Thursday 4 May 2017

AKAN SO 11

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

               11

Hannu tasa ta goge hawayen da suka zubo mata.

"Safiyya da baki mare shi ba"

Wani guntun murmushi tai da baikai zuciyarta ba. Tana jin yanda komai ya kwance mata.

Tun dazun ta kasa manta shi. Data rufe idanuwanta shi yake mata yawo. Ta kuma rasa dalili.

Bata taba zaton zata sake ganin shi ba. Saboda bai mata kama da yan garin ba.

Dakyar ta iya samun yar nutsuwar da tace.

"Babu wanda zai daga hannu ya mare ka a gaba kawu"

Girgiza kai yayi yace.

"Yanayin shi dan masu shine. Ina gudun abinda zaije ya dawo bakiga yanda ya tafi a zuciye ba"

Ita kanta ta tsorata sosai da yanayin dataga ya tafi dashi. Tana jin maganar shi dayai mata kamun ya tafi

"Fu.ad. Sunana fu.ad dan ina son kisan sunan mai fuskar da kika taba. Kisan sunan wanda kika taro ma dangin ki rikici dashi"

Wasu hawayen suka sake zubo mata. Ta sa gefen hijab dinta ta goge su.

"Bara in shiga gida kawu."

Ya jinjina kai sannan yace.

"Allah yai miki albarka. Nagode safiyya. Allah ya jishe mu alkhairi"

Ta amsa da amin tana shiga gida. Yanayinta inna ta kalla tace

"Lafiya safiyya?"

Abinda ya faru ta zayyano mata. Inna tasa salati.

"Ni maryama meke faruwa damu ne haka. Yau dan uwanki ya sha dakyar hannun yan sanda ke kuma kina son janyo mana wani rikicin?"

Murya can kasa kasa tace

"Inna kawu fa ya mara. Kuma shine bashida gaskiya. Ina wajen tsaye komai ya........ "

Harara inna ta watsa mata tana katse da fadin

"Rufemun baki. Shine me? Kema da nake gani da hakuri kin fada daukar halin dan uwanki ko?"

Wasu hawaye taji suna bi mata fuska

"Kiyi hakuri inna. Bazai sake faruwa ba in shaa Allah"

Safiyya ta fadi tana mikewa. Inna ta kalle ta tace

"Allah shi kyauta. Ina kuma zaki?"

Rausayar dakai tai. Muryarta a sanyaye tace.

"Makaranta wai ko addu.ar tashi in samu"

"Ai saidai ki hakura yau tunda yamma tayi sosai. Ki zauna ki tayani karasa tuwon nan kawai"

Hijabinta ta cire ta amsa inna da to. Tana shiga daki ta ajiye ta fito suka shiga hidimarsu tare.

****

Yana karasawa wajen motarshi ya bude ya shiga ciki. AC ya kure ya dora kanshi kan abin tuqi.

Numfashi yake mayarwa. Yarinyar nan tayi babban kuskure. Bazai saurari bangaren zuciyar shi dake kokarin tausar shi ba.

Bazai saurare shi ba saboda tsakanin safiyar yau da yammacinta wani abu ya samu matsala a ciki.

Wani abu ya kwance a cikin zuciyarshi da baisan yanda zai ya gyara ba. Kamun koma meye yaci galaba a kanshi ya zaro wayarshi.

Hamza ya kira. Kamun lukman da haneef da zuciyarshi su hanashi ya kira hamza.

Ringing din farko ya dauka hadi da fadin.

"Moh.... "

Bai bata lokaci yace

"Ina bichi hamza. Inason kome kake kai dropping. I will pay you. Mota uku nake so ta yan sanda. You call me inkun karaso. Ion' care how much it will cost and be fast"

Bai jira amsar dazai bashi ba ya kashe wayar.

Sauke kujerar yai sosai ya kwantar da bayanshi yana lumshe idanuwanshi.

Marin yana dawo mishi kaman lokacin akai komai.

*

*One hour later*

Zaune suke wajen zaman makokin suna ta hira abinsu.

"Nikam ka karasa kallon The 100 kuwa?"

Girgiza kai haneef yai yace.

"Ni zaman makoki nake fa."

Dariya lukman yai.

"Zaman makokin wa?"

Ya tambaya. Haneef na dariya yace

"Finn mana"

Dariya sukai su duka kamun lukman yace

"Koni fa naji haushin mutuwar finn. Wannan banzar clark din haushi take ban wallahi. Nafison Octavia"

Tabe baki haneef yai hadi da fadin.

"Octavia broke my heart. Ina son shegiyar taje ta zabi Lincoln"

Wata dariyar suka sake yi tare. Haneef ya fara jin jiniya kaman ta yan sanda. Ya juya ya kalli lukman shima da alamu yaji.

"Ina fu.ad?"

Haneef ya tambaya yana kallon lukman. Mikewa yai daga kishingidar dayai yana dauko wayarshi.

"Damn it. Chargy na ya dauke. Goddammit lukman call him yanzun nan"

Lukman jikinshi har kyarma yake. Ya lalubo wayarshi yai dialing number din fu.ad.

Wayarshi a kashe take. Sake trying yai. Still a kashe. Ya kalli haneef ya girgiza masa kai.

Mikewa haneef yai. Da gudu gudu ya dauki takalmin shi. Lukman nabin bayanshi.

Pha.iza suka ci karo da ita ta fito daga cikin gida. Kallo daya tai musu tace

"Lafiya kuwa?"

Girgiza mata kai haneef yai yace.

"Lafiya kalau. Ki ajiye wayarki kusa dake dai"

Lukman pha.iza ta kalla tace

"Yaya lukman me ya faru?"

Shiru yai baice komai ba. Zuciyarshi dokawa kawai take.

Haneef ne yace mata

"May be fu.ad ne. We are not sure yet. Zamuje mu duba mugani"

Dafe kai pha.iza tai. Bata kawoma ranta wani abu bane ya samu fu.ad. Yana fadar haka ta soma addu.a Allah yasa ba wani bane ya haye masa.

Tasan yana yawan shiga rikici. Wasu su sani wasu kuma haneef da lukman su boye musu.

"Zan biku please"

Haneef ya soma girgiza mata kai lukman yace.

"Ta biyo mu please. Inhar abinda nake tsoro ne ya faru. We need all the help we can get"

Tare da pha.iza suka tafi. Saida suka fara duba fu.ad ko zasu ga motarshi wayam wajen yake.

Motar haneef suka dauka suka mike hanya. Batare da sun san ina  zasu fara neman fu.ad din ba.

****

Ruwan take ja amman zuciyarta bata mata dadi. Ga wani irin yanayi tana ji kaman wani abu zai faru dasu.

Kaman daga sama taji muryar babansu yana.

"Safiyyaaaa"

Da hanzari ta karasa janyo gugar daga rijiya. Ko juye ruwa. Batai ba ta ajiye ta tana nufar hanyar soro data jiwo muryarshi.

Iccen dake kanshi ta kama mishi suka sauke tana fadin.

"Sannu da zuwa baba. Ruwa nake ja shisa ban jika ba"

Murmushi yai mata yana fadin.

"Baki je makarantar bane yau?"

Gabanta taji ya yanke ya fadi. Ta bude baki zata amsa shi. Jiniyar yan sandan da suke ji nesa nesa ta matso kusa.

"Oh Allah dai yasa lafiya. Tun dana taho nakejin kukan nan kaman motar asibiti kaman ta yan sanda"

Safiyya ta amsa da.

"Amin dai baba. Nima naji. Allah yasa ba gobara bace"

"Allah sarki. Amin kuwa. Kauda itacen nan gefe mana. Ko ki dora su saman na jiyan can dana kawo"

Iccen ta tsugunna ta fara shirin dauka kamun suji kukan kaman cikin gidansu ake yin shi.

Fasa daukar iccen tayi ta dago kai ta kalli baba dake tsaye fuskar shi dauke da mamaki.

"Bari in......... "

Bai karasa ba yar sanda mace ta shigo ko sallama babu.

Bata ko bi takan baba da safiyya dake rafka salati ba.

"Ku shigo"

Yar sandar ta fadi. Wasu guda hudu ne suka shigo maza. Cikin rawar murya baba yace

"Subahanallahi. Lafiya kuwa?  Meke faruwa..... "

Alamun sungane me yake nufi basu nuna bama ballanta na suyi yunkurin amsa shi.

Cacumar shi sukai kaman barawo suna janshi yana turjewa sukai waje dashi.

Safiyya data ruga cikin gida yar sandar na bin bayanta ke kiran.

"Inna mun shiga uku. Innaaa yan sanda sun tafi da baba"

Da gudu inna ta fito daga daki tana gyara daurin zani. Hannunta dana safiyya yar sandar ta kama ta a jansu suna kuka har kofar gida.

Lokacin unguwar harta cika kaman zata fashe. Mutane tsaye cirko cirko suna kallon ikon Allah.

Wasu kuma na tambayar me Malam audu zai aikata haka har yan sanda mota uku.

Dan kowa yasan halayyar shi. Mutum ne mai fara.a ba.a taba ganin yai rigima da kowa ba.

Safiyya dake wani irin kuka tana kokarin kwace hannunta daga rikon da yar sandar tai mata.

"Me mukayi muku? Me......... "

Cik maganarta ta tsaya mata a wuya ganin fu.ad jingine da mota. Kayan dazunne a jikinshi. Saidai fuskarshi sanye take da wani baqin gilashi na rashin mutunci.

Wani karfi taji yazo mata. Ta ture yar sandar. Da gudu tana kokarin karasawa inda fu.ad ke tsaye wasu yan sanda suka sha gabanta.

Cikin isa da iko yace.

"Allow her wasu cikin ku su tafi da wancen mutumin gidan kawunta ku tattaromun kansu gaba daya. Bance kubar ko jariri ba"

Suna bata hanya ta karasa. Tsugunnawa tai gabanshi. Kuka take kaman zata shide.

"Dan Allah..... Dan..... Dan girman Allah ka sake su. Ni... Ni nai maka laifi. Ni zaka hukunta"

Wani rawa yaji zuciyarshi nayi. Glass din idonshi ya sauke. Ya kafa idanuwanshi kan safiyya dake durqushe gabanshi tana kuka.

Gaskiya ta fada. Rikicin shi tsakanin ita da shine da kuma kawun ta.

Sai dai yanda yakejin wani yanayi na saukar masa da kasala ya tabbatar masa ita bazai iya hukuntata ba.

Bakuma zai yafe hannun data daga mishi ba. Ba halin shi bane a taka shi a bashi hakuri ya hakura. Ba halin shi bane a roke shi ya amsa.

Yana da tabbacin abu dayane.  Za.a taba kowa banda ita. Zai tabbatar da marin shi ya fita a jikin duk wani wanda ta damu dashi.

Wani numfashi ya sauke yana cije leben shi na kasa. Kallonshi ya maida kan yan sandan da tuni sun tura inna bayan mota.

Baba kuma an tafi dashi aje a dauko su kawu.

Da ido ya kira yar sandar data riko inna.

"Bana son ganinta. Don't touch her. Ki hadata waje daya da mahaifiyarta"

Babu musu ta cacumi safiyya. Rike masa kafa tai tana rushewa da kuka.

"Na shiga uku ni safiyya. Dan Allah ka rufa mana asiri. Ka kyalemun su inna. Ni kome zakai mun kayi mun. Ni nai maka laifi basu ba"

Tsugunnawa yai yasa hannu ya banbare yan yatsun safiyya yana fadin

"Let go of me........."

Tureta yai yar sandar ta cumimiye mata hijab ta jata tana ihu.

Wani irin abu yaji kirjinshi nayi. Kai yake girgizawa saboda baya son me yake ji.

Sam baya son abinda yake kokarin faruwa.......!

No comments:

Post a Comment