Tuesday 23 May 2017

AKAN SO 50


*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

www.Loobnerh.blogspot.com

Wattpad: LubnaSufyan

          50

*EPILOGUE*

*Tabbas zan kewar characters din dake cikin AS gabaki dayansu. Sai dai ina jin dadin yanda suka taba rayuwata ta fanni da dama. Da kuma yanda suka taba rayuwar readers din*

*Abu uku daga Luβπα Sufyαπ zuwa ga dubban mutanen dake nuna mata kauna*

*1. Rayuwa makaranta ce mai fadin gaske. Zata hadaka da mutane kala kala. Zata tabaka ta inda baka zato. Ta wani fannin farin ciki. Ta wani fannin akasin hakan. Ka riqe ALLAH a komai*

*2. Kaddara. Banda kalaman da zan amfani dasu wajen kokarin fassarata. Saboda haka zance duk kalar daka tsinci kanka a ciki. Abu biyune mafita. Ka karbeta sanin kana daga cikin masu kusanci da Ubangiji. Mummuna ko mai kyau. Ka riqe ALLAH a komai*

*3.Zumunci da hakuri. Abubuwane da suke gogayya da juna a lokacin da rayuwa ta tabaka ta rukuni da dama. Karka duba kalar kaunar yan uwanka a gareka. Ba wannan bane mai muhimmanci. Ka duba girman kaunarka a garesu. Ka riqe ALLAH a komai. Zai kasance dakai a komai*

*Nagode. AnaTare. Like sosai AnaTare. Like seriously AnaTare. Irin totally AnaTare*

"I feel ridiculous cikin kayan nan wallahi"

Dakuna fuska safiyya tayi tana balle mishi maballin rigar. Ta kalle shi sosai. Kalar shaddar ruwan kasa ne mai haske sai yai shige da idanuwanshi.

"Kaga yanda kai kyau"

Damqe fuska yai yana jin gabaki daya manyan kayan sun takuranshi. Duk ya shake.

"Nikam dakin barni nasa riga da wando abuna"

Daure fuska safiyya tayi.

"Ka kalli luku da mimi sun girma. Ko affa (Mai sunan baban safiyya) ya girma. Yaushe zaka fara saka manyan kaya.

Oya muje"

Fuska a daqune da alamar takura ya fita falon. Mimi ce a zaune da litattafan islamiya baje a kasa tana assignment.

Jin tafiya yasa ta dago. Sauke idanuwanta tai kan fu.ad lokaci daya ta yamutsa fuska.

Kallonta safiyya tayi. Gaba daya expressions din nan irin na fu.ad ne. Duk ya koya mata.

"Menene wannan kasa dady?"

Ta tambaya fuska a yatsine. Hararta safiyya tayi. Fu.ad ya kalli safiyya dake fassara 'Bana gaya miki ba'.

"Kaya sunan su. Manyan kaya"

Safiyya ta amsa ma mimi.

"You look different"

Mimi ta fadi tana maida kanta wajen assignment din da take. Karasawa fu.ad yayi bai damu da zaman dayai a kasa zai squeezing mishi kyanshi ba.

"Daban in a good or bad way?"

Ya bukata. Dagowa mimi tayi tadan murmushi ta rausayar da kanta gefe alamar tana tunani.

Dakuna mata fuska fu.ad yayi. Hakan ya bata dariya.

"Kana sakawa ko yaushe. In a good way"

Murmushi yayi.

"Kome queen take so"

Ware idanuwa safiyya tayi.

"Tunda yar ka tace kayi kyau ka yarda. Ni da na fada ai baka dauka ba"

Kallonta Mimi tayi da smug face.

"Yafi sona ko dady?"

Tsare shi da idanuwa safiyya tayi. Yadan ware mata idanuwa. Mikewa yai daga kusa da mimi ya taka inda take.

Idanuwanshi ya sauke cikin nata. Godiyarshi da kaunarta yake nuna mata. Yake son tabbatar mata. A shekaru goman nan rayuwa ta musu wani irin sauyi naban mamaki.

Allah ya musu kyauta yara har biyu bayan mimi dukkansu maza. Yanayin kallon da yake mata ya kashe mata jiki.

"Ina sonki sosai"

Ya fadi kasa kasa. Dakuna mishi fuska tayi alamar Mimi na falon. Dan juyawa yayi yaga bama ta su Mimi take ba.

Rankwafawa yai. Tai saurin matsawa. Da sauri ta juya tai bedroom dinsu. Yabi bayanta. Yana shiga tasa hannuwanta jikin wuyanshi.

"Kai ko"

Tarin wasa ya fara. A dole ta shaqe shi. Sauke hannayenta tai tana dariya.

"Ka bata mun yarinya. Duk irin abinka ta dauka"

Cute face yai mata.

"Like daughter like dady"

Murmushi safiyya tayi. Tana kai hannu tare da ja mishi hanci.

"Allah ya rayamun ku"

"Amin. Tare dake ma"

Ya fadi yana janyota jikinshi. Sumba ya manna mata mai taushi a lips.

"Alhamdulillah da kyautar iyalai irinku"

Ta amsa da.

"Alhamdulillah da kaddara irin tamu"

Lumshe idanuwanshi yayi. Yana hugging dinta jikinshi.

"Ina tunanin me Nana zata ce ne da zata ganni da wannan kayan"

Dariya safiyya tayi. Cikin kwaikwayon muryar Nana tace.

"Dady me mumy ta baka kasa haka?"

Sosai yake dariya da dukkan zuciyarshi. Yanajin dadin yanda har yau memories din Nana na saka su farin ciki irin wannan.

Ta wani fannin yana jinjina ma rayuwa. Yana kara ganin yanda take tamkar makaranta. Kowa da yanda zai fahimci tashi.............!!!

Nikuma anan nake muku sallama. Da fatan alkhairi a rayuwa gabaki daya.

*ALHAMDULILLAH*

*Aliyu tsagem. Fahad. Ayna.u mardiyya. Ummie jafar. Yusra abdu fari. Biebie Isa. ALLAH YA SADAKU DA ALKHAIRI A DUK INDA KUKE*

*Whatsapp*

Daukacin wa.annan groups din

- Taskar novels.
- Taskar Lubabatu maitafsir
-Taskira
-Ummie jafar novels
-Billy galadanchi novels
-Da sauran da ba zasu lissafu ba.

*Ina godiya da karamcinku. Ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke*

*WATTPAD*

*Bazan taba iya lissafo gabaki daya sunayenku ba. Ku sani. Wallahi dukkan comments dinku yana da muhimmanci gaske a wajena. Dukkan kwarin gwiwarku yana da tasiri a rayuwata data rubutuna gabaki daya. Kaunata a gareku mai girma ce*

*Architect ishaq (Bifham) fatana a gareka guda dayane. (Ka zama cikin nutsuwa da kwanciyar hankali)

*YAYA. (Kana nan a bakin ciki da farin ciki. Kana nan sanda na rasa hope akan komai. Kana nan a ko ina. Ina fatan Allah ya kasance dakai a ko ina na rayuwarka)

*Allah ya hadamu a aljanna*

*Ina neman gafarar duk wanda na batama. Na yafe ma kowa. Laifin dayaimun a bisa sani ko rashin sani. Allah ya yafe mana gabaki dayanmu. Amin amin*

*AnaTare*

*ALLAH YA NUNA MANA RAMADAN LAFIYA* (Amin thumma amin)

AKAN SO 49

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

www.Loobnerh.blogspot.com

Wattpad: LubnaSufyan

               49

*Abubuwa da yawa suna faruwa damu a rayuwa. Na bakin ciki. Na farin ciki. Sai dai a cikin kowannensu idan muka duba akwai darasi*

*Zumunci na da girma. Wasu lokutan zumuncin dake tsakaninka da wanda baka hada jini dashi ba yana kaiwa mataki babba*

*In zaka yarda karka yarda da yawa. Karka daga burinka akan komai. Ka yarda da Allah. Ka muka burikanka a wajen Allah. Sauran zasu zo da sauki*

*Allah ya nuna mana Ramadan lafiya*

*Farida Aminu.(A duk lokacin dazan kwanta da dare inda zan iya ganin yanda taurari suka tsaru muryark nakeji anty farida. "Baby ki kalli yanda Allah Yai ma sama ado da taurari masu kyau. Hikimomi na Ubangiji yawa ne dasu.)*

*She was so sick. Ban taba ganin kalarki ba. Nakan tunaki da hawaye. Saidai girman murmushin saninki yakan rinjayi hawayen*

*Auwal Aliyu.(Nai kuka. Nai kuka uncle auwal. Sai da baka nan nagane muhimmanci zumunci. Mutuwarka tazomun da darasi na fahimtar gaggawa cikin ziyara a duk lokacin dana samu dama*

*Dalilai da yawa basu sa nasanka ba. Hakan bai hanani kewarka ta yanayin da bazai fadu ba. I wish and wish......*

*Adam Abdullahi Gambo. (You raised me. Kana nan lokacin dana fara tafiya. Lokacin dana bude bakina. Lokacin dana dora tukunya danyin girkina na farko. A tare dakai nasan menene rayuwa. A tare dakai nasan menene hakuri. A taka rayuwar na samu shafukan nawa)*

*Ba kakana bane kawai kai. Babana ne. Mamana ne. Yayata. Yayana. Abokina. Abokiyata. Alhamdulillah dana sanka a rayuwata*

*Ummiee (Har yau idan wani ya kira LUBA da muryarki sunan yake karasowa kunnuwana)*

*Me zance? Me zan fada akanki ummie? Ina kalaman suke? Ina kaunarki yayi kadan wallahi. Nayi kewarki bai isa ba*

*Uncle sulaiman (Kewarka na damuna idan na duba abubuwa da dama. Ya Allah. Ban taba ganin fuskarka da wani abu daya wuce fara.a ba.)*

*Allah ya jikanku. Allah ya sadaku da Rahmarshi. Allah ya haskaka kabarinku. Allah ya hadamu a aljanna in gaya muku kalar kaunar ku da nake daban samu na fada muku ba*

*Wannan ba bankwana bane. Wannan yana nufin sai na taho*

*SA.ADATU HABEEB (May Allah ease your pain and suffering. May Allah make your departure an easy one)*

*I..... I feel your pain? Scratch that. I will never know what you are going through. It just hurt a lot (Allah kaine abin godiya a kowanne hali)

*#AnaTare*

*Saura epilogue in shaa Allah*

*BAYAN SHEKARA DAYA*

Wani irin zama su jana suke mai natsuwa. Duk da wata doguwar hira bata hadata da ayna.

Yara dai tunda ita tama fita zama dasu. Wani lokaci ma ko tana gidan ayna ke kula dasu. Hakan bai dameta ba.

Tadai saka idanuwa ne saboda taga ko yanayin tarbiyar da ta dora yaranta akai ya sake. Ga mamakinta sai dai ya karu.

Kananan abubuwan da bata tsayawa ta kula ko ma tace bata da lokacin kula dashi ayna na tsaya mata akan hakan.

Yau ma kaman kullum ta gama shirinta tsaf da yake dakinta jabir yake kuma yama rigata shiryawa tare zasu fita.

"Jana sai mun latti ko?"

Ya tambaya yana sake duba agogon dake hannunshi. Da murmushi a fuskarta tace.

"Ka tafi inka gaji da jira"

"Zaki hau napep kenan?"

Ya bukata yana tabbatar da idanuwanshi sun sauka cikin nata kamun yai tambayar. Yana kallon yanda take wani matse labba yasan tsokana ce fal cikinta.

"Kadai hau napep honey j"

Dafe kirji yayi.

"Yes. Ka manta motata ce? Inkuma ayna zata ara maka tata ne to kaje ka amso"

Rausayar dakai yai gefe

"Allah ya horemun in sake siyan wata motar yanda in dayar ta samu matsala ba sai an mun goriba"

Dariya jana tayi sosai.

"Amin. Ko in ara maka? Ka siya inka samu ka biyani"

Karasawa yayi inda take ya zagaya hannuwanshi zai rungumeta ta mike da sauri.

"Nagama shiryawa"

Girgiza mata kai yake alamar bai yarda ba.

"Zo nan kiga in tayaki"

Pillow ta dauka kan gadon ta jefa mishi tana daukar jakarta. Ya rike yana dariya.

Tare suka fita. Jana ta tsaya a falon ya wuce bangaren ayna ya fada mata sun wuce. Bata daukarma kanta gulmar yima ayna sallama ba dan zata tafi work.

Tana danne abubuwa da yawa. Saidai bata takura kanta ba. Shi dai da yake wajibi akanshi yayi. Sai dai ayna ta burgeta yanda kullum ko da jabir na dakinta saita zo da kanta sun sallama da janar.

Fitowa yayi ya ce ma jana.

"Bata da lafiya. Zazzabi ne ruf jikinta"

"Subahanallah......"

Jana ta karasa tana ture jabir din ta wuce dakin ayna din. Karo na farko sa kafafuwanta suka taba taka bedroom din ayna a shekara daya datai a gidan.

Koma tace bangarenta gabaki daya. Sai dai insun hadu a babban falo sannan. Sosai ta dudduba  ayna.

Sannan ta taimaka mata ta tashi daga kan gadon. Take fadama jabir sai sunje asibiti dole. Bai musa ba ya bata mukullin motarta ya dauki na ayna din.

*

Abinda jana take zato ne. Ta lumshe idanuwanta tana danne wani kishi da take jin ya taso mata.

Wayarta ta dauko ta kira jabir. Ringing din farko ya daga.

"Albishirinka amman saika bani goro"

Tana jin murmushin da yake cikin muryarshi.

"Saikin zabi kalar goron da kike so. I promise"

Yar dariya tayi.

"Ayna nada shigar ciki sati hudu"

Tana jin yanda yaja numfashi hadi da fitar dashi kamun addu.o.i su biyo baya. Sosai ta rintse idanuwanta.

Hakan dayai ba bakon abu bane saboda itama yayi duk cikin yaransu. Ta rasa ko menene na jin kishi a ciki.

"Thank you jana. I love you. Ki zabi goronki"

Saida tadan yi jim tana son danne abinda take ji kamun tace.

"Sai nayi tunani tukunna. Barin fada musu ina da patient mu koma gida.

Babu dadi in kaita in barta ita kadai"

"You don't have to do this jana. Atika na nan ai"

Girgiza kai tayi.

"Badon kai nayi ba. Ko ni. Nayi saboda karamcin da ke tsakanin su da yarana."

Shiru jabir yadanyi kamun yai mata sallama.

*

Kaman yanda ta fada hakan tayi kuwa. Har daki ta raka ayna ta tambayeta ko tana bukatar wani abun tace mata aa.

Sosai tai mata godiya. Murmushi kawai tayi ta fada mata tana dakinta indai tana bukatar wani abu ko flashing tai mata sannan ta fice.

Gyara kwanciya ayna tayi. Jana mutuniyar arziqi ce. Bakowa ne zai dace da kishiya irinta ba.

****

Zaune suke tana yanke ma farhan farce. Sukaji sallama da sauri ta saki kafarshi ta mike tana amsawa.

A fadace yace.

"Nuriyya ki daina saurin mikewa haka. Saikin jika baby na ciwo ne ke kam?"

Dariya tayi tana mamakin farhan. Cikin da bai wuce sati uku ba ko motsin kirki bata da ikon yi sai yayi fada.

Sosai fara.arta ta karu ganin anty maimuna.

"Anty maimuna. Sannu da zuwa"

Nuriyya ta fadi.

"Ki kara so mana"

Da fara.a a fuskar anty maimuna ta karaso dakin. Farhan ya kalleta yana murmushi.

"Anty maimuna. Ina wuni"

Saida ta samu waje ta zauna sannan tace mishi.

"Lafiya kalau farhan. Ya mai jiki?"

Ya amsa da

"Ta warware sosai anty. Muna cewa mu samu lokaci mu shigo mu gaishe daku"

Zuwan nuriyya ya katse musu hirar. Lemo da cup ta ajiye ma anty maimuna a kasa. Ta na samun waje gefe ta zauna.

"Aikam dakin bar drink din nan. Daga gida nan nayo fa. Ya jiki?"

Murmushi nuriyya tai a kunyace.

"Naji sauki"

"Allah ya kara sauki ya raba lafiya"

Farhan dake zaune kan kujera ya amsa da.

"Amin thumma amin"

Zungurinshi nuriyya tayi tana mamakin rashin kunya irin ta farhan. Anty maimuna kanwar babanshi ce uwa daya uba daya.

Mikewa anty maimuna tayi.

"Bara kuga inzo in wuce. Nan har gidan hajja zanje"

"Anty wannan irin zuwa da wuri haka?"

Cewar farhan. Nuriyya ta karbe da fadin.

"Wallahi kuwa. Daga zuwa sai tafiya"

Dariya anty maimuna tayi.

"Daman jikinki nazo dubawa. Zumunci ai yanzun aka fara in banda abinku.

Duk ana tare"

Har kofa suka rakata suna shigowa nuriyya tasa kafadarta ta ture shi.

"Kai ko? Harda cewa amin. Kasa inata jin kunya"

Dariya sosai farhan yayi.

"Jimun ke please. An mana addu.a me kyau bazan amsa ba?"

Turo baki tayi tana dakuna mishi fuska. Hannuwanta ya kamo yana janta jikinshi.

"Me nace kan turo bakin nan a gabana?"

Kanta ta boye a kirjinshi tana dariya. Rungumeta yai tsam a jikinshi yana jin duminta.

Yana godema Allah daya tsara mishi rayuwarshi da ita a cikinta. Yana kuma sake gode Ma Allah da yasa ya bi shawarar nuriyya ya nemi dangin babanshi.

Laifin babanshi mai girma ne a gare shi. Waya sani wata rana ya iya yafe mishi. Ba zaka taba fadar me zai faru dakai ba a rayuwarka.

Sosai ya sake matse nuriyya a jikinshi. Kasa kasa tace mishi.

"Idan mace muka haifa sunan ta farhana in shaa Allah"

Murmushi yayi.

"Idan namiji ne sunanshi nawaf"

Dago wa tai daga jikinshi hawaye ba taruwa a idanuwanta. Wasu irin emotions na mata yawo.

"Da gaske? You will name him that?"

Kai ya daga mata yana sa hannu ya tallabi fuskarta.

"Da gaske sunanshi nawaf. Indai muka haifi namiji ko ba wannan cikin ba"

Sumbatarshi tai tana nuna mishi godiyarta. Kamun ta kwantar da kanta a kirjinshi.

"I love you. Thank you"

"I love you more. Allah ya jikan nawaf"

Ta amsa da.

"Amin. Allah ya jikanmu muma. Munfi nawaf bukatar wannnan addu.ar saboda karshen shi yayi kyau.

Namune abin tsoro"

"Shhhhhhhhh. Zaki kashemun jiki"

Farhan ya fadi. Dan maganganunta sun tsorata shi lokaci daya. Kuma sun shige shi. Dariya nuriyya tayi.

"Idan jikinmu yana sanyi lokaci lokaci kilan yasamu shiryama mutuwarmu kamun ta same mu"

Sauke numfashi yai. Yai shiru yana jin duminta da kamshinta. Lokaci daya kuma maganganunta na zauna mishi.

****

Blocks din robar dake gabanta take shiryawa kaman katanga. Mimi dake zaune saitasa hannu tarwatsa tana wata dariya dake saka safiyya dariyar itama.

Sunkai rabin awa zaune suna wannan shiriritar. Intai dariya saitai wani gwaranci da ita kadai take son fada.

A shekara daya mimi yarinya ce mai cikakkiyar lafiya. Gashi bata da rikici sam. Indai tayi kuka to bata da lafiya. Indai da kayan wasa to bata da matsala.

Tun ranar sunan mimi safiyya tai resigning. Tagaji da aiki. Tunda fu.ad na tsare mata duk abinda take so. Tana son bama Mimi dukkan kulawar da take bukata.

Sallama safiyya taji. Sake baki tayi tana kallon fu.ad daya turo kofar ya shigo. Ware mata idanuwa yayi.

"Ki amsa sallamata ba kina mun wannan kallon ba"

"Seriously ka gudo daga kasuwa ne ko?"

Dakuna fuska yayi.

"Ni ban gudo ba. Kuma akwai su lawal a shagon. Missing ya'ta nake na zo in ganta"

Karaso wa yai falon hadi da fadin.

"Hey sweetheart. Dad is home"

Tanajin muryarshi ta ci gaba da doka hannuwanta tana tarwatsa blocks din tana dariya. Kallon safiyya yayi dake fassara kingani itama tayi kewata.

Girgiza kai safiyya tayi da murmushi a fuskarta. Fu.ad sai abarshi. Haka yake yi daga kasuwa zai gudo gida yaga mimi sannan ya koma.

Wani lokacin ma daukarta yake yi. Sai safiyya taita fada tukunna. Wasu ranakun saidai tagaji tabarshi.

Hannu yasa ya dauki mimi yana hada goshinshi da nata. Yarinyar ta saba wasan da yake mata. Ita ta soma girgiza kanta jikin nashi suna dariya tare.

"Mimi is so cute. She is so cutee"

Dariyarsu tabama safiyya dariya sosai.

"In zubo maka abinci ko?"

Ta bukata. Ya girgiza kai.

"Restaurant naje naci delicious"

Mikewa safiyya tayi tana kallon shi.

"Res....  Me? Aidaka kirani kace kar insa abinci dakai. Zaka je kaci wanda yafi shi dadi"

A kasalance ya kalleta.

"Nikam banajin yin ringima sofi. Yunwa naji and restaurant din yana kusa damu.

Mukaje muka ci abinci. Ba saiki barshi da dare muci ba?"

Sosai take kallonshi.

"Da daren ma kaje restaurant. Akwai wani a kusa damu"

Ta fadi ta na matsawa hadi da karbe mimi daga hannunshi ta juya da yarta a hannu tana barin falon.

Dariya fu.ad yake sosai. Yana so yaga safiyya na fadan nan. Kyau take kara mishi kaman ya mayar da ita cikin shi.

Saida yai mai isarshi sannan ya tashi ya bita bedroom din. Tana zaune kan gado da mimi a tsakiyar gadon. Sarai taji shigowarshi.

Taqi juyowa. Tsayawa yai wajen katon hoton nana daya ke cike da bangon dakin ya kalleta. Yana jin wata irin kewarta taban mamaki.

Hannu yasa ya shafi kumatunta a jikin hoton. Sannan yadan daga kafadarshi.

"Mumynki fushi take mun. Harda kwace Mimi daga hannu na bayan tasan saboda ita kawai na baro da kasuwa"

Shiru yai. Zai iya rantsewa yaji sautin dariyar nan ta nana dake saka shi farin ciki na daban.

"Yeah mumynki akwai rigima sosai"

Juyowa safiya tayi.

"Dadynki akwai son kai sosai. Ya fada miki kome yaimun.

Abinci fa a restaurant bayan yasan ni kaina bana iya ci saiya dawo"

Kallon hoton fu.ad yayi ya daga girarshi da ke fassara mumynki bata karantata kaman yanda kikeyi. Yasan da tana nan tunda ya bude baki zata gane wasa yake.

Sannan ya juya ya taka har inda gake. Gefen gadon ya zauna. Ya dauko mimi ya dorata kan cinyarshi sannan ya kalli safiyya da take wani basar dashi.

"Ki kalle ni sofi"

Kauda kai tayi gefe.

"Please........ Sofiii"

Ya fadi yana jan sunanta yanda yasan ba zata iya mishi gardama ba. Juyowa tayi ta sauke idanuwanta cikin nashi.

"Goodness. Kina kyau da fada"

Naushin shi tai a kafada. Ya wani dakuna fuska yana fadin.

"Ouchhh yi hakuri sofi"

Hannuwanta tasa ta matse mishi kumatu tana fadin.

"Kasan in akwai abinda na tsana baifi kaci abinci a wani waje ba"

Ture hannunta yai yana gyara ma mimi zama kan cinyarshi.

"Ki kyaleni nikam. Yunwa nakeji cikina sai ihu yake tun dazun"

Dariya tayi tana mikewa. Wani irin jiri ya dibeta ta tafi luu. Da zafin nama fu.ad ya fisgota yana zaunar da ita kan gadon.

Kanta ta dafe da hannuwa biyu tanajin yanda dakin ke wulwula mata. A rikice fu.ad ke fadin.

"Subahanallah. Sofi menene? Lafiyarki kuwa?"

Gaba daya hankalinshi ya tashi. Saida tadanji jirin ya fara tsaya sannan tace mishi.

"bakomai fa. Kawai ina jin jiriri ne wasu lokuttan"

Muryarshi babu alamun wasa a ciki yace.

"Tun yaushe?"

"Wajen sati biyu. Amman bai fara damuna ba sai kwana biyun nan"

A kufule yace.

"Sati biyu sai yanzun nake ji? Damn it sofi in wani abu ya same ki fa?"

Ganin yanda ya birkice yasata dafa hannunshi.

"Really ba wani babban abu bane ba. Kawai jiri ne. Babu inda kemun ciwo banda shi"

Ture hannunta yayi.

"Tashi mu tafi asibiti"

"Ba wani......."

Kallon dayai mata yasa ta katse maganar.

"Kaci abinci sai muje"

Muryarshi a dake ya mike da mimi a hannunshi.

"Bana jin yunwa"

Mikewa tayi tana dafa shi da fadin.

"Kayi hakuri"

Kallonta yai taga yanayin dake cikin idanuwanshi.

"Har yau inajin cewa kaman da nazo da wuri nana zata kasance tare damu.

Nasani ba tunani me kyau bane ba. Amman na kasa dainawa. What if wani abu ya sameki?

Dan Allah karki sakemun irin wannan. Da ciwo sosai"

Jikinta a sanyaye tace.

"Bazan sake ba. Please kayi hakuri"

Dan dafe kai yayi.

"Ya wuce. Dauko mayafinki muje mu dawo"

"Dakaci abincin sannan"

"Abinci can wait. Saimun dawo"

Tasan halinshi.  Tsayawa gaddama babu amfanin dazai dan haka ta wuce ta dauki hijab dinta ta saka. Suka fita.

****

Kallon jana suke su dukansu. Kallonta suke kaman kaho ne ya fito mata tsakiyar kai da maganar data gaya musu.

Kallon da suke mata ya bata dariya sosai.

"Wai menene kuke kallona haka? Nace matarka nada ciki na wata daya da sati biyu. In baku gane turancin ba"

Safiyya kallon fu.ad take zuciyarta na wani irin dokawa. Shima kallonta yake lokaci daya maganganun doctor din daya jagoranci yi mishi surgery na vasectomy suka dawo mishi.

Cikin harshen turanci yake fada ma fu.ad din cewar.

"Ko da bayan shekaru ko watanni matarka ta samu ciki karka zargeta. Ka dauka jikinka ya warkar da kanshi.

Yana faruwa ga wasu mutanen."

Hannu fu.ad yakai yana tsane gumin daya tsattsafo mishi. Zufa yake ta ko ina.

Ta bakinshi yake jan iska saboda ya daina jin shigarta na wani lokaci. Mimi ya sake gyara ma zama kan jikinshi.

Su dukansu sun kasa magana. Hawaye ke zubo ma safiyya wasu nabin wani. Tunani take wanne kyakkyawan aiki ta yi da Allah ya bata wannan kyautar.

Shi ka shi fu.ad tunanin da yake kenan.

"Oh Allah. Ina bayin da suka sake ka suka kama waninka? Hakika suna cikin bata mai muni"

Ya karasa maganar yana jin wasu hawaye masu dumi sun zubo mishi. Hannunshi safiyya ta kamo da nata duka biyun.

Ya dago dasu ya sumbace su saboda mimi dake hannunshi. Ya kasa tsaida hawayenshi. Allah Ya dube shi da Rahma ya mishi kyauta daya yanke rai da samunta.

Hakika indai kana da rai. Baka fidda rabo. Saidai Rabonka yai jinki. Inda Allah ya rubuta maka shi to saika samu.

Mimi kaman tasan farin cikin da suke. Ta kyalkyale da dariya. Kallonta sukai a tare suna murmushi though hawayen da suke zubdawa.

Doc jana kuwa gyara zama tai tana kallon su tana koyan darussa masu dama daga rayuwarsu. Da murmushi a fuskarta.

Kallon cikin safiyya fu.ad yayi ya kalli mimi. Ita kuma kallonshi take. Lokaci daya abinda su duka biyun suke tunani ya bayyana a fuskarsu.

Hannu safiyya takai da sauri ta karbi mimi tana rungumeta. Hawaye na sake zubo mata.

"No please. Ba zasuyi mana haka ba"

Yanda tai maganar yagane so take ya tabbatar mata. Sadda kanshi kasa yai da wannan sabon farin cikin daya same shi fargaba na rabuwa kusa dashi.

Mikewa yayi ya mika mata hannunshi tasa nata ciki suka juya. Jana murmushi ta sake yi dan ganin sun tafi wata duniya ta daban.

Sanda suka samu natsuwa sun nemeta.

****

Daga bedroom ya fito zee na zaune a
falo kan kafet da plantain chips a gabanta tana ci tana danne danne da wayar lukman din.

Kusa da ita ya tako ya zauna. Hannu yakai zai dibi chips din ta janye. Dakuna fuska yayi.

"Bani wayata nima. Wai meye ma amfanin wayarki? Kullum sai kin cinye mun charge"

Dariya tai tana janye wayar gefe.

"Taka tafi dadin amfani"

Kallonta yai yana daga mata gira. Dan wayarta tafi tashi tsada da komai.

"Muyi musanya to"

Makale kafada tayi.

"Ni dai ka kyaleni ina karatuna"

Kwanciya yayi yai filo da cinyarta ta ture kanshi. Ya sake komawa.

"Dee ka dagani. Duk ka mokalemun ci nya."

Dariya ta bashi sosai.

"Dan kan nawa guda nawa yake? Nafijin dadin kwanciya anan dinne kawai"

Cikinta ya kalla.

"Nifa na kagu inga ajiyata ta nuna"

Murmushi zee tayi.

"Kwanan shi nawa dazai fito? Dan ba a jikinka yake girma bako?"

Gyara kwanciyarshi yayi.

"Da kinga yanda ake laulayin ciki kuwa."

"Allah ko? Me zakayi?"

Juya kwanciyar yai yana kallon fuskarta.

"Ai ko wanka sai kinmun. In na zauna waje daya sai dai ki daukeni ki mayar wani waje in nagaji.

Ke abinci ma inba a baki ba kuka zansa. Rikici kala kala"

Jinjina kai zee take da wani murmushi a fuskarta. Mikewa lukman yai daga kan cinyarta yana kallonta muryarshi babu wasa yace.

"Wallahi wasa nake miki."

"Aifa. Ashe ni wahala nake sha. Ga yanda ya kamata ace ina yi......."

Katse mata magana yai da fadin.

"Aa wallahi. Yanda kike yin nan ma ya isheni"

Girgiza kai tayi. Zatai magana kenan sukaji sallamar su fu.ad. Da fara.a suka tarbesu.

Zee ta kawo musu ruwa da lemo. Bama su sha ba. Mimi na hannun fu.ad tana bacci. Yanayin sanyin jikinsu lukman ya kalla.

Yasan akwai damuwa a tattare dasu.

"Lafiya dai ko?"

Ya tambaya cike da kulawa. Takardar dake hannun safiyya fu.ad ya karba ya mikama lukman.

Cike da rashin fahimta ya karbi takardar ya duba. Ta asibiti ce. Sunan safiyya ne rubuce a jiki. Wani irin dokawa zuciyarshi tai ya soma dubawa babu wata nutsuwar kirki a jikinshi.

Idanuwa ya ware. Yana sake daga takardar yana dubawa. Mamaki karara a fuskarshi. Fu.ad ya kalla da ya zuba mishi idanuwa da wani irin yanayi.

Sakkowa fu.ad yai daga kan kujerar gwiwoyinshi a kasa gaban lukman. Safiyya ma sakkowa tayi hawayenta har sun soma zuba.

Kan fu.ad na kasa yace.

"Daga asibiti nan muka zo. Bamu je ko ina ba. We have to know. We need to know ko hakan zaisa ku karbeta......"

Da rashin fahimta zainab take kallon su duka ukkun. Dan taga alama ita kadaice bata fahimci meke faruwa ba. Takardar dake hannun lukman ta karba ta na dubawa.

"Please don't take her away. Please lukman wallahi......"

Kasa karasawa fu.ad yayi saboda yanda wani abu ya tsaya mishi a wuya. Ga kirjinshi na wani irin zafi.

Kallon Mimi yake dake baccinta a jikinshi. Hannunta daya rike gam da rigarshi. Wani zafi yake ji a kirjinshi kaman wuta.

Tunanin rabashi da yarinyar nan kawai ji yake zuciyarshi na neman bugawa. Wasu hawaye masu zafi suka zubo mishi.

Safiyya dake gefen fu.ad taja hijab dinta ta goge idanuwanta muryata na sarqewa tace.

"Zamu..... Zamu hakura da babyn jikina.....dan Allah kubar mana ita"

Kallon zainab lukman yayi. Muryarshi dauke da wani emotions da ya kasa tsayarwa akan komai yace mata.

"Kingan su ko zee?"

Ita har sun sakata hawaye ma. Tasa hannu ta goge su. Har ranta tana musu murnar kyautar nan da Allah yai musu.

Kuma zuciyarta na mata wani irin yawo kan kaunar da take karanta suna ma Mimi. Kaunar da ta dauka jininka ne kawai zakai ma.

Ko tsakanin fu.ad da lukman ta fahimci akwai yiwuwar bare yai maka kaunar da dan uwanka ne zai maka.

"Allah saina fada ma abbah abinda kaimun. Taya ma wannan banzan tunanin zai zo maka?

Safiyya kema ya shafa miki yarinta ko? Allah zaku sani idan na fadaku da abbah"

Dago kai fu.ad yayi ya kalle shi. Yasa hannu ya goge fuskarshi. Muryarshi a dakushe yace.

"You are not a fucking kid lukman"

Hararshi lukman yayi.

"Kasan fu.ad ai ko? To ka kalle shi zaka san na girma sosai. Marar hankali kawai.

Wallahi da ba gaban yarka bane saina kwada maka mari ko zaka dawo hankalinka"

Zainab ta fara dariya. Kamun safiyya ta dauka. Fu.ad kanshi murmushi yake.

Lukman kam ya kasa ganin abin dariya har yanzun.

"Kubarmun gida please. Ku tafi kamun ku kara batamun rai"

"Sorry......."

Fu.ad ya fadi. Sake dakuna fuska lukman yayi.

"Please...."

Kallonshi lukman yai ya ware idanuwa.

"Dan sake cewa please muji?"

Dariya fu.ad yayi.

"Fucking grow up"

Dariya sukayi a tare. Kamun in a serious murya fu.ad yace.

"Nagode. Kamun abinda ko haneef baimun shi ba lukman. Kaunarka a gareni mai girma ce.

Taya zan iya biyanka?"

Dafa kafadarshi lukman yayi.

"Ka kasance dan uwana har karshen rayuwata. Ka kasance cikin farin ciki gwargwadon iyawar ka. We are even"

Wasu hawayen fu.ad yaji sun cika mishi idanuwa. Baisan me ya same shi da kuka ba kwanakin nan. Sai dai kawai yaji suna fitowa.

"Hakika hanyoyin Ubangiji Masu Girma ne. A kanku na yarda ko asibiti ka hadiye in Allah yai niyyar baka kyauta baka isa ka kauce mata ba.

Akanku na yarda da cewa a dukkan hakuri akwai riba. A dukkan tsanani akwai sauki saidai jinkiri zai iya samuwa.

Allah ya dawwamar muku da farin ciki"

Cewar zainab da takejin wata nutsuwa ta daban. Ko da family dinta basu damu da ita ba. Ga wasu da bata hada jini dasu ba tana jinsu har cikin jininta.

A kasalance safiyya tace.

"Hmm zainab. Amin. Amman Allah ya bamu zuciyar karbar jarabawarshi shine addu.ar da muka fi bukata.

Da yawan farin ciki da yawan jarabta. Wannan shine asalin Kusancin mu da mahaliccinmu"

Kai suka jinjina cike da jin maganganunta. Ganin yanda jikin kowa yai sanyi yasa lukman cewa.

"Kunsan da nana taga fuskokin ku me zata ce? Nayi laifi ko? Uncle ya naga kowa is looking so serious?"

Yanayin muryarshi da tuna Nana yasa su dariya su dukansu.

Nana ta musu nisa amman memories din data bar musu nasa su farin ciki.

Har bakin mota su lukman suka rakasu.

****

Saida suka biya gidansu inna. Babu wata kunya fu.ad ya fadama su inna kyautar da Allah yai musu.

Addu.a sukai musu gabaki daya kamun su wuce gidansu fu.ad. Yana parking din motarshi suka fito suna
cin karo da haneef.

Gaisawa yayi da su yana tambayar ya mimi. Mika mishi ita safiyya tayi yaga bacci take yace tabarta karsu motsata ta tashi.

Wuce wa cikin gida safiyya tayi abinta. Tabarsu nan. Hugging din haneef fu.ad yayi cike da farin ciki.

Harya sake shi da mamaki a fuskar haneef. Kamun fu.ad yace.

"Allah heal me haneef. Sofi ciki gareta"

Ware idanuwa haneef yayi kamun jikinshi yai sanyi.

"Allahu Akbar. Allah kenan fu.ad. oh.  Alhamdulillah"

Sosai haneef yai murna da mamaki da kuma jinjina lamari na kaddara. Kamun suyi sallama fu.ad ya shiga cikin gidan.

Safiyya ya samu da momma a zaune. Sallama yai ko jira momma ta amsa baiba ya karasa tsakiyar falon ya zauna kasa.

Kafafuwanta ya kama da hannayenshi yana dora kanshi a cinyarta. Wai saida yazo gabanta girman abinda ya samu ya sake lillibe shi.

Hawaye ke zubo mishi. Ya rasa bakin dazai fada ma momma wannan labarin.

"Fu.ad lafiya? Subahanallah. Safiyya me ya faru?"

Sadda kanta kasa tayi. Kukan da fu.ad keyi nasa hawayenta sake zuba.

Jin yanda momma ta daga hankalinta yasa shi cikin kuka fadin.

"Momma sofi ciki take da. Zan sake haihuwa. Momma addu.arku a kanmu da albarkarku tayi tasiri."

Hamdala momma take. Addu.arta kullum bai wuce Allah ya basu rabo ba.

"Fu.ad ai abin farin ciki ne bana kuka ba"

Dagowa yai gana goge fuskarshi.

"Kukan farin cikine momma."

Murmushi tai musu. Basu jima gidan ba suka wuce.....!

****

Tsakiyar dakin suka tsaya. Mimi na hannun safiyya. Mayafinta ta cire ta ajiye. Tana kallon Mimi sannan ta kalli fu.ad.

"Allah ya jikan Nana. Zata so ganin wannan ranar"

Karasowa fu.ad yayi kusa da ita yana hade sauran space din dake tsakaninsu. Yasa hannu ya dago da habarta.

"Tana inda yafiye mata nan sau dubu. Saimu cika aikin daza mu sameta"

"Allahumma amin"

Safiyya ta fadi da murmushi.

Rikota yai ita da mimi jikinshi yana kissing goshinta.

"Alhamdulillah da rayuwarmu ta baya ta koya mana darussa da dama. Alhamdulillah da rayuwar da muka samu yanxun.

Alhamdulillah da duk tsarin da Allah yai mana nan gaba"

Rikoshi tai da dayan hannunta tana jin wata kaunarshi ta daban tana ratsa ta.

"Ina sonka sosai. Kaddarar data hadamu ta koya mana darussa da dama. Alhamdulillah"

Murmushi yayi.

"Ta kara mana imani. Alhamdulillah. Ina sonki sosai"

Ya fadi yana lumshe idanuwanshi. Wata nutsuwa na ratsa shi. Tabbas duk wanda ya Rike Allah ya yarda da Kaddara mai kyau ko marar kyau yana tare da Nasara.

*#TeamAS*

AKAN SO 48

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

www.Loobnerh.blogspot.com

Wattpad: LubnaSufyan

                48

*A ko da yaushe a rayuwa idan kace zaka dinga duba baya. To da wahalar gaske gaban tai maka dai dai*

*Bazai rageka da komai ba dan ka yafe. Ba ace ka manta ba. Wannan abune mai wahala. Baiwa ce da bakowa Allah yaiwa ba*

*Sai dai ka sani ana ci gaba da zama da juna ne bawai dan an manta bacin ran daya faru ba. Ana zama ne saboda an YAFE*

*Allah ya nuna mana RAMADAN lafiya. Amin thumma amin*

*Ba saina ce nagode da comments dinku da prayers ba saboda ai #AnaTare. Like sosai sosai*

*TWO MORE pages In shaa Allah*

Yana shigowa gidan da sallama yaga baiga nuriyya ba. Ciki ya shiga ya duba bedroom dinta.

Dan yasan bata cika zama falo ba. Tafi gane tai kwance a bedroom din in bashi ya dawo yazo ya fito da ita ba.

Zuciyarshi yaji tana dokawa babu dalili. A rikice ya fito yana fadin.

"Nuriyyaaaa"

Da saurinta ta fito daga cikin. Idanuwanta ta sauke cikin nashi. Wata ajiyar zuciya ya sauke yana tura hannunshi daya cikin sumar kanshi.

Da mamakin ganin tsoron da har lokacin bai barshi ba yasata fadin.

"Yaya farhan. Lafiya dai ko?"

Kai ya daga mata yana dora murmushi a fuskarshi.

"Ina kitchen ne banji shigowarka ba"

Ta fadi a sanyaye hadi da dorawa da.

"Ka daina tunanin zaka nemeni ka rasa yaya farhan. You are the only family da nake da.

Please banajin dadi"

Kunyarta yaji ta rufe shi. Har ranshi yana tsoron ya nemeta ya rasa. A yanzun shima bashida wani family bayan ita.

"Na daina. I am sorry"

Kai ta daga mishi alamar komai ya wuce.

"Nace ki daina damuwa da dafa abinci. Zamu iya fita waje muci"

Dan murmushi tayi mishi tana jin wani quna a zuciyarta. Nawaf ya koya mata kyamar abincin waje komin tsaftar restaurant ko hotel kuwa.

"Ba wani aiki bane. Tunda babu yawa"

Kai ya daga mata ya zagaya ya zauna kan kujerar.

"Zo mu zauna"

"Barin sauke girki sai inzo"

Ta fadi tana juyawa. Bata fi mintina goma ba ta fito. Waje ya samu gefenshi ta zauna.

Kallonta yai sosai. Muryarshi da fuskarshi tana nuna mata muhimmancin maganar da yake son fada.

"Naje gidan anty ne yau. Naje inji ko tana da wani abu da ya rage na lokacin data tsince ki.

So ba a samu komai ba sai School back dinki. Na karbo amman ban bude ba. Banma san yanda zakiyi handling abin ba na bari in fara fada miki"

Kan nuriyya a kasa tana jin hawayen da suka taru a idanuwanta suna zuba. Zuciyarta dokawa take.

"Nuriyya....."

Ya kira a hankali. Tun a hanya yake tababar fada mata. Yadan samu a satin nan ta fara warwarewa har tana dan hira dashi.

Zai jagula komai akan maganar da babu tabbas a cikinta. Babu ma wani hope ko za.a samu wani clue cikin jakar.

Hannunta takai ta kamo na farhan ta dumtse. Karo na biyu da jikinsu ya hadu tun zuwanta gidan. Kaman yanda yai mata alkawarin zama duk abinda take son shi ya zame mata har saita shirya canzuwar hakan.

Bai karya ba. Beside inya kula bata son magana bata waje yake.

"Ina tsoron a bude jakar da kace ka karbo a samu babu komai a ciki. Ina tsoron ko bazan taba ganin dangina ba.

Idan ina dasu kenan. Bansan me ya kamata inyi ba"

Dayan hannunshi yasa ya hade nata cikin nashi duka biyun. Cikin idanuwa yake kallonta. Sannan yace.

"Rashin budewa a duba zai sa ki zama cikin tambaya a ko da yaushe.

Budewar bazai cutar dake ba nuriyya.  Kilanma ki tuna wani abu. Allah kadai yasan me ya boye miki a bayyanar gaskiyar nan.

Inkuma kina so magana da anty ne directly sai muje"

Da sauri ta girgiza mishi kai. Wani irin tsoro na shigarta. In akwai abinda tafi tsana bai wuce ta sake dora fuskarta kan azzalumar mata kaman anty ba.

Ko a mafarki bata fatan Allah ya sake hadasu ballantana kuma idanuwa biyu.

"Bana son sake ganinta yaya farhan. Na tsaneta wallahi"

"I understand...."

Da rauni a muryarta tace.

"Zamu bude jakar tare. In babu kai bazan iya ba"

Kasa controlling emotions dinshi yayi. Ya kara matsawa ya sumbace ta a kunci sannan ya saki hannunta ya mike yana ficewa daga falon.

Hannu tasa ta goge fuskarta. Zuciyarta na wani irin dokawa. Tana jin ya shigo da sauri ta daga kai ta kalle shi.

Kamun ta maida kallon kan yar jakar dake hannunshi. Kurar da jakar tayi ya hana asalin kalarta ta fito. Kaman ash colour. Kara sowa yayi ya zauna.

Sannan ya mika mata jakar ta karba tana jujjuyata. Da duk wani abu na jikinta take son taji wani connection tsakaninta da jakar ko ta tuna wani abu ko ya yake amman ta kasa.

Muryarta na rawa tace.

"Na kasa tuna komai yaya farhan"

Dafa hannunta yayi. Ya na karbar jakar ya ajiye kan kujera.

"May be shekarunki ba masu yawa bane da zaki rike wani abu. Ki bude"

Kai ga daga mishi. Zuciyarta na wani irin dokawa. Ji take kaman inta bude jakar zata iya ganin wani abu dazai tuna mata asalinta.

Ta wani fannin kuma tanajin tsoron yanda ta daga burinta har haka. Jin farhan ya sake dafa hannunta ya sata jan wani numfashi sannan ta sa hannu kan zip din jakar ta bude.

Bugun zuciyarta na karuwa. Hannu tasa ta daga jakar hadi da zazzageta kan kujerar. Tasa hannu tana taba kayyakin da suka zubo daga ciki kaman zasu bata amsar data kasa samu.

Books ne a ciki gabaki daya na yan Nursery 1. Farhan ne yasa hannu ya dauki guda daya daga ciki. Yaga inda anty taga asalin sunan Nuriyya kenan.

Gashi nan da manyan baki a rubuce. 'Nuriyya habeeb danori'. Habeeb danori farhan yake maimaitawa cikin kanshi yana tunanin inda ya taba jin sunan.

Sosai yake dubawa. Dan ware idanuwa yai ya kalli nuriyya da idanuwanta ke kafe kan littatafan da take ta shafawa.

Ya bude baki sai ya fasa. Gidan mai ne yagani wajen bachirawa. Sai dai zai iya yiwa habeeb danori da yawa cikin garin kano.

Baya son ya daga mata burinta sai ya tabbatar tukunna. Duk da yana da wani irin feeling mai karfi kan hakan. Bazai daga mata buri yazo ya tarwatsa shi ba.

Yana kallonta ta dauki littafi daya tana sa hannu tana shafa wajen da sunan yake.

"Asalin sunana Nuriyya. Anty tagani. Taga sunana ta kasa kaini inda dangina zasu nemeni.

Saboda me? Meye ribarta na tsintata ta kasa kaini inda za a ganni? Amfanin me nai mata?"

Shiru farhan yayi saboda baisan me ya kamata yai mata ba. Matsawa yayi ya kama Hannuwanta. Kwacewa tayi.

"Saboda me? Ina da family kaima kagani. Kaga shaida yaya farhan me yasa zata tarwatsa mun rayuwa?

Duk shekarun na ina tunanin ko kalar mahaifina bazan taba sani ba. Ina tunanin mahaifiyata karuwa ce.

Kasan tashin hankalin dake cikin hakan?"

"Nuriyya please calm down....."

Farhan ya fadi. Cikin hargowa tace.

"No yaya farhan. Ba zaka taba ganewa ba saboda kayi normal rayuwa ba irin tawa ba"

Kallonta yake maganganun data fada suna masa wani irin zafi. Muryarshi can kasa yace.

"Nuriyya. Ki bar maganar nan. Zan nemo miki su in shaa Allah"

Hawayen da suke zuba idanuwanta tasa hannu ta goge.

"Idan kuma ba sa nan fa? Ba zaka taba ganewa ba"

A tsawace yace.

"Yes bazan gane ba nuriyya. Na dauka kinsan kadan daga cikin rayuwata.

Kinsan waye babana. Bance yafi anty ba. Ban kuma ce kalar su daya ba. Ki kalle ni sosai.

Na miki kama da wanda yai rayuwa normal?"

Shiru tayi tana kallonshi yanda ya birkice lokaci daya.

"Ko kin taba tambayata ina kanwata da nake baki labari?

No baki tambaya ba. Ni kuma ban fada miki ba saboda what is there to tell?

Ince nuriyya kinsan me ya faru da farhana kuwa? Ina kallo babana ya sha giya ya bugu yace saita bishi sun fita unguwa.

Ina tsaye saboda tace tana son zuwa gudunma tashin hankalin shi nabarta.

Bayan komai na jikina na mun ihun kuskuren hakan. Ina kallo yaja mota suka bar cikin gida ban tsayar dasu ba.

Yeah naga kuskurena awa biyu tsakani da aka jeramun gawarsu a gabana.

Sai dai kinsan me? I deserve the pain na mutuwar farhana saboda ni ne sila. Him? That Monster? I wish baiyi mutuwa mai sauki ba......"

Inalillahi wa ina ilaihi raji.un kawai nuriyya ke fadi cikin zuciyarta. Sai yanzun taji dalilin da duk murmushin da farhan zai akwai wani irin sadness a karkashi shi.

Hannu tasa ta dafa mishi cinya. Amman kaman ma baya jinta.

"Yaya farhan....."

Ta fadi hawaye na zubo mata ganin yanda jikinshi ke kyarma. Yanda komai nashi ya canza. Yanayin ciwon abinda yake ji bayyane a fuskarshi.

Juyowa yai ya kalleta sosai.

"I don't know exactly yanda kike ji. But bake kadai kike hurting ba. Bake kadai bace nuriyya"

Mikewa tai ta matsa ta zauna kan cinyarshi. Kamun yagama mamaki tayi hugging dinshi sosai. Kuka take. Shikam ya kasa. Yanajin kalar raunukan da yake dasu zafinsu da ciwonsu ya girmi hawaye.

Riketa yai a jikinshi yana jin yanda yanayin ke fifita mishi inda yake masa zafi. Sumba ya manna mata a gefen fuska.

"Ki daina kuka. In shaa Allah zan nemo miki family dinki. Za.a gansu"

Kai take dagawa tana sake kankame shi. Cikin kunnenshi tace.

"Kaima ka gano naka please. Ka gano mana family dinmu"

Shiru yayi yana juya maganarta.

"No naki dai nuriyya. Mum na bata da kowa. Shikuma....... Yeah sunyi gefe lokacin da yake abusing dinmu.

Saboda yana da kudi babu wanda zai iya mishi magana"

Sake rike shi tayi.

"Nasani. Ka yafe musu dukkanmu muna kuskure a rayuwarmu"

Lumshe idanuwa farhan yayi.

"Mu bar maganar for now please"

Dagowa tai daga jikinshi. Ta kalli fuskarshi sosai.

"For now"

Ya daga mata kai da yake nuna alkawarin zasu sake maganar amman ba yau din ba. Komawa tai jikinshi ta kwanta luf.

Ya riketa yana lumshe idanuwanshi. Rayuwa makaranta.....!

"Na dauka sai da yamma zamu tafi"

Safiyya ta fadi a sanyaye tana kallon fu.ad. Girgiza mata kai yayi.

"Mu koma gida kawai. Zama anan bazai sake komai ba."

Kai ta daga mishi ta na dauke idanuwanta daga fuskarshi. Tana jin ciwon yanda zata koma gidan su da yake cike da memories din nana.

Yau kwana hudu kenan da rasuwar. Su dukansu kallo daya zakai musu ka fahimci yanda rayuwa ta koya musu darasi da dama.

Musamman safiyya da fu.ad da sukai wata irin rama. Ya karanci me take gudu tsaf. Ya share ne saboda yasan gudu wa feelings dinsu bazai canza komai ba.

Da yawan gudun da suke da yawan yanda zai musu zafi idan ya kamo su. Ya riga da ya fada ma momma zasu koma gida tun dazun.

Itama da taga kaman yayi sauri dayai mata bayani saita fahimta.

"Bara to in dauko mayafina sai in sallama da momma"

Kai kawai fu.ad ya iya daga mata. Baiko zauna ba dan yasan ba dadewa zatai ba.

Shi kanshi zuciyarshi cike take da tsoron kalar ciwon da zaiji in suka karasa gidan. Kewar Nana har cikin tsokarshi yake jinta.

A zuciyarshi wani irin fili ne tabari da babu wanda zai iya maye shi. Wajenta ne ita kadai. Lumshe idanuwanshi yai hannuwanshi cikin aljihu.

Murmushinta ya tuna da yanda take bude idanuwanta idan taganshi. Baisan sanda murmushi ya kwace mishi ba. Cikin zuciyarshi yake fadin.

"Allah ya haskaka kabarinki nana. Kin barmu da kewa ko? Nagode da tare da kewarki akwai moments irin wa.annan"

Tabashi yaji anyi. Da sauri ya bude idanuwanshi ya sauke su cikin na safiyya. Lokaci daya murmushin dake fuskarshi ya bace.

"Murmushin me kake?"

Hannunta ya kama suka nufi hanyar fita. Cikin sanyin murya yace.

"Bakomai kawai na tuna yanda Nana take nata ne bansan sanda ya bayyana ba"

Ga mamakin su duka biyun dariya safiyya tayi. A karo na farko tun rasuwar nana.

"Kasan akwai lokacin da ina fever. Naji nana shiru inata kira ashe tana kitchen.

Kasan me take?"

Da murmushi a fuskarshi ya girgiza mata kai. Dariya ta sake yi lokacin sun karasa bakin motar. Tsaye fu.ad yai yana kallonta yana son ta karasa bashi labari.

Cikin fuska take kallonshi.

"Kwai ta soyamun ta hado tea. She was 7 lokacin. Karka ga fuska ta sanda ta shigo dakin.

Ranar na fara jin tsoro a rayuwata. Ina tunanin data kone fa? Ko ta zubo ma kanta ruwan zafi.

Abinda tayi ya tabani sosai na kasa mata fada. Karka ga fuskata lokacin da nai tasting wainar kwan.

Goodness. It was awful"

Wanna karin fu.ad ne yai mamakin daga inda dariyarshi ta fito. Daga shi har ita dariya suke. Kamun wasu hawaye masu zafi su zubo ma safiyya.

"I miss her. Every second da bata nan ina jinshi a ko ina nawa wallahi"

Rikota yai jikinshi yana matse ta dam. Shi kanshi yanajin irin ciwon da take ji.

"Sofi kina da memories irin wannan ke. Banda su da yawa.

Dan Allah ki dinga sharing mun nima in samu? Zamu saba da kewarta a hankali. Komai zaiyi mana sauki"

Dagowa tai daga jikinshi tana goge fuskarta.

"Zan sharing maka duka. Duk wani babban abu da karami dazan iya tunawa"

Kai ya daga da murmushi a fuskarta. Itama kasa boye nata murmushin tayi. Tace mishi.

"As much as tunanin nana zai mana ciwo. Farin cikin dake tattare dashi mai girma ne"

"Ta tafi tabarmu da kewarta ne. Shisa zaiyi ciwo. Amman kuma tabar mana abubuwan farin ciki da yawa. Ina jina da sa.a sosai dana santa a rayuwata"

"Nima haka...... Muje gida dai"

Kai fu.ad ya daga yana sauke numfashi hadi da bude ma safiyya motar. Shiga tayi ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima.

*

Suna hanya sun kusa kai gida ma wayarshi ta hau ihu. Saida ya rage gudun da yake sannan ya lalubota daga aljihunshi.

Dubawa yai yaga lukman ne. Ya daga ya kara a kunnenshi. Kamun yace wani abu lukman yace.

"Fu.ad please ka gayama hajiya muna nan Aminu kano. Zainab ke labour.

Inata kiran wayarta baya zuwa"

Ware idanuwa fu.ad yayi.

"Wallahi nima na fito. Bara na kira momma sai taje su taho"

Kaman lukman zaiyi kuka yace.

"Please kai sauri. Ni kadaine a wajenta"

Katse wayar yayi. Fu.ad ya mikama safiyya wayar.

"Lukman ne. Kira momma kice su taho ita da hajiya. Zainab ke nakuda kuma ba kowa wajenta"

Da sauri safiyya ta lalubo number din momma. Allah ya taimaka ringing daya momma ga dauka. Fada mata tayi.

Sannan ta ce ma lukman.

"Da munje asibitin ma ai"

"Are you sure?"

Kai ta daga mishi tana masa kallon dake fassara tambayata ma kake. Lukman da zainab ake magana ba wasu ba.

*

Sun riga su momma zuwa asibitin. Lukman suka samu kallo daya zakai masa kasan yana cikin tashin hankali.

"Ya zainab din?"

Safiyya ta tambaya. Kai ya girgiza mata alamar bai sani ba. Kallon wajen fu.ad yake yana mamakin ganin lukman din ne kawai.

"Ina family dinta. Ka kira mamanta?"

Kallonshi lukman yayi. A sanyaye yace.

"Bata san babanta ba. Da cikinta ya rasu. Wajen haihuwarta mamanta ta rasu. Ita kadai ce wajensu"

Kai fu.ad ya girgiza. Yana jin wani abu daya tsaya mishi a wuya. Har safiyya kasa cewa komai sukai. Lukman ya yatsina fuska.

"Basu damu da ita ba. Lokacin da naje neman aurenta yi sukai kaman sun gaji da ita. Kaman daman jira suke su samu maraba da ita"

"Hmm duniya kenan. Rayuwar duka guda nawa ce"

Fu.ad ya fada yanajin wani tausayin zainab din ya cika zuciyarshi. Safiyya ta bude baki zatayi magana su momma suka karaso.

Kaman zuwansu wajen ya taho da sa.a. kamun ma suce wani abu. Nurse ta fito tana tambayar wanda suka kawo zainab.

Su dukansu suka nufe ta suna tambayar yaya. Murmushi tayi.

"Ta sauka lafiya. Ta samu baby girl. Suna cikin koshin lafiya. Zaku iya ganinta nan da mintina sha biyar in an shiga da ita dakin hutu"

Su duka hamdala suke. Cikin yanayin murnarsu fu.ad ya matsa ya kamo hannun safiyya ya rike. Dumtsewa nashi tayi tasan tambayarta yake ko she is okay.

Shisa ta amsa shi itama. Duk da halin rashi da take ciki bai hanata taya su zainab farin ciki ba. Haihuwa kyautar Allah.

Momma ta bude jaka ta zaro kudi taba nurse din hadi da yi mata godiya. Nan suka tsaya suna jira a fito da zainab din dan su shiga su ganta.

Aikam ana zuwa aka fada musu zasu iya shiga su ganta. Suka dunguma su dukansu. Tana kwance babyn na gefenta.

Momma ta fara daukar babyn ta mika ma lukman ya karba. Hamdala yai daya saukar da matarshi lafiya kamun ya kai kunnen babyn saitin bakinshi.

Kiran sallah yai mata cikin kunnen kamun da addu.o.i sannan ya matsa wajen fu.ad mika mishi ita yai.

"Kai mata huduba"

Ware idanuwanshi fu.ad yayi cike da alamar tambaya.

"Ko wanne suna yai maka"

Lukman ya fadi kasa kasa.

"Ya sunan maman zainab?"

Fu.ad ya fadi yana karbar yarinyar da yakejinta yar kararrama a hannunshi. Kallonta yake so cute. Yanajin wani abu a xuciyarshi daya kasa bama suna.

"Aisha"

Kai fu.ad ya daga ma lukman saboda bazai iya magana ba a yanayin da yakeji. Addu.o.i sosai yaima yarinyar ya mika ma lukman ita.

Yanajin yanda yai kewar dan nauyinta a hannunshi a iya mintinan datai wajen shi. Hajiya lukman ya mika ma yarinyar.

Ta karbeta itama tai mata addu.a sannan tabawa safiyya. Idanuwanta cike da tausayawa. Karbarta safiyya tayi ta kura mata idanuwa kamun tace.

"Zainab kamarku daya lukman ka bata mun daughter da guntun hanci"

Dariya sukayi. Suna jinjina ma karfin halin safiyya din. Da idanuwa lukman ya ke rokon hajiya da su dan bashi waje da zainab.

Tasan dalilin hakan ta dafa momma kamun ta mike. Ta fahimci so take subar dakin. Dan haka babu wani bata lokaci ita da momma suka fice.

Fitarsu ta fahimtar dasu safiyya. Ta mike hadi da bama zainab babyn.

"Allah ya raya ya sanya mata albarka"

Kasa dakai zainab tayi. Tana jin kunyar safiyya din. Dan murmushi tayi ta kalli fu.ad suka fice daga dakin suma.

Karasawa gefen gadon lukman yayi. A tsorace yake kallon zainab. Hannu yakai ya taba fuskarta.

"Sannu zee na. Allah ya miki albarka. Allah yasa kece matata har a aljanna"

Cike dajin dadin addu.arshi ta dafa hannunshi dake kan fuskarta

"Amin. Zan yi alfahari dee. Samun miji irinka sai an tona. Bazan taba manta karamcin da kaimun ba.

Kaime komai nawa kai....."

Saurin janye hannunshi yai daga fuskarta yana rufe mata baki.

"Shhhhh. Bana so. Banaso kina fadar haka. Abinda nai miki in kyauta ce kinbani linkinta da junior. Idan bashi ne kin ribamun riba mai girma.

Ina sonki zee. Zan fahimta in kin fasa niyyarmu. Wallahi bazan taba kallonki da abin ba.

Saboda cikin ba a jikina ya zauna wata tara ba. Bani nai miki naqudarshi ba.

Bana so kiyi abinda zakiyi nadamarshi dan farin cikina ba....."

Wannan karin ita ta rufe mishi baki.

"Ko da nake nakuda da niyyarmu daram a zuciyata dee"

Sauke numfashi yayi ya mike. Sumbatar ta yayi yana nuna mata godiyarshi. Yana daukar mata alkawarin kin manta wannan karamcin.

*

Leqo da kanshi yayi wajen dakin yace.

"Momma ku shigo. Fu.ad......"

Su momma wucewa sukayi. Ganin su fu.ad sun tsaya yasa shi fitowa daga dakin gabaki daya.

"Ku shigo mana"

"Zamu dawo lukman. Gida zamu tafi yanzun"

Girgiza kai yayi alamar bai yarda ba.

"Nidai ku shigo. Safiyya kema biyema fu.ad zakiyi ko?"

Kallon fu.ad safiyya tayi da idanuwa take rokonshi dasu koma din. Gani yake kaman ba zata iya handling emotions din ba shisa yake cewa su tafi gida.

Kai yadan daga mata. Ta saki hannunshi dake cikin nata. Suka shiga dakin a tare lukman na gabansu.

Tsaye sukai daga dan nesa su duka wannan karin sun rasa me ya kamata suyi.

Hada idanuwa safiyya tayi da zainab. Zainab din tai mata wani murmushi data kasa fahimtarshi. Kasa mayarwa tayi dan yanda take jinta.

Suna kallo lukman ya je wajen zainab tasa hannu ta miko mishi babyn. A hankali ya tako inda su fu.ad suke ya tsaya da babyn a hannunshi.

Juyawa yai ya kalli hajiya. Yaga alfaharin dake cike da idanuwanta. Farin cikin dake kan fuskarta dazai jima tunosu kawai na saukar mishi da nishadi.

Dan daga mishi kai tayi dake nuna me yake jira? Yayi kawai. Juyawa yayi ya sauke idanuwanshi cikin na fu.ad.

Fuskarshi dauke da wani yanayi yace.

"Lukman ni me zan da yara? Idan ina bukatarsu ga naka nan zaka haifa. Ga  haneef ga su pha.iza zan gansu"

Sosai yake kallon idanuwan fu.ad din saida yaga alamar ya tuna exact maganganunshi shekarun da suka wuce. Yaga dana sani da nadama dake cikin idanuwanshi.

Sannan yace.

"Yes rabin maganarka babu karya a ciki fu.ad. kana da mu. Kuma yanzun kana bukatar ya'ya. Saidai daya kawai zamu iya haifa maka......"

Lukman ya karasa maganar yana mika mishi babyn. Kallon safiyya fu.ad yayi sannan ya kalli lukman ya kalli babyn.

Muryarshi na rawa yace.

"Me kake nufi?"

Dan ya kasa fahimta. Duk da kunnuwanshi sunji maganganun lukman. Zuciyarshi taki yarda ta karbe su.

"Kaji ni ai. Baby muka haifo maka ni da zainab...."

Hannu fu.ad yakai kan kirjinshi yana dafe inda zuciyarshi ke wani irin tsalle kamar zata fado.

Momma ya kalla ita kanta mamaki ne karara a fuskarta. Ta kalli hajia idanuwanta cike da tambaya da hawaye.

Tana so taji ko da saninta lukman zaiyi wannan abin. Kai hajiya ta daga mata hadi da fadin.

"Wacece ni in shiga tsakanin yan uwa?"

Hawayen da suka zubo ma momma ta goge tana fadin.

"Na rasa abinda zan fada"

"Ki sanya musu albarka"

Kai momma ta daga ma hajiya tana kallon su fu.ad wanda dakyar ya iya cewa.

"Lukman please. Ka daina mun irin wasan nan"

Kallon baka da hankali ko? Lukman yai mishi kamun ya sake mika mishi babyn.

"Ka karbeta fu.ad....."

Jikinshi ko ina bari yake. Idanuwanshi cike taf da hawaye ya mika hannu ya karbi babyn.

Safiyya ya kalla. Ta matso kusa dashi tana sa hannuwanta jikin nashi suna rike babyn tare. Ta kasa tsaida hawayenta.

Sun kuma kasa daina kallon babyn. Dakyar fu.ad ya dago da kanshi yace ma lukman.

"Wallahi zamu riketa da kyau. Zamu kula muku da ita"

Zainab data dafa gadon ta mike zaune tace.

"Mu asuwa? Zaku kula da yar'ku dai."

Kallon ta sukayi sannan suka kalli lukman. Suna son jin ko gaskiya ne abinda ta fada.

Daga mishi kai lukman yayi.

"Ba riko muka baku ba fu.ad. Aisha fu.ad Arabi. Mu muka haifeta. Amman yar'ka ce fu.ad.

Allah ne shaidarmu akan wannan. Zamu amsa sunan masu haihuwarta ne kawai."

Hawayen da suke idanuwan fu.ad suka zubo. Bai kokarin gogesu ba saboda yanajin yanda wasu ke sake fitowa.

Kuka suke sosai shida safiyya suna rike da yarinyar har lokacin. Shi kanshi lukman kukan su yasa hawayen zubo mishi.

Harsu hajiya ma da zainab din. Hannu lukman yasa ya goge fuskarshi.

"Enough please."

Girgiza kai fu.ad yake. Saboda ya kasa tsaida su. Bai taba tunanin wannan karamcin daga wajen lukman ba.

Bai taba tunaninshi daga wajen haneef bama balle lukman. Allah kenan. Ya karbi nana cikin Hikimar shi kuma ya basu wata kyautar.

Kyautar dako a mafarki basu taba zaton ta ba. Mikama safiyya babyn fu.ad yai duka yasa hannu yana goge hawayen dake bin fuskarshi.

"Lukman........"

"Shhhh inhar zumuncin mu yakai inda na dauke shi zakai shiru ba zaka ce komai ba"

Shiru fu.ad yai yana runtse idanuwanshi. Takawa yai ya karasa wajen zainab. Tsugunnawa tai kan gwiwoyinshi.

Hannuwanshi na rike da gefen gadon. Kasa ce mata komai yayi. Ya kife kanshi jikin gadon kawai hawaye na ci gaba da zubi mishi.

Me zaka ce ma wanda ya dauki farin ciki ya baka? Babu wasu kalamai.

Muryar zainab na rawa tace.

"Nagode da karamcin dakaimun. Nagode daka sakama yarka sunan mahaifiyata.

Allah ya raya muku ita"

Dago kai yayi ya kalli momma yace.

"Momma kinji itace takemun godiya wai. Really? Wai nine nai mata karamci.

Momma da wanne baki zan musu godiya? Wallahi ban cancanci wannan karamcin daga wajensu ba sam"

Hajiya ce tai mishi dakuwa.

"Gidanku fu.ad da irin maganganun nan. Kar in sake ji. Ka tashi ku wuce gida ma.

Mu ma da zainab ta warware gidan zamu tafi"

Mikewa fu.ad yayi. Ya karasa inda lukman yake tsaye. Hugging dinshi yai. Lukman ya ture shi yana dan tari.

"Maza ragargazamun kashi kar inci naman suna da kyau"

Dariya fu.ad yayi yana girgiza kai. Safiyya ya kalla datake takowa ta karaso wajensu.

Lukman ta kalla.

"Allah ya karramaka linkin yanda kai mana. Allah ya baka aljanna"

"Amin safiyya. Allah ya jikan Nana"

Kai ta daga mishi hawaye na zubo mata. Karasawa tayi ta zauna gefen zainab.

Hannunta daya rike da babyn dayan kuma ta saka shi cikin na zainab.

"Mahaifiya tace kadai zatai mun irin abinda kikaimun.

Allah yabarki da mijinki yasa zamanku har a aljanna. Zamu kula da ita na miki alkawari"

Murmushi zainab tai mata.

"Kome zaisa lukman farin ciki. Amin Allah ya jikan Nana ya raya muku baby"

Kai safiyya ta daga tana jin hawayen na sake zubo mata kamun tace

"Ki shayar da ita. Kar a dauki alhakinta. In yaso sai mu karba in....."

Katse ta zainab tayi.

"Banda enough milk. Ko junior madara yasha. Karki damu"

Lumshe idanuwa safiyya tayi tana sauke ajiyar zuciya. Kai kawai ta daga ma zainab ta mike. Fu.ad ta kalla.

Basu da sauran abinda zasu fada. Wannan karin sun manta da su momma dake wajen. Hannunta safiyya tasa cikin nashi suka juya suka fice.

Zainab ta kalle su tana sauke numfashi. Tana jin kewar yarta har ranta. Sai dai tana da yaqinin zasu kula da ita fiye da su ma kila.

Kallon lukman tayi. Kalar yanda ya kalleta ya wanke mata duk wani shakku daga zuciya.

*

Basu bar asibitin ba saida suka nemo  doc din yara ya basu shawarwarin dazai basu tukunna.

Suna mota safiyya rungume da babyn. Lokaci lokaci fu.ad na juyowa ya kalle su. Sun kasa cewa komai har yanzun.

Kamun fu.ad ya kori shirun da fadin.

"Muje mu siya ma Mimi kaya tukunna"

Kallonshi safiyya tayi.

"Mimi?"

Kai ya daga mata hadi da fadin.

"Sunan maman zainab ne. So zamu boye ko daman.

Kuma nana tace inda tana da kanwa zata dinga kiranta mimi"

Murmushi safiyya tayi.

"Nana ga kanwa kin samu. Saidai Allah baiyi zaki ganta ba"

Jin rawar da muryar safiyya take yasa fu.ad fadin.

"Mimi kinji mumynki ko? Big sis dinki ba zata taba ganinki ba. Amman ke zaki ganta. Ina da pictures da labarai da yawa"

Murmushi safiyya ta sake yi. Tana jin su inna kawai take son tai magana dasu ta fada musu sauyin daya shigo rayuwarta.

Ta nuna musu kyautar Allah yawane da ita. Inya jarabceka badan ya manta dakai bane. Saidan Yafi kowa sonka ne.

*

Aikam biyawa sukayi. Siyayya kawai fu.ad yake kaman baisan wahalar neman kudi ba.

"Ya isa haka"

Cewar safiyya. Girgiza mata kai yayi yana dakuna fuska.

"Bafa a baby zata zauna ba. Inta kara girma zamu dawo. Kaga wanna zasu zama waste. Abarsu haka"

Jim yadanyi kamun ya jinjina mata kai cikin yarda da abinda tace din. Zuwa sukayi suka biya kudin kayan aka diba aka zuba musu.

Boot ya cika dam. Kaya har bayan motar. Suka shiga sannan safiyya tace.

"Mimi akwai hakuri. Har yanzun batai kuka ba. Bacci take tayi ma. Da naso muje gidansu inna mu nuna musu ita.

Mu dai je gida in hada mata madara tukunna.

Inmun huta sai muje ko"

Kai ya daga yace mata.

"Ke kika riketa dazun. Yanzun ni zan riketa kiyi driving"

Kafada ta makale alamar bata yarda ba.

"Inji waye? Kai zakai driving"

Shagwabe fuska fu.ad yayi.

"Please......"

Bude motar tayi ta fita tana zagayawa ta bude shi. Fitowa yayi ta bashi Mimi sannan ta shiga wajen daya fito shikuma ya zagaya.

A hankali ya shiga yana rufe kofar hadi da kallon mimi da take ta baccinta kamun safiyya ta tayar da motar su tafi.

*

Fitowa tai da madara a hannunta ta samu fu.ad a tsaye inda tabarshi tun shigowarsu.

Hankalinshi kwance yake zuba ma mimi labari. Dan murmushi tayi. Yanayin da take ji bazai barta ta fada mishi mimi bata jin me yake fada ba.

Karbarta tayi ya shiga bedroom din yayo alwalar sallar la.asar ya fito ya wuce masallaci. Jin gidan take yi shiru.

Tasan da gaske Nana ta rasu. Tai accepting hakan. Amman wani bangare na zuciyarta gani yake kaman Nana zata fito daga dakine tana tambayarta inda ta samo baby.

Lumshe idanuwanta tayi tana maida hawayen da take ji.  Addu.a sosai taima Nana. Mimi nagama shan madarar ta sake komawa bacci.

Taso ta sake mata wankane. Saita hakura tabarta ta huta. Dan gadonta da suka siyo ta dauka  sannan ta wuce bedroom din.

Saida ta saka ta a ciki ta lillibeta sannan ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito tai sallar la.asar.

*

Tana kwance kan gadon abinta hannunta daya kan gadon mimi ta dora shi. Sosai tunanin rayuwa take da abinda ke cikinta.

Taji an hawo gadon an riketa ta baya. Sauke numfashi tayi.

"Banji shigowarka ba"

Sumbatar ta yai a kai ta baya sannan ya amsa da.

"Bana son tunanin nan please"

Shiru tayi. Tunani kam dole ne sai a hankali tukunna. Jin yanda ya riketa yasa ta dora hannunta kan nashi tana shirin zame jikinta.

"Sofi. I miss us. Please....."

Shirun da tayi ya bashi amsar da yake bukata. Cikin mintina ya fara nuna mata kalar kewarta da yayi shekarun nan.

Yake nuna mata yanda soyayyarta take tare dashi duk nisan da sukayi.....!

**

Bai iya fita magrib masallaci ba. A gida yaja musu shida safiyya da wata kalar kaunarta ke masa yawo.  Ga wata nutsuwa.

Tare suka shiga toilet din da abin wankan da suka siyoma mimi. Safiyya tai mamakin ko uhm mimi batayi ba. Tace ma fu.ad

"Kasan Nana kukan wanka take?"

Ware idanuwa yayi sannan ya kwace da dariya.

"Nana da kukan wankan. Baki fadamun ba ai dana tsokane ta"

Murmushi safiyya tayi. Jin yai shiru yasa ta dagowa ta kalle shi. Ruwan tadan diba ta watsa mishi a fuska. Da sauri ya kawo hannunshi ya kare yana fadin.

"Sofi mana....."

Ware mishi idanuwa tadanyi kamun ta maida hankalinta kan mimi da take sakawa a towel.

"Kai kace banda yawan tunanin"

Kallonta yai yace.

"Ina jin kewarta sosai...."

"Nasani nima haka. Allah ya bamu mimi. Duk da samunta bazai hana mana kewar nana ba.

Zai bamu sabon farin ciki."

Kai ya jinjina mata.

"Me zamu ci? Wani abu simple dai"

I
ta batama jin cin komai saidai tasan in taki shima haka zai kwana tun breakfast din da momma ta takura su suka ci da safe.

"Ka zauna da mimi karmu barta ita kadai. Sai in dafa mana indomie"

Karbar mimi din yayi yana kallon yanda tayi kyau cikin fararen kayan sanyin da aka saka mata. Wani irin kaunarta ke shigarshi a hankali.

"Mi daughter"

Ya fadi a hankali kaman yana son sake tabbatarwa tashi din ce. Babu mai kwace mishi wannan kyautar.

*

Indomie din sukaci. Sukai sallar isha.i. Ya zauna da mimi safiyya ta watsa ruwa sannan ta fito shima ya shiga.

Tana kwance kan gadon ya hau ya kwanta gefenta yana nazarin fuskarta.

"Gadon inajin shi very empty babu Nana."

Baice komai ba ya sauka daga kan gadon. Mimi ya dauko daga nata gadon a hankali. Har mamakin ina ya iya daukar jariri yake.

Towel dinta ya mika ma safiyya yana nuna mata ta shimfida. Batai musu ba ta shimfida. Ya kwantar da mimi tsakiyarsu sannan ya kwanta.

Murmushi yadan mata.

"Better?"

Kallon mimi tayi ta lumshe idanuwa tana ma Allah godiya kamun ta bude su kan fu.ad.

"Much better"

Sake gyara kwanciya yayi yana kallon fuskarta yace.

"Ya kikayi all the years da bana nan?"

Girgiza mishi kai tayi.

"Bana son tuna baya. Ina son kallon gaba ne kawai"

Shagwabe fuska yayi.

"Ina son ji ne"

Kai ta daga a hankali ta fara mishi bayani da fadin.

"Ba wani abu much fa. Sati biyu bayan nagama kukan nagama zuba idanuwa baka dawo ba.

Nakoma school. Ina amfani da kudin dake cikin gidan inayin komai da nake bukata kamun su kare.

Cikin Nana bamai wahala bane. Dan bana wani amai ko wani abu. Ina cin abinci sosai sosai dai. Anty Laurat ta fara cemun ina da ciki.

Kamun in noticing Changes din da kaina. Saina fara dibar kudin dake bank. Muna zuwa da ita mu dauko.

Tun ina mamakin yanda suka ki karewa har nazo nasan kaine kake turowa. Really bana son tuna duk wannan.

Kawai i was so happy bayan haihuwar Nana and sad da baka nan. Sad da bansan ko inkana nan zaka so ta ba.

So koma yanai rayuwa ba abin dubawa bace a yanzun. Kasan abu daya koda kai nisa. Ko yanda bana son in fada.

Da kulawarka na rayu. Da kulawarka muka rayu duk shekarun nan ni da Nana. If bakai tunanin turo mun kudade ba........"

Sauke numfashi tayi tana kasa karasawa. Muryarta a sarke tace.

"Please mubar maganar nan. Baya ta zauna a baya. Mu duba gaba kawai"

Hannunta ya kamo ya dumtse yanajin wani abu ya tsaya mishi a wuyanshi.

"Kisani wallahi dazan iya. Da inada iko dana koma baya na canza komai"

Dan murmushi tayi.

"I know. I.... I love you"

Ta fadi. Ware idanuwanshi yai da hakan yai mata yanayi da nana sosai.

"Thank you."

Ta daga mishi kai hadi da hamma. Dariya yai. Itama haka kamun suyi addu.a su kwanta. A karo na farko tun rasuwar nana da suka samu bacci.........!

****

"Ina zamuje baka fadamun ba har yanzun yaya farhan"

Kallonta yadanyi sannan ya maida hankalinshi kan tuqin da yake da murmushi a fuskarshi.

"Home. Your home"

Da rashin fahimta tace.

"Bangane ba"

"Zaki gane nuriyya....."

Girgiza kai kawai tayi ta gyara kwanciya cikin kujerar. Ga mamakinta corner suka shiga.

Bata sake mamaki ba saida taga sun nufi wani katon gida an bude musu. Kallon farhan take har yai parking. Sannan ya juyo ya kalleta.

Fuskarshi da wani farin ciki yace mata.

"Kin shirya ganin family dinki"

Hannu takai tana rufe bakinta cike da mamaki. Idanuwanta na kawo hawaye.

"Da gaske yaya farhan"

Ya daga mata kai.

"Da gaske nuriyya. Family dinki na jiranki"

Ko ina jikinta rawa yake. Ta kasa cewa komai saboda gani take data sake bude baki zuciyarta fitowa zatao saboda dokawar da take.

Tana kallo har farhan ya fita ya zagayo ya bude mata. Hannunta ya kamo ya fito da ita. Dakyar kafafuwanta ke daukarta.

Dam ta rike hannun farhan dake cikin nata. Ta kasa yarda. Gani take da tai wani wrong motsi wannan mafarkin bacewa zaiyi.

Kamata yai suka hau steps ukku dazai kaika kofar gidan sannan suka tura kofar. Farhan ya shiga da sallama.

Muryoyi taji fiye da biyu sun amsa farhan. Idanuwanta cike suke taf da hawaye ba sosai take ganinsu ba. Blinking tayi tana fito da hawayen da suka tarar mata.

Sannan ta ware idanuwanta tsakiyar falon. Kan wata mata idanuwanta suka fara sauka. Ta kuma kasa janye su saboda yanda take jin zuciyarta na wani irin abu.

Wata irin kaunar matar na shigarta data kasa fahimta. Kaman daman can an halicci zuciyarta ne kawai dan ta kaunace ta.

A hankali take takawa zuwa inda matar take tsaye idanuwanta itama kafe kan nuriyya da batasan tana karasawa ba.

Tsakiyar falon suka hade da matar. Hannunta takai da yake rawa tana taba fuskar nuriyya.

"Nuriyya....."

Ta fadi. Hannunta dake fuskarta nuriyya ta kama ta dumtse tana jin wani yanayi da bata tabajin shi ba a rayuwarta.

Batasan lokacin data rungume matar ba. Kuka suke a tare. Ko ba a fada mata ba zuciyarta tasan wannan mahaifiyarta ce. Sosai suke kuka kamun wani babban mutum dake tsaye yace.

"Hajiya aikin saketa muma muganta ko"

Sakinta hajiya karima tayi. Tana goge fuska kawai bata taba sa ran zata sake ganin yartata ba. Duk da kullum da tunanin halin da take ciki take kwana take wuni.

Takowa yai. Hannuwanshi yasa ya tallabi fuskar nuriyya. Yana kallon yar tashi da suka cire rai da sake ganinta sai yau da farhan ya same shi yake mishi tambayoyi.

Hawaye yaji sun zubo mishi kamun yai hugging nurriya suna ma Allah godiya. Sun dauki mintina a hakan kamun ya dago nuriyya yana goge mata fuska.

Hannunta ya kama ya shiga janta wajen yayyanta maza har biyar. Sai kannenta su biyu maza. Ita kadaice ya mace da Allah ya basu.

Yinin ranar cikin yan uwanta tayi shi. Dan farhan tafiyarshi yayi. Saidai bata yarda ta kwana ba. Duk yanda take so da yanda yan uwanta suka so.

Ba zata iya barin farhan shi kadai ba bayan wannan halaccin dayai mata. Tai alkawarin shima saita sa ya nemi nashi yan uwan dan yaji abinda take ji itama.

Wannan farin cikin wajen shi da ban ne. Girman kaunar yan uwantaka bata taba haduwa da wata. Allah ne ya hada jini daya waje guda.

Shi kadai Yasan hikimar haka. Zumunci abune mai girman gaske.......!

*#TeamAS*

AKAN SO 47

*💘💖AKAN SO💖💘*

~Written by~ :Luβπα Sufyαπ

www.Loobnerh.blogspot.com

Wattpad: LubnaSufyan

            47

*Tabbas babu wani abu da yake da tabbas a cikin duniya. Babu komai cikinta sai tarin dauda da rashin kwanciyar hankali*

*Ba zaka gane hakan ba sai lokacin da kaddararka ta jarabta ya juyo kanka*

*Gabaki dayan littafin nan yana tabani fiye da yanda yake taba ku. Saboda kaso 60% cikin 100% ba fiction bane gaskiya ce*

*Yana tabani ta yanda babu wanda zai fahimta. Ta wani fannin yana fifitamun ciwuka da raunikan dana samu a tsahon rayuwata*

*Ciwukan da basu gama ciwo ba. Ciwukan da nasan in har ina duniya ban gama samun kalarsu ko fiye dasu ba*

*Godiya ta tabbata ga Allah a kowanne hali*

*zainab Askira. Rukayya Abdulkadir. Mardiyya isyaku and Nasiba. Amina mashasha. Yasmeen Tafeesu. Ummie khaleel. Fatima Aliyu(childhood friend). Sha.afatu saleh. Da wanda ma ban lissafo ba kusan AnaTare. Like AnaTare sosai sosai*

Doc jana na shigowa dakin na.u.ororin dake manne jikin Nana ta shiga dubawa. Kallonta fu.ad yake cike da tashin hankali.

Da gudu yaga ta fita basu fi mintina biyar ba suka dawo su hudu. Kama hannun safiyya yayi tana tirjewa tana ce mishi.

"Ka sakeni. Kabarni babu inda zan tafi....."

Gam ya riketa jikinshi tana wani irin kuka. Tashi zuciyar ta bushe. Wani iri yake jinta yanda babu kalaman da zai bayyana ta dashi.

Bakin kofar dakin da Nana take ciki suka tsaya har lokacin safiyya dake kuka tana jikinshi. Habarshi ya dora saman kanta ya lumshe idanuwanshi yana fadin.

"Allah kabamu juriya. Allah duk yanda kai damu dai dai ne...."

Baisan iya lokacin da suka dauka a haka ba sai da yaji bude kofar. Da sauri safiyya ta zame daga jikinshi tana kallon doc jana.

Ta gabansu sauran likitocin suka fito suka wuce. Safiyya bata jira komai ba ta wuce cikin dakin. Shikam fu.ad tsayawa yayi ya zuba mata idanuwa.

Nata idanuwan taji sun cika taf da hawaye. Daga kan Nana tai alkawarin ba zata sake karbar wani cancer patient ba. Zuciyarta ba zata iya dauka ba.

Muryarshi a dakushe yace.

"How many days?"

Saida takai mintina biyu tana kokarin controlling emotions dinta sannan tace mishi.

"A few hours max......"

Tana rufe bakinta ta juya da gudu tana barin wajen saboda bata son fu.ad yaga hawayen dake zubar mata. Bata son yaga yanda take ji ita da bata hada jini da nana ba kenan.

Bangon wajen yasa hannu ya laluba jikinshi na bari. Kalmomi hudu ta fada amman shi a wajenshi gabaki daya farin cikin su ta tarwatsa.

Cikin kunnuwanshi yake jin amsa kuwwar da kalmominta suke mishi. Yasan yana cikin shock saidai baisan yanda zai ya fita ba.

Wata dariya ce yaji ta kubce masa da baisan ta inda ta fito ba. Wayarshi ya dauko ya kira haneef ya daga da fadin.

"Fu.ad ya Nana din?"

Cikin muryar da bai gane ko tashi bace yace.

"Kuzo ku mata bankwana haneef. Awanni kadan take dashi"

Yanajin yanda haneef yaja numfashi ta cikin wayar ya sauketa daga kunnenshi bai damu daya kashe ba ya sata a aljihunshi.

Handle din dakin ya kama zuciyarshi na wani irin yawo da zai iya rantsawa yanajin bugun da take har cikin kunnuwanshi.

Turawa yai a hankali. Safiyya na rike da hannun Nana tana tsugunne kasan gadon tana wani irin kuka da yaji ya tsaya mishi a wuya.

Gefen gadon ya zauna ta dayan bangaren yana kama hannun nana daya ya rike shima. Jiyai kaman tayi motsi hakan yasa shi fadin.

"Princess......"

"Daadyyy......"

Ta fada. Da sauri safiyya ta dago ta na zama kan kujera. Hannunta daya tasa tana goge hawayenta.

"Nana kina jina"

Idanuwanta a rufe take.

"Mumy ya aljanna take?"

Ta tambaya muryarta na rawa tana wata irin kokawa da numfashinta. Kuka ya hana safiyya magana. Fu.ad ya hadiye wani miyau yace.

"Princess babu wanda yasan exact yanda take. Waje ne mai cike da ni.imomi fiye da zaton dan adam.

Wajene da yake da farin ciki. Kwanciyar hankali da natsuwa ta har abada"

Murmushin da Nana tayi har cikin ranshi yaji shi.

"Babu rashin lafiya?"

Kai fu.ad ya girgiza duk da bata ganin shi.

"Babu ko kishin ruwa Nana. Babu komai banda farin ciki.........!"

Yana kallon yanda kirjinta ke dagawa dakyar saboda yanda take kokawa da shigar iska abin na mishi wani iri.

"Duk ciwon nan zai tafi?"

Wannan karin kasa amsata yayi. Saboda wani abu ya rike kalamanshi. Bakinshi ya bushe tas.

Muryar safiyya na rawa wasu sabbin hawayen na zubo mata tace.

"Zai tafi Nana. Babu kunci ko kadan a cikinta. Wajene da mai laifi da marassa laifi ke da burin shiga"

Murmushin Nana ya sake fadada. Hannayensu dake rike a cikin nata da dan sauran karfin da take ji ta dumtse.

"This is not a good bye. Wannan na nufin sai kun taho. Yana nufin ina jiranku a aljanna......"

Lumshe idanuwanshi fu.ad yayi. Safiyya ta kife kanta jikin gadon in tana zaton taji mutuwar usman abinda take jina yanxun ya linka wancen fiye da zatonta.

Wani irin daci ne har cikin naman jikinta. Wani ciwo ne marar misaltuwa.

"Ya Allah......"

Nana ta fadi kamun fu.ad yaji ta saki hannunshi. Bude idanuwanshi yayi lokaci daya da dagowar safiyya. Jikinta na bari da wata irin fargaba marar misaltuwa take kallon nana.

Kaman tana bacci da murmushi a fuskarta.

"Nana...."

Ta kira a hankali muryarta dauke da fargabar da take ji. Idanuwanta cike taf da hawaye ta dago ta kalli fu.ad da tashi zuciyar ke son fitowa daga kirjinshi.

Sam basu ji turo kofar haneef da lukman ba ballantana sallamarsu. Idanuwansu na kafe da juna. Kamun safiyya ta sake maida hankalinta kan Nana.

Wani irin abu fu.ad ya hadiye daya tsaya mishi a wuyanshi. Haneef na kallon nana yakai hannunshi ya dafe kanshi.

Lukman ya kalla ya girgiza mishi kai yana son gaya mishi ba abinda suke zato bane ba. Bashi bane sam.

Karasawa lukman yai ya dafa fu.ad. Ya juyo ya kalle shi ya sake maida hankalinshi kan Nana daga shi har safiyya tsoron tabata suke ji.

"Nanaaaa"

Safiyya ta sake kira muryarta na karyewa. Lukman yakai hannu ya tabata kafarta. Dumtse kafar yai cikin hannunshi.

Yaji tayi sanyi. Da sauri ya saki kafar nana yana goge hannunshi sosai jikin kayan jikinshi yana son cire yanayin dayake ji manne jiki har lokacin.

"Barin kira doc"

Haneef ya fadi a tsorace yana fita daga dakin. Ko mintina biyar baiyi ba ya dawo da wani doc.

Aune aunen shi ya shiga yi. Kamun yadan runtsa idanuwa ya dafa kafadar lukman dake tsaye sannan ya girgiza ma haneef kai.

Yana ficewa daga dakin. Mikewa tsaye safiyya take tana ja da baya tana girgiza kanta.

"Dan Allah ku cemun lafiyarta kalau. Dan Allah kucemun wani abu bai sami Nana ta ba.......!

Kar kucemun tabarni. Kar kucemun wannan shine bankwana.......!

Wallahi ban shirya ba. Ban shirya ba....."

Hannu fu.ad yakai a tsorace ya dora kan kirjin Nana dai dai zuciyarta. Wani irin shiru yaji. Ya dago idanuwanshi ya kalli lukman.

Hawaye yaga sun zubo daga idanuwan lukman din. Cike da wani yanayi yace ma lukman.

"Ta rasu ko?"

Juya baya lukman yayi. Haneef ne ya karaso yana dafa fu.ad din. Ture hannunshi yayi still dayan nakan kirjin Nana.

"Em okay. Kawai ku fadamun. Ina so wani ya tabbatar mun ne. Ta rasu?"

Dakyar haneef yace.

"Ta rasu fu.ad"

Hannunshi ya dauke daga kirjinta ya mike daga kujerar dayake zaune ya koma gefen gadon ya zauna.

Hannunta dayake karara ya kamo ya sumbata. Sannan ya tsugunna ya sumbaci goshinta yanajin wani yanayi da bai taba ji a jikinta ba.

Batare daya dago ba yace.

"Allah yasa mutuwa hutu ce a gareki Nana. Allah yai miki Rahma. Allah ya sadaki da fiye da abinda kike zaton Aljannarki ta kunsa"

Yana karasawa ya mike tsaya. Wajen safiyya dake girgiza mishi kai ya nufa. Hannuwanta ya kama yana kallonta.

"Safiyya zo ki mata addu.a"

Wasu hawaye masu ciwo da dumi suka zubo mata.

"Ku duba sosai. Dan Allah ka duba. Bata rasu ba"

Kamata yai ya rungume tsam a jikinshi yana rocking dinsu. Yasan shirun nan da yakeji cikin kanshi da zuciyarshi ba na lafiya bane.

Yasan dole ne koma ina ya adana ciwon daya kamata ace yana ji zai dawo mishi. Zai dawo mishi batare da shiri ba.

Wani yawu ya hadiya. A hankali yake ce ma safiyya.

"Dukkan mai rai mamaci ne sofi. Bakiji me Nana tace ba? Wannan ba bankwana bane ba. Kizo ki mata addu.a"

Kai take daga mishi tana jin zuciyarta na wani irin tsaitsayawa da ciwon da take ji.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un....."

Fu.ad ya fadi cikin kunnenta. Ai kaman ya tuna mata abinda ya kamata tayi ta shiga jero wa jikinta na wani irin bari.

Wani kwarin gwiwa taji ta samu wanda batama san daga inda ya fito ba. Tare da fu.ad suka taka wajen da Nana take kwance.

Kallonshi tai ya daga mata kai alamar zata iya.

"Ki mata addu.a tana jinki sofi. Taji yanda kike kaunarta"

Muryarta na rawa tace.

"Allah ya sadaki da Rahmarshi Nana. Allah ya baki hutun da kike ta nema. Zamuyi kewarki.

Allah ya haskaka kabarinki kamun ki karasa mishi....."

Yanda ta karasa maganar yasa fu.ad kamota yana janyeta daga wajen nana.

"Bangama ba fu.ad banga mata bankwana ba"

Kanta yakama ya kwantar a kirjinshi yana janta a hankali yana fadin.

"Zaki kara wani in munje gida"

Da kanshi ya fita da ita ya bude mota ya sakata a baya ya kullo sannan da gudu ya dawo.

Lukman na jingine da bango idanuwanshi kafe kan Nana da take kwance kan gado. Fuskarshi ta wani irin kumbura.

Fu.ad ya sauke numfashi.

"Lukman taho ku tafi gida da safiyya"

Girgiza mishi kai lukman yayi yana kasa magana. Kama hannunshi fu.ad yayi kaman karamin yaro har lokacin idanuwanshi na kafe kan Nana.

Yana sake ganin yanda duniya ba komai bace ba. Yar yarinya kenan da bata da wasu tarin zunubai. Ballantana kai babba da gulmar wasu ma kadai ta isheka tashin hankali.

Bude mishi gaban motar fu.ad yayi ya shiga ya mika mishi mukullin motar.

"Can you drive?"

Ya tambaya. Kai lukman ya daga mishi. Ya sauke numfashi yana kallon safiyya data hade kanta da gwiwa a bayan motar.

"ka kaita wajen momma gamu nan zuwa"

Sake komawa fu.ad yayi yana mamakin kanshi. Ya kamata ace yanajin wani abu amman kawai dai ya rasa ko me yake ji.

Inda yabar haneef nan ya same shi. Baibi takanshi ba ya shiga tattara kayayyakinsu yana zubawa cikin jakar da suka fito.

Saida ga gama tas sannan ya mikama haneef daya karba yana kallon fu.ad din da mamaki.

"Fu.ad?"

Ya kira cike da shakku yana son tabbatar da ko yana lafiya. Saida ya dauki takalman nana dake ajiye a kasa ya hada su waje daya sannan ya amsa da.

"Na.am.......sa takalman Nana a ciki kar abarsu"

Jinjina kai haneef yayi ya karbi takalman yasan akwai matsala tare da fu.ad din. Yana kuma tsoron sanda mutuwar zata gama zauna mishi.

Karasawa kan gadon da Nana take fu.ad yayi ya dagota a hankali kaman tana bacci ya sabeta a kafadarshi. Ya kalli haneef hadi da fadin.

"Muje ko"

Ba musu haneef ya kama hanya jikinshi a sanyaye. Suna fita daga dakin suna cin karo da doc jana. Kallo daya tai musu tayi baya.

Fu.ad yace mata.

"Doc......!"

Dawowa baya tayi. Kallonta yai.

"Ki mata bankwana. Kina da muhimmanci a wajenta"

Sai da ta lumshe idanuwa sannan tace.

"Allah ya jikanta ya baku hakurin rashin ta"

"Amin mungode. Sai wata rana"

Ya fadi suna wucewa. Mamakin shi haneef yake. Akwai babbar matsala.

*

Kofar gida haneef yai parking saboda mutane har sun fara taruwa kofar gidan. Ya zagayo ya bude ma fu.ad bayan motar.

Ya fito sannan ya tallabo Nana ya sake sabeta a kafadarshi. Haneef kadai ya tsaya gaisawa da mutane suna mishi gaisuwa. Cikin gida fu.ad ya wuce.

Saboda baya son yanda kowa ke kallonshi din nan. Lokaci daya maganar nana ta fado mishi. Haka suke kallonta cike da wannan yanayin a idanuwansu kenan?

Sake tallabeta yai jikinta yana rasa menene yai mishi daban cikin hakan. Yana sallama yasa kafarshi cikin gidan anty fatima na sakin wani irin kuka.

Momma ma fuskarta harta kumbura. Tasowa tayi ta karbi nana daga hannun fu.ad din tana nazarin fuskarshi.

"Fu.ad...."

"Em okay momma. Kuyi mata wanka bara mu siyo abinda ya kamata.

"Hassan ya tafi"

Momma ta fadi tana goge fuskarta da dayan hannunta.  Kai fu.ad ya daga mata.

"Abbah fa?"

"Yana waje. Bai jima da fita ba"

Kai ya sake daga mata ya juya. Yana shirin fita inna na shigowa tana goge fuska. Kaucewa yai gefe dan yaga yanda tana ganinshi wasu hawaye suka sake zubo mata.

Da sauri yabar dakin.

*

Su haneef ya samu suna alwala. Kofar gidan ya cika makil da mutane. Shima alwala yayi yace ma haneef.

"Ina lukman?"

A sanyaye haneef yace.

"Yaje ya taho da zainab"

Kai ya daga mishi kawai yana mikewa. Ansar ya hango ya nufo su. Tsayawa yai ya karaso ya mika ma haneef hannu sannan fu.ad din.

Muryarshi na rawa yace.

"Yanzun naje asibiti ake fadamun. Na kira safiyya ta sai wata ta daga taban address din nan. Ya Allah. Oh Nana......"

Kasa karasawa ansar yayi sai fuskarshi daya sa cikin hannayenshi yana wani irin jan iska. Mutuwar nana yake ji har cikin zuciyarshi.

Dafa shi yaji anyi ya bude fuskar ya sauke idanuwanshi kan fu.ad.

"Sai hakuri. Kai mata addu.a shi tafi bukata"

Kai kawai ansar ya daga ma fu.ad din. Sai kuma ya sake kallonshi sosai wannan karin. Girgiza kai yake kamun ya maida dubanshi kan haneef.

Abbah fu.ad ya hango yabarsu haneef nan tsaye. Ansar yace ma haneef.

"Is he okay?"

Dan daga kafada haneef yayi hadi da girgiza kai.

"Allah dai ya rufa asiri"

"Amin. Oh Allah"

Cewar Ansar yana samun waje ya tsugunna dan rasuwar na tabashi ba kadan.

*30 minutes later*

Su hudu suka shigo cikin gidan. Dashi da lukman,haneef sai babban yaya dan su dauko gawar nana.

Ai nan tashin hankalin yake. Suna nufo inda take kwance an hadata. Safiyya ta taso da gudu ta rike nana jikinta.

"Dan Allah ku tsaya. Ku tsaya ban gama ganinta ba"

Momma dake wani irin kuka ta taso ta kama safiyya.

"Kiyi hakuri safiyya. Kiyi hakuri"

"Momma dan Allah kice su kara tsayawa. Kar su tafi da ita....."

Riketa momma tayi a jikinta. Kamun anty fatima ta taso ta tayata. Fu.ad da kanshi yasa hannu ga dago Nana yana jin shiru cikin kanshi da ko ina na jikinshi.

Sosai gidan ya sake rikicewa banda.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un....."

Babu abinda suke fadi. Haneef ya runtsa idanuwanshi yana bude su. Yana jin dadin yanda basu saki Allah ba.

Yana kuma da tabbacin zai saukaka musu dacin rashin Nana. Hakika sabo ake yiwa kuka. Safiyya ba kallon sun nufi kofa da nana ta rarrafa dan ta kasa tashi.

Ta karasa wajen inna tana boye kanta cikin cinyar inna hadi da sakin wani kuka da takejin fitowarshi daga wani waje na zuciyarta da bata san yana nan bama.

Shikenan ita da Nana har abada.....!

Inna ta riketa itama kukan take saboda yanda mutuwar nana ta sake fama mata ciwon mutuwar usman. Tasan me yarta take ji. Tasan halin da take ciki.

Abu daya inna take da yaqini akai. Allah daya dora musu yasan dasu. Inhar suka rike shi zai basu mafita.......!

****

Dakyar ta iya kai kanta gida. Dan lokacin tashi baiba ma tace gida zataje bata da lafiya.

Ko sallama batai ba ta zauna falon ta na ajiye komai anan. Dafe kanta tai cikin hannayenta.

Tun mutuwar mahaifinta rabon da ai mata wata mutuwa data tabata. Sai yau rasuwar nana ta girgizata sosai.

Hawaye ke zubo mata. Wani nabin wani. Bata ji fitowar ayna ba sai maganarta taji.

"Anty? Yaushe kika dawo? Sannu"

Dagowa tayi wasu hawaye na sake zubo mata data sa hannu ta goge su. Ware idanuwa ayna tayi ta karasa inda jana take ta zauna.

Kusan sati daya kenan da zuwanta gidan nan. Banda gaisuwa babu abinda yake hada su da jana din. Hakama yaranta zasu gaishe da ayna din kullum.

Ko bata fito ba sanda zasuje school zasuyi sallama bangarenta su gaishe da ita sannan su wuce. Kuma hakan ya mata dadi yanda jana tasa suke bata girma.

"Anty lafiya dai ko? Ko wani ya rasu?"

Kai jana ta daga mata. Ba zata ce ta tsani ayna ba. More like tana kishi da ita ko tace tana kishin jabir da soyayyarshi.

Cikin sanyin murya tace.

"Wata yar yarinyace. Nana sunanta patient dina ce kusan shekaru uku. Mun saba sosai yau ta rasu"

Dafa ta ayna tayi tana jin duk babu dadi. Ita mutuwar yara na mata wani iri. Jikinta sanyi yake.

"Allah sarki. Allah ya jikanta ya ba iyayenta hakurin rashi"

"Amin ayna nagode"

Kayan da jana ta cillar tsakar dakin ayna ta tattara mata waje daya hadi ta kauda mata gefe tana wucewa.

Dawowa tayi da ruwa da cup. Ta bude ta zuba ta mikama janar. Ta karba tasha. Sosai taji dadin karamcin da ayna tai mata.

"Nagode ayna"

"Bakomai anty. Kiyi hakuri ki mata addu.a sai tasan kin damu da ita sosai.

Ko kije kidan watsa ruwa ko zaki samu natsuwa"

Mikewa jana tayi ta kalli ayna tace.

"Nagode fa. Bara in shiga daga ciki"

Kai ayna ta daga mata hadi da murmushi. Jakarta ta dauka ta wuce ciki. Ayna ta bita da kallo.

Tana fatan wannan zaman lafiyar da suke ya da jana da ganin girman juna ya dore. Yanda bata shiga harkarta bata damu da harkarta ba kawai yana burgeta.

Bata son tashin hankali sam. Ta kuma kula jana bata da matsala. Sai yanzun taga dalilin dayasa kullum sai jabir ya yabi halayyarta.

Tai ma kanta alkawari zata sa ido ta karanci jana tsaf ko itama zata dinga samun koda rabin yabon da jabir yake mata ne.

****

Tun daga hanyar dawowa daga makabarta lukman ke kallon yanda fu.ad ke ta duba hannayenshi kaman yana son ya tabbatar da su na nan ne ko yana mamakin ganinsu a jikinshi.

Haneef ya tabo ya nuna mishi fu.ad din daketa jujjuya hannunshi sauri sukayi suka karasa wajenshi suka jera tare.

Lukman ya kira sunanshi a hankali. Baiko juyo ba balle suyi zaton yaji. Kawai tafiya yake yana kallon hannuwa shi daya dago su.

Haneef ya kai nashi hannun ya kama daya na fu.ad. Sai lokacin ya dago ya kalli haneef idanuwanshi cike da wani irin ciwo da yake ji a kirjinshi.

"She is gone haneef. Da hannuwana na kamata na sata a kabarinta. Da hannuwana na dibi kasa na taya aka zuba mata.

Haneef wannan shine soyayyar ko? Da kaina na dinga duba ko an manta ba a rufe wani waje da kyau ba. Iya kaunar dazan nuna mata kenan ko?"

Lumshe idanuwa haneef yayi.

"Ya Allah...."

"Itama haka tace kamun Allah ya dauki abinshi......."

Fu.ad ya fadi yana juyawa ya kalli lukman.

"Daman aronta aka bamu ko lukman? Kaga Allah ya dauki abinshi tunda yafi mu sonta"

Hannunshi dayan lukman ya rike yana matsewa dam. Dayai magana hawayen dayake ji zubo mishi zasuyi. Fu.ad na bukatar dukkan strength din dazai samu daga gare su.

Haneef addu.a yake su karasa gida lafiya kar fu.ad ya samu break down a hanya. Hankalinshi bai kwanta ba sai da yagansu kofar gidansu.

Sai da yaga sun shiga harabar gidan tukunna. Fu.ad dake tsaye idanuwanshi kafe a kasa ya kalla ya sauke numfashi. Saida ya dafa kafadarshi sannan yace.

"Fu.ad kayi hakuri. Dukkanmu babu mai tabbacin bazai bi Nana yanzun nan ba. Ita mutuwa ba sallama take ba.

Ba kuma jira take ka shirya ba. Idan bata zo kanka ba kasa a ranka a kullum kaine ko wani makusancinka ko wani wanda baka sani ba.

Bazan ce nasan ciwon da kake ji ba. Amman kayi hakuri dan Allah"

Girgiza kai fu.ad yake.

"Haneef ta rasu. Shikenan ko?"

Har ranshi ciwo yake ji marar misaltuwa. Ganin fu.ad din cikin yanayin da yake yanzun. Amman yasan gara yanzun da dazun.

Dazun sam ba cikin hankalinshi yake komai ba.

"Ta rasu fu.ad da gaske ta rasu. Allah ya baku juriya"

Hannunshi yasa ya ture na haneef. Yanajin kiran shi da suke shi da lukman bai ko juyo ba balle ya kalle su.

Lukman ne zai bishi haneef ya rike mishi hannu.

"Kabarshi yaji ta lokaci daya ya huta"

Kai lukman ya daga ma haneef yana karasawa cikin rumfunan da aka kafa a harabar gidan ya zauna ya hade kanshi da gwiwa.

*

Cikin gidan ya shiga bai damu da yawan matan dake ciki ba. Asalima baya ganinsu abu dayane ke yawo cikin idanuwanshi.

Yanda suka binne Nana. Hotone daya san ya zauna zuciyarshi na har abada. Hanyar dakinshi ya nufa. Kafarshi ta taka benen farko yaji an rike hannunshi.

Juyowa yai ya sauke idanuwanshi kan fuskar momma.

"She is gone momma. Ta rasu"

Ya fadi yana wani irin fitar da numfashi. Momma ba zata iya ganin shi hakan ba. Sakin hannunshi tayi ta juya.

Ba mutuwar nana take tsoro ba daman. Wannan tana kan kowa. Abinda mutuwarta zata haifar shi take gudu.

Safiyya ta kalla da ke zaune can gefe. Suna hada ido momma ta juya ta kalli fu.ad sannan ta sake kallon safiyya tana son nuna mata suna bukatar juna.

Shikam fu.ad da gudu ya karasa hawa benen. Kawai so yake ya karasa dakinshi. Jikinshi na rawa ya murza handle din yako ci sa.a babu key ajiki dakin ya bude.

Kafafuwanshi suka kasa daukarshi a tsakiyar dakin. Durkushewa yayi yana dafe kanshi cikin hannayenshi. Jikinshi ko ina bari yake yi.

Da sauri sauri yake fadin.

"Allah na karbi jarabawarka da hannu bibbiyu. Allah ka kawomun dauki. Allah ka kawomun dauki......"

Jiyai an dafashi. Hakan yasa ya dago da kanshi daga cikin hannayenshi sannan ya juyo safiyya ce fuskarta a kumbure.

Wasu hawaye suka zubo mata. Kama hannayenta yai yana gogasu kan fuskarshi.

"Sofi ta rasu. Nana tabarmu har abada"

Kai take daga mishi tana wani irin kuka. Ta kwantar da kanta a cinyarshi. Nashi kan ya dora a bayanta yana jin hawayen shi na zubowa.

Kuka suke sosai. Kukan rashin yarsu. Kukan tausayin kansu domin ita da tata tai kyau ba ita bace abin tausayi. Su da tabari cikin duniyar da babu tabbas sune abin tausayi..........!

*#TeamAS*
*#AnaTare*