Thursday 4 May 2017

AKAN SO 17

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

       17

*A ton of thanks to my big sister from another mother BABYN UF for being #1teamFu.ad. LVYONG*

"Inalillahi wa ina ilahi raji.un....."

Momma ta fadi bayan haneef ya gama gaya mata kome yake faruwa.

"Yanzun duka fu.ad din nawa yake?  Hankalin kirki bashi da shi haneef"

Jinjina kai yai ya gyara zama yace.

"Nasani momma. Amman ki kalli fa abinda yake yi. Wallahi zai iya samun matsala. Nikam dai a taimaka aje aji"

"Hmm bayan tozarcin dayai musu kana zaton zasu saurare mu ne?  Kafi kowa sanin halin abbahnku. Da wahala yaje"

Shiru haneef yadanyi kamun yace

"In yaga yanda fu.ad ke shirin zaucewa zaije. Nasan bashida wani hankalin kirki. Amman wallahi yana sonta. Kema kinga alama ai"

"Kai. Oh Allah na"

Momma ta fadi tana sauke numfashi. Wannan wacce irin kaddara ce.

Ita tunda take inba a film ko a littafi ba. Bata taba ganin irin wannan abu ba.

Bama tasan ta yanda zata fara tunkarar abbah da wannan maganar ba.

"Barin je sallah"

Cewar haneef yana mikewa. Kai kawai momma ta iya daga masa.

*

Da yammacin ranar abbah ya dawo daga abuja. Sai da yaci abinci yai wanka ya huta sannan momma ke fada masa fu.ad bashi da lafiya.

Dayake zamansu babu boye boye a ciki. Zata iya tunkarar mijinta da kowacce irin damuwa.

A nutse ta fada mishi komai da yake faruwa. Shima salatin yake yana mamakin lokacin da fu.ad ya zama haka.

"To nikam yazanyi maman fatima. Allah ne yake hora shi"

Dayake uwa daban ce a tausa she tace

"Alhaji nasani. Amman sai a duba halin da yake ciki. Ko neman auren yarinyar sai a je masa"

Girgiza kai yayi.

"Bayan abinda kika ce ya musu. Kina tunanin ko fu.ad ya isa aure zasu bashi yarsu ne?  Ku rabu dashi kawai. In yagaji zai hakura"

"Allah ya kyauta."

Ta fadi tana mikewa ta fice daga dakin. Da alama ranta ya sosu da maganganu shi.

*

Haneef da lukman ne zaune dakin fu.ad. kallon shi kawai suke. Dan lukman ma da ba.ayi a gabanshi ba a tsorace yake.

Gani suke da sunyi magana zai kara shiga matsala. Tunda ya tashi dai baice musu komai ba.

Suna kallo ya sauko daga kan gado yai hanyar kofa. Suka hada ido basu ce masa komai ba.

Kasa ya sauka ya nufi bangaren su momma. Karo yaci da ita ta fito dakin abbah.

"Momma kin masa magana?"

Ya tambaya. Ta kalli yanda ya wani fada ya kara haske.

"Na masa magana ka kwantar da hankalinka. Zasu je gobe in shaa Allah"

Wani murmushi yaji ya kwace masa yana sosa kai ya wuce abinshi.

Momma wayarta ta dauko ta kira yaya babba. Dayake dare yayi ta waya tai masa baya nin komai.

Tace masa kome yake yazo da safe su kara tattaunawa.

*

A gidan lukman ya kwana. Baccin shi ya sha hankali kwance.

Fu.ad ma ya samu bacci da nutsuwa ta wani bangaren tunda momma tace masa za.a je ai maganar auren shi da safiyya.

Haka ya kwana mafarkinta.

*

Babu yanda yaya babba baiba ya fahimtar da mama cewar fu.ad din ma duka nawa yake. Amman ina tsakanin da da uwa sai Allah.

Catai ma umarni ne ta bashi bawai neman shawararshi take ba. Haka dole ya shirya suka dauki hanyar bichi shi da haneef.

*

Fu.ad ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake. Ya kagu yaga sun dawo yaji ya ake ciki.

Gashi jibi zai koma. Lukman ya kalle shi yace

"ka soma sakani jiri. Ka zauna waje daya dan Allah"

Dariya yai da tunda yazo lukman baiganta ba.

"Ina ruwanka dani. Wai su haneef sun awa daya da tafiya ko?"

"Ko minti goma basuyi ba"

Zaro idanu yai.

"Ni bana son karya. Kasan ko lukman. Allah ina son ta sosai"

Dariya lukman yai. Tun jiya yake fada musu yana son safiyya kaman wani cikinsu yace karya yake yi.

*

Lokacin da suka isa bichi. Suka aika ai musu sallama da babansu safiyya.

Akace yaje gona. Jin da inna tai sun aiko cewa daga nesa suke kuma magana ce mai muhimmanci ta aika usman ya kira shi.

Cikin soron gidan aka shimfida musu tabarma suka zauna. Harda ruwa aka kawo musu.

Yanda babansu safiyya ya karbe su a mutunce zaka rantse dama can ya sansu.

A nutse babban yaya yai masa bayanin cewar kaninsu yaga yarshi yana so.

Cikin taushin murya yace.

"Allah sarki. Gaskiya mungode kwarai da gaske. Saboda wanda ya nuna ma naka so har abada ya wuce wulakanci.

Sai dai kudin sadakinta yakai wata biyu a hannunmu. Yanzun haka bai shige sati hudu ya rage a daura mata aure ba.

Kuma gashi bata da wata kanwa ballantana"

Wani abu haneef yaji ya kulle a cikin shi. Murya a sake yace

"Yanzun baba babu yanda za.ai a dan duba mana. Wallahi yana sonta matuka"

Murmushi yai.

"Dan nan ka taba ganin inda akai nema cikin nema?  Dama ace ba.a amsa su bane.

Mungode matuka"

Baki haneef ya bude zai sake magana yaya babba ya katse shi da fadin.

"Mungode muma. Ga wannan. Allah yasa hakan shi yafi alkhairi"

Sam baban su safiyya yaki karbar kudin da yaya babba ya bashi. Dakyar daban baki ya samu ya karba.

Suka tashi suka tafi.

*

Tabar mar ya shiga da ita gida. A tsakar gida ya ke nuna ma inna kudin yana labarta mata abinda ya faru.

Safiyya dake daki tana jiyo su. Tanajin baba ya kira sunan fu.ad zuciyarta ta wani doka.

Hade kai tai da gwiwa. Bata san kuma me zatayi ba. Kukane tayi shi harta godema Allah.

Wato saida ya turo neman aurenta gidansu. Taya zata samu ta manta dashi inhar a duk rana yana aikata abinda zai sake zaunar mata dashi.

Kwanciya tai tanajin daman ace duk wannan abubuwan sun farune a wani yanayi na daban.

Saurin kulle shafin dake son hango mata rayuwarsu da fu.ad tayi. Ta shiga na daban.

****

Daman a tsaye yake. Tunda yaya babba ya fara ma momma bayani yake matsawa.

Kwata kwata babu wanda ya kula da fitar fu.ad. Haneef ne yace

"Ba fu.ad nan yake tsaye ba"

Sai lokacin kowa ya kula da baya nan. Kallon kallo suke. Da gudu haneef ya haura sama ya tura dakin shi.

Baya ciki. Sakkowa yai ya fita. Motarshi bata wajen. Baba mai gadi ya tambaya yace ya fita.

Dawowa yai yace musu.

"Mota ya dauka"

"Fara kiran lukman kaji ko tare suka fita"

Wayarshi ya dauko ya kira lukman ya tambaye shi.

"Ina gida wallahi. Baikuma cemun zai fita ba. Ya Salam"

Kashe wayar haneef yai ya girgiza ma momma kai. Cikin tashin hankali tace

"Oh Allah. Wannan wanne irin abu ne"

Haneef ya dauki mukullin motarshi yabiya ya dauki lukman batare daya san inda zasu je nemo shin ba.

Wayarshi yake ta kira sai ringing take yaki dauka.

*

Hankalinshi baya tare dashi harya karasa bichi. Yanajin wayarshi na ihu bashida lokacinta.

So yake yaje ya ga safiyya ya fada mata bafa zata auri wani ba.

Inma ba zata aure shi bane yaji. Inma bata sonshi ne duk zai dauka. Badai zai dauki ta auri wanin ba.

Parking yai nesa da gidansu ya fito. Kofar gidansu ya karasa ya aika yaro a kira mishi ita.

*

Tana kwance abinta. Dan batajin zata iya zuwa islamiyya ranar.

Yaro ya shigo wai ana sallama da ita. Bata kawo komai a ranta ba.

Zatonta Ado ne. Dan yace mata ta duba lambar takalminta ta fada mishi ya manta.

Ta dauka shine ya dawo. Hijabinta ta dauka ta zira takalmanta ta fita.

Wani bugawa zuciyarta tayi ganin fu.ad. Gefe gefenta ta kalla ko wani ya taho. Ko ina na jikinta bari yake.

Muryarta na rawa tace masa.

"Ka tafi kar wani yaganka. Dan Allah ka taimaka ka tafi"

Kallonta yake yana wani saukar da numfashi.

"In bakya sona na yarda. Inba zaki aureni ba na yarda. Amman sofi karki auri wani. Karki auri wani dan Allah"

Ba shi take sauraro ba. Hanya take kallo kar a ganta tsaye dashi.

Kai kawai ta daga mishi..

"Najika. Ka tafi"

Karamar wayar rannan ya zaro ya mika mata.

"Ki karba zamuyi magana"

Kai take girgiza masa alamar a.a.

"Wallahi inbaki karba ba anan zan zauna. Babu inda zanje"

Rufe idonta tai ta bude su. Wannan wanne irine shi cikin mutane. Ta san zai yi abinda ya fada.

Jikinta na bari tasa hannu ta karbi wayar. Batare da tasan me zatai da ita ba.

"ka tafi to"

Kallonta yai sosai. Wayarshi babba ya zaro daga aljihu. Baima tsaya duba yawan kiran da akai masa ba.

Safiyya na kallonshi idanuwa bude. Gabaki daya a tsorace take. Batasan me zai ba ya dago wayar idanuwanshi nakan wayar.

Hotuna yake daukarta. Yasan zai bukace su kodan kwanciyar hankalinshi. Baya son tsoron dake cikin idanuwanta sam.

Ji yake kaman ya dauketa ya kareta daga dukkan abubuwan dake bayyana wannan firgicin cikin idanuwanta.

Wayar ya damtse a hannunshi ya sauke idanuwanshi cikin nata.

"Ba wannan bane karshe sofi. Zan dawo. Zan hada duniyarmu waje daya. Ban damu da rashin dacewarsu ba......."

Bude baki tai ya daga mata hannu.

"In har ba zaki fadi abin da zai sama mun sauki ba kiyi shiru.

Akwai muryarki cike da kaina da maganganun da suke mun ciwo. Ba saikin kara musu abokan zama ba"

Ta nutsu tana kallon fuskarshi. Yanda yake magana. Muryarshi da kominshi.

Tana kallonshi ne saboda yanda zuciyarta ke mata bata son manta shi. Tana son ta dauki hotunan shi da zata adana a zuciyarta.

Yanda take kallonshi yake kallo. Dige digen bakin dake fuskarta yake jin kaman yasa hannu ya gogesu.

So yake yaganta babu su. Yaga fuskarta ita din babu kari ko ragin komai. Da duk wani abu mai motsi a jikinshi yake jin ciwon tafiyar dazai yabarta.

Ya rasa ko menene ke fada mishi zata zama tashi. Yanayi ne ko murya ya kasa fahimta.

Dakyar safiyya ta iya ce masa

"Ka tafi"

Kai ya daga mata ya soma tafiya da baya a hankali.

"Idan na kira ki dauka"

Itama kai take daga mishi idanuwanta kafe akanshi. Takunshi a kasa yake yi amman nauyin shi a zuciyarta take ji.

Tana kallonshi harya juya. Yasa hannuwanshi cikin aljihu ya tafi.

Jingina tai da bangon wajen. Wasu hawaye masu dumi suka zubo mata. Tasa hannu ta goge su tana hadiye kukan ta.

Wayar ta kalla. Batasan ya zatai da ita ba. Danma yar karama ce sosai. Zata iya taita boyonta a jikinta dan bata da abinda zata fada in inna tagani.

Cikin gida ta koma. Taji dadin yanda inna bata ko dubeta ba. Tana ta tankaden garin tuwo.

Daki ta shiga. Ta boye wayar cikin zaninta. Ta hada kai da gwiwa tana sauke wani irin numfashi.

****

Murfin motar ya bude dai dai karasowar motar haneef. Parking sukai. Haneef ya fara fitowa. A fusace yake takowa inda fu.ad yake.

"Babu hankali a jikinka ne? Inma tahowa zakai ba zaka iya gaya ma mutane ba? Haba fu.ad?"

Tunda ya fara fadan idanuwa kawai fu.ad yake binshi dasu. Dan bayajin yana da karfin amsa shi.

Daya tabbatar ya gama mota kawai ya shiga. Ya rufe ya soma kokarin juyawa. Haneef din wucewa kawai yai ya koma motarsu.

Lukman daman bai kai ga fitowa ba ma. Dan baisan me zaice ma fu.ad ba. Damuwarshi daya ko wani abu ya same shi a hanya.

Bin bayanshi kawai haneef yai da motar. Amman dayake wani irin gudu yake. Fintinkau yai musu.

"Dana sani na fito na karbi tukin can"

Cewar lukman da alamun damuwa a muryarshi.

"Allah ya kyauta. Daman ya lafiyar kura....."

Shiru kawai lukman yayi.

***

Duk ranar babu wanda yai ma magana. Kome zakace mishi da idanuwa kawai zai bika.

Fuskar nan babu annuri sam. Garama momma data tambaye shi ko lafiya yake ya amsa mata da babu abinda ke damun shi.

Sundai ki subar shi ya zauna shi kadai. Dole ya kwanta falo har aka dawo sallar isha.i.

Matsa masan da momma tayi da karin bayason ko bakinshi ya bude yai magana yasa ya tura ma cikinshi doya da kwai.

*

Lukman ya zo gidan wajen tara. Sannan suka yi dakin fu.ad din tare. Kwanciyarshi yai yana karatu domin yanada test washegari.

Fu.ad kam number din wayar daya ba safiyya ya duba yai dialing. Zuciyarshi na wani dokawa.

****

Karin tauhid din da akai musu take zauna tana dubawa tunda tai sallar isha.i.

Wani zuuu taji cikin kugunta dai dai inda ta boye wayar da fu.ad ya bata. Da alaman tsarguwa a fuskarta ta dago ta sauke dubanta kan inna.

Hira suje tayi ita da baba da alama ma basu san meke faruwa ba. Wani numfashi ta sauke ta mike.

"Inna sai da safenku. Allah ya bamu alkhairinsa. Usman da yaya sai da safe"

Su usman suka amsata da amin dayi mata fatan tashi lafiya.

Inna ce tace

"Baki ci abinci bafa safiyya. Haka zakije ki kwanta?"

Girgiza kai tayi.

"Ai da yammaci naci abinci inna. Kin manta. Banajin yunwa yanzun"

"To Allah ya tashemu lafiya. Adai yi addu.a"

Ta amsa da

"In shaa Allah"

Wayar bata daina zuu din da takeyi ba. Daki ta shiga. Ta saki labulen. Can karshe ta koma. Ta dauko wayar.

Kallonta takeyi. Irin wayar yayanta ce. Sai dai sabunta ta banbanta su. Zuu din da take ta sake dauka.

Cikin kanta take tunanin yanda ya nuna mata ko da zai tafi gona ko wajen express din shi yabar wayar.

Green ta danna ta kara a kunnenta zuciyarta na wani yawo wajajen da bai kamata taje ba.

Zata iya rantsewa har cikin kunnuwanta tanajin yanda zuciyarta ke dokawa.

*

Karo na hudu kenan daya sake dialing number din. Hannuwanshi har zufa suke da baisan daga inda ta fito ba.

Ji yai an daga. Ya sauke wani numfashi dayake rike dashi.

"Sofi........."

*

Lumshe idanuwanta tai. Tana jin kaman yana gabanta. Bata san me yasa yake ce mata sofi din nan ba.

Badai zatai ma kanta karya ba. Sunan na mata wani irin abu da ta kasa fahimta. Muryarta can kasa tace

"Sai da safe"

*

Kai ya daga kaman tana ganinshi kamun yace

"Thank you. Thanks for picking. Zan sake kira amman ba da wannan number din ba. Kiyi bacci mai dadi. Cike da mafarkina"

*

Bata amsa shi ba ta sauke wayar daga kunnenta. Jikinta ko ina bari yake.

A hankali ta tashi tazo wajen kofa. Labulen dakin ta daga ta leka taga ko su inna sun jiyota. Suna nan zaune inda tabarsu.

Komawa tai. Ta gyara shimfidarta ta kwanta. Cikin kanta take sake dawo da maganganun fu.ad.

Bama saiya wahalar da kanshi na cewar tai mafarkin shi ba. Tasan abune da yake a ajiye.

****

Yana nan kwance har lukman ya fice dan yana da test karfe takwas na safiyar ranar. Dan haka yaima fu.ad sallama. Yasan sanda zai dawo ya koma.

Lukman na fita yai wanka ya fito ya shirya tsaf. Son jin muryar safiyya na damunshi.

Waya ya dauka har ya kai kan number dinta ya fasa baya son taji kaman ya takurata.

Zai iya lallaba zuciyarshi nadan wani lokacin. Instead hotunanta na wayarshi ya bude.

Murmushi ya kwace masa. Hannu yasa ya shafi screen din dai dai fuskarta. Hakan kawai ya saukar masa da nishadi.

Jakarshi yar ta system ya dauka. Ya rigada ya zuba komai da yake bukata a ciki.

Harya sauka kasa da murmushi a fuskarshi. Haneef ya fara karo dashi.

"Wannan murmushin fa?"

Kawai sai yaji wata yar kunya tadan kama shi.

"Ina kwana.... "

Ya fadi maimakon amsa tambayar da haneef yai masa. Zaro idanuwa haneef yai.

Gaisuwar da fu.ad yai masa bakon abune a wajen shi. Banda su momma baya gaida kowa.

Ko yazo ya same su zaune maganarshi bata wuce 'Hey guys'  ko ya kalle ka ya daga maka kai.

Momma ce ta fito kamun ya samu daman tsokanar fu.ad din. Kallon shi tai tace

"Badai tafiya ba?"

Dan sosa kai yai.

"Wlh kam. Ina kwana"

"Lafiya kalau..... Amman dai ka tsaya ka karya ko? Kana lafiya dai?"

Murmushi ya kara fadadawa.

"Lafiya kalau momma. Banajin yunwa. Zan grabbing ko burger ne. Abbah fa?"

Kai ta jinjina tace

"Yana dakinshi"

"Bara inje mu gaisa muyi sallama to..... "

Bai jira amsarsu ba ya wuce. Suna nan tsaye ya fito sukai sallama da momma.

Pha.iza na bacci. Su hassan kuwa sun tafi makaranta. Dan haka haneef ya tafi ya raka shi.

"I mean are you okay?  About...."

Katse haneef yai da fadin.

"Absolutely..... Ion' wanna talk bouh' it"

Bai sake masa maganar ba harya suka kai airport. Sallama sukai da cewar sai sunyi waya, haneef din ya juya da mota......!

No comments:

Post a Comment