Thursday 4 May 2017

AKAN SO 8

   *💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

         08

Lukman ne ya zo gyara kwanciya yaga mutum a zaune. Idanuwanshi ya ware sosai. Ya lalubo wayarshi ya haska.

"Fu.ad?"

Ya kira muryarshi cike da bacci. Dagowa fu.ad yai ya kalle shi da idanuwanshi cike da bacci.

"Ka kwanta mana"

Ya yatsine fuska.

"Bazan iya bacci anan ba lukman. Ga zafi ga sauro. Wajen kuma ya matse da yawa. Just go back to sleep i will manage"

Girgiza kai yai alamar eh. Haneef dake bacci gefensu ya motsa saboda yanajin maganganu sama sama.

"lafiya?"

Ya tambaya yana kare idanuwanshi daga hasken fitilar wayar lukman.

"Fu.ad ne wai bazai iya bacci ba"

Cewar lukman. Wani guntun tsaki haneef yaja. Matsalolin fu.ad yawane dasu.

Pillow kawai ya ja ya sauka daga katifar zuwa kasa. Lukman ma pillow ya dauka ya sauka kasa kan leda.

"Ku dawo bacci ne bazan iya ba. Zafi ga sauro"

Fu.ad ya fadi irritated.

"Ka kwanta malam"

Inji haneef. Girgiza kai yai. Yasan taurin kan fu.ad kaman yunwar cikinshi.

"Lukman tashi mu koma. Dan ubanka karka kwanta"

Baccinsu suka koma suka kyale shi. Shikam daya fara baccin ma farkawa yake. Ga kanshi na wani irin ciwo.

Kan kunnenshi aka kira sallar asuba. Ya tashi su haneef. Abu dayane matsala. Bandakin dazai shiga.

Haneef suka bari dakin suka fita zuwa motar fu.ad din cewarshi zai dauko ruwan dazai alwala.

Suna hanyane yace.

"Damn. Wallahi nabar brush dina. Ban dauko komai ba"

"Karka damu. Sanin halinka yasa na dauko extra"

Numfashi fu.ad ya sauke. Sukaje suka dauko. Suka koma. A bakin shagon sukai brush dinsu.

"haneef fitsari fa nake ji"

"zo ga bakina. Kayi a ciki"

Lukman ya bushe da dariya. Wani mugun kallo fu.ad ya watsa mishi kamun yace.

"wallahi da gaske. Lokacin sallah na wucewa"

Cikin shagon haneef yakoma ya kira khalid mai shagon. Ya tambaye shi ko da akwai bandaki kusa sannan ya fito.

"Saika taso"

Ba musu ya tashi ga mamakinshi cikin shagon suka koma. Haneef ya bude wani kofa da duk zatonsu wadda zata kaika cikin gida ce.

Ban dakine dan matsakaici. Shafe da siminti. A bushe yake tsaf. Bokitin karfe a gefe sai kwandon soso. Sai masai irin namu na gargajiya da murfi a rufe.

Wani baya fu.ad yai yana bata fuska kaman zaiyi amai.

"Karka cemun anan zanyi fitsari"

Takaici ya hana haneef magana. Fita yai yabar masa shagon. Ya fito ya samu lukman yace.

"Seriously kana kokari. Ya kake baka fasa bakin fu.ad ne?"

Dariya lukman yai ya girgiza kai. Suna nan fu.ad din ya fito fuskarshi a yamutse.

"Allah ya kiyaye in ban kwashi infection ba. Ina komawa gida zance asibiti a mun check ups"

Fu.ad ya fadi yana samun wani dutse ya zauna zaiyi alwala.

"Asibitin murtala ka kwasa ba infection ba"

Haneef yace yana masa kallon ka kure rainin hankali.

Wannan karon harshi fu.ad din saida ya dara. Tare sukaje asuba suka dawo.

Fu.ad nason yadanyi gudu ko ya yake. Nan fa shi dole saiya cire dogon wandon shi yabar gajere da singlet.

Ba yanda haneef baiba tunda baizo da kayan gudu ba. Ko yaje dana jikinshi ko ya hakura yaqi.

"Idan baka kwashi infection a bandakin nan ba. Zaka makalo a jikinka ne"

Lukman ya fadi. Ai ba shiri ya dauki kayanshi ya maida yace ma lukman suje. Tare suka fita gudun.

Sun sami wajen awa daya. Dan gari ya fara wayewa. Mike hanya kawai sukai. Dan ma lukman na dan taba kwallo lokaci lokaci. Duk da haka s yana ce ma fu.ad yadan rage gudu.

Fu.ad yaji takalminshi yadan kwance. Dan haka ya tsaya ya gyara. Lukman yake ma dariya dayai ma nisa.

Tsayawa yai yana jiranshi. Kaman daga sama yaji saukar wani ruwa mai danqo danqo tun daga wuyanshi har bayanshi.

Wani numfashi yaja na mamaki. Lokaci daya wani bacin rai ya maye gurbin mamaki.

"What the hell!!!......"

A fusace ya juya ya sauke idonshi kan yarinyar dake tsaye kofar gida da wata tukunya da bayanta ya gaji da yin baqi.

Yanayin fuskarshi kawai ta kalla tace.

"Na shiga uku ni safiyya. Wallahi banganka ba"

Ta fadi tana zaro idanuwanta.

Baisan me ya kamata ya fara yi ba. Gaba daya gefenshi a jike yake. Ruwan koma menene har cikin sumarshi da yake bala.in ji da ita.

Har gefen fuskarshi. Da tashin hankali lukman ya karaso yana rike baki.

"Fu.ad......"

Ya kira da alamomi da dama. Ban hakuri. Tsoro da jimamin abinda zai auku tun kamun faruwarshi.

Takawa fu.ad ya soma yi zuwa inda yarinyar take. Numfashi yake ja yana fitarwa. Yana kokarin calming kanshi.

Idanuwanshi harsun kara hasken nan da sukanyi idan ranshi yakai karshe wajen baci.

Lukman ya riko masa hannu yana fadin.

"Please fu.ad......."

Kwace hannunshi yayi. Ganin datai ya tunkaro ta har yana gab da ita yasa ta tura masa tukunyar.

Da sauri ya rike tukunyar da ta rigada ta gama lalata masa gaban riga. Cikin gida ta kwasa da gudu.

*

"Innaaaaaa!"

Take kira da tashin hankali. Sanin cewar safiyya bamai kwaramniya bace ba. Yasa inna fitowa da sauri dan taga ko lafiya.

Bayanta safiyya ta labe tana sharar hawaye.

"Ke wai lafiyarki. Meya koro ki?"

Inna ke tambaya tana kokarin janyo safiyya daga bayanta.

*

Ganin fu.ad rike da tukunya a hannu yana danna kai gidan mutane yasa lukman riko shi.

"Fu.ad gidan matan aure ne fa. Dan Allah kayi hakuri kazo mu tafi"

Juyowa yai da tukunyar a hannu.

"wallahi ko ka sakeni ko in kafta maka tukunyar nan. Like hell inyi hakuri"

Ganin ran fu.ad ya gama bi yasa lukman sakinshi. Yasan ba.a tempting maganar shi. Tsaf zai kafta masa wannan bakar tukunyar.

*

Inna nata kokarin banbaro safiyya daga bayanta amman ina. A banza sake makalewa take tana share hawaye.

Tafiya inna taji data sata kallon shigowar fu.ad rike da tukunya da hannuwa duka biyu.

Ga rigarshi da take fara kal ta gama tashi daga aiki. Jikinshi daga gefe rabi a jike.

Dafe kirji inna tai.

"Na shiga uku ni lami. Safiyya badai ruwan dan waken bane kikai masa wanka dashi???"

Tukunyar fu.ad ya ajiye a kasa. Yana kare ma gidan kallo. Gidan kasane na asali ma kuwa.

ko shafe babu a kasan gidan. Kaurayen langa langa. Duk da tsaf yake babu shara. Akwai komatsai cikin gidan.

"Dan Allah dana kayi hakuri"

Inna ta fadi a raunane. Dan kallo daya zakaima fu.ad kagane hutu da kudin dake tattare dashi. Ga wata isa da gadara dake fita daga jikinshi kaman hayaqi.

Daga ma inna hannu yai.

"Karki sake hada sunanki da nawa a waje daya. And bake kikaimun laifi ba. Yarki ce da take labe bayanki. Hakurin daga bakinta nake son ya fito"

Kallon shi inna take baki a sake. A ranta tace safiyya ta janyo musu bala.i. Wannan tsageran kuma ko daga ina ya fito oho.

Da alama dai bako ne a garin dan ko kala kalarshi bata taba gani ba. Safiyya ta fisgo.

"Bashi hakuri...."

Hawayenta safiyya ta share. Ta sauke idanuwanta cikin na fu.ad. Ta kasa magana saboda tunda take sau daya ta taba ganin mai irin idanuwanshi.

Shima aikenta siyan ruwan sanyi akai da azumi gidan malam.mudi ta samu suna kallo. Aka nuno wani bature har tana mamakin kallar idanuwan.

Kallon da take masa yasa shi yaji wani iri. Lokaci daya yaji abinda bai taba ji ba a zuciyarshi.

Wani squeezing yaji tayi har numfashin shi na son tsayawa. Idanuwanshi ya lumshe dan wani abu dake fizgarshi cikin nata.

Dai dai shigowar lukman dayaga shirun yai yawa kar ace wani danyen aikin lukman yayi. Dan yasan kadan da aikin shi.

Inna lukman yace ma.

"Ina kwana"

A mutunce ta amsa ta dora da.

"Yaro dan Allah kuyi hakuri. Wallahi safiyya bamai kwaramniya bace na tabbatar da kuskure ne"

Hannun fu.ad da yake tsaye kamar an dasa shi lukman yai. Tunda har Allah ya tsare baiyi wani rashin mutuncin ba.

Fu.ad kam duk wani rashin mutuncin dayai niyya yanajin shi yana narkewa. Saidai koma menene ba.a masa laifi a tafi a banza.

Fisge hannunshi yai yace.

"Sai tabani hakuri. Wallahi sai taban hakuri"

Da sauri safiyya ta sauke idanuwanta daga cikin nashi jin maganar dayayi. Wani yanayi take ji. Kaman zazzabi ya kamata.

Muryarta a sarke ta tsugunna gaban fu.ad tace.

"Ka...ka kayi hakuri dan Allah"

Sanda ya shigo gidan yai niyya ta ja ma kowa. Duk sai an kulle yan gidan. Saiyai rashin mutuncin da basu taba tunani ba.

A karo na farko a rayuwarshi dayaji ya kasa abinda yai niyya ya kuma rasa dalili.

Hannu yasa yadan daki goshin shi. Yana son koma menene ya same shi ya warke. Dan ji yai tsugunnawar da safiyya tai mishi baya so.

Har lukman ya zaro wayarshi daga aljihu zai kira haneef. Fu.ad ya kalle shi yace

"Muje please"

Ba musu lukman ya dauki hanyar waje. Dan gaji yake idan ya tsaya fu.ad zai iya sake shawara.

Suna fita ya mike hanyar da suka biyo da gudu ba tare da ya waigo yaga ko lukman na biye dashi ba.

Wata hamdala lukman yake jerowa dan har ya gama hango su ana rikici a police station. Shi kanshi mamakin abinda ya faru yake.

Sai kuma ya tuna yanda fu.ad yake rike da tukunya. Mai zaiyi inba dariya. Hanya ya mika yana sassarfa yana shan dariya.

*

Babu ko sallama haneef yaji an turo kofar shagon. Kallo daya yaima yanayin fu.ad ya mike da hanzari yana fadin.

"Ya Rabb. Fu.ad me ya same ka haka?"

Cikin wani sanyin murya ya tsinci kanshi da fadin.

"safiyya ce ta watsamun ruwan dan wake"

"Ruwan dan wake? Safiyya?"

Haneef ya tambaya yana son ya gane ma.anar maganar fu.ad. Sake kallonshi yake daga sama zuwa kasa.

"Gaban rigarka kuma fa?"

Ya tambaya yana kallonshi sosai.

"Tukunyar dan waken ce ta mikomun"

Abin yai yawa. Wata irin dariya haneef ya kwashe da ita harda hawaye. Sai da ya samu waje kan katifa ya zauna ya dafe ciki yana dariya.

Lukman ne ya shigo da sallama. Kallon fu.ad da yake tsaye yai cuku cuku yake. Ya maida kallonshi ga haneef da ya kasa controlling dariyar da yake.

Gefe ya zauna ya tusa tashi. Da sun fara dainawa suka sake kallon fu.ad sai su kwashe da wata dariyar.

Tsaye yake yana kallon su. Abin ma ya wuce na takaici. Murmushi kawai yai ya juya musu baya yana kwance takalmin shi.

Dakyar fu.ad ya iya controlling kanshi yace.

"Wanne police station yan gidansu suke?"

Yana mikewa dan yasan dole yaje solving rigima.

Girgiza masa kai lukman yai yace.

"Ba abinda ya faru fa......."

A nutse ya gaya masa duk yanda sukai. Da tsananin mamaki ya kalli fu.ad da yake tsaye daga shi sai boxers yasa rigar daya cire yana goge gashin kanshi yace.

"Who are you and ina ka kaimun kanina?"

Rigar dake hannunshi ya jefa ma haneef daya cabe ta yana dariya.

"But guess what. I am proud of you. Like sosai little one. Yau kaine da hakuri?"

Murmushin da ba ko yaushe yake yi ba yaima haneef saboda wani rawa zuciyarshi take yi har yanzun.

"In kun gama dariyar wanka nake sonyi. And lukman ka dauko mun kaya a mota"

Lukman da yanayin maganar fu.ad bai dame shi ba ya daga kai kawai alamar yaji. Dan inda sabo ya saba da yanda yake magana cikin gadara.

"Yan gidan nan suna da karamci. Ga ruwa nan ansa an jawo mana. Kai amfani da bokiti daya kabar ma lukman daya"

Haneef yai masa bayani. Wani kwalo idanuwa yai waje. Ya taka a hankali ya tura bandakin yaga ruwa a bokiti.

Tunda yake a rayuwarshi banda dazun da asuba baima taba shiga irin wannan bandakin ba. Baima san yazai fara wanka da ruwa a bokiti ba.

Juyowa yai ya kalli haneef.

"Dame zanyi wankan?"

Daure fuska haneef yayi yace.

"Wannan ruwan na bokiti. Ka watsa kawai tunda bamu dauko sponge dinmu ba. Yau zanje gida nima in dauko kaya sai in taho dashi"

Girgiza kai fu.ad yake alamar ai shifa bai yarda ba.

"Ni momma nake son magana da"

Ya fadi yana kallon haneef da lukman a lokaci daya kaman wani yaron da akaima laifi yake neman mamanshi ya gaya mata.

Ganin sun banza sun kyale shi yasa shi shiga bandakin yana doko yar kofar langalangar kaman zai karya musu ita.

Hada idanuwa sukai shida lukman suka sake bushewa da dariya.

No comments:

Post a Comment