gado.

Ledar ya ajiye. Da murmushi a muryarshi yace.

"Ina ta jiranki. Shine kikai zamanki ko?"

A rauna ne tace.

"Bansan kana jirana ba."

Ledar ya bude ya fito mata da milkshake da burger.

"Kici ki sha magani"

Kai ta girgiza masa.

"zan dai sha maganin. Banajin yunwa"

Daure fuska yai sosai. Muryarshi babu wasa yace mata.

"A haka ne zamu ki komawa asibiti allura"

Da sauri ta dauki burger din. Milkshake din ya bude mata. Ta rike a hannu.

Wani kunyar cin abu a gabanshi take ji. Sai take jinta wani iri. Kanta a kasa tana jinshi yanata ci.

Kallonta yake baya son takurata. A hankali ta gutsiri burger din tai shiru. Taste din na mata wani iri dan ba sabawa tai ba.

Kadan tadan kara ta ajiye. Milkshake dinne ma tasha sosai. Ya ballo mata magungunanta. Ya bata ya bude mata ruwa suma ta sha.

"Zaki iya zama ke kadai inyo sallar isha.i in dawo?"

Karema dakin kallo tayi. Kaman tana so ta tabbatar babu abinda zai cutar da ita kamun ta daga masa kai.

Fita yai yaja mata kofar. Itama sallar isha.i tai. Ta zauna tana tunanin yanda a rana daya komai na rayuwar taya canza.

Tana nan fu.ad ya dawo. Gefenta ya zauna a kasa shima. Wayarshi ya zaro. Sai lokacin ya tuna yana bukatar sabuwar waya.

Dan screen din wannan duk ya farfashe. Zai bayar dashi sai ya cika ya dauki wani gobe.

Gidajen da isma.il ya tura masa ya budo. Ya mikama safiyya yana fadin.

"Zabar mana daya. Wanda zamu zauna ciki"

Hannu tasa ta karbi wayar. Ta zuba ma gidan ido. Yayi kyau sosai da alamu da bene. Sai dai wannan gidan ai yayi girma.

A ranta take tunanin oh Allah. Iyayenta nacan a wani hali tana nan tana kallon kawatattun gidan da zata zauna ciki.

Rashin kyautawar hakan ya lillibeta. Yanayinta fu.ad ya karanta. Wayar ya karba.

Ya ajiye gefe. Hannuwanta duka biyun da sai lokacin ya kula dauke suke da jan lallae dayai kyau sosai ya kama.

Kallonta yai.

"Ki yarda dani ko na dan lokacine sofi. Ni kadai bazan iya gyara komai ba.

Bance ki manta damuwar da kike ciki ba. Nasan ni ne silar komai.

Amman ki dubeni mana. Ya zanyi? Banida wani zabi ne. Ki bani dama zan gyara komai in shaa Allah"

Dazun take tunanin hawayen ta sun kare. Sai gasu suna zuba yanzun. Hannuwanta dake cikin nashi a dumtse ta kalla.

Sannan ta maida kallonta kan fuskarshi da idanuwanshi da suke cike da gaskiyar maganar daya fada mata.

A hankali tace.

"Ba laifinka bane kai kadai. Kowa zaifi duba nawa laifin akan naka kuma...."

Hannunta ya saki ya rufe bakinta yana fadin.

"Shhhhh. Nagaji da jin laifikanmu sofi. Why not muyi kokarin gyarasu?"

Kai ta daga masa jikinta na kara wani sanyi. Murmushi yai mata da ta kasa mayar masa.

"Ki tayani mu zabi gidan da zamu zauna a ciki"

Yace yana daukar wayar shi dake gefe ya mika mata. Turewa tai a hankali hadi da fadin.

"Ko ina ma. Kawai kar yai girma. Kar yakai wannan dan Allah"

Fito da idanuwa yai.

"Sofi daki ukunne fa nan din"

Kai ta daga masa.

"Yayi girma. Indai so kake in zaba. Karami ne zabina"

Lumshe idanuwa yai. Shi yace ta zaba. Dole yai hakuri da zabinta. Kai ya jinjina mata alamar yarda.

Mikewa yai ya fice falon. Riga daya ya dauko mata. Wata marar nauyi. Fara kal da ita hadi da toiletries yakai bandaki ya rataye mata rigar.

"Kiyi wanka. Ki sake kayan nan. Kizo mu kwanta"

Da sauri ta dago ta kalle shi. Kalmar mu kwanta daya ambata ta kulle mata ciki. Jikinta yai wani iri.

Badai ta musa mishi ba. Ta shiga bandakin. Ta sha wuya sosai. Ita kam babu wahala sai wankan fanfon nan.

Dayake na wajen alwala kawai taga ya bude dazun. Hakan yasa tai zaton shi kadai ne yake aiki.

Sai ta sa hannu ta tari ruwan sannan ya watsa tunda baya taruwa cikin abin. Ta jima sosai. Dakyar ta wanke kunfar dake jikinta.

Ga sanyi ruwan na dasu. Da yake shirins dawo mata da zazzabin da ya sauka.

Inners dinta ta mayar sannan ta saka rigar da fu.ad ya rataye mata. Loose ce. Sai dai ta mata tsayi. Dan kwalin atamfarta ta daura a kanta.

Ta fito. Duk da girman rigar bai hanata jin wani iri ba. Kallonta fu.ad yake.

Yanda fuskarta tai wani fayau. Ba kwalliyar nan. Yanda ya so yaganta. Tayi mishi kyau. Gabin duk ta takura yasa shi tashi.

"Kije ki kwanta. Karki manta da addu.a. Sai da safe."

Takawa yake zuwa kofa kafafunshi da nauyi sosai. Saboda yanda duk wani abu na jikinshi ke masa ihun ya tsaya.

Kallon shi take. Ina zai tafi yabarta anan. Bata san kowa ba. Wani tsoro na daban ya kamata. Murya na rawa tace.

"Dan Allah karka tafi...."

Wani abu yaji ya ratsa shi. Baya son ya tsorata tane. Shisa zai tafi wani dakin ya kwana daman.

Komawa yai. Hannunta ya kama. Ya jata kan gadon batai masa musu ba. Ta zauna.

"Ba inda zani. Kwanta to"

A tsorace dai take. Kwanciya tai. Ya gyara blanket din ya lillibeta"

Sai ta danji dadi kadan. Balle da taga fu.ad din ya zagaya gefenta ya zauna. Sai dai ya doro kafafunshi kan gadon.

Duk da tazarar daya bayar tsakaninsu bai hana komai nata jin kusancin shi ba. Wani irin kusanci daya bata mamaki.

Sai ta alaqanta shi da cewar wani namiji bai taba yin kusa da ita haka ba. Abin da take ji harda hakan da kuma karin daga ita sai shi a dakin.

Ga zuciyarta na wani irin dokawa. Shi kanshi fu.ad din tashi zuciyar dokawa take sosai. Saboda yanda yake son yaji ko da hannunta ne ya rike.

Dan ya tabbatar da dagaske babu inda zata. Da gaske ta zama tashin. Dole ya hakura.

Shiru ya bakunci dakin. Banda fitar numfashin su babu abinda kake ji. Sai kuma bugun zuciyoyinsu.

Safiyya ta kasa bacci. Ko motsin kirki bata son yi. Data rufe idanuwanta sai abinda ya faru ya dinga dawo mata.

Can wani bacci ya fara fizgarta tai wani irin hargitsattsen mafarki.

Tunani yake tayi na makarantar daya kamata safiyya tayi. Dan baya so kowa ya raina masa ita.

Wata gigitacciyar kara yaji ta saki. A rikice ya rikota tana ture shi. Dakyar ya samu ta tsaya.

Kuka take sosai. Ya rungumeta a kirjinshi yana lallashi.

"Sofi. It's okay. I promise......."

Ta jima a haka. A hankali ta zame jikinta daga na fu.ad din dan wani bakon abu da take ji.

Duk da tana bukatar lallashin da yake mata. Bai hanata ba. Ganin su duka sun kasa bacxi yasa shi fadin.

"Muyi hira. Kinga bansan komai naki ba.  Kibani labari. Nima in baki"

Shiru tai kaman ba zata ce komai ba tana tauna maganar shi. Kilan in sukai hakan ya dan dauke mata hankali daga abinda take ji.

A hankali yaji tace.

"Su waye haneef da lukman a wajenka"

Murmushi yai. Ya amsa mata. Tambayoyi take masa. Duk abinda yazo kanta. Can tace masa.

"Kana da sana.a?"

Dariya yai kadan. Sannan yace.

"Wasan kwallon kafa nake"

Da mamaki a fuskarta tace.

"Sana.a fa nace. Ina nufin me kake na samun kudi"

Dariya ya sake yi.

"Na jiki ai. Kwallon kafa shine sana.ata"

Shiru tai tana tauna maganarsa. Tana mamakin yanda kwallon kafa zata zama sana.ar mutum.

Hakan yaba fu.ad damar tambayarta.

"Kinyi makaranta?"

Tambayar ta mata bazata.

"Nayi makarantar boko zuwa aji uku kawai.

Nayi ilimin addini fiye dana boko. Amman zan iya karanta hausa in rubuta.

Ina gane larabci sosai. Duk da kadan zan iya mayarwa. Sai dai bana jin turanci"

Kai ya daga mata alamar ya fahimta. Da duk mintunan da suke wucewa da saukin yin magana dashi da safiyya ke ji.

Shiru yadanyi kamun yace.

"Kina so ki ci gaba da karatu?"

Da sauri tace.

"Ina so. Sosai ina son makaranta"

Murmushi yai mata hadi da fadin.

"Zan mayar dake makaranta"

Wani dadi taji. A rayuwarta tana son karatu. Hali na rashi ne yasa ta hakura da mafarkinta. Tare da fu.ad taga hango mafarkinta na kusantota.

Sai dai kuma tare dashi ta hango sauyi da dama na rayuwa. Idanuwanta cike da hawaye tace.

"Ina son karatu sosai. Amman nafison afuwar su inna akan shi.Kamun alkawari zaka daidai ta komai"

Kafadarta ya dafa ta saman blanket din da take rufe da shi.

"Na miki alkawari sofi. Kimun alkawari zaki rage damuwar nan. Zamu fuskanci komai mu biyu"

Kai ta daga masa tace.

"In shaa Allah. Nagode"

Murmushi yayi.

"Now ki rufe idonki. Kiyi addu.a. Dare yayi sosai"

Tsoron rufe idanuwanta take. Karta sake cin karo da wani mummunan mafarkin.

Hannunta ta fiddo. Ta kamo na fu.ad dake gefe ta rike dam. Sannan ta rufe idanuwanta tana jero addu.o.i.

Yana kallonta har bacci ya dauketa. Gyara kwanciya yai shima. Bacci ya dauke shi.

*

Da yake ya rigada ya saba da tashi sallar asuba. Abin harya zame mishi kamar agogo a zuciya. Lokaci nayi ya tashi.

Hannunshi yaji rike da abu mai dumi. Da sauri yakai kallon shi kan safiyya dake kwance.

Hamdala yayi saboda komai daya faru ba mafarki bane ba. Baya son tashin ta. Shi kanshi harya manta randa ya samu bacci irin wannan.

Babu mafarkin komai. Bacci mai dadi. A hankali ya zame hannunshi daga nata. Falo ya fita ya dauko jakar shi da lukman ya kawo masa.

Kaya ya dauko. Ya shiga wani bedroom din daban. Yai wanka ya sake kaya sannan yai alwala ya fito.

*

Tana bude ido ta fahimci bakuntar wajen da take. Komai ya dawo mata. Ta duba bata ga fu.ad ba. Saukowa tai daga kan gadon.

Jikinta ko ina ciwo yake saboda rashin sabo. Bandaki ta shiga ta bude fanfo.

Ruwan sanyi sosai. Dakyar ta iya wanka dashi tayo alwala ta fito. Sallar asuba ta gabatar tai zamanta.

Tunani take da tana gida da yanzun tanata ayyukanta. Koya su inna suka tashi Allah kadai yasani.

*

Da sallama ya tura kofar. Ta amsa a hankali tana dagowa. Muryarta babu kwari tace masa.

"Ina kwana......"

Saida ya karasa ya zauna gefen gadon. Sannan ya amsa da.

"Kin tashi lafiya? Ya jikinki?"

"Da sauki. Nagode"

Shiru suka danyi. Saboda kawai sai yaji ya rasa me zaice mata. Itama hakan take. Jinta take duk wata daban.

"Me zakici?"

Dagowa tai ta kalle shi. Sannan ta mayar da kanta kasa.

"Komai ma"

Shiru yadanyi. Yana tunanin me ya kamata ya siyo dan in tashine baida matsala. Ita dai baisan me tafi so ba.

Ajiyar zuciya ya sauke. Abu daya yasani kan safiyya. Yana sonta. Banda shi sai iya abinda ta fada masa jiya.

Zama sukai shiru. Kowa da abinda yake tunani. Text yaji ya shigo wayarshi. Yai mamaki daya ga har bakwai da rabi tayi.

Murmushi yayi. Hussaina ce.

"Are you okay? Pls text back am worried"

Duk da bai taba fada ba. Yafi kaunar hussaina duk gidansu. Rigimarta. Komai nata daban yake. Reply yai mata.

"Em' okay lil sis"

Yana shiga tana dawo masa da.

"Thank God. Take care of you and her"

Murmushi kawai yai ya ajiye wayar yace ma safiyya.

"Hussaina tace in kula dake"

Wani gajeran murmushi tayi. A kunyace tace.

"Nagode da karamci"

Mikewa yai. Dan yana son ya fita har gidansu lukman yaje ya dibo kayanshi dake can. Kuma su gama magana da isma.il.

"Akwai burger da sauran milkshake a fridge. Zan fita. Wayarki na nan?"

Shiru tadanyi. Bata san inda wayar take ba. Ko ina ta sullube oho. Sai yanzun ma dayai magana ta tuna.

Kai ta girgiza masa.

"Alright. Tam za.a siyo wani in shaa Allah. Bansan ko yaushe zan dawo ba. Ina so har maganar gidan a gama yau.

In yaso ran Monday in Allah ya kaimu sai in kaiki makaranta"

Murmushi tai masa da ya kara mata kyau yasa shi manta me yake so ya fada mata next. Dan dafe kai yayi yanajin wani bugu bugu a zuciyarshi.

"Kinga na manta me zance ko sofi?"

Ga mamakinta dariya tadanyi. Yanayin shi ya bata dariya.

"A dawo lafiya"

Tace masa. Kallonta yake yana wani mamaki. Wai shine da mata haka. Murmushin dake fuskarsa yake kara fadada.

"Zaki iya zama ke kadai?  Ko zakiyi kallo a falo?"

Kai ta daga masa alamar eh. Dan kallon ma kila ya hana mata tunani. Yaushe rabonta da kallo. Inba ko sunje gidansu jummai ba sun samu da wuta.

"Taso to"

Ba musu ta mike. Kayan dake jikinta yabi da kallo.

"Sofi akwai kayanki na jiya a falo. Akwai man shafawa ma. In kina bukatar wani abu ki fadamun in taho dashi"

Ita kam wahalar ta isa. Tsakanin jiya da yau Allah kadai yasan kudin daya kashe mata. A sanyaye tace

"Bana bukatar komai"

Bai amsata ba ya fita daga dakin tana bin bayansh. Kayan kallon dake falon ya hada dan komai a ware yake tunda bamai amfani dasu.

Babu ma films din dazai hada mata dvd dasu. Sai satellite ya hada. Ya na tuna channels din da ake films din hausa.

Arewa24 yakai mata. Ya ajiye mata remote din kusa da ita. Dakanshi yaje ya bude fridge ya dauko mata burger din da milkshake ya ajiye mata kan table din tsakiyar falon.

"Na tafi sofi"

Kallon shi take. Kawai sai taji wani iri.

"Allah ya tsare"

Ya amsa da amin yana ficewa da sauri dan so yake ko pecking dinta yayi kamun ya fita.

*

Gidansu lukman ya fara zuwa. Yana school. Yana da key jikin mukullan motarshi. Ya bude dakin ya dauki abinda zai dauka ya fice.

Wajen isma.il yaje suka gama magana kan wani 3 bedroom mai matsakaicin girma a cikin sharada.

Tare sukaje aka gama komai da komai ya biya kudin. Ya karbi takardun. Gaba daya yagaji.

Fruits ya tsaya ya siya. Ya tsaya yai musu take away dan lokacin har azahar tayi. Gaba daya hankalin shi nakan safiyya.

*

A falo ya sameta zaune tana kallo. Da sallama ya shiga. Ta amsa masa tana mikewa.

"Sannu da zuwa"

Ya amsa da yawwa yana cire takalminshi. Karasawa yai ya zauna yana wani lumshe idanuwa. A tabare yace.

"Nagaji sosai"

"Sannu"

Safiyya tace masa. Shiru yai ya wani lafe cikin kujera. Yunwa ke cinta sosai dan wannan abin daya bar mata ga sanyi dayai.

Wani iri yai mata sam kasa ci tayi. Rabon cikinta da wani abinci na kirki tun shekaranjiya. Muryarta can kasa tace masa.

"Yunwa nake ji sosai"

Dagowa yai yana dan ware idanuwa. Da sauri ya mike ya fice. Mota yaje ya dauko take away din dayayo ya dawo.

Ajiyewa yai gabanta. Budewa yai. Kallon abincin take. Shinkafa ce jalof da kaji. Sai hadin salad. Cokulan ya dauko ya mika mata hadi da fadin.

"Sauko muci"

Karbar cokalin tayi ta sauko. Yunwar da take ji yadan rage mata kunyar cin abincin a gabanshi. Da kuma yanda taga sam bai ko kallonta.

Abincin shi yake taci da cokula biyu. Itama ke kallonshi tana mamaki. Shinkafar kawai take ci da tai mata dadi sosai. Bata jin zata iya cin hadin salad din da fu.ad yake ta aikama cikinshi dan haka ko kusa bata gwada ba.

Cokalin dayaga ta ajiyene yasa shi dagowa ya kalleta.

"Har kinyi me?"

"Na koshi"

"Kin tabbata?"

Ta daga masa kai. Ledar fruits din dake gefenshi ya janyo kusa hadi da fadin.

"Fara kamun in gama"

Sai da ta bude robar ruwan tasha sannan ta dauki lemon zaki ta koma kan kujera ta zauna.

Fu.ad take kallo. Tas ya cinye abincin shi da salad din. Nata take away din ya janyo da ko rabi bata cinye ba.

Tas ya cinye. Ya bude exotic din dake gefe ya sha. Mika ma safiyya yai. Ta girgiza masa kai. Ajiyewa yai.

Ya janyo ledar fruits din ya sha kankana sosai. Ya ci ayabar dake ciki takai goma sannan ya mike.

Cikinshin safiyya tabi da kallo cike da mamakin ganin duk lodin dayai mishi yana nan a shafe.

Expression din fuskarta ya sa shi yar dariya. Rabon daya jishi shidin ta bangaren cin abinci harya manta.

Yau jinshi yake wani normal. Ya dawo fu.ad dinshi. Duk wani abu da yake tunanin ya rasa ya dawo.

Bude baki yai zai magana wayarshi tai ringing. Hakan ya tuna mishi da yana bukatar sake fita.

Dauko ta yai kan kujerar daya tashi. Wani iri yadan ji. Sam bai shirya jin wani dogon zance ko nasiha ba.

Dagawa yai ya kara a kunne. Haneef yace.

"Fito"

Kan ya amsa ya kashe wayar. Ajiyar zuciya fu.ad ya sauke hadi da fadin.

"Just when i thought yau babu wani drama........!"

No comments:

Post a Comment