Thursday 4 May 2017

AKAN SO 36

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

          36

*Dukkan mai rai mamaci ne! Allah ka kawo mana sauqi cikin tamu tafiyar. Page din nan ya tabani fiye da tunaninku*

Yana so ya bude idanuwanshi ya kasa. So yake ya kwace daga inda tunanin shi keson janshi.

Ya kwammace ya ziyarci ko ina banda nan. Banda ranar farko da ya karbi abinda ya rusa mishi rayuwa. Saidai ya zamana bashida karfin komai.

Bashida karfin fisgewa daga riqon da koma menene yai mishi. A hankali ya bayar dakai. Ya daina kokarin kokawar da yakeyi.

Ya bari koma menene ya dauke shi yaja shi inda yake son kaishi.

****

*Nawaf in ss3*

"Nawaf ka cika tsoro wallahi. Wannan yafi komai daka taba trying bada kalan charge din da ake buqata"

Girgiza kai nawaf yayi yana kallon awwal hadi da fadin.

"Nifa Codien din nan ma ina so inbari ne. Na kasa kar a gane a gida"

Dariya sosai awwal da haroon suke mishi. Kamun haroon yace.

"Kaban dariya maza. Saikace wani karamin yaro. In zaka ja kaya kaja kaya kawai"

Ajiyar zuciya nawaf ya sauke. Yana tsoron karban kwayoyin dake hannun awwal dan baisan kalar karfinsu ba. Codien dinma dan ya zamana kowa a ajinsu yana sha.

Kullum kallon karamin yaro suke mishi. Shine abinda ya fara jan hankalinshi. Shekara daya kenan ya kasa dainawa. Sam baya jin dadi inhar bai sha ba.

Dafa kafadarshi awwal yayi. Yana mika masa kwayoyin dake hannun shi.

"Ka karba. Ba zakai dana sani ba. Duka kwana nawa ya rage mana mu karasa jarabawar mu?  Wannan ne lokacin holewa"

Dariya haroon yayi.

"Kaman kasan yau akwai clubbing ba"

Karban kwayar nawaf yayi. Yasa a aljihu ya wuce yabarsu nan. Dan yaga lokacin sallah yayi. Ba damuwa sukai da suyita ba.

Shikam in akwai abinda ya tsana bai wuce wasa da sallah ba. Ko da lokacin sallah baiba shi bazai zauna ya saurari shirmensu kan mata ba.

Har addu.a yakanyi. Allah ya kare mishi zuciyarshi daga zina. Shan codien wani abune daban. Amman zina na daya daga cikin manyan laifukan da baya so ya hada shi da Ubangijinsa.

*

Wannan rana itace ta farko da nawaf ya fara shan kwaya. Abin bai tsaya iya nan ba. Kamun su gama makaranta saida ya zamana har cocaine suna sha.

Alh. Haladu shine mahaifin nawal. Dan kasuwane da yaranshi hudu duk maza da suka haifa da matarshi haj. Asiya.

Kabir, khamis, Ibraheem sai autansu nawaf. Tarbiya dai dai misali sun yi kokarin baiwa yaran nasu. Nawaf ne kawai kaddara ya rubuta musu.

Ibrahim shiya fara gane nawaf din na shaye shaye. Kuma shiya sanar da mahaifiyarsu. Lokacin yagama jarabawarshi ta waec da neco. Babu iya kokarin da basuyi ba na ganin sun rabashi dasu haroon.

Amman ina. Hakan yasa su yanke hukuncin su turashi karatu England. Haka kuwa akai. Saidai wannan ya zamana babban kuskuren su.

Dan abin harya so ya taba mishi kwakwalwa. Lokaci da dama zai dinga abubuwa kaman marar hankali.

Maimakon ya zama silar shiriyar nawaf kaman yanda suke tunani saiya qara zama sanadin lalacewarshi. Dakyar ya kammala karatun shi ya dawo gida nigeria.

Rayuwa taci gaba da tafiyar musu. Saboda Alh. Haladu yasan mutane da dama. Yasa nawaf samun aiki a wani company da suke atamfofi.

Yana zuwa aiki. Ga biyayya kaman me. Saidai shaye shayen kawai. Duk da dawowarshi nigeria yasa sun sake jonewa dasu haroon bai sauke mishi aqidarshi ta kin son kusantar zina ba.

Har lokacin daya hadu da Nuriyya. Ita ta soma dauke hankalinshi daga shaye shaye. Kamun daga bisani wata irin soyayyarta ta shige shi.

Tasan matsalarshi. Hakan baisata kyamatarshi ba. Domin shi yana da asali koda kuwa a cikin rijiyar giya yake kwana ya wuce gori.

Nuriyya ta soma zama silar shiriyar nawaf. A hankali har iyayenshi suka san da ita. Da gudu suka karbeta. Babu kyamata babu komai.

****

"Nawaf........"

Yanajin muryar Ibrahim yana kiranshi sama sama. Bama tashi kadai ba. Ta mutane da yawa.

Muryarsu yake ji cikin kunnuwanshi amman nuriyya yake gani a zuciyarshi.

"Nuri...."

Ya fadi. Ibrahim dake bakin gadon ganin bakin nawaf yai motsi yasa shi kara matsawa da sauri yana kasa kunne.

Su mama kam banda kuka babu abinda sukeyi. Dan harsun rigada sun hakura da nawaf. Yakai awa biyu da kawowa asibiti kamun a samu zuciyarshi ta ci gaba da bugawa.

"Nuri...."

Ya sake fada wannan karin da dan karfi. Khamis dake tsaye ibrahim yaima nuni da su kira likita. Da saurin shi yaje ya taho dashi.

Zuwa yai ya sake duba nawaf. Suna tsaye cirko cirko. Bai bude idonshi ba. Banda Nuri da bakinshi ke kira babu inda ke motsi a jikinshi.

Doc din ne yake tambayarsu ko wacece Nuri. Ibrahim ya amsa shi da cewar matarshi ce.

"Ku kirata. Ku kirata da sauri......"

Cewar likitan yana ma nawaf din wata allura kamun ya fita. Su dukansu ibrahim suka zuba ma idanuwa.

Tashi yai jiki a sanyaye ya fice daga dakin yana ja musu kofar. Wayarshi ya dauko ya lalubo number din nuri yai dialing........!

****

Yana zaune ya zuba ma sarautar Allah ido doc da nurse din suka fito. Doc din ya dafa farhan yace ya biyo shi.

Babu musu ya tashi ya bishi har office din. Sosai yake kallon farhan.

"Nasan wannan ba hurumina bane. Saboda Allah me matarka zatai maka kai mata wannan dukan?"

Wani daci farhan yaji cikin zuciyarshi. Cike da qunan rai yace.

"Hakane kam. Ya take?"

Baison kallon da likitan yake masa. Duk da yana son fada mishi bashi bane ba. Gara Allah ya dauko rayuwarsa daya gwada masa rabar dazai daga hannu akan mace.

Kaman yanda ya fada. Ba huruminshi bane ba. Yan rubuce rubuce yayi a takarda sannan ya mikama farhan din hadi da fadin.

"Ka siyo wannan magungunan yanzun. Inka shiga dubata taci wani abu sannan a bata"

Karba yai ya mike hadi da fadin.

"Nagode"

Bai kula shi ba. Shima bai damu ba ya fice. Kai tsaye pharmacy ya wuce ya siyi magungunan da aka bashi sannan ya koma zuwa dakin da aka kwantar da Nuri.

Duk da gadaje uku ne cikin dakin. Ba kowa sai ita kadai. Da dori a hannunta daya karye. Kallo daya farhan yai mata ya sauke idanuwanshi.

Baya son sake kallonta saboda ji yake yana son shakare nawaf. A hankali ya karasa inda take yaja kujera ya zauna.

"Sannu"

Idanuwanta ta dago dakyar saboda nauyin da take jin sun mata. Cike suke da hawayen dasu basu zubo ba. Su basu koma ba. Cikin sanyin murya tace.

"Inajin kaman wani abu ya faru dani daban sani ba"

Kallonta yai. A tausashe yace.

"Banda wannan akwai wani abu dazai faru dake?"

Daga kafadu tai alamar itama bata sani ba. Takai hannunta mai lafiya tana goge hawayen da suka tarar mata cikin idanuwa.

"Koma menene yana da girma. Saboda ina jin shi har raina"

Sauke numfashi farhan yai. Baisan amsar daya kamata ya bata ba. Saboda haka yace.

"Me zakici? Ance kici wani abu sannan kisha magani"

Ita kam batajin tana son cin wani abu. Banda jin da take wani abu ya faru da ita. Ga nawaf ya mata tsaye a zuciya.

Ta so nawaf. Tana son nawaf. Saidai tana jin tsoronshi sosai. Bayan abinda ya faru yau. Bai barta da wani zabi ba.

Wayarta dake hannun farhan ta soma ringing. Kallon juna suke. Ya zaro wayar daga aljihunshi ya mika mata.

Gani tai yaya ibrahim ne. Gabanta ya yanke ya fadi. Allah kadai yasan abinda zai faru yanzun kuma. Tasan wajen shi nawaf yaje.

Wani irin tsoro ya cika mata zuciya. Idan nawaf yaji tabiyo farhan bata san me zai faru ba. Hawayen da suka zubo mata tasa bayan hannu ta goge.

Wayar ta yanke. Kamun ta sake daukar wani ringing din. Kallon ta farhan yake. Shi bai isa ya tayata yanke hukunci ba. Duk kuwa yanda yake so.

Sakata tai a silent. Tana jujjuya wayar a hanunta kanta a kasa tace.

"Shekarar mu daya da wani abu da aure. Babu wanda yamun dole. Ina son shi saboda ya taimake ni kaman yanda kaimun.

A kasan duk wannan dukan nawaf na da halayya me kyau. Yana da zuciyar da kowacce mace zata so......"

Shiru tadanyi. Dan batama san dalilin dayasa take wannan maganganun ba. Kawai tana jin ya kamata taima farhan don bayani ne. Ta so shi shima. Son shi dabanne dana nawaf.

Tana son ya fahimci tana son mijinta har yanzun. Tsoron shine yake son girmar son. Wasu hawayen suka sake zubo mata dataga kiran yaya ibrahim na sake shigowa kamun tace.

"Yana da matsala. Yana shaye shayen manyan kwayoyi kamun aurenmu.

Yabari na wani lokaci kamun satika biyu da suka wuce. Ban tabbatar ba amman naga alamu ne kawai.

Yana bukatar taimako. Yana bukatata nikuma......nikuma kaganni anan"

Murya a dake farhan yace.

"Kalle ni nan Nuri. Ba ina son yanke hukunci bane. Ko in nuna nafi karfin kaddara ko makamancin hakan.

Komenene dalilinshi. Ko menene naki. Babu amfanin zama da namijin da yake miki wannan dukan. Shi ya baki rayuwa?"

A hankali ta girgiza mishi kai.

"Saboda me zaki mika mishi ita yai yanda yaga dama? Saboda kina jin cewa ya miki taimako?"

Sai lokacin ta dago kai ta kalli farhan.

"Ina zanje? Gidan magajiyar karuwai da abin dariya itace mahaifiyata?"

Dafe kai farhan yayi cikin hannuwanshi yana girgiza kai. Baisan ta inda zai fara mata bayani ba.

Sai yanzun datai wannan maganar abin ya fado mishi. Ta ina zai fara gaya mata lokacin dayaje aka fada mishi tayi aure bashi bane kawai labarin daya samu?

Wayarta ta sake kallo. Message ne ya shigo. Hannunta na rawa ta cire wayar daga key. Ta bude message din.

"Nasan abinda zaisa ki tafi ba karami bane Nuri. Bansan me zance ba. Ko ta ina zan fara. Dan Allah kizo......."

Bata karasa karantawa ba farhan yace mata.

"Ba ita ta haifeki ba Nuri. Baki da alaka ta jini da ita ko kadan......"

Cikin kunnuwanta take jin maganar na mata wani irin yawo. Tana son fahimtar abinda maganganunshinke nufi. Idanuwanta kafe kan screen din wayar.

"Accident da nawaf"

Tagani cikin sentence daya da suma ta kasa fahimtarsu. Sosai ta bude idanuwanta kan screen din wayar. Kalma ukku kacal take ganewa.

Sunan asibitin. Nawaf da kuma hadari. Kamun wani abu ya yamutsa cikin cikinta. Jiri take ji yana dibarta daga zaune. Dakin na wani irin juyawa.

Hannu takai ta na dafe kanta hadi da rintsa idanuwa. A razane farhan yace.

"Nuri!!!"

Sama sama take jinta. Wani irin yanayi ne da wanda ya san tashin hankali kadai zai iya fahimtarshi. Yanayi ne da ba kowa ne zai gane ba.

Kafafuwanta ta sakko daga kan gadon. Tadanyi jim tana jin garin yadan saitu sannan ta diro tana mikewa. Kalle kalle take.

Ta hango mayafinta. Tana kallon bakin farhan na motsi saidai kunnuwanta basa jin me yake fadi. Nawaf kawai.

Wajen nawaf take son zuwa. Takalmanta ta janyo ta saka a kafarta. Ihun magana farhan ke mata amman yaga alama bata ganewa.

Cikin wata irin murya tace.

"Ka kaini wajen nawaf. Yaya farhan ka kaini wajenshi......"

Ya kasa gane me take nufi ko meye sanadin faruwar wannan abin. Ko maganar daya fada mata ce?

Gani tai kaman baya ganewa. Wayarta ta dauko dake kan gado ta mika mishi ya karanta text din. Ware idanuwa yai. Ba tare da tunanin komai ba yace mata.

"Muje......"

****

Zame jikinshi yai a hankali zuwa kasa. Ya zauna batare da damuwa da cewar kan tile bane ba. Ya dafe kanshi da dukkan hannuwanshi biyu.

Addu.ar duk da tazo bakinshi yake karantawa ko zai samu sauqin abinda yake ji. Bai taba sanin haka ake jin mutuwa ba sai da yai tunanin babu numfashi a tattare da nawaf.

Bai taba sanin haka daci da radadin rabuwa da wanda ka shaqu dashi kake kauna yake ba sai yau yadan dana kadan daga ciki.

Sai dai da daukrwar wancen yanayin da mayewar gurbin shi da wani sabo. Fargaba da tashin hankali. Tunanin zai iya rasa kaninshi kowanne lokaci.

Fatanshi Nuriyya ta bude text din dya tura mishi. Ko da nawaf rasuwa yai bazai ji baiyi wani kokarin komai ba. Rawa yaji zuciyarshi nayi.

Wayarshi yaji tana ringing. Ya daga ganin nuriyya ce yasa shi saurin dagawa da sauri. Sai dai ba muryarta yaji ba.

Wata murya yaji daban an mishi sallama. Ya amsa gabanshi na wata irin faduwa. Roqon Allah yake karya hada musu abu biyu lokaci daya.

Can yaji an dora da

"Muna cikin asibitin. Daga farko. Kuna ina?"

Dakyar ya iya cewa.

"Barin zo"

*

Daga nesa yake hango wata kaman nuriyya. Inka dauke raunukan dake fuskarta da kuma hannunta dayake a karye.

Tsaye take da wani matashi da inbai girmi nawaf ba zasu zo shekaru daya. Da sauri ya karasa inda suke. Kallon nuriyya yake.

Kar dai ace nawaf ne yai mata wannan dukan. Girgiza kai ibrahim yake yana rike baki. Idanuwa nuriyya ta ware a kanshi.

Idanuwanta a bushe suke. Babu alamar komai a ciki. Bai taba ganin idanuwa haka ba sai yau. Muryarta a dake tace.

"Yana ina?"

Ko sallamar farhan ibrahim bai tsaya amsawa ba balle ya karbi hannun daya miko masa ya juya. Bawai dan wani abu ba. Sam bai kula bane.

Suka bishi a baya.

*

Bata jin komai. Kaman an rufe mata duk wata kofa da kafa ta jin wani tashin hankali tun dazun. Komai ya tsaya mata cik.

Har lokacin data tura kofar dakin da nawaf yake. Bata hango shi daga inda take tsaye saboda su mama da suke zagaye dashi.

Kafafuwanta da wani irin nauyi ta karasa cikin dakin. Suna jin takun tafiyarta suka juyo. Ganinta yasa suka matsa daga jikin gadon.

Tana sauke idanuwanta kan nawaf zuciyarta tai wata irin dokawa da take ji har cikin kanta. Kallonshi take. Kanshi nade yake da bandage. Gefen fuskarshi ma haka.

Inhar baka sanshi ba ba zaka gane shi ba. Inda ba shida bandage din dinkine yakai hudu. Da duk takun da take da karin karfin bugun zuciyarta.

Gaba daya jikinshi na.urorine harda abin abinci ta hancinshi. Gani tai tafiyar daga inda take zuwa gadonshi ta mata wani irin tsaho.

Kaman so ake ta kare mishi kallo. Taga yanda ya koma kamin nan ta karasa inda yake. Hakan kuwa take.

Kafafuwanshi duka biyun a nade suke da irin abinda hannunta ke ciki. Bata taba sanin zaka iya jin tarwatsewar zuciyarka ba sai a wannan lokacin.

Bata taba sanin haka tashin hankali yake ba sai a yanzun nan. Bata taba gane rayuwa ba abakin komai take ba saida ta karasa bakin gadon da nawaf yake kwance.

Hannunta na rawa sosai tai kokarin kaishi kan fuskar nawaf. Saidai ta rasa inda zata ajiye shi.

Ko ina ciwuka ne. Kafafuwanta taji suna wata irin rawa. Ta dafa gadon dakyar tana zama. Bakinta ta bude saidai kalma ko daya ta kasa fitowa.

Banda wani irin ihu da take jinshi cikin zuciyarta da kanta amman sautin shi yaki fita.

Hannunta ta sauke kan kirjin shi. Kai take girgizawa. Fata take ta farka daga wannan mafarkin da takeyi. Su koma gida abinsu da nawaf dinta.

Koda kuwa markadata zai dingayi karewr duka inhar zata ga fuskarshi babu wannan abin.

Yanayin Nuriyya da nawaf din ya sake karya zuciyar duk wani wanda ke cikin dakin. Su kansu mazan daurewa kawai suke.

Can Allah ya taimaketa muryarta ta dan dawo.

"Nawaf......"

Ta fadi. Baiko motsa ba ballanta na tai tunanin yajita ko zai bude ido.

"Nawaf......!"

Ta sake kira wannan karin da karfi.

*

Ji yai kaman muryar nuriyya. So yake ya bude idanuwanshi amman sun masa wani irin nauyi. Yana ji da wata irin murya ta sake fadin.

"Nawaf ka tashi......!"

Kokarin bude idanuwanshi yake yi daga duhun dake riqe dasu. Nuriyya ce. So yake ya tashi ya bata hakuri. So yake ta yafe mishi. Yana jin yafiyarta ce kawai zata yaye wannan duhun.

Da wani irin karfin hali ya samu ya soma motsa idanuwanshi. Ji yake komai ya mishi nauyi. Kamun a hankali ya bude idanuwanshi. Ya dade sosai kamun ya fara ganin alin haske haske.

"Nawaf......"

Ta sake fadi. Baya son yanayin da yakeji cikin muryarta. Raunin da yakeji fiye dana kowanne lokaci ne. Sake kiran sunanshi tai.

Sai lokacin ya fara ganinta dishi dishi. Yanaji daga can gefe wani kaman yaya khamis na fadin.

"Call the doc"

Saidai baya ganinsu. Nuriyya dinma dishi dishi yake ganinta. Kanshi yakeji kaman ana doka mishi wasu irin karafa ciki. Ya rasa a ina ma yake jin ciwon a jikinshi.

Har cikin tsokarshi ciwo yake ji mai tsanani. A hankalo fuskar nuriyya ke washe mishi. Dakyar muryarshi can kasa yace.

"Nuri...."

****

Bude idanuwanta tayi ta sauke su kan fu.ad dake zaune yana rike da hannunta. Wani murmushi yai mata dayau ta kasa mayar mishi.

Kamun ta kalli gefenta. Sofi ce zaune.  Sake maida kallonta tai kan fu.ad.

"M....."

Ta kira shi a hankali. Hannunta ya sake dumtsewa cikin nashi yana jin yanda zuciyarshi ke bukatar suna mabanbancin wanda take kiranshi dashi.

Sumbatar hannun yayi hadi da fadin.

"Princess. Sannu"

"Ku kaini wajen shi"

Wani numfashi fu.ad yaja saboda safiyya ta mishi bayanin komai tun dazun. Harta gama fada mishi baice komai ba.

Saboda baya son zuciyarshi ta fara tauna dukkan maganganun. Komai zai iya faruwa. Nana tafi bukatarshi. Komai da nashi lokacin.

Ba Nana kadai ke son ganin wannan bawan Allah  ba. Har shima yana son ganinshi. Yana son mishi godiya akan karamcin dayai ma Nana.

Yana son mishi godiya duk da tayi kadan akan abinda shi yai mishi. Baida wani abin da zai iya bayarwa banda wannan.

"Zaki ganshi. Yanzun ki huta sosai. Kici abinci kisha magani sannan"

Kai ta girgiza mishi tana dakuna fuska.

"Yanzun nake son ganinshi"

Sauke numfashi fu.ad yai yana kallon sofi data kawo mishi dauki. Kauda kanta tayi gefe. Tasan halin Nana. Ba ta cika nacewa kan abu ba.

Saidai duk lokacin da tayi haka din. Lankwasata abune mai wahala. Kawai sai dai ai mata abinda take so shine kwanciyar hankalin kowa.

Hannunta ya sake dumtsewa cikin taushin murya yace.

"Baki yarda dani ba? Nace miki zamu je. Kici abinci kisha magani tukunna........"

Kwace hannunta Nana tayi. Ta kauda kai gefe idanuwanta na cikowa da hawaye. Ba zasu gane ba. Ta jima tana son sake ganin shi tai mishi godiya.

Ko sunanshi bata sani ba. Ranar ta dauka zasu fito su same shi a waje. Sanda suka fito baya nan. Tun ranar duk fitar da zata yi tana duba fuskarshi a fuskokin mutane da dama.

Dawowar fu.ad yasa ta sake son ganinshi. Saidai taba mishi addu.a. Tana mishi addu.ar samun wadatacciyar lafiya a rayuwarshi.

Dan a wajenta tana jin banda mumynta da babanta babu abinda yafi mata lafiya muhimmanci. Yanzun data ganshi.

Cikin jini. Tana so ta ga halin da yake ciki. Hawayen dake idanuwanta suka zubo.

"Ba zaku kaini inganshi ba sai na mutu ko shi ya mutu tukunna ba......"

Da sauri fu.ad yakai hannu ya rufe mata baki. Fuskarshi babu walwala ko kadan yace.

"Shhhhhhhh zamuje. Zamuje Nana ki daina wannan maganar. Ya girmi shekarunki"

Hannunshi ta kama dayaje bakinta ta sauke shi. Mayarwa yai yana goge mata hawayen dake fuskarta. Kamun ya mike.

Safiyya na kallonshi ya fice daga dakin sannan ta taso daga inda take ta zauna kan kujerar daya tashi.

"Kinsan ba....."

Da sauri Nana tace

"Mumy please. Ina son ganinshi. Kuma ina son magana da yan jaridar nan."

Da mamaki safiyya take kallonta. Ta dauka ta manta da maganar tunda fu.ad din ya dawo. Duk da bawai hakura sukai su da son magana da Nana din ba.

"I thought M ya dawo. Shikenan"

Girgiza kai Nana tayi.

"Ina son magana dasu har yanzun. You promise mumy"

Jan numfashi safiyya tayi ta fitar kamun tace.

"Zan kira su. Damun bar asibiti in shaa Allah"

Sai lokacin tai murmushi.

"I love you mumy"

Dariya safiyya tayi takai hannu taba dan jan hancin Nana din.

"Sarkin rigima. I love you more"

Girgiza kai tayi bata yarda ba. Zatai magana fu.ad ya turo dakin da sallama. Suka amsa mishi.

"Nagano dakin da yake. Saidai family kawai ake bari ganinshi"

Da sauri Nana tace.

"Kuje dani. Zasu barni"

Girgiza kai fu.ad yayi. Baya son sake ganin hawaye a fuskarta. Kai ya sake zurawa waje ya hango likitan da sukai magana dashi ya taho.

Hanya ya bashi ya shiga cikin dakin. Ya cire ma Nana karin ruwan dake jikinta yana barin abin a jiki dan in sun dawo a mayar mata.

Da idanuwa fu.ad yai mishi godiyar fahimtarshi da yayi. Tahowa yai inda Nana ke kokarin sakkowa daga kan gado yana son kamata.

Hannunshi ta dafa ta kalle shi tace.

"Zan iya fa"

Tana saukowa. Takalmanta ta saka. Ta dauki yar hijab dinta ta saka a kanta. Sai yaga tayi wani irin kyau kaman ya saceta.

Daukarta yaxo yi ta matsa baya. Da murmushi tace.

"Um um. Zan iya"

Girgiza mata kai fu.ad yai yana kawo hannuwa zai dauketa. Ta rike su duka biyun. Idanuwanta take yawatawa cikin fuskarshi kamin ta furta.

"Ina son yin komai da kaina yanzun da zan iya. Zakuyimun amman da dan saura"

Runtsa Idanuwanshi yai yana jin nauyin da zuciyarshi tai a kirjinshi. Yama kasa cewa komai sai hannunta kawai daya kama cikin nashi.

Kallon safiyya yake da wani irin yanayi da shi kanshi ya kasa fassarawa. Kamun yaja Nana a hankali suna takawa zuwa kofa.

Binsu safiyya tayi tana jin wani irin abu na daban. Ta kasa fassara kallon da fu.ad yai mata. Sai dai ta kwammace hararar data kan samu lokaci lokaci a wajenshi da wannan kallon mai cike da fassarori da yanayoyi kala kala.

*
Kaman yanda fu.ad din ya fada. Family ne kawai zasu iya ganin nawaf. Fu.ad nata fama amman sunqi saurarenshi.

Nana ta ja mishi hannu. Nuna mishi tai daya dagata. Dan basa hangota saboda counter din data boye su. Dagata yai.

Likitocin dake wajen ta kalla idanuwanta cike da hawaye.

"Please please ku barni inganshi. Bazan yi wani hayaniya ba. I promise.

Yamun taimako a rayuwata. Shi ya tayani gano babana. Ina so in ganshi please please"

Kallon Nana suke su dukansu. Daya daga cikin likitocin ya gane Nana. Murmushi yai. Koma bai ganeta ba bazai iya hanata ba.

Cayai su jira yaje yai magana da wani cikin family din nawaf din. Yakai mintina goma kamin ya dawo yace zasu iya wucewa.

Sosai sukai mishi godiya. Wannan karin fu.ad bai sauke Nana ba. Shibya dauketa har suka karasa dakin da aka fada musu.

****

Sam allurarar baccin da sukai ma nawaf taqi kama shi. Wani irin kuka nuriyya keyi mai taba zuciya. Tana kallon murmushin da nawaf keson mata cikin idanuwanshi.

"Ki yafemun Nuri. Ki yafemun duk abinda nai miki"

Hannunshi ta sake damtsewa gam. Bata son wannan kalaman da yake ta maimaita mata tun dazun.

"Ki fada kin yafemun inji da kunnuwana"

Dakyar cikin kuka tace

"Na yafe maka nawaf. Ka yafemun nima"

Dakyar yadan gyara kanshi da alama hakan ba karamin wahala yai mishi ba.

"Nagode nuriyya. Ina sonki. Zuciyata ke kadai take so. Kece ta farko a cikinta kuma ke zaki zama ta karshe.

Ina farhan?"

Tambayarshi ta mata wani iri. Dago ido tayi ta sauke su kan farhan dake gefe. Yaji tambayar da nawaf din yayi.

Dan haka yadan karasa. Sai lokacin family din nawaf suka gane wanene shi din. Dan bama tashi suke ba.

"Ka kula da ita. Ka sota fiye da yanda na sota. Karka bar hawaye ya zuba a idanuwanta kaman yanda nayi.

Karka daga hannunka akanta kaman yanda nai. Ka zama farin cikin ta tunda na kasa. Ka kula da Nuri farhan"

Duk wani haushin nawaf da yakeji ya nema ya rasa. Dan yanzun ya tabbatar da nawaf da babanshi mutanene ne mabanbanta.

Duk abinda ya faru daya masa fahimta ya fahimci nawaf na son nuriyya. Son da yake tunanin ko shi bazai iya mata ba.

Sai yanzun ya fahimci taimakon da nuriyya ke fadin nawaf na buqata. Muryarshi a dakushe yace

"Kai zaka kula da nuriyya. Kai zaka zama farin cikinta. Saboda duk muna tare dakai.

Zamu taimaka maka"

Baice komai ba. Saboda yanda yake jin a jikinshi sun gama taimaka mishi. Idanuwanshi yakai kan mamanshi da babanshi da suke tsaye sun zuba mishi idanuwa.

Kallon da yake musu yasa ya suka karasa inda yake da sauri. Farhan ya matsa musu ya na komawa gefe.

Cikin sanyin murya yace.

"Ku yafemun. Na saka ku bacin rai da yawa a rayuwata. Ku tayani roqon Allah ya yafemun......"

Kuka sosai mama takeyi. Yana jin kukansu har cikin zuciyarshi.

"Ina su yaya khamis"

Dukkansu suka karaso inda yake. Suma yafiyarsu ya nema. Ibrahim ne karshe. Shakuwarsu dabance ko a cikin yan uwanshi.

Kallonshi ibrahim yake da wani irin yanayi.

"Karka fara nawaf. Muna tare. Babu inda zaka je. Inka tafi dawa zan kula?"

Da karfin hali yai masa murmushi saboda ciwukan dake fuskarsh.

"Zaka kula mun da su mama. Zaka kulamun da duk wanda na damu dasu. Zaka kulamun da kanka.

Yaya nagaji sosai."

Dafa shi ibrahim yai. Ya mike yana fita daga dakin. Dai dai zuwan wani likita dake tambayarshi wasu abubuwa da bai fahimta ba. Yadai amsa shi da to ne kawai.

Yana nan tsaye ya hango wasu su biyu suna karasowa inda yake tare da wata yarinya kyakkyawa a sabe a kafadar namijin.

Karasowa sukai wajen shi sukai mishi sallama ya amsa musu. Fu.ad yace.

"Nan ne dakin da nawaf yake?"

Kallonsu yake dan baigane su ba sam. Zai iya rantsewa bai taba ganin su ba. Hakan fu.ad ya fahimta yace

"Muma bamu sanshi ba. Kaga wadda ta sanshi nan. Yamana karamcin da bazai mantu ba.

Shisa muke son ganinshi inba damuwa"

Yanda nana ke kokarin ya sauketa ne yasa shi sakkota a hankali. Karasawa tai ta kama hannun ibrahim.

"Dan Allah kabarni inganshi. Zan mishi godiya ne kawai"

Dan dafe kai ibrahim yayi. Inhar sunce nawaf ya musu karamci waye shi zai hana su ganshi. Da kanshi ya kama hannun Nana zuwa dakin.

Su fu.ad na biye dasu. Kallo daya safiyya tai mishi tai baya idanuwanta na kawo hawaye. Bata da juriya irin wannan dan haka ta dakata.

Koshi fu.ad daga gefe ya tsaya. Kallon family din nawaf yake. Yanda suke a hargitse yana jin zuciyarshi na cika da wani irin tsoro.

A hankali Nana take takawa har inda nawaf yake kwance da wata a gefenshi tana wani irin kuka. Su dukansu kallon nana suke.

Dai dai fuskarshi ta tsaya tana kallon shi.

"Ya jikinka?"

Ta tambaya. Sosai nawaf yake kallonta yana son gane inda ya taba ganinta. Ga zuciyarshi na wani irin zafi. Yana jin yanda yake kokawa da numfashin shi.

"Da sauqi"

Ya fadi a hankali.

"Naga babana."

Tace mishi. Sai lokacin ya tunata. Oh rayuwa kenan. Cike da taushin murya yace mata.

" Naji dadi. Ya jikinki"

Dan daga kafada tai alamar yana nan kamun tace.

"Zan maka godiya ne. Da banga babana ba badan kai ba. Ba haka naso in ganka ba.

Na kasa ganewa ni fa. Na rasa me yasa mutuwa ta zabeni. Kuma kaganka yanzun."

Murmushi nawaf yai mata kamun yace.

"Lokaci da dama mutuwa tana da rudani. Sai dai hutu ce ga mumini.

Ina son in huta. Ina son in samu nutsuwa"

Jinjina kai Nana tayi kaman ta gane me yake nufi. Fuad yadan dafa kanta. Ya kallo nawaf.

"Mungode sosai nawaf. Allah ya baka lafiya"

Sai yake jin wata nutsuwa ta daban. Ko ba komai sanadin shi wannan yar yarinyar ta gane babanta.

Da idanuwa ya amsa saboda ya gaji sosai. Sosai nana ta matsa kusa da kunnen shi yanda bamai iya ji tace.

"Kana jin tsoro?"

Shima da rada takai kunnenta yace mata.

"Sosai. Amman ganinki yasa na daina"

Wani murmushi tayi kamun ta sake ce mishi cikin kunnenshi.

"Nagode. Allah ya baka aljanna. Sai mu zama abokai acan"

Lumshe idanuwanshi yai yana jin kaunar Nana har ranshi. Kama hannunta fu.ad yayi. Tace.

"Zan dawo....."

Baice mata komai ba. Har sunkai kofa yace

"Ya sunanki?"

Juyowa tai da murmushin nan sannan tace

"Nana safiyya"

Kai yai kokarin daga mata wani irin tari ya sarqe shi. Da gudu Nana tai niyyar karasawa ganin yanda jini ke fitowa daga bakinshi fu.ad ya dauketa.

Kwantar da ita yai a kirjinshi tana wani irin ihun kuka ya fita da ita daga dakin da gudu.

Gaba daya family din nawaf suna kanshi. Sun rikice sosai kowa kwala mishi kira yake.

Nuriyya tana rike dashi da hannunta tana jijjigashi.

"Nawaf ina zaka tafi kabarni?"

Sosai take kuka. Shi kanshi farhan wasu hawaye yaji sun cika mishi idanuwa. Mama kuka take kaman zata shide.

Yaya khamis ya kasa koda motsawa daga inda yake. Babane yaga yanda numfashin nawaf ke sama ya soma karanto mishi kalmar shahada da karfi.

Aikam kaman nawaf ya na saurarenshi. Yana karanto mishi muryarshi na rawa. Nawaf din na maimaitawa daya bayan daya.

Dagaji harshen shi harya karye. Kuka suke sosai. Ibrahim na rike da hannunshi daya yana kallon yanda numfashin shi ke sarqewa.

Muryarshi bata fita sosai. Kamun komai ya tsaya.......!

Fita baba tai daga dakin. Yaya khamis ne ya karaso yasa hannu ya rufe mishi idanuwanshi yana zubda hawaye.

Kallonshi nuriyya take yi. Tana jinta kaman ba a duniya take ba. Ibrahim mikewa yai yana ja da baya. Ya kasa yarda nawaf yabarsu.

Ya kasa yarda da abinda yake gani. Mama na mikewa ta yanke jiki ta fadi. Da gudu sukai kanta. Nuriyya kuwa ta  zuba ma nawaf idanuwa.

Tana kallon murmushin dake kan fuskarshi. Hannu tasa a hankali ta taba jikinshi. Sanyi taji yayi karara.

Girgiza kai take yi. Sake taba shi tayi kamin a hankali ta jijjigashi. Gani tai yaqi motsi. Gabaki daya yanayinshi ba iri daya bane da nata.

Mikewa tayi tana girgiza kai. Wata irin gigitacciyar qara ta saki tana faduwa kasa......!

*#TeamNawaf*

No comments:

Post a Comment