Thursday 4 May 2017

AKAN SO 4


*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

           04

*20/02/2017*

Wani irin ciwo kanta yake mata da take da tabbacin yana da alaka da kukan datayi.

Sai yau ta tabbatar rashin sanin ranar mutuwarka ba karamar Rahma bace.

Ba ranar mutuwar nana aka gaya mata ba amman ji take kaman anyi yakin duniya na farko da zuciyarta.

Ko ina na ciwuka ne da take da tabbacin ko da sun warke tabonsu zai kasance da radadi har karshen rayuwarta.

Tana nan falo kwance Nana ta dawo daga makaranta. Ita take dauko ta.

Text din da ansar yai mata cewar ta huta zai je dauko nana dinne ya sa tai zamanta.

Wani gajeran murmushi ta dora saman fuskarta ta mike zaune tana amsa sallamar Nana.

Tana kallonta ta cire takalminta sannan ta karaso inda sofi din take zaune.

"Mumy kinga uncle tunde wai a test din maths ne naci 9.5 cikin 10. Kuma ni nasan na cinye duka 10 din"

Cewar nana da take cire hijab dinta da jaka tana ajiyewa gefe.

Wannan karon murmushin da sofi tayi ba iya fuskarta ya tsaya ba. Har a zuciyarta.

Kallon nana take a ranta tana lissafa tsahon watannin da suke dashi. A fili kuma tace

"Banda abinki nana. Ai kinci da yawa"

Cikin idanuwa ta kalli sofi da yasa zuciyarta wani kai kawo a kirjinta. Da wani yanayi a muryarta tace.

"Mumy meke damunki?"

Murmushinta ta fadada dan tasan nana. Yanda yarinyar ke karantarta har mamaki yake bata.

Maimakon ta amsa mata tambayarta sai catai.

"Tashi ki sake uniform"

Babu musu ta mike. Harta tafi ta dawo.

"Me anty jana tace?"

Kaman yanda take kiran likitar tata da a shekaru biyu da fara rashin lafiyarta sukai wani irin shakuwa.

Wani abu sofi taji yazo ya tsaya mata a makoshi.

Ta ina zata fara fadama yarta da bata karasa shekaru goma sha daya ba cewar babu tabbacin samun sauki a ciwonta?

Wani kasalallen murmushi nana tai dayake fassara damuwa. Loosing hope.

Koma me murmushin yake dauke dashi ya taba zuciyar sofi dan bata san sanda hawaye suke zubo mata ba.

Karasawa nana tai ta zauna kusa da ita. Riketa sofi tai tana wani kuka marar sauti.

Hawaye nana ta shiga goge mata tana fadin.

"Mumy ki daina kuka. Ni banajin tsoro. Kawai ina so inga M ne"

Sake riketa tai. Tunda ta fara wayau take kiran sunan shi da M kawai. Sofi tayi tayi.

Tace intai kokarin claiming wani dangantaka tsakaninsu dashi zai ki dawowa.

Hakan kawai na sake tsaya ma Nana a rai. Saboda tasan laifinta wajen taimakon rashin babanta a kusa da ita.

Dan haka bata sake kokarin hanata kiranshi duk yanda take so ba.

Dakyar ta samu tadan nutsu. Tasa hannu tana goge fuskarta.

"Mumy please karki ce a.a bazan iya ba. Inason magana da yan jaridar da suke bakin school kullum"

Kai kawai sofi ta iya daga mata alamar ta yarda. Dan magana ta makale mata.

Rungumeta nana tai da wani murmushi a fuskarta hadi da fadin.

"I love you so much mumy"

Shirun dai shi sofi tai har nana ta tashi daga jikinta ta ruga zuwa dakinta.

Kafafuwanta ta dora kan kujera ta hade kanta da gwiwa ta sake sakin wani irin kuka.

Nana ce kadai hope dinta. Kwarin gwiwarta. Dalilinta na farin ciki.

Nana ce kadai adalci data samu a rayuwarta. Ga kaddara da ba zata kautu ba na shirin rabasu.

****

21/02/2017

A kalar tukin da yake yi Allah ne kadai yakai shi kofar gidan yayanshi lafiya.

Dan shi kanshi nawaf zai iya rantsewa ko hanya baya gani. Wani irin duhu yake ji cikin kanshi.

Zabi daya yake dashi banda gidan yayanshi. Shine club. Saidai duhun da yake ji bai fi karfin alkawarin dayai ma Nuri ba.

Yaga alama itace sanadin shiryuwarshi kuma ita zata sake sanadin komawarshi ruwa.

Matakin nutsuwarshi har yanzun kokawa suke ta gaske da na rashin nutsuwar.

Fitowa yai ko motar bai rufe ba  da gudu gudu ya karasa shiga gidan yana kiran.

"Yaya........!"

Jidderh da take kitchen tana girki taji kiran bana lafiya bane ta fito a tsorace.

Kallo daya tai ma nawaf da yake tsaye hannu daya kan kugu dayan kuma cikin sumar shi.

Ta karanci damuwa karara dan haka bata kula shi ba tahau sama da hanzari.

Ko sallama batai ba ta tura dakin ibrahim da yake zaune yana ayyuka da laptop dinshi.

"Dear ga nawaf ya...... "

Bata karasa ba ya mike da hanzari. Yasan abinda zai kawo nawaf gidan shi da wannan lokacin ba karami bane.

Hanyar waje ya nufa Jidderh zata bi bayanshi yai mata alama da hannu data dakata. Batai musu ba.

Dan in zata fadi gaskiya yanayin nawaf kawai tsoro yake bata.

*

Yana ganin saukowar t.j bai jiraba ya karasa inda yake.

"Yaya nuri. Nuri tana so ta kashe ni. Yaya bazan iya bafa"

Ganin yanda ko ina na jikin nawaf yake kyarma yasa t.j kamashi yaja shi zuwa tsakiyar falon.

Kan kujera ya zaunar dashi kaman wani karamun yaro. Ya koma da gudu kitchen ya dibo ruwa ya fito.

Nawaf ya mikawa hadi da fadin.

"Calm down. Sha ruwa sai muyi magana"

Cike da kulawa. Babu musu nawaf ya karbi ruwan ya shanye yana maida numfashi cikin kokarin son samun nutsuwa daga halin da yake ciki.

"Yaya hira fa muke. Ina bata labarin Mexico. Nine a gabanta. Amman farhan yazo mata a rai tana gayamun yana son garin...... "

Dafe kai t.j yai. Dole yai magana da Nuri yake tunani. Ya nutsar da hankalinshi kan nawaf da cewa.

"Calm down for goodness sake nawaf. She is yours. Taka kai kadai. Dan ta tuna farhan ba wani abu bane da zaka daga hankalinka and......... "

Bai jira ya karasa ba ya mike da hanzari ya nufi hanyar waje.

Binshi t.j yai ya riko yana fadin.

"Ina kuma zakaje???"

Lumshe idanuwanshi yai ya bude su sannan yace.

"Na fada maka matsalata kana nunamun ba komai bane. I beat her up yaya! "

Sakin shi t.j yai da wani shocked expression a fuskarshi yake girgiza kai.

"No nawaf. Karka fadamun ka daki Nuri"

Zafin da zuciyar nawaf yake yi yaji ya karu. Shi kanshi yasan baya kyautawa.

A ranar daya fara dukan nuri mari ne kawai. Daga daya zuwa biyu.

Wani abu yake ji cikin kanshi da baya iya controlling. Yau ya dake ta sosai.

Da bata ruga ta kulle daki ba. Zai mata wanda yafi wannan. Muryarshi na rawa yace.

"Yaya please help me. Bazan iya rasa nuri ba. Wallahi bazan iya rasata ba yaya"

Hannunshi t.j yaja yana fadin.

"Zo ka huta sai muje gidan tare"

****

Tunda ta koma aiki taje ta duba ikram a dakinta taganta zaune ma tana karatun Qur.ani.

Ja mata dakin tai. Fushi suke mata daga ita har babanta. Da lafiya ma ikram bamai yawan magana bace.

Shi kanshi jabir din share shi tai. Dan sam bata son rikicin. Nana ce tsaye a ranta da tunanikan rayuwa da dama.

Tana yin sallar isha.i ko takan abinci bata bi ba. Tadai fita ne ta kammala yaranta tasa sunyi addu.a itama tai musu.

Tana dawowa dakinsu ta saka rigar bacci ta kwanta abinta.

Tanajin jabir ya hauro kan gadon. Rikota yai jikinshi ta sauke wani numfashi.

Juyowa tai ta fuskance shi. Idanuwanshi kawai ta kalla taga gajiyar dake cikinsu.

Wata gajeriyar sumba ya manna mata hadi da fadin.

"Nayi kewarki"

Murmushi tai mishi

"Nima haka. Nayi kewarka sosai na kiraka dazun baka dauka ba"

Ya wani langabar dakai

"Ke da kika dawo aiki baki bi takaina ba"

Kara matsawa tai jikinshi sosai. Bata da amsar tambayarshi dan haka tai shiru.

Rungumeta yai sosai. Cikin kunnenta yace.

"Jana kibar aikin nan. Please ki barshi"

"Honey j baka da matsala da aikina a duk shekarun na.  Me ya canza a cikin wata daya? Menene nake maka da da bana maka yanzun?"

Saida ya sumbace ta sosai sannan yace.

"Mubar maganar nan for now. Bana son yin fadan"

Daga mishi kai tai hadi da fadin.

"I love you"

"I love you more"

Ya fadi ya lalubi switch din dakin ya kashe kamun ya janyota su soma raya darensu cikin kauna da son juna.

No comments:

Post a Comment