Thursday 4 May 2017

AKAN SO 41

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

            41

*Hakika babbar kyauta da zaka samu a duniya itace ta 'Ya'ya. Idan har ina jin yanda nake ji a zuciyata idan na dauki yaran wasu. Zan so sanin me ake ji randa zan rungumi nawa yaran. Allah ya azurta duk wani mai bukatar haihuwa da Yara masu albarka*

*Soyayyar iyaye wata baiwace da wanda Allah ya azurta da ita ne kawai zai fahimta. Allah ka sakama iyayen mu da mafififin alkhairi*

*TO ALL MUMS and DADS. Thank you for loving us duk da ba zamu taba muku rabinta ba*

*#AnaTare*

Three piece suit yasaka Baki da fari. Bai sha wahalar dora ta saman ba dan baya son takura ko kadan.

Yanzun ma dan inda zashi baya son a mishi kallon karamin yaro kuma bashida wasu manyan kaya ko daya.

Dacan ma ba sakawa yake ba. Ballantana yaushe rabonshi da nigeria. Turaruka ya feshe jikinshi dasu sannan ya fito.

A falo ya samu su momma suna karyawa. Ya gaishe dasu a ladabce sannan ya zauna. Wata irin yunwa yake ji.

Sosai yaci dankali da kwan da momma ta zuba mishi ya hada da tea sannan ya mike yana fadin.

"Momma barin je in kawo Nana din. Amman ina so in biya ta gidan lukman dan karya fita aiki kamun in wuce in dauko ta"

"A dawo lafiya. Ka gaishe da lukman din. Nace kwana biyu bai kawomun junior ba"

Murmushi fu.ad yai hadi da daga mata kai. Ya maida hankalinshi kan abbah.

"Abbah bakaimun addu.a ba"

Murmushi abbah ya mayar mishi.

"Allah ya tsare ya sanya albarka"

"Amin. Hassan bai tashi bane?"

Fu.ad ya bukata. Momma ta amsa shi da.

"Ai ya tsufa wajen aiki. Yana rigan kowa tashi"

Wucewa fu.ad yai yana fadin.

"Alright. Saina dawo"

****

"Mumy dan Allah in kwana?"

Dan jim safiyya tayi tana jinjina maganar Nana din. Bawai bata so ta kwana bane. Tasan kewa zata dame ta.

Amman tana bukatar sanin dangin babanta. Suma su santa. Ko ba komai sun nuna mata kauna lokaci daya.

"Sai dai zaki tafi da magungunanki. Ki bama momma su duka"

Da sauri Nana tace.

"I promise zan sha duka. Nagode mumy"

Murmushi kawai safiyya tayi mata. Ta dauko mata kayan da zata saka da kuma wasu kala biyu sai na bacci sa takalma guda biyu.

"Mumy kibani cikin wanda dady ya siyo mun jiya."

Dan dafe kai safiyya tayi. Ta manta da kayan shaf. Mikewa tai taje ta dauko mata su. Ta zazzage wa.ancan daga leda ta saka mata sababbin.

Purple hijab din data dauko mata zata mayar. Ta rike da fadin.

"Zan sa wannan"

Sakar mata safiyya tayi. Ta barta anan tana daukar wani riga da pencil trouser cikin wanda fu.ad ya siyo mata. Tasan Nana bata son a tayata shiryawa inba bata da lafiya sosai ba.

Dan haka ta shiga wanka tabarta anan tana shiryawa abinta.

****

Fu.ad bai samu junior a gida ba. Kasancewar juma.a ce ya tafi makaranta. Yau dai saida lukman yaja shi har cikin gidan suka gaisa da zainab.

Yanayin karamcin zainab ya burge fu.ad. Suna gama gaisawa tai mishi godiyar machine din daya saima junior ta bar musu wajen.

Lukman yace mishi.

"Allah ya bar zumunci"

Dakuna fuska fu.ad yai yana harar lukman.

"Bana son iskanci lukman."

Dariya yai.

"Daga na maka godiya"

Juya idanuwanshi yai. Sarai yasan lukman din neman magana ne. Dan haka ya share. Numfashi ya sauke yace.

"Naga no iyayen sofi lukman. Ga address din nan ma"

"Ma shaa Allah. Kai amman naji dadi sosai wallahi. Allah kenan. Gaskiya naji dadi. Ka fada mata ne?"

Girgiza ma lukman kai yayi.

"Nace ta shirya dai zamuje wani waje amman ban fada mata ba. Nafi son in surprising dinta"

Dan daga kafada lukman yai.

"Daka fada mata dai"

Sake girgiza kai fu.ad yai.

"Ni ba wannan ba kasan me?"

"Saika fada...."

Kaf yanda sukai da Nana fu.ad ya fada ma lukman ya dora da cewa.

"Bazai zama adalci wa sofi ba lukman. Banda abinda zan bata. Nabarta shekarun nan dan ta samu farin ciki.

In.... In har akace babu Nana zai zama kaman zamu raba zunubaina ne da ita bayan batai komai ba......"

Dafa kafadarshi lukman yayi.

"Idan ka duba rayuwar fu.ad ba komai bane a cikinta sai tarin wahala. Jin dadin dake cikinta kalilan ne.

Nasan tabbas bazai zamana adalci wa safiyya ba. Rashin yara ba karamin abu bane ko ga matar da batasan dadin su ba ballantana.

Amman na yarda da Nana. Ba fata nake ba. In babu ita kana bukatar safiyya. Haka duk yanda safiyya zata nuna akwai soyayyarka a tattare da ita.

Tana bukatarka...... Inhar zata aureka ina bayan Nana"

Dafe kai fu.ad yayi. Zai iya jure rashin safiyya inhar zatai farin ciki.

"Banda abinda zan bata......"

Katse shi lukman yayi.

"Bance kana dashi ba. Amman akwak soyayyarka ko? Zaka cemun baka sonta ne?"

Daga girarshi yai sama duka biyun hadi da fadin.

"Ina jin haushinta. Ta boyemun Nana"

"Really? Da gaske kana jin haushinta ta boye maka Nana?"

Lukman ya tambaya cike da jin haushin rashin adalcin dake cikin maganganun fu.ad din.

Cikin dacin rai yace.

"Sosai ma. Bata da right din da zata boye mun ita. Bata dashi......"

Gyara zama lukman yai. Yasa hannu yadan daki goshin fu.ad din. Daya ture hannun lukman yana fadin.

"Meye haka?"

Wani murmushin takaici lukman yayi.

"Ina so inga ni ko kana bacci ne in tasheka?"

Daga mishi gira fu.ad yai cike da alamun cewar bai fahimci me ya kawo wannan cikin maganar da yayi ba.

"Me kake so safiyya tayi fu.ad? Kasa kafa ka tafi? Ta je filin jirgi ta sa musu kuka su kaita kasar daka ke? Bayan bata sani ba?......"

Magana fu.ad zai lukman ya katse shi.

"Ka bari ingama please. A halin daka barta dan sauran hankalin dake jikinta kake so shima ta mika maka?

Ka taba tunanin bari ka dawo saboda bata da kowa a garin kano sai kai?

Ka taba tsayawa kace me zatayi taci abinci?

Ka taba tunanin ita kadai zata ringa kwana a karancin shekarunta?

Ko ka manta *Akan so* tabar komai da kowa nata?

Fu.ad ka manta kaine komai nata kamin ka yanke hukuncin sakinta lokacin data fi bukatarka?

Rannan a asibiti bata fada maka tai kokarin nemoka lokacin data gane tana da ciki ba?

Allah kadai yasan rudanin da ta shiga da dimauta na renon cikin Nana ita kadai batare da mataimaki ba.

Ina tare da zainab daga randa ta samu cikin junior har haihuwarshi. Wallahi saida na kara ganin darajar hajiya ba kadan ba.

Dan Allah inhar zakaga laifin safiyya ka daina furta shi a gabana. Saboda raina baci yake sosai.

Kana tunamin abubuwan dana zabi na manta"

Maganganun lukman yawo suke masa cikin kai suna sanyaya mishi duk wata gaba dake jikinshi.

Lokaci daya wani irin laifi mai girma yake mishi mayafi. Cikin son kauda yanayin yace.

"Nasa ana turo mata kudi. Ana turo mata kaso biyu cikin duk wani abu dazan samu"

Girgiza kai lukman yai yana fadin.

"Hmm. Babu abinda zaima laifinka adalci fu.ad. Kudi bakomai bane in har babu kulawa"

Lumshe idanuwa fu.ad yayi. Lokacin dayake jin komai ya kusan dai daita sai kuma komai ya dawo mishi baya.

Ajiyar zuciya ya sauke. Ya mike tsaye yana saka hannayenshi duka biyun ya goge fuskarshi dayake jin alamar zufa.

"Zan gyara komai"

Mikewa lukman yayi.

"Karka ce zaka dora sabon gini kan foundation din daka bari. Ya riga da ya lalace fu.ad.

Ka sake komai daga farko. Ka tabbata kayi shi da kwari"

A sanyaye ya amsa da.

"In shaa Allah. Nagode lukman. Nagode da komai"

Jinjina mishi kai yai sukai sallama. Da wani irin nauyin jiki fu.ad ya bude mota ya shiga.

****
Handle din kofar ya kama ya murda. A hankali ya tura hadi dayin sallama. Bai rufe bakin shi ba yaji Nana a jikinshi ta makale shi.

Baisan lokacin da murmushi ya kwace mishi ba. Duk yanayin da yake ji bai hana wani farin cikin ganin Nana dabaisan daga inda ya fito ba ziyartarshi.

Tsugunnawa yai dan tsayinsu yazo dai dai yace mata.

"Princess tayi kyau"

Dariya tai a kunyace hadi da fadin.

"Kayi kyau sosai kaima. Ina kwana"

"Kin tashi lafiya? Yanzun dana shigo ne kika shafamun kyanki"

Dariya Nana ta sake yi.

"Ni ina lafiya. Kai mana pictures....."

Kamun ya amsa tace.

"Kai!  Na manta. Barin dauko camera dina....."

Ya bude baki ta bar jikinshi tana rugawa da gudu.

"Oh. Nana!  Kibi a hankali"

Ai bata ma jishi ba ta shige daki da gudu. Ita take gudun shi zuciyarshi ke dokawa karta fadi. Safiyya ta fito sanye da atamfa. Dinkin simple ne sai dai ya karbeta sosai.

Fuskarta babu yabo ba fallasa tace mishi.

"Ina kwana"

Idanuwanshi kafe kanta. Zuciyarshi na karanta mishi kyawun datai ya amsa da fadin.

"Kin tashi lafiya? Su momma na gaishe dake"

"Alhamdulillah. Ina amsawa. Nagode. Kace ina gaishe dasu nima"

Zai amsa Nana ta fito da gudu da camera din a hannunta. Gaban fu.ad ta tsaya tana danne danne a jiki.

Kamun ga daga 📷 din saitin shi tana fadin.

"Dady me kafi so?"

Dariya yai. Ya kalli safiyya yana bude mata idanuwa yana son tambayarta me zai ce?

Tabe baki tayi. Tana sake damqe fuska. Ganin da Nana tayi ya kalli safiyya yasa ta tabare fuska tana turo baki tace.

"Dady na dauka kafi sona"

Sai lokacin ya dawo da hankalin shi kan Nana yana mata kallon 'Me kika ce?'

Sake turo baki tayi.

"Haka nace me kafi so. Ka kalli mumy"

Safiyya dake tsaye tace.

"Nana.....!"

Dariya tayi ta juya camera din saitin safiyya.

"Ke me kika fi so?"

Fu.ad safiyya ta kalla? Daya amsa tambayar Nana da hankalinta na kanshi.

"Mumy!  Kema?"

Da sauri safiyya ta ce.

"Ke princess. Nafi sonki"

Shagwabe fuska Nana tayi.

"Dady kika fara kallo kema. Zanje wajen granny nasan ita tafi sona"

Dariya fu.ad yayi ya kamo Nana jikinshi.

"Inji waye. Ina son princess fiye da kowa."

Murmushi Nana tayi taba daga camera din saitinsu ita da fu.ad hadi sa fadin.

"Hello. Ga M. Shine dady na. Dady say Hi"

Dariya fu.ad yake sosai. Yanda take ma camera din magana kaman wata mutum.

"Nana camera ne fa"

Dire kafafuwa nana tayi.

"Dady be nice. Ina son camera din nan sosai fa."

Dariya fu.ad ya sake yi. Nana ta dakuna mishi fuska sannan ya soma kokarin controlling dariyar.

Yanda kome Nana tayi yake sashi dariya har mamaki yake bashi. Da dariyar a muryarshi yace.

"Hi camera"

Yana daga hannu. Gaba daya yanda ya biyewa Nana suka zama wasu yan yara yaba safiyya dariya.

Da sauri ya daga idanuwa ya kalleta. Murmushi yake. Yana tuna yanda yake son dariyarta.  Yanda idanuwanta ke cika da wani abu da bazai iya dora ma kalamai ba.

Camera din Nana ta mayar saitin safiyya tana fadin.

"Mumy na dariya"

Girgiza kai safiyya tayi. Tasan video Nana ke daukar su.

"Ban iya shiririta ba Nana. Wuce ki dauko kayanki ku tafi"

Sai lokacin Nana ta juyo cike da jin dadi tace ma fu.ad.

"Mumy tace in kwana wajen granny"

Shima yaji dadi. Nana ta wuce zata dauko kayanta. Da idanuwa yake nuna ma safiyya godiyarshi can gefen zuciyarshi girman laifin shi da lukman ya nuna mishi na nan manne.

"Kin shirya? In mun sauke Nana kuka gaisa da momma sai mu wuce ko?"

Sauke numfashi safiyya tayi

"Na dauka tun jiya nace maka ba zanje ba"

Mikewa tsaye fu.ad yayi. Ya tabbata ya sauke idanuwanshi cikin nata kamun yace.

"Ki yarda dani. In baida muhimmanci bazan tambaye ki ba"

"Kaman yarda dakai a baya yamun wani amfani"

Ta fadi muryarta cike da takaici. Yaji zafin maganar data yaba mishi har ranshi. Sai dai wannan ba lokaci bane dazai tsaya yana mata bayani tunda yasan kome ta fada shi ya janyo.

"Sofi please....."

Wani murmushi tai da hakoranta kawai ta bude mishi. Kamun ta hade fuska.

"Ka iya wannan ka tsaya kana bani umarni kaman yarka"

Shirun dai yai. Dan bashida bakin magana yau.  Yana kallon hararar data watsa mishi kamun ta wuce cikin bedroom din. Sauke ajiyar zuciya yai.

Bata san ina fu.ad yake so suje ba. Sai dai ta rasa me yasa gabanta yake ta faduwa tunda safe. Bata kuma san dalilin daya sa take son ta bishi ba.

Koma ina ne koma menene zata iya tarar napep ta dawo in bai mata ba. Mayafinta ta dauka ta yafa. Ta kamo hannun Nana suka fito.

Murmushi ya kwace ma fu.ad saboda yanda sukai mishi kyau kaman ya sace su. Wayar shi ya dauko ya bude camera yana karasa inda suke ya tsaya gefen Nana.

"Me zakayi?"

Safiyya ta tambaya. Bai kulata ba ya daga camera din yana musu hotuna kala biyu sannan ya kama hannun Nana suka fice. Ta girgiza kai kawai. Karfin halin shi na bata mamaki.

Sam bata so ta tuno bukatar Nana akanshi. Yanda ta kwana da abin a ranta kawai ya isheta ba saita tsokano shi da safiyar nan ba. Saida ta kulle gidan sannan ta same su a mota.

Nana ta shiga gaba ita da fu.ad. safiyya kam bayan motar ta bude ta zauna. Tana jero addu.o.i a zuciyarta saboda bata san dalilin bugun zuciyarta ba.

**

Ba karamin dadin ganinsu momma taji ba. Suka gaisa da safiyya. Su zauna fu.ad yace.

"Momma sauri muke. Akwai inda zamuje ki mana addu.a"

"Aika bari dai tadan huta ko?"

Girgiza kai yayi.

"Yau juma.a fa. Gashi har sha daya ta kusa. In muka dawo sai mu biyo"

Jinjina kai momma tayi.

"A dai kula dan Allah. Sai kun dawo. Allah ya bada sa.a"

A sanyaye safiyya tace.

"Amin. Mungode momma"

Dan tsugunnawa fu.ad yai ya sumbaci Nana a kumatu.

"Banda rashin ji okay?"

Kai ta daga mishi tana murmushi.

"Love you kai da mumy"

Murmushi safiyya tayi sannan suka juya ita da fu.ad din suka fice. Bayan motar ta bude ta shiga tana wani daure fuska.

"Ba magana zan miki ba. Ni bana son neman rigima ko kadan"

Cewar fu.ad daya shiga motar yana jan murfin. Taji shi sarai. Ta zabi tai shiru ne kawai saboda jin su ita kadai dashi cikin motar ya isheta.

Yanda zuciyarta ke son kwacewa da gudu ta kaita ziyara lokutta da yawa ya isheta yaki da. Basai ta tsaya kula fu.ad ba.

Ta mudubi ya kalleta. Yanda ta lafe jikin kujerar motar tana lumshe idanuwa. Addu.a yai ta neman sa.a kamun ya murza key din motar.

****

Ga mamakin safiyya bakin wani gida sukai parking. Fu.ad ne ya fito ya barta cikin motar. Tana kallonshi yana daga kai yana kallon number din gidan.

Tsaye yai yana yan waige waige kamun yaga wata yarinya tazo wucewa.

"Ke!  Zo dan Allah"

Kallon fu.ad yarinyar tadanyi a tsorace ta tsaya. Shi ya matsa inda take yace mata.

"Anan unguwar kike?"

Kai ta daga mishi. Yadan ja numfashi ya fitar hadi da fadin.

"Ko kinsan sunan mai gidan nan?"

Da mamaki bayyane a fuskar yarinyar ta amsa shi da fadin.

"Malam audu."

Wani tsalle zuciyar fu.ad tayi

"Matarshi fa?"

"Ni bansan sunanta ba. Kowa Inna yake ce mata"

Ganin ta soma gajiya da tambayoyinshi yasa shi fadin.

"Nagode sosai. Dan Allah ki dan shiga kice musu sunyi baqi"

Ba musu yarinyar ta shiga. Bata fi mintina uku ba ta fito tace.

"Ance ka shiga"

Godiya yai mata. Ta jinjina mishi kai kawao ta wuce abinta. Ji yai jikinshi yai wani iri. Dakyar ya karasa yace ma safiyya.

"Fito muje"

Yanayin shi data ga ya sauya lokaci daya yasa ta mayar da musun da take son mishi ta bude motar ta fita.

Matsawa yai yasa hannu ya zare key din motar shi ya kulle ta yasa a aljihu sannan ya kama hanya suka nufi gidan.

Tunda suka taka cikin soron gidan zuciyarta ta tsananta dokawar da take har fu.ad yai sallama yana danna kai.

*

"Ai da kin bari na leqa naga ko su waye"

Jinjina kai inna tayi dake zaune kan darduma. Shikuma yana saman kujera.

"Bazai shige yaron nan ya yake da suna ba. Abokin wannan dan da yace zai kawo matarshi ta gaishe damu yau"

"Au. Nama manta fa"

Sallama suka ji.

"wa alaikumussalam. Ku shigo"

Inna ta fadi. Tana janyo hijab dinta dake ajiye gefe ta saka.

*

Wani irin dokawa zuciyar safiyya tayi. Muryar data amsa sallamar. Shekaru sha biyu bazai sa ta manta taba. Sai dai gasgata cewar ba kunnenta bane yake mata gizo abu ne mai wahala.

Kafafuwanta taji suna mata rawa. Ga wani irin tsoro da ya cika mata zuciya. Fu.ad ya soma sakai cikin gidan yana sake yin sallama.

Sosai Inna ke kallon shi tana son tuna inda ta san fuskarshi. Baba dake zaune ya dafa kujera ya mike saboda yanayin rauni na manyantaka daya kama shi.

Duk da sajen dake kwance fuskar fu.ad bai hana shi gane shi ba. Babu yanda za.ai ya manta fuskar dayake kwana da ita a zuciyarshi ya tashi da ita ba.

Fuskar datai sanadiyar salwantar yarshi. Baki baba ya bude yana kallon fu.ad ya daga hannu yana nuna shi sai dai kalma ko daya ta ki fitowa daga bakin shi.

Duk da zuciyarshi cike take da tambaya guda daya.

"Ina 'Ya ta?"

Sai dai ya kasa furtawa saboda yanda yake jin wani jiri na dibar shi. Kallon su fu.ad yake yana jero godiya wajen Ubangiji daya tabbatar mishi da wannan nasarar.

Matsawa yai gefe ya kasa karasawa cikin gida. Sai lokacin safiyya ta samu damar shigowa dan fu.ad ya tare hanya.

A hankali idanuwanta suka sauka kan Inna dake zaune. Sannan ta maida dubanta wajen baba dayake tsaye idanuwan shi cike da rashin yarda cewa ita ce.

Wani abu take ji. Yana mata yawo tun daga dan yatsan kafarta har zuwa tsakiyar kanta. Lokaci daya jikinta ya dauki kyarma.

Kafafuwanta take so ta matsar su karasa da ita wajen su Inna da take hangowa ko sau daya ne ta nemi gafararsu kamun su bace mata.

Kamun ta farka daga mafarkin nan da takeyi su sake subuce mata. Amman ta kasa. Ta kasa saboda yanda babu karfi ko kadan cikin kafafuwanta.

Tana kallo baba yana takowa. Duk da tsufan dayai bai hanata ganin shi ba. Bai hanata gane shi ba. Tana jin raunin da take gani cikin tafiyarshi har zuciyarta.

Gani take yafi awa daya bai karaso ba. Gani take wata kaddara zata iya giftawa kamun ya karaso gareta saboda ita ta kasa kaiwa inda yake.

Numfashinta take kokawa dashi wajen fita saboda tashin hankalin da take ciki.

Gab da ita baba ya karaso ya kura mata idanuwa. Rike numfashi safiyya tayi tana tsoron kar ta sake shi baba ya bace. Karta saki numfashin da taja ta farka daga mafarkin da take.

Tana jin yanda kirjinta ke zafi da neman iska. Kanta ke wani irin juyawa saboda karancin iska amman taqi sakin wadda take rike da ita ballantana ta shaki sabuwa.

Zata iya jure kowace azaba a yanzun in har hakan na nufin ba zata kokawa azabar rashin su inna ba.

Cikin rawar murya baba ya juya ya kalli inna yace.

"Taso kigani. Safiyya ce. Safiyya ce ta dawo......!"

Da sauri inna ta taso har tana sassarfa. Gefen baba ta tsaya. Dan ta ki tasowa ne kar tazo taga ita kadai ce safiyya kema gizo kaman yanda take mata lokutta da dama.

Hannu tasa ta taba kuncin safiyya tana son jin ko da gaske ita dince. Jin hannun inna a kuncinta ya sa safiyya sakin numfashin da take rike dashi.

Muryarta na wani sama sama ta rike hannu inna gam tana fadin.

"Innaaaaa!"

Idanuwanta ta mayar kan baba dake tsaye. Dayan hannunta takai ta kamo nashi tana dumtse wa sosai cikin nata zuciyarta na wani irin dokawa.

"Babaa!"

Tana jin yanda zuciyarta ke rage gudu alamar zata iya samun matsala ko da yaushe. Tana jin yanda dan karfin halin da take dashi saboda Nana yana rugujewa.

Tana jin yanda ko ina na jikinta ke budewa da bukatar iyayenta data dinga dinkewa a tsahon shekarun nan saboda Nana na bukatarta.

Wani irin jiri na dibarta take fadin.

"Ku yafemun inna...... Baba ka yafemun. Dan Allah........ku yafemun....."

Tana jin yanda duniyar ke juya mata. Kafun kafafuwanta su karasa mutuwa. Da neman yafiyar su inna a bakinta tai kasa. Tana wani irin fitar da numfashi kamun komai ya tsaya......!

Su duka ukkun kanta sukai. Inna na tallabe da ita a jikinta tana jijjigata.

"Safiyya ki tashi. Wallahi mun riga mun yafe miki da dadewa. Dan Allah ki tashi......"

Hannunta baba ya kama.

"Safiyya tashi kinji. Mun yafe miki ai tun tuni. Kinji innarki ma tace ta yafe miki. Ki tashi tunda Allah ya hada fuskokinmu da rayuwarmu"

Fu.ad ya rasa me ya kamata yayi. Buta ya hango da gudu ya karasa karshen gidan ya dauko butar. Ruwan ya zuba a hannunshi ya yayyyafa ma safiyya dake jikin inna.

A hankali take motsawa kamun ta soma bude idanuwanta. Sama sama take jin muryar Inna na fadin.

"Safiyya...... Safiyya ki tashi kiga mun yafe miki...."

Ware idanuwanta tayi jin muryar inna. Ta ko sauke su kan fuskar inna. Da sauri ta mike daga jikinta. Hannuwanta tasa ta tallabi fuskar inna.

Tana so tagani da gaske ba mafarki take ba su inna ne a gabanta. Sannan ta maida dubanta wajen baba dake zaune kan siminti batare daya damu ba.

Yanda take ji a zufiyarta ba zai taba faduwa ba. Allah kadai yasan yanda take jin rashin su domin shi ya rubuta mata kaddarar rabuwa dasu.

Kanta ta kifa jikin inna tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya. Inna ma kuka take sosai ta dora kanta a bayan safiyyar.

Kuka suke sosai daya sa fu.ad dayake a tsaye jin wani abu na mishi yawo cikin idanuwa. Su duka sun dandana rashin iyaye sunji yanda yake.

Gara shi akan safiyya. Bazai taba misalta yanda take ji ba a yanzun sai dai ya kwatanta. Kuka take sosai. Batare da sun kula ba fu.ad ya fice ya basu waje.

Dagowa safiyya tayi ta kama hannun inna jikinta na wani irin bari hawaye na wanke mata fuska.

"Inna da gaske kune? Ba mafarki nake ba inna?"

Kai inna ta iya daga mata. Wani irin kuka take da take jin fitowarshi na mata ciwo a zuciyarta da idanuwanta. Baba ta kalla muryarta na rawa.

"Baba dan Allah ka yafemun. Wallahi na muku laifi mai girma nasani. Na kunyata ku a idan duniya.

Na jefar da soyayyar da kukaimun akan wadda ta ziyar ceni daga baya. Baba nayi wauta mai girma"

Kwallar data taru a idanuwanshi yasa riga ya goge. Cikin rauni yace.

"Safiyya kinyi laifi kam. Sai dai kaddara bata wuce kan kowa. Bacin raine ya hanamu fahimtar kaddararki ce tazo a haka.

Mun jima da yafe miki duk da baki sake waiwayarmu ba"

Kallonsu take cikin tashin hankali take fadin.

"Naje baba. Wallahi naje aka ce mun kun tashi.......ba wanda yasan inda kuka komaaa"

Ta karasa maganar wani irin kuka na kwace mata. Sosai inna ta rike safiyya jikinta.

"Surutun mutane yasa muka tashi. Maganganun su yasa muka baro bichi"

Kuka safiyya take yanzun kam kaman zata shide. Sanadinta sun jure kunci mai girma. *Akan so* ta ja ma iyayenta muzanci da tozarta mafi girma.

"Inna rayuwata ba zata taba yin dai dai ba idan baku yafemun ba"

Riketa inna tayi ganin yanda jikinta ke kyarma tana fadin.

"Mun yafe miki safiyya. Mun yafe miki duniya da lahira. Kasancewarki tare damu yanzun shine abu mafi girma daya faru damu a shekarun nan"

Baba ya dauka da cewa.

"Laifinki baisa mun daina kaunarki ba safiyya"

Kai kawai ta iya daga ma baba saboda tasan yanda girman wannan kaunar tasu take. Tasan yanda ciwonta yake.

A haka inna ta kama safiyya tajata suka shiga daki. Baba da kanshi ya je ya dauko cup yazo ya fasa ruwa ya zuba ya mika ma safiyya.

Hannuwa biyu tasa ta karba ta shanye tas tana jinjina kalar kaunar dake tsakanin da da mahaifanshi.......!

*#TeamAS*

1 comment:

  1. Harrah's Resort Southern California Casino - JetXtra
    Harrah's Resort 전라북도 출장마사지 Southern California Casino - JetXtra 화성 출장샵 offers the latest in lodging, dining and 충주 출장마사지 gaming, as well as 김천 출장안마 a wide variety 계룡 출장샵 of entertainment venues and

    ReplyDelete